Showing 9001 words to 12000 words out of 12562 words
Chapter 4 - Binta Yar Jagaliya Book 1 Hausa Novel Complete
tasa sukai sallama
WANNAN KENAN
shugaban jam'iya yace
mu'azzam zaɓe na ƙaratowa amma banji maganar auran ka ba kasan a tsarin ƙasar nan ba a bawa mara aure takara mu gashi mun tsayar da kai ƙar ka bamu kunya fa kowa ya zuba ido yaga yarda zata kaya kuma kasan jam'iyar hamayyah ce ke mulki suna da damar kawar da mu
*BINTA YAR JAGALIYA*
By
Oum yasmee
Free page ya kusan karewa fa ku hanzarta mallakar naku
Shiru yayi nawasu sakanni yasan gaskiya suka faɗamai amma shi har yanzu be jin zai iya aure domin bega wacce ta kwanta mai a rai ba yace
"Insha Allah zan kawo ƙarshan matsalalnan Allah ya dafa mana,
gabaki ɗayansu suka amsa da amin taro ya watsai fito wa yayi ya sami sam na jiransa ya shiga mota yace me ya kaishi airport domin jirgin 10:45 zai hau gashi goma saura waya ya ɗauka ya kira muzamfar bugu ɗaga ya ɗaga yace
Aslm muzamfar
daga can ɓangaran yace
"wslm gauro ya gari ,
tsadadɗan murmushi shin sa yayi yace
"tsoho ya sanran ka ?,
wallahi azzam shan tablet ne be ishe ka ba wata ran ba zai maka illa nasan ka sani sai ka ƙarar mana da ƙwaiƙwayan mu ko
A gaskiya muzamfar baka da kunya ya kasuwancin komai na tafiya daidai
"Alhmdllh na rabawa kowa na turo baka da komai ta email sai ka duba ,
Masha allah ina daughter ta tana lafiya
tana lafiya qalau tace tana so taga ɗan daddy ɗinta
hhhhh ai wannan da ku take ba dani ba wallahi wayon yarinyar nan yana ban mamaki
wani zancan intayi wallahi cikin mu ƙullewa yake kai ma da tuni kana da yar ka ko ɗanka
"to to sai anjima ai ka haifamin shikkenan ,
be bari yayi magana ba ya kashe wayar ya lumshr idanuwansa ya shiga tunani wanne mataki baffansa ya ɗauka zai kawo ƙarshan matsalalnan ne ko kuwa me son ɓata mai suna zai ci gaba da ɓata mai suna har suka zo airport be sani ba sai da sam yayi mai magana ajiyar zuciya yasake ya fito ba abin da ya dauko sai brief case ɗin sa kaya ma yana da su a nan ya shiga reception sai nan nan ake dashi masauki ma me kyau a ka bashi kafin jirgin su ya tashi
wannan kenan
"ƙawas ƙwas kina ina ?,
jin muryar rufaida da sauri ta fito daga ɗaki tace
"RUFAIDA sannu da zowa shi go ,
kayan ta ta tattare domin a ƙwai ƙwata a gun tace
wallah ƙawas ni ba zuwa gidan ku ba sai mutum ya ɓaci
wani banzan kallo ta jefe ta da shi tuni ta haɗiye sauran zancan baƙin ta ta sani sarai duk amintar dake tsakanin ta da binta yanzu za aji kan su tace
"Allah ya baki haƙuri ƙawas ina su kahu naji gidan shiru ko anfita nemane,
kallon ƙofar ɗakin sa tayi tace
"tun safe suna ɗaki har iya me yashin madina ,
haɓa rufaida ta kama tace
"Topa lafiya?,
haɗa rai binta tayi tace
jeki ki tambaye su ta shige ɗakin ta bata da wata da bara ban da ita mata bita domin alƙawari ne ta ɗauƙar wa ƙanta sai ta raba binta da kuɗin nan a komai ta fita ita ta jawota harƙar siyasa amma sun yada ita sun ɗauki binta mutumin da take bala'in so suke ƙwallata da shi alhaji me tasa yana son binta da aure duk da haryau binta bata san irin alaƙarsu ba shiga ɗanki tayi ta sami gefen katifar binta ta zauna mayafin da ta ruƙe shi a hannuta ta rataya a huyan ta tace
"ƙawata ashe haka abin alkhairi ya faru ?,
kallon rashin fahimta binta take mata
dafata tayi tace
"zancan yiwa azzam ƙazafi nake nufi,
shiru binta tayi ta saki a jiyar zuciya tace
"rufaida na fasa shigowar ki nake jin wani wa'azi duk da banyi wani karatun addini me zurfi ba nagane ba abu bane me kyau ina tsoran randa ubangiji zai tsayar dani da shi yayi mana hisabi sharrin zina ba ƙaramin sharri bane abin duniya fararrene ƙararre bansan ko ina cikin yin masa sharri in mutu ince da ubangiji me da wanne ido zan kalle shi kina ina shekaran jiya jami'an tsaro har gidan nan suka zo suka tafi dani we yan unguwar nan sun kai musu ƙara zan ɓata yaran su Rufaidah abubuwa summin yawa ga yawan mafarkai marasa daɗi danake,
wani kallo rufaida tayi mata na baki da hankali tace
"BINTU anya kuwa ba asami wani ko wata sun jefe ki ba domin wallahi wannan maganar da kike kama tayi da wanda aka jefe iya sanina ba ƙƴashan ƙwaya anya kuwa lafiyar ki qalau ƙawata kuɗi fa yanke taƙaicin duniya ,
dan murmushi tayi tace
"Sister wallahi lafiya ta ƙalau kawe yanzu bana son wannan aikin,
Dafa ƙafar ɗarta tayi tace
"Dan girman Allah bintu ki rufa mana asiri ki duba fa ki gani mu muke ci da kanmu sittira gashi kina so ki nemo mahaifin ki in bata wannan hanyar ba ki faɗamin ta ina zamu samu kuɗi har gwarani jikina shine jarina kefa kinƙi sakin jiki ki mori duniyar ki ,
shiru tayi tana auna zancan rufaida tambas ta wannan hanyar ne zata nemo mahaifin ta tunda bata da wani kudi sai wanda yan siyasa in tayi musu posting su bata na kashewa
ganin tayi shiru rufaida tace
"ƙawata tashi muje gidan gwamnati kinsan fa yau muna da taro ko ankusan primary Election ko ?,
ajiyar zuciya ta saki tace
"Eh gobe ne ,
yauwa yar gari tashi yanzu lokacin samun mune yau ba zamu dawo ba sai dare
tashi tayi tace
Bara in shirya gashi wannan yaron be kawo min abin kari ba wallahi tsiyar aiƙen saminu kenan zani ta dauka ta cire kayan ta
duban ta rufaida tace
"Wallahi bintu da zaki fara harƙar nan zaki sami kuɗi komai naki me kyau ne ,
Wani banzan kallo Binta ta jefe ta dashi tace
"Wallahi wallahi rufaida kika ƙara yimin maganar nan sai nayi maganin ki wato ke kin sulhuntar da naki so kike nima in bayar dashi ba lada sai huya da zunubi ko ,
kwanciya tayi kanta na kallon rufin ƙwano tace
'Allah ya baki haƙuri na dena,
ƙwafa tayi ta fita
Wannan kenan
MU'AZZAM ita siyasa kasuwar buƙata ce wasu mutanan kana zamane da su bawe dan suna sonka ba a'a sai dan akwai abin da suke nema a gunka lokacin da ya ƙare to zasu gudune su Barka ka kula sosai da kowa in Allah ya baka kujerar nan
sai a lokacin ya iya duban kakan nasa yace
"BAFFA ina tunanin ajjiye takarar nan baffa abin har ya kai da yi min ƙazafi lamarin ƙasar nan bashi da lokacin gyaruwa komai an lalata ,
kaf cikin jikoƙina kai na dauko saboda nasan zaka iya zuciyar ka irin tawa ce ko mai nawa naka ne ƙar ka zamo me sarewa kai al'umma ke jira in ka fasa gwiwowin su zasu sare bame iya kula da ƙasar su in sukai rashin adalin shugaba wa zai maye gurbin ka sau da yawa muna kuskure amma in muka dawo muna iya gyarawa ina gab da gama binkice akan yarinyar nan
Duban sa yake da manyan idanuwansa yace
"BAFFA wacce yarinya,
Binta yar jagaliya nasa a dinga bibiyar ta ko inta kanta bata sani ba saboda tana da mahimmanci a tafiyar su me tasa dole ta dawo ƙarƙashin iƙon ka bayan mun gama sai mu jefar da ita saboda amfaninta ya ƙare zata iya sawa kujerarka ta waɗi amma in muka ɗauke ta komai yazo ƙarshe bazan yafewa kaina ba inhar ka waɗi saide ban cika me faɗa aji a ƙasar nan ba suwane dadtawan in bamuba su me tasa yarana ne butulcemin sukai
baffa banga amfanin sako mace a cikin siyasar mu ba
tashi yayi ya ɗo gara sandar sa ya fara tafiya yace
zaka iya tafiya ni kaifi ɗaya ne na gama magana duk abin da na ce maka dole kabi bazan taɓa cutar da kai ba maganar aure kan tana hannu na insha Allah baza kai dana sani da ni ba yana fadar haka ya shige ciki yabar shi da kallon hanya gun hajiya babba ya shiga domin su gayyasa sosai tayi murna da ganin jikannata tace
Mijina yau kaine a gari
Zama yayi yace
Hajiyan kura ina huni
"Lafiya qalau ya Maman taka ?"
Tana lafiya tsohuwa
Akwai tsohonwan tuzuru irinka shekaru na ja ba aure anya ba zan zaɓo yarinya in aura maka ba wacce zaka iya haifarta kaga girma ya wadi ko
tanƙwashe kafafunsa yayi yace
"Uhmm kina auramin a ranar zata zama karamar bazzawara ya kikaji wannan zancan,
Muzuba mu gani (next book ɗina )
ba yarda zakai dani wallahi dole ka zauna da ita
Hajiya ina da taro na tafi ki gaida su hajiyan taura
pillow case ta jefu mai tace
Ja'iri anya ba aljana ce ta aure ka ba ana maganar aure sai guduwa
Au tsohuwa baki sani ba ai sunan ta yar mero yafita yana ɗan murmushin
Ya mu'azzam sannu da zuwa
Yauwa jiddah ya Maman taki
Tana lafiya shiga gun hajiya tayi shi kuma ya fita kullum addu'ar ta Allah ya mallaka mata azzam amma ko kallon ta baya yi ......✍🏻
*BINTA YAR JAGALIYA*
By
Oum yasmeen
Ƙarshan free page
Ku hanzarta mallakar ci-gaba. *BINTA YAR JAGALIYA*
Me suna
*JIFAN GAFIYAR ƁEDU*
(Ba tsuntsu ba farko)
Ku biyoni domin jin harda zata kaya domin kowa yasan
*Ramin kura da wuyar shiga a gayawa kare ya yi hankali*
Ya wasan zai kaya tsakanin mu'azzam da binta yar jagaliya
shirya wa tayi cikin wani lace onion colour an mai ado da flower blue ba wani me tsada bane amma saboda kwalliya ta zauna mata sai ka rantsai me tsada ne anmai dinkin have bubu ɗaurinnan tayi ture kaga tsiya ta yafa mayafi a kafada tasa have shoe ta feshe jikinta da turarurruka agogo tasa da sarka tace
"Rufaida taso ba muga ta zama ba ,
tashi tayi ta ɗauki jaƙar ta da wayar ta suka fice tsayawa tayi dai dai ƙofar su iya domin ita wallahi tayi dana sanin abin da tayi musu ta buɗe labule tace
"Uwani kahu saminu zai kawo muku indomie sai kuci yau bani da wani kudi sai wanda zan hau a dai dai ta ,
idon su a rufe uwani tace
"mun gode binta ,
Kahu kuwa da ƙarfe ya ƙare mai yana jin ci ya taso yace
"Bara in kar ɓo,
karab iya tace
Wallahi labahani kar ka sake ka fita ba fatalwa ta hanaka fita ba kuma in kafi ta balalle mu sami abincin ci ba saboda nasan halinka cinyewa zakai danni yau zan tafi gida
Iya we wacce fatalwa kuke zance
Uhmm yar nan ba za'aji mutuwar sarki a bakina ba
Uwani ce tayi ƙarfin halin kwashe komai ta faɗa mata
Wallahi ku saki idanku ba wata fatalwa
Banza sukai mata dan ba ita za'a yi sama da itaba
Sister kawe ki ƙwace abincin ki tunda sunke yar da kowa yayi harkar gabansa
Kahu labahani yace
"to manna illir khairi irin ku ubangiji ke faɗa shegiya me yawo da fuska yawa ta hoda bahur duk kin kwaye fata jijjiɓar kawe matsamin daga gani ba shakka tauraruwa me wutsiya ganinki ba alkhairi ba hammata duk wari a daure a dinga aski ni wallahi ina tausaya wa masu neman ki yo ubangiji ya kamaki duk warin zina kike,
fuuuuu ta fice yawa kubu buwa dan yasin ta gaji da cin mutuncin da kahun binta yake mata wataran sai ta rama dan tana tsoran binta
Kahu kahu kahu wallahi kaji sau uku nakira Sunan ka kadena ciwa ƙawata munci in kaƙi ba zaka ƙi ganiba su cleaner zan ɗauko maka ku kuma tun kafin in saƙar muku muciji kubuɗe indon ku
ae suna jin haka suka buɗe idon su saidai basu saki jikin suba dan gani suke za ayi sama da su tafiya tayi ganin sun dan warware ta saki ajiyar zuciya ae hakkin sai yayi mata yawa masu majalisar gidan su suna zaune ana zaman banza juyowa tayi zata yiwa rufaida magana taga anliƙa mata poster din azzam cikin bala'i tace
"Wanne dan bura ubanne ya manna min hotan ko dadɗan mutumin nan wallahi yau alo tsiya alo danja ,
ganin ta fara bala' wani ya taso yace
"Ki haƙuri bara in ɗaye wanine ya manna yau su namatasa zai fito zagaye ,
banza tayi mai ta kama hannun rufaida suka tafi ko da suka je gidan gwamnati a waje suka tsaya suda yan da ba Alhaji ne ya fito yana gyara babbar rigar sa yace
"Yauwa binta ke zaki ja wannan runduna ku watsa taron wannan shegen ƙwaron kai laboss,
Tashi yayi yana lanƙwashe ƙafafuwa yana cije baki yace
"Yess oga gani ,
da ga yau binta ce shugabar ko wanne shege a gidan nan sannan duk wanda a Ka kama karya sake ya ambaci sunana ni zan san yarda na fito da mutum duk da mun hada maki da yan sanda
Angama oga amma zuciyarsa cike take da haushin binta ko wanne matsayi ta ƙwace musu
Binta ungu ki raba musu ku tafi daga nan inaso yau media ta ɗauka da zancan nan yau kura ba zai bacci ba Insha Allah.
murmushi tayi tace
"To ,
Mota biyu sukai sosai gari ya cika an kashe tituna domin tarbar sa da yake ya boyar yiyar hanya ya shigo cikin garin har yaje kura ba wanda ya sani
Yana cikin mota yana ɗagowa mutane hannu sosai zuciyarsa take cikin farin ciki ashe ba ƙaramin so suke mai ba el'bashir ya duba wanda shine mate maƙinsa yace
"Allah ya bani iƙon cikawa al'ummar ƙasar nan burikansu,
Murmushin jindadi yayi yace
"Ameen ya Allah kai me nake gani yan daba suna kaiwa mutanan mu sara,
Cikin sauri ya dubi yan daban tuni mutane suka fara yin ta kansu wasu masu taurin kai na tsayawa cikin sauri ya ɗauki waya domin kiran c.p na yansanda amma har ta katsai be ɗauka ba ƙara ƙira yayi
EL'BASHIR yace
"Bisa duk kan alamu c.p yasan da wannan abun shi yasa yaƙi ɗauka kasan gwamnatin nan bata da imani kafin ya ƙarasa,
ansa madoki an bugemai glass ɗin mota ido biyu sukai da binta wacce taci ɗamara raga raga tayi mai da glass tuni security ɗinsa sukai Kan ta zasu har beta fitowa yayi
Kallonta yayi idanuwanta a tsaye bako tsoron murɗadɗun security ɗin dake kanta sun saita ta da bin diga mace har mace amma ta zubar da kanta shi wallahi rayuwarta tausayi ta bashi tuni yan jaridu suka saita camera Jira ake a ga me zai faru kau da kansa yayi da barin kallon ta yace
"Ku sake ta ƙar ku taɓata ku kununa mata kunsan darajar mace tun da ita bata san ciwon kanta ba kamata yayi ki nutsu ki aure shekarunki ƙanana amma kin biyewa ruɗin duniya ,
yawu ta tofa ya fallatsai mai fuska ta ɗaga murya tace
"Munce bamayi anayi dole ne mazinaci kawe ,
Tuni idanuwansa suka ƙada sukai jaaa yarinya ƙarama ta jefeshi da mugayan kalamai inda yayi aure da huri da tuni ya haifi kamarta domin bazata huce shekara goma sha takwas ba handkerchief ya ɗauko ya goge fusƙarsa tuni mutane suka yo kanta ɗaga musu hannu yayi alamun su dagakata matsowa yayi kusa da ita yarda ba wanda zaiji me yace
"Yanzu wasan ya fara ƙarki ga kinyi ban dau ection ba aa ki jira lokacina wasan bazai miki daɗi ba sai na koya miki hankali ,
yana kaiwa nan ya shiga mota yace su sake ta jikin ta asanyaye ta koma gidan gwamnati gwamna yace
"Ina tafa miki bisa namijin ƙoƙarin da ke kai zamu baki makafa zuwa gari ya dai dai ta sannan a yanzu zaki ga kuɗin ki zamu baki hannu da hannu saboda gudun matsala ba zamu sa miki ta account ba ,
murmushin jindadi tayi tace
"Nima ina godiya amma kahuna Kar su taɓa shi ,
Alhaji mai tasa yace
"Ƙarki damu ba abinda za su yi mai mu yau kin gama yi mana komai wallahi kin biyamu kina ga har jaridon kasar waje anɗora al'umma ƙasar laimon basa son dan takarar shugaban ƙasa ,
Tuni wani wayo ya zowa rufaida tace
"Saiki bani kuɗin in ajjiye miki kafin ki koma normal ko?,
Shiru tayi tace
"Ki saiwa su kahu abinci ki dinga bashi kuɗin cefane ko Allah zai temaka ya bar bara har kaya ki siya musu sannan ki faɗa musu ina lafiya ƙarya damu rabi zan baki sai in ruƙe rabi a hannu na har gida ki siyamini ,
murmushin cimma nasara tayi tace
"Okay ba matsala ,
Sannan dubu ɗari ki ɗauka naki ne
Bayan an sun bawa binta makafa
Wannan kenan
Kahu binta ce ta aiko ni
Kallon hadarin kaji yayi mata yace
Ina jinki bintar da ake cewa an kamata yau ƙwana na ɗaya ina neman ta
kahu binta tana lafiya qalau tace ma in baka dubu hamsin
Keee rufaida bana son hulaƙanci
Wallahi kahu jaka ta buɗe ta ɗauko kudi ta bashi
Buɗa yayi yace
Kuɗin aure ya samu
To ni kahu na tafi
Uhmm ke gaida babarki
Banza tayi mai ta fita domin miliyan ukku binta ta bata tayi take domin har mota ta siya wani gu ta tsaya inda tayi danne danne a waya tace
nazo ta kashe wayar wani koɗaddan mutumine ya fito yace
Hajjaju iƙon Allah gani an samo gida fa
Glass ta ɗaga tace
"ka samo gidan ?,
washe baki yayi yace
"Na samo amma dubu ɗari biyu,
Yauwa hayar wata zan kama
"Okay ki bada dubu dari kawe ,
Okay muje Ka nunamin
Wanna kenan
Baffa wata alfarma nake son nema
Shiru yayi yace
"Ina jinka Allah isa bata fi ƙarfina ba ,
ƙasa yayi da kansa domin yana ganin Baffa ba lallai ya amince ba da bukatar sa yace
"Bani da wata hanya da zan ƙuntatawa binta sai ta in aure ta in hulaƙanta ta ina ganin zan iya hucewa,
Baffa yace
"Kai ka rasa wazaka aura sai wannan banzar yarinyar zaka jawowa zuri'ar mu abin faɗa mu'azzam sake wata alfarmar ,
Muzamfar yace
"Baffa ka dubu yar da ta kunya tashi a gaban jama'a bashi da hanyar a zai a zabtar da rayuwar ta sai ta wannan ka duba munyi nasara a primary election muna saka ranci tasan sirrin su me tasa sun ɓoye abubuwa da dama ka duba ƙisan mahaifinsa da akai ana zargin suna da sa hannu fa kaga binki can mu zai zamo cikin sauki fa ,
Tambas kunyi tunani me kyau a