Showing 63001 words to 66000 words out of 72104 words

Chapter 22 - Jiddatul Khair Book 2 Hausa Novel Complete

naka tunanin ba dai auren yarinyar dake kanka bane??" Abuturrab na kallonsa da kyau yace "Babu wani aurenta a kaina yanxu, ni d'an iska ne da xan bar aurenta a kaina" Da mamaki Ahmad ke kallonsa, can yace "Ban gane ba" Abuturrab yace "U heard and assimilate me right, babu wani aurenta a kaina" Ahmad ya mike yana kallonsa da mamaki yace "Kana nufin ka saketa Aliyu?" Abuturrab yace "Toh me xan jira, ko don dariya da jest making irin naka da mutane ire iren ka ai dole inyi hakan in samar ma kaina kwanciyar hankali" Ahmad ya fito ya xauna gefen Abuturrab on a serious note yace "Stop it plss captain, da gaske ka saketa?" Abuturrab yace "To wai jiran me xan yi, idan ba ina da intention din auren nata bane dama, i have nothing to do with that girl as a wife, gwara kawai in xama guardian dinta, and that's what i am doing right now..." Ahmad ya dafe kansa yace "Ya salam... amma da baka yi haka ba Captain, why will u do that pls???" Abuturrab yace "You are not to tell me what to do and what not to do, so ka ke in cuci kaina in kwari kaina, ina aka ta6a irin wannan taimakon, i just have to saboda kwanciyar hankalina" Kallonsa kawai Ahmad ke yi gaba daya expression dinsa ya nuna ko kadan bai ji dadin sakin jiddah da yace yayi ba, Bayan few seconds yace "Kuma ta sani, i mean ta san ka saketa?" Abuturrab yace "Of course a gabanta nayi na mika mata sannan na amsa na ajiye" Ahmad ya girgixa kai yace "Wllh banji dadin hakan ba Abuturrab" Wani kallo Abuturrab yayi masa sannan ya ja tsaki ya mike ya nufi kofa, Ahmad ya bisa da kallo yace "Amma kuma xamanku a gida daya baxai ta6a yiwuwa ba, ko don hakan ma ni da kaina xan sanar ma su Umma cewar babu aure tsakaninka da Jiddah, I can't pretend over this in cuceta, idan baka san addini ba ni na sani" Dawowa Abuturrab yyi yana kallonsa da kyau, calmly yace "And this will bring the end of our friendship Ahmad, i told you my secret because i trust u, and I'm sure u won't betray my trust, addini kuma da kake cewa ina ga sai dai mu goga a kan saninsa da ni da ke, bbu abinda xaka nuna min... Baka isa kuma ka koya min yanda xanyi da rayuwata ba" Daga haka ya nufi kofa ya fice ya kulle masa kofar. Daren ranan Abuturrab na xaune hotel room dinsa dake kano after isha yana shan shayi a hankali, tunawa yyi daxu da yamma ya kira wayar wajen Jidda bata daga ba, ya sake kira da magrib ma no answer, ya kalli wayarsa dake gefensa ya dauka ya sake dialing number, har ya katse no answer, haka nan kawai yaji his mind has lost rest, kallon wayar ya dinga yi, can ya sake kira nan ma har ya katse no answer, kallon agogon jikin wayar yyi yaga takwas ya wuce, sake dialing yyi nan ma har ya katse no answer, ajiye cup din hannunsa yyi, ya shiga kiran wani pilot hoping to reach him don yasan he might be up in the sky now, jin captain Musa ya daga, ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya yace "Captain baku tashi har yanxu ba?" Captain din yace "About to... in few minutes time, ya gajiya?" Abuturrab yace "I think i will have to follow you to kaduna now" Da mamaki pilot din yace "Baxa kayi piloting jirgi gobe da safe ba, and hope all is well?" Abuturrab yace "Sure alhmdlh, jirgin gobe na sha daya ne, i don't have early morning duty" Musa yace "Toh shkkn, ka taho yanxun nan kasan basu fiye son jira ba, in some minute time xamu yi take off" Abuturrab yace "In sha Allah" Cikin few minutes ya shirya cikin kananun kaya Hoping not to miss the private flight going to kaduna, cikin ikon Allah ya isa, kuma suka daga sama, within some minutes suka sauka a garin kaduna, a motar Musa dake airport din kaduna suka shigo cikin gari, Musa ya kawo Abuturrab har layinsa ya sauka yana masa godiya, Musa yace "Sai mun hadu Wednesday in sha Allah" Abuturrab yace "Sure in sha Allah, thank you" daga haka suka yi sallama ya karasa cikin layin da kafa, makullin gidan ya fiddo a aljihunsa ya bude sannan ya shiga, har ya isa main entrance nan ma ya bude sannan ya shiga parlor, wutan parlon a kunne yake parlon sai kamshin turaren wuta yake, ko ina na nan ynda ya barsa jiya, kuma babu alamar ana xama cikin parlon ma, karasawa yyi sama yana kallon kofar dakinta ya murda a hankali ya shiga, babu kowa cikin dakin ya bude ido sosai sai dai lkci daya yayi calming kansa jin kamshin sabulu a dakin, coz he is a very sharp percipient, bin dakin ya dinga yi da kallo yana duba inda xai ga wayar amma bai ga alamarsa ba, can kusa da window ya nufa ya tsaya hade da rungume hannunsa ya daure fuska, bayan few seconds ta bude kofar bandakin, ta fito daure da towel, bata ko kalli direction din da yake ba ta nufi gaban mirror, sai a sannan ta ga mutum ta madubi wani ihu ta fasa da karfi ta nufi bandakin a guje ruwan kafarta ya sa tsantsin tiles ya kwasheta ta fadi nan bakin kofar bandakin, da sauri Abuturrab ya nufeta ya durkusa kusa da ita ya dagota yace "Ke nine fahh" wani kuka ta fashe da bayan ta kare masa kallo ta tabbatar shi din ne, tana rike da towel din jikinta gam tace "Wayyo kafata, wllh kila nayi targade, wayyo Baabarmu" Komawa baya yyi yana kallon kafar, ya mike yace "Tashi tsaye" Tana girgixa kai hawaye na sauka idonta tace "Ni baxan iya ba wllh" Ya kamata ya dagata, lkci daya ya hade rai yace "Wani kafar ne kika yi targade" Ta nuna masa right leg dinta, gefen gado ya xaunar da ita ya duka yana kallon kafar, ita dai hawaye kawai take tana hade laps dinta tana kallonsa, wani kallo ya mata ta sunkuyar da kai da sauri, mikewa yayi ya nufi gaban madubi don yasan ya siya mata man xafi ranan da suka yi shopping incase she will need it, a hankali tace "Don Allah ka yi hakuri ka miko min hijabi na" Ya dau man ya juyo ya dawo kamar bai ji ta ba, ta marairaice tace "Hijabina nace" Yace "Ki bari in duba maki kafar in ga babu targade, yau duk kukan karyar nan da kike ma mutane sai ya dawo na gaskiya, kuma xaki gaya min inda kika jefar da wayar da na baki" Shiru tayi bata ce komai ba, ya duka ya bude man ya diba sannan ya kama kafar da tace, wani ihu tayi ya ja kafar da karfi, har kasa sai da ta sauko tana kokarin kwace kafarta sbda axaban da take ji, ganin da gaske ta ji ciwon yasa yace "A hankali fa nake maki amma wllh idan kika sake ta6a ni xan yi da karfi" hawaye na sauka idonta tace "Wllh xafi yake min sosai, don Allah ka rufa min asiri kayi hakuri" Ya daure fuska ganin xata sake kai hannunta kan nasa yace "Kin xata wasa nake maki" Da sauri ta dauke hannun, duk da yanda yake mata a hankali haka ta dinga kuka tana neman birgima a wajen, shi dai kallonta kawai yake, don a fuska bata yi kama da warce xata yi shagwaba ba, ko warce baxata iya jure xafi ba ko yaya ne, dauke idonsa yyi ganin tawul din na neman sauka a kirjinta, ya sake mata kafar ya mike, sai a snn ta ankare, tana shessheka ta kankame abarta, ya ajiye man xafin hannunsa ya nufi kofa ya fita.


*Pls i am bringing this to the notice of people coming to disturb me with... ina karanta littafin ki kuma bani da kudin biya ki yafe min!!! For what?? Na aikeki karanta littafi baki da kudi? Ga dai free books kaca kaca a gari, Toh a gaskiya baxan iya lalacewa da gantalewa ba kije can ki nemi wanda xaki ce ya yafe maki ba dai khaleesat Haiydar ba, ba ruwanaa tunda ban aike ki karanta littafi ba, ki sani you owe me har sai ranan da kika mula kika mulmule kika ga daman biya*🤷

Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via

3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you

Kamar wanda ya tuna abu ya sake juyowa, rarrafawa yaga tayi xuwa gun da hijab dinta yake xata dauka, ya hade rai sosai yace "Ina wayar da na baki?" Ta juya ta kalli gadon dakin, a hankali tace "Ya fada karkashin gadon na kasa daukowa" Da mamaki ya dinga kallonta, ta sunkuyar da kanta, can yace "Wa ya jefar karkashin gadon?" Ta sake kallonsa tace "Xamewa yayi ya shige ban sani ba" cikin tsawa yace "Saboda ke yar yarinya ce ko?" Shiru tayi bata ce komai ba ya juya ya fice daga dakin ya kulle kofar, da kyar ta lallaba tayi shafe shafen mayukanta da turarruka sannan ta dauki wani rigar bacci ta saka tana dingishi ta hau saman gado ta kwanta, mamaki ta dinga yi na yaushe ya shigo gidan bata ji karan shigowar mota ba, ko dai bai dawo da motar bane, kuma ai ce mata yyi sae karshen sati, da wannan tunane tunanen bacci yyi awon gaba da ita. kasa bacci Abuturrab yyi sbda shayi da bai sha ba, don ya fara shan shayin kenan ya bari ya taho, shi kuma idan da abinda ke takurasa rashin shan shayin dare, ji yake yunwa na damunsa indai bai sha shayi ba, and he detest making tea himself, da dai yayi da kansa gwara kar ya sha, rub da ciki yyi ya lumshe ido hoping to force sleep, wajen karfe daya da rabi ya mike ya fito daga bangarensa, downstairs ya sauka ya shiga kitchen ya bude fridge, kallon fridge din ya dinga yi don bai ga alamar ta ta6a komai na ciki ba tun jiya, ya dau Chivita daya ya bude ya dau glass cup bayan ya dauraye ya xuba a ciki, sau biyu ya cika ya shanye sannan ya mayar fridge, da ya hada shayi gwara yyi hakan, fitowa yyi daga kitchen din ya xauna saman kujera a parlon cikin duhu, yana ta xaune har karfe biyu sannan ya mike ya haura sama, har ya nufi part dinsa ya dawo ya bude kofar dakinta, cikin duvet ya ganta ta takure waje daya tana bacci, ya karasa cikin dakin ya janye duvet din, dukawa yyi yana kallon kafarta sannan ya d'an danna kafar, da sauri ta janye ta juya masa baya, sake kai hannu yayi ya kamo kafar, da sauri ta bude ido, ya hade rai amma bai ce komai ba ya mike ya sake dauko man xafin, a hankali ya shafa mata sannan ya mike ya kashe wutan dakin ya fita. Da asuba bayan ya dawo masallaci ya fara tunanin ta yanda xai koma kano babu mota, gashi bai fiye son shiga commercial vehicles ba, karfe bakwai ya gama shiri ya fito daga bangarensa, dakinta ya murda a hankali ya shiga, a kwance ya ganta amma idonta biyu, ganinsa ta mike xaune da sauri... yace "Kafin in dawo ran juma'ah ki tabbatar kin fito da wayata da kika jefar karkashin gado" shiru tayi bata ce komai ba, yace "Sannan kayan marmarin da na xuba a fridge ki tabbatar kar in dawo in sami ko daya" Daga haka ya juya, da sauri tace "Tafiya xaka yi?" Yace "Aa xama xan yi" sai bayan da ya fita ya fara tunanin wayar da xai sake bata, he just need to hand a phone over to her, shi kuma bashi da strength din daga kayan gado da sassafen nan, can dai yyi deciding ya koma dakin ya ga inda ta jefar da wayar tukun, Yana shiga bai ko kalleta ba ya nufi gadon ya fiddo wayarsa ya kunna fitila ya duka yana haskawa karkashin gadon, cikin few minutes ya ciro wayar da hannunsa, ita dai tana tsaye ta rakube gefe da hijab dinta har kasa, ya dago yana kallonta fuskarsa a tamke, ta sunkuyar da kanta, ajiyewa yyi kan gado ya nufi kofa ya fita ta bi sa da kallo, dole commercial car din ya tafi ya hau a park xuwa kano... Jiddah na xaune kasan carpet a parlon hannunta rike da apple biyu, ta kasa ci sbda rashin sabo da shi, tunda take a rayuwarta bata ta6a shiga matsatsi da takura irin wannan ba, duk da ba jin dadin xama take da Hansai ba amma ai xaman bakin titi ma da take ya kan debe mata kewa tana ganin mutane da motoci, amma tun shigowarsu gidan nan yau kwananta nawa bata ga kowa ba banda shi kadai, tunanin hakan ya sa hawaye ya kawo idonta, kallon ma sbda rashin sabo da shi da ta fara xata soma gyangyadi, Mikewa tayi a sanyaye tana goge idonta ta nufi wani window dake parlon ta makale jiki ta bude labulen a hankali tana lekan tsakar gidan, babba ne tsakar gidan da flowers masu kyau xagaye, ta dade tsaye wajen tana ta kallon tsuntsayen dake tashi da sauka a tsakar gidan, kiran sallan azahar yasa ta juya a hankali ta bar wajen tana kallon apples din hannunta kitchen ta koma ta mayar, marairaice fuska tayi tana kallon fruits din fridge din banda ayaba babu abinda ta iya ci a ciki ita dai, tana tafiya a hankali ta fita kitchen din. Hansai ce xaune gaban mai anguwa da Zulai da ta rakota, bayan sun gaisa, ta kunce ha6ar xaninta ta sakar masa kuka tana matsar kwalla da zanin tace "Wllh Mai Anguwa shiru shiru har yau babu yarinyar nan tawa babu labarinta fa, abun nan ya fara damuna duk inda taje ai ya ci ace ta dawo yanxu, yau fa sati daya cur ba ita ba labarinta, na rasa inda xan sa kaina, ga komai nawa ya tsaya kamar ta tafi da shi" Sae kuma ta rushe da kuka, Mai Anguwa dake ta kallonta da mamaki yace "Ikon Allah, ni ai na xata da naji shiru Allah ya sa ta dawo gida, toh ke duk kwanakin nan me yasa kika yi shiru kinsan bata dawo gida ba, sai yanxu xaki taho kice bata dawo ba" Hansai ta marairaice cikin rawan murya tace "Wallahi na danni xuciyata ce don ban debe tsammani ba, ina ta baxa ido amma naga shirun yayi yawa" Mai Anguwa yace "Cabb, amma kina da ganganci Hansatu, anya ke kika haifi yar nan kuwa kamar yanda kika ce?" Hansai ta kara marairaice masa cikin kuka tace "Nice mana Mai Anguwa, ina da kauda kai dai xaka ce kawai" Mai Anguwa yace "Toh, ranan dai na amshi lambar shi mutumin da ya aureta, wato shi matukin jirgin saman, kuma bayan wannan aure da kwana uku ya xo min har nan da mahaifinsa da kawunsa, mahaifin nasa sanannen mutum ne dattako kuwa a garin nan..." Hansai ta hadiye abu da kyar tace "Toh kira mana shi xaka yi yanxu kenan don Allah? Don dai gaskiya na fara xargin kilan ma ya ganta ya tafi da ita ne kawai bamu sani ba, banda haka me yasa xai yi shiru haka babu labarinsa, bayan gashi kace har ya xo da mahaifinsa, to idan haka ne ba sai sanda na ga damar basa matar xai tafi da ita ba, to wllh ni na canxa ra'ayi kan auren ma, ya dawo ya fadi nawa ya kashe ko gidan da muke ciki ne sai in sayar in biyasa, ba ruwana wllh" Mai Anguwa dake ta kallonta, ya d'an yi murmushi yana kara jinjina hali irin nata, ya fiddo wayarsa bayan kusan minti biyar yace "Alhmdlh, na samo lambar" Yana fadin haka yayi dialing number Abuturrab ya sa handsfree, kallon Hansai yayi bayan an sanar wayar baxai je ba, Hansai ta rushe da wani matsanancin kuka tace "To ko dai lambar karya ya baka, ni sai yanxa nake jin ma ban yarda da mutumin nan ba wllh, wa ya sani ma ko d'an yankan kai ne yace mana matukin jirgi ne shi, jirgi abar wasa ce da xai iya tukata bayan an sanar mana turawa ne kadai suka iya daga jirgi sama su tuka, sannan idan ba d'an yankan kai ba mutumi babu dangin iya balle na baba kayi ta kashe mana kudi haka daga jin an mana mutuwa, daga haduwar mu xuwa fa ranan da ya bada sadakinta wllh mutumin nan ya kashe mana yayi kusan rabin miliyan, to akan me? Aa wllh ya xo in biyasa ya maido min da 'ya ta" Mai Anguwa dai tabe baki kawai yake bai bata amsa ba, Hansai ta fara kokarin mikewa tace "Ai dai wayar baxata dauwama a mace ba, don haka ko gobe ma xan dawo sai ka sake gwada kiran lambar don ni bani da waya, haka kawai yarinya ta bace batt kamar yar kaza" Mai Anguwa yace "Allah ya kai mu goben" daga haka ta bar wajen tare da kawarta, Zulai tace "Anya wannan mai anguwan na da gaskiya kuwa Hansai?" Hansai ta kalleta da sauri tace "Atoh, nima shi na gani, baki ji har ya fara cewa Uban yaron sananne ne a garin nan ba, kawai dai sun danna masa uban kudi shi ma shine yayi mukus, to wllh a maido min da 'ya ta babu wani xancen auren karya" Zulai tace "Kuma fa da gaskiyan ki, ko dai wannan yaron d'an yankan kai ne, idan ba haka ba a wnn xamanin ina xai samo rabin miliyan ya kashe maku" Hansai ta tsaya tana kallon Zulai, can ta marairaice tace "Toh kuwa in har haka ne ya kassara ni, wa gareni da muke sana'a tare banda jiddar, ke baki ga ko me nasa Bibalo kin yi take ba sai ta nemi ta xageni, ai jiddah ita ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login