Showing 6001 words to 9000 words out of 12562 words
Chapter 3 - Binta Yar Jagaliya Book 1 Hausa Novel Complete
tuni wani irin tashin hankali ya ruske shi Oni labahani a haka mutuwa ta zo ban cika burina ɗaya ba a duniya ashe a fili yake
Gyara tsayuwa tayi tace
"Ai kuwa yau zaka baƙunci lahira domin mun gani ana ta'asa a gidan ,
Dan girman Allah mala'ikan mutuwa kai min rai Wallahi ban sani ba cikin yar da bara ya sa ƙafa ya doka a wa uwani domin Wallahi ba zai fuskanci tashin hankalil nan shi ka ɗe ba yace
"Uwani tashi daman ance in da rai zaka sha kallo yau ga mala'ikan mutuwa a kan mu,
Aikuwa cikin masifa ta ɗauko tasar da taci abinci ɗazu ta buga mai tace
"Zan fasa maka kai kafin ni ka fasamin fatsarmama in ban da ka mai dani mara hankali mala'ikan mutuwa ne ya zo gidan nan?"
*Ya ku yan adam har kuna da lokacin yin faɗa alhalin yau zaku mutu*
Innalilahi dan girman Allah ai bansan gaskiya yake faɗa ba kaimin rai Wallahi bacci nake ya ta sheni
Ai kuwa yau zaku yi kwanan barzahu
Tuni uwani ta saki gudawa a zaune yayin da numfashin labahani da ƙƴar yake fita saboda ta shin hankalin da yake ciki ko mutsi ba yaso yayi ƙoƙari yake ya tuno addu'a amma ina ya kasa sai mun jaye nu'ara kulya li'ilafi yake mai mai tawa tun yanayi ahankula har ya dawo da ƙarfi.........…..✍🏼
*BINTA YAR JA GALIYA*
Wannan littafin na ƙuɗine bazanyi free page da yawa ba ki garzayo ki mallaki naki domin bansa kuɗi da yawa ba ₦300 kacal
Account number Ja'iz bank 0014853443 Amina Muhammad alhasan ko katin kira MTN ta wannan number 08141785374 ko wannan number 09061890481 kiyi screen shot ki toromin ta pc
*KU HANZAR TA KU SIYA FREE PAGE YA KUSAN ƘAREWA*
*DOMIN WASAN YANZU YA FARA*
free page
Dariya ce ta kusan kuɓucce mata ta danne tace
"zan baku zaɓi ku zaɓa in kuna so in barku da ranku sai kun hana saurayin meragaje zuwa gidan nan in da gaske yake ya fito ya aure ta
ko in hana ku ba haya na tsawan shekara ɗari ko in saƙar maka gudawa ta tsawan shekara tamanin ,
zaro ido yayi tuni wata gudawa ta kuɓucce mai ji kake tsuuuuuu yawa an saki fanfo taɓa ƙasan shi yayi ga wani irin wari da ya game ɗakin a zuciyar shi yace
"anxu gun har an fara saƙar min tawa yasan wataran ba gudawa zaiyi ba sai de ya kashayar da ƴa'yan hanjin sa ,
duban uwani yake amma a baɗini wasu taurari yake gani sun za gaye shi yau yasan ƙar shan sa ya zo shekara ɗari ba kashi ko ƙwana ɗaya mutum beba yake ji gata balle mutum yayi shekara ɗari futsari ne ya biyo baya jin har da gudawa yo rana daya mutum yayi gudawa yake fita hayyacin sa balle shekara tamanin ai kawe mutuwar tsaye zaiyi da kƴar ya iya buɗe baki yace
Innalillahi fatalwar gimbiya ku yimin min rai dan allah wallahi ba laifina bane laifin uwani ne na matsani yaron nan ita ta dage sai ya zo gun mairo
Zuface ta ƙaryowa uwani tace
Wallahi sharri yake mun kullum sai ya bashi kuɗi ko mero
MERO da ta fita hayyacin ta tayi dana sanin shigowar ta ɗakin nan tace
"Eyyy eh wayyo allah,
banzan kallo labahani yayi mata yace
"tsakani na da gimbiya a ƙwai ƙauna ta gaskiya da amana kowa na garin nan ya sheda,
FATALWAR GIMBIYA ni na zaɓi na farko zan hana shi zuwa
a'a ke naki da banne waccan tsohowar da ta kwanta a ɗakin binta zaki taso ta sannan ƙarta ƙara ƙwana in ba haka ba mu shanye muku ƙafafuwa ke da ita
"To, zan taso ta insha allah haka baxata faruba ,
Duda halin da yake ciki be hanashi zabgawa uwani wata uwar harara yace
"hmmmm ai duk ke kika jamini saboda san ƙuɗin ki shegiya me subfar ƙaguwa ,
"kun ceci kan ku ni zan tafi chaina ,
Ɗif suka ji da sauri uwani ta tashi ta fito domin tada iya mahaifiyar ta da tazo daga ƙauye
da gudu binta ta waɗa ban ɗaki cikin ta har murɗewa yake saboda dariyar da ke cin ta
Jin alamar gudu yasa uwani ta dafe kanta domin a tunaninta fatalwar gimbiya ce ta tashi sama domin ƙarta warce kanta yasa ta dafe shi
"IYA IYA IYA ,
sosai tsohowar ke sharar munshari har da yahun bacci
Hannu uwani tasa ta buga matashin iya a fusace iya ta sa hannu ta buge hannun uwani tace
Dan allah ku barin na huta tun ɗazu kuke ta shina yawa wanda na ciwa wani bashi
"hmmmm iya yau fatalwar gimbiya ta zo gidan nan ɗazu ta tafi wallahi tace ƙar ki ƙara ƙwanciya a ɗaƙin ƴar ta in ba haka ba sai ta shanye mana kafafu,
cikin sauri IYA ta tashi ta zabgawa yar tata harara tace
Owani lami me yashin madina ƴar da na haifa da cikina ita ke sharara min ƙarya uwani bura'uban ki uwani na yi miki kama da wacce fatalwa zata ambaci sunan ta to yasin har in bar gidan nan a ɗakin nan zan ƙwana
Wasu hawayene masu yaji suka zubu a idon uwani tace dan girman allah iya ki zo mu tafi ƙar suji ja'in jar da muke da ke
zani ta gyara ta face majina ta sai ta matashin ta ƙwanta tace
Alƙur'an uwani ki fita adona in rufe wallahi uwani ina raga miki da iliyane da tuni na zubar mai da haƙura ai ɗazu itama shegiyar ina jinta nayi mata shiru domin ban zo gidan nan in ƙwanta a tabarma ba nazo inji laushin katifa ai gashi ta haƙura ta fuce tasan duk tujararta na fita hhhhhhh gaba da gaban ta
majina uwani ta face ta haɗa hannu wanta biyu tace
"IYA dan girman Allah ki haƙuri ki taso mu tafi ,
wata uwar ɗirga sukaji a lamun abu buwa sun sauka tuni hanjin cikin uwani ya cure gu ɗaya ta fara zare idanuwa domin ba baƙin magana IYA ta ja musu da ta taso da duk haka bata faru ba
"wani irin ƙugi su kaji guggugug wata ku bil adama kuna da taurin kai na maku dama ku fita ƙunƙi gashi ni har naje chaina na dawo kuna zaune ,
zaro ido IYA tayi ya dafe ƙirji daman tun zuwan uwani da ta bita Allah sarki ashe sona uwani ke yi oni lami na shiga ukku yau sai ta Allah tace
*"UWANI* in kin sami kuɓuta ina bin matar me gari naira hamsim kuɗin daddawa ki amso kiyi min sadaƙar ashirin da biyar sannan ki gina min masallaci da raguwar kuɗin tun huri na keso in iya sa'alun amma sakalci na ya hanani yanzu da tayi min rana ina zuwa ƙabari ana tambayata in amsa kuka tasa domin ba haka ta so ba taso abar mata jiran duniya ,
zuba mata ido uwani tayi da alama IYA ta fita hayyacinta bata san me take faɗa ba yanzu har yaje chaina ya dawo ji tayi fa a radio ance ba ƙasar da takai chaina nisa
"ɗazu na ƙafa muku sharaɗi kun bujere min to zaku rufe idanuwan ku har sai wani daran yayi sannan ku buɗe in kuka ƙus kura kuka buɗe to fa rundunar aljani gushshu zatayi sama daku sannan ki faɗawa labahani ƙar ya sake ya ƙara fita waje da sunan bara sai de yaji anyi sama dashi bashi ba dawowa,
"To mun gode ,
tuni suka rufe idon su suka fara laluban ƙofa ruge ruge suka shi ga yi ganin uwani ta bangaje IYA ba ta luraba yasa IYA ta fusgota ta dawo da ita baya tayi wuf ta futa gani take in ta ƙara second ɗaya rundunar aljani gushshu zata yi sama da su
Ganin iya ta futa yasa itama ta fita a guje har ta buge da garo ɗakin uwani suka shiga suka cure gu ɗaya ha kama malam ya zuba ta gumi dan ko shakka babu yasan fatalwar gimbiya ce ta zo musu ba mala'ika ba duk abin da ake yana ji har da hana shi bara duban mero yayi duk ta fita hayyacin ta sai surutai take allah ya rufawa saminu asiri da yau be ƙwana a idan nan ba da ya ƙwana da dashi wannan rundunar gushshu zata haɗa domin ai ba zasu bar shi ba saboda kajin mutane da yana sakat a garin nan kullum cikin cin kaji yake suma harya sammu su
*WANNAN KENAN*
"wallahi momcy duk abin da zan ja hankalin sa ina yi amma wallahi a banza anya kuwa yana da lafiya?,
YUSRAH ki nutsu ki gano abin da baya so da wanda yake so shine fa amfanin zaman ki kenan a gidan wallahi na ƙwaɗayin dukiyar gidan alhaji ƙura kin san kaf ƙasar nan ba na biyun su a ƙuɗi da mulki ke ce wacce zata zamo silal dawamar mu a daula kinsan a kullum sai naji ɓakin cikin hajiya turai saboda mahaifin mu ya fi son ta shiyasa har ya bawa bilal auran ta lokacin da na gane haka wallahi har ƙwanciya nayi a asibiti ƙarshe sai ya haɗani aure da mahaifin ki wanda bashi da wata shahararriyar dukiya dan haka wallahi ko zan yawo tsirara sai na rusa hajiyan turai akomai
MOMCY yanzu wanne mataki zamu ɗauka naji hajiyan turai tana cewa we waccan shegiyar yarinyar zata dawo gidan nan
ƙwafa tayi tace
"Uhmm zanyi maganin ta ,
MOMCY ya zanyi ya so ni duk abin da nake kamar baya gani fa
Dariya tayi tace
"YUSRAH yana kula da komai halin su ɗaya da mahaifinsa zai nuna miki kamar besan komai ba to kisam mummuƙe yake yana lura da komai sannan duk kan wani taƙun kowa yana sa mai ido amma zanje gun bokana gibi,
"TO bye,
"Bye,
washe gari 🌅
cikin sauri yake komai saboda yau suna da taron jam'iya gashi sauran ƙwana sittin zaɓe wani satin za ai primary election za su yi tsare tsaran abubuwa geznar yasa blue black tayi mai kyau abinka da farar fata yasa black shoe ga rolex black a hannusa hula ya sa tangaran gyara babbar rigar sa yayi ya sai ƙamshi yake zab gawa ɗauki brief case ya ɗanna remote ya kashe komai na ɓangaran sa cikin nutsuwa yake taka stairs case wayar shi ce tayi ƙara alamun shigowar message be biya ta ƙai ba ya nufi shashin hajiyan turai duk inda yabi sai sojojin nan sun gaishe da shi amsa musu yake cikin sakin fuska
a bakin ƙofar hajiyan turai ya tarar da sam driver sa sam yace
"good morning sir ,
morning sam
ɗur ƙusawa yayi ya amshi brie case ɗin sa
miƙa mai yayi
Cikin hausar sa mara fita yace
"sir ga sabuwar jaridar c.n trues ,
cak ya tsaya be juyo ba yace
innaje office zan duba ta
"sir is important ,
juyowa yayi ya amsa shafin farko yaga picture ɗin shi anyi rubutu da manyan baƙi *SHIN KO KUN SAN DALILIN DA YANA ƊAN TAKARAR SHUGABAN ƘASA AZZAM BILAL ƘURA HANA SHI AURE* ✍🏻
Zubawa rubutun ido yayi yawa me shirin gano wani abu wato in kana so ka san asalinka shiga siyasa rintsai don sa yayi a hankali bakin sa ke furta
*HASBUNALLAHU WANI'IMAL WAKIL*
ba abin da ya ɗaga mai hankali sai we ana zargin sa da yana hurɗa da karuwa shi yasa yaƙi aure ring ɗin wayar shine ya dawo da shi hayyacin sa da sauri ya ɗauka ganin mahimmancin kira yasa dole ya ɗaga yayi shiru
AZZAM kana dawo wa daga taron jam'iya ka biyo jirgi ka tawo akwai matsala duk da alhmdllh nayi maganin matsalal
to kawe yace mai sukai sallama kai tsaye shiga ciki yayi domin gaishe da hajiya turai sai wanda ya karan ce shi zai gane cewa yana cikin fushi sosai fuskar sa har ja tayi abinka da farin mutum cije leɓansa na ƙasa yayi a rasa da me za ahaɗa shi sai da zina rumtsai ido yayi tambas siyasa mugun wasa ne in baka da juriya ka shigeta sai a haukata ka ba abin da ya tsana ya ƙƴamace shi irin zina dai dai ta kansa yayi yayi sallama
cikin fara'a ta am samai yace
"lafiya azzam naga yanayin ka ya sauya wannan fa jaridar da ka duƙunƙune ta me ke faruwa?,
risina wa yayi ya ƙaƙalu murmushin dole yace
"hajiya bakomai barka da safiya kin tashi lafiya,
ajjiye chokalin hannuta tayi ta dauki tissue ta goge bakin ta ta miƙe cikin nutsuwa take takowa inda yake tace
"Azzam ni na haifeka dan haka kome zakai ka ɓoyemin abin da ke zuciyar ka ni me iya karantar shine ta idonka ko fuskar ka azzam kai ka ɗe muka haifa duk da haka mun baka tarbiya ta gari mun hane ka da yin ƙarya me yasa yanzu xaka fara alhalin fusƙar ka ta nuna ? ,
ƙasa yayi da idanuwan sa jikin sa yayi sanyi ya miƙo mata jaridar amsa tayi ta sami gu ta zauna ga banta ne ya waɗi tayi shiru na wasu sakanni kana tace
"ɗaukaka bata zuwarwa mutum ta cikin sauke dukƙan wata nasara tana zuwa da ƙalubale ba kowa ne zai yarda da wannan zancan ƙazafi ne duk wanda yayi maka nasan ubangiji ba zai barsa ba ɗana ƙar ka sa komai a ranka Allah yayi albarka ya dafa maka ,
sosai nasiyar mahaifiyarsa ta shige sa tambas duk wanda yayi sa'ar uwa ta gari ya dace yace
"hajiya zan tafi taron jam'iya sannan zanje kura baffa na nemana,
okay Allah ya tsare
"ameen yau muzamfar zai dawo na barmai komai na kasuwanci na kafin komai ya dai dai ta,
"To allah ya rufa asiri ya buɗa,
"Ameen ya allah,
miƙewa yayi zai tashi yaji ance
yaya ina ƙwana
be juyoba ciki ciki ya amsa yayi gaba abinsa
haɗiye wani yahu me ɗaci tayi tayi zaman daɓaro a ƙasa kai kace yar borice zuciyar ta tayi wani irin baƙi dan ma Allah ya temake ta hajiya turai ta shiga ɗakin ta sallamar ramlat taji da sauri ta ɗago kai tana jifanta da wata iriyar harara
Mayafi ramlat ta cire tayi ɗamara tace
"wallahi kinsan ni bana ɗauƙar raini ko dan wallahi yanzun nan zanyi ƙasa ƙasa da ke banza ƙaruwa ,
cikin zafin nama yusrah ta ɗaga hannu zata mare ta haseena ta tare tace
"ƙarya a kai miki ai yusrah baki ga komai ba sai ance miki yau an daura aure na da yaya azzam ,
Ramlat da zuciyarta ta kawo har huya ta ɗauki takalmin ta ta bugawa haseena abaki tana huci tace
"wallahi kaf cikin ku ni ya azzam ya dace ya aura saboda ni daga dangin ubansa nake kufa yan karan ƙaɗa miya banza ye kawe,
dariya yusrah tayi ta tafa hannaye ta rangaɗa buɗa tace
"anayi muna jin daɗi ku gama haukan ku ni zan aure shi,
sosai bakin haseena ya fashe yana zub da jini dafewa tayi ta zuba uwar ƙara da sauri hajiya turai ta fito tace
"lafiya haseena ramlat yusrah me ya same ki haseena ?"
yusrah tayi carab tace
"faɗa sukai ita da ramlat ta sami gu ta zauna ta kurɓi lemo ta sa earpon a kunnanta tana bin waƙa,
hmmm ni ba zuwanku gidan nan shine matsalata ba aa faɗa kuke ace har yanzu baku girma ba ko wacce a cikin ku da tayi aure da tuni da ƴa'ƴanta wallahi yanzu nan zan ƙira azzam yayi maganin ku nasan beyi nisa ba
Haseena tace
hajiya ɗan allah kiyi haƙuri insha Allah ba zamu ƙara ba
Ramlat kuwa sai hura hanci take domin tare suka tashi da azzam ya bata shekara ukku saboda shi taƙi yin aure yanzu haka tana aiki a asibitin kura ta ɗauki hutu ta tawo nan gu ta samu ta zauna tace
hajiya ki haƙuri insha allah ba zamu ƙara ba yaran nan ne basu da kunya
hajiya turai tace
yusrah ki basu mukullan ɗakuna su zaɓa wannan barin ku gu ɗaya a kwai matsala
wani uban murmushi ta saki me cike da ma'anoni tace
"To hajiya ,
miƙewa tayi ta tashi domin wallahi ba zasu zauna a ɓamgaran nan ba in da ake kai baƙi zata kai su ba har gori sukai mata ba
wannan kenan garin kura
fitowa tayi ta zabga wata uwar hamma ɗakin kahu labahani ta kalla tuni wata dariya ta kubɓuce mata ta dinyi harda ruƙe ciki ganin saminu ya shigo yana waka tayi sauri ta haɗe ranta tace
"ke saminu zo ka siyomin indomi da ƙwai,
washe baki yayi domin yasan in ta aike shi tana yi mai hasafi abin hannunta be rufe mata ido ba yace
"to anty binta gani ,
ɗaki ta shiga ta miƙo mai ATM card ɗinta tace
"kai ma ka siyi ta 500 sauran ka daɗe ,
anty binta bazan dade ba allah isa kar in sami lahi
Banza tayi mai ta sami gu ta xauna tana yar waka aguje kahu labahani ya fito riƙe da ciki da alama bayi zaishi ga ɗaga murya tayi tace
"kahu lafiya kake tafiya a ɗur ƙushe?,
wani to tuƙuƙin bakin ciki ne ya zomai huya yace
"Binta ƙar de duk abin da akai ki ce baki jiba ?,
Zaro manyan idanuwanta tayi tace
Kahu ban sani ba me akai
banza yayi mata ya shiga ban ɗaki domin gaskiya fatalwar gimbiya su ta raina gashi ta hanashi fita nema ta tsame yarta a ciki duk ta'asar da binta keyi
ringing ɗin wayarta taji da sauri ta shiga ɗaki ganin sunan alhaji ta saki murmushi domin har ta ganota tana fantamawa da kuɗi hello alhaji
"my beb yau zai zo kura zan toro miki address ɗin sa kije mu gwada sa'ar mu kowa ya dubi halittarki dole ya yaba ,
fari tayi da ƙƴawawan idanuwanta tace
"okay toromin amma da sharaɗi inga kuɗina ,
binta shegiyar kaya duk wata hanya da zaki cutu sai kin ƙauce mata
Alhaji kenan ina tare da ku ba dole in koyi fusaha ba ai sai abarni abaya
hakane my beb yaushe za muyi aurene
"hmmmm alhaji sai na gama cin duniyata da cinke ,
ni kuma zan baki allurar tsiƙarar ta
dariya