Showing 6001 words to 9000 words out of 23415 words
abubuwa da yawa wadanda a da ba haka suke ba.
Wato sai da Ibrahim ya zo ne da ‘yar mu’amalarsu ta tsahon lokacin nan ta soma rarrabe abubuwa. Ta fahimci ta so Khalipha so ba irin wannan da take yi a yanzu ba. So ne na rama halacci ga wanda ya yi maka alheri.
So ne wanda ba ta taba jin tana sha’awar hada jiki da Khalipha ba, zuciyarta ba ta taba rikicewa don ta ga Khalipha ba, ko don ya kalle ta. Amma shi wannan (Ya Himu) ….... ??? Ta girgiza kai.
Ba za ta iya fassara abubuwan da take ji a zuciya da gangar jikinta a kansa ba. Shine ke gigitata, shine ko magana ya yi mata ko ina a jikinta sai ya amsa. Shine bacin ransa ke kassarata ya sanyata kasa yin komai including barci da cin abinci dolen dan adam.
Shine mutum na farko da ya rungumeta ya hada da jikinsa da nata ya zuba mata wasu chemicals cikin bakinta da sassan jikinta gaba daya, da suka karkashe kwayoyin son Khalipha da birbishinsu daga kowane sako da kowanne lungu da kusurwa na jiki da zuciyarta.
Suka dasa wata bishiyar, wadda ta yi sauri ta fidda rassa da korran ganyayyaki suka yi girman da suka rufe kofar zuciyarta ruf, daga tunanin kowanne Da namiji cikin dan lokaci kadan, suka shimfida tasu katuwar dardumar suka zauna suka baje, suka yi kane-kane suka kankane ko ina, suka yi babakere a kowanne angle. (Kusurwa).
Wannan shine matsayin Ya Himun a yanzu da ba za ta iya fassara masa ba. Ba ta san kuma wata hanya da za ta bi ta nuna masa hakan ba. Ta yarda ya ci gaba da zargin nata da tone-tonen nasa in sha Allahu ta daina damuwa, in ba haka ba Himun so yake ya tarwatsa mata zuciya.
Sai ta soma nemawa kanta abin debe kewa don ta raba kanta da damuwa da fitinar Ibrahim, kawai sai ta dauko biro da exercise book ta ce
“Bari in fara RUBUTU!”
Sunan farko da ya fado mata a zuciyarta shine, bari in sawa littafin suna RAYUWAR RAYHANAH! Bari in rubuta labarin rayuwata tun daga kauye zuwa birni. Bari in bawa ‘yan’uwana mata da masu irin lalurata labarina ko sa sanyawa zuciyarsu hope da salama… (kada su fidda rai da rahamar Ubangiji (waraka) domin shine mai sanya cuta mai kuma yayeta a sanda ya so.
Babu wata cuta da aka saukar a bayan kasa ba tareda an saukar da ita tareda maganinta ba. Cuta lokaci daya take shiga, amma waraka sai lokacin da Allah YA so. Duk kudin ka duk mulkin ka, lafiya ta Allah ce.
Rai dai, baya rabuwa da rabo, saidai idan ya kare!
Cikin littafin nan ba zan manta da mutum biyu masu muhimmanci ga rayuwata ba. (DADDY) Dacta Mansur Balarabe Takai da Abdullahi Mansur Takai (YAYA KHALIPHA…..) ba zan manta da IYA BILKI ba, da ADO da ya yi sanadiyyar da na fito daga kauye har a yau na samu alfarmar zamantowa barin rayuwar YA HIMU na mallakeshi a matsayin MIJI NA.
Really it’s a blessing….. a mysterious miracle ba isa ta ce ba dabara ta ba......!!!
Watakila idan na rubuta yadda nake son YA HIMU zai fi fahimta ya yarda dani ya daina zargina a kan Yaya Khalipha........
Ya daina azabtar dani da fushinsa, wanda ya fi zafin bulala a dukkan jikina….......
Ba zan manta da Jawahir ba…. Ita ma MAMI ba zan taba mantawa da ita ba. Na yi mata uzuri sau (70) a bisa yadda rabuwar mu ta kasance, domin a da, ba haka take ba…. “
Haka ta yi ta rubutu tana tsiyayar da ruwan biro. Sallah da wanka, shan tea, cake da juice dake cikin firij a kicin dinsu kadai ke tada ita tsawon kwana uku.
Ta tattara Ibrahim da iyayen cefanensa ta watsar, ko tattasai daya ba ta taba ba. Daga baya ta fahimci ya samu kuku da mai gyaran gida duka Turawan Ohio ne. Taji yana kiransa Benjamin.
Idan ya gama girkin yana aje mata a dining ya kuma danna mata intercom ya sanar da ita, ‘to’ kawai take cewa, amma yadda ya aje haka yake daukar abinsa.
Ibrahim ya soma damuwa, me yarinyar nan take yi a daki tsayin kwana hudu ba ci ba sha? Kada fa yaje wani abu ya sameta, ga shi ta garkame kofa da mukulli ta ki cire shi daga jikin kofar.
Wai ita ma nan fushi ta yi kenan? Ban da ya damu da rashin cin abincin ta Allah sai dai ta yi ta gaji ta fito ko sati daya ne.
Dawowarsa kenan daga asibitinsu ko farar rigar likitocin dake jikinsa da abin wuyan sa bai cire ba ya doso dakin nata, da karfi yake bugawa sosai yana fadin
"Ba za ki bude ba Rayhanah?"
Banza ta yi da shi ta ci gaba da rubutunta. Tana fadi cikin ranta,
"Idan ka balla kofar ai taka ce ni ina ruwana?".
Bugun duniya Ibrahim ya yi amaryar ta ki budewa, har hannayensa sun fara zafi. sai ya juya ya nemo sikundireba da wuka ya zo yana kwance kofar. Ita dai ta ji dan sukur-sukur amma ba ta kawowa ranta kofar yake kwancewa ba.
Ibraheem so ya yi ya bata bahagon mari hagu da dama, amma a yadda ya risketan bisa study table tana ta rubutu sanye da belted- waist –shirt din da ya fara ganinta da ita a singapore, ta yiwa gashin kanta tufka mai kauri guda biyu ta makalesu da farin dutse (bead) ta zama kamar wani fure da mutum zai so daukewa ya gudu ko ba’a bashi ba, sai ya daskare a tsaye.
Rayhanah ta ji ya kwance kofar ya kuma shigo, amma juyowa wannan ba ta yi ba. Ya tabbatar ba za ta kalle shi ba, ba za ta yi mishi magana ba.
Sai ya tabbatar lallai fushin nata na gaske ne. Wace irin miskilar mata Allah ya hada shi da ita haka!
Allah sarki Doctor I.M Takai, komi nasa kwancewa ya yi ya kasa marin da ya shigo da niyyar yi, ya jingina da kofar sakamakon kafafunsa da suka ce; ba za su iya daukar nauyin gangar jikinsa ba.
"Rayhanah!"
Ya fada a hankali cikin kwantaccen sauti da tausasawa mai nuna amsar laifi. Amma ba ta juyo ba. Rubutu kawai take ta yi kamar SUMAYYAH TAKORI.
A lokacin ne kuma hawayen da suka cika mata ido suka mirgino a kan takardunta..... ta zari tissue guda daya tana tsane su da hannun dama tana ci gaba da rubutunta da hannun hagun (lefter) ce.
Ya sake kira, wannan karon da rawar murya
"Rayhanah….. Rayhanah...... Rayhanah, am your husband…… kin zabi azabar Allah ta tabbata a kanki ta hanyar wulakantani………..???”
Da sauri ta dago fuskarta jike da hawaye ta dube shi. Sun dade suna kallon juna kafin Ibrahim yayo tattaki ya zo dan tebirin nata ya rungumeta gabadaya ta baya, ya rufe idonsa sosai yana ajiyar zuciya kafin ya bude idonsa a kan takardun nata.
Hawayen da suka jika mata fuska, da kuma saukar su a kan katoton exercise book din, suna jika shi, da kuma rungumar da Ibrahim yayi mata daga bayanta bai hanata ci gaba da yin rubutun da take yi ba, don gudun kada ta manta. Duk da cewa ya dora mata nauyinsa kadan. Idona akan takardun nata. Dai-dai sanda take rubuta;
“.......he didn’t trust me anymore........
Yana referring kowanne motion na zuciyata a kansa da KARYA… Bayan kuma sau tari tsoron kar ya ce na yi KARYAR yake kidima ni in yi masa shiru. Idan ni munafuka ce don ina son YAYA KHALIPHA, nayi zaton an halicci zuciya ne da soyayyar mai kyautata mata? Shi da yake sanya zargi a cikin AURE ya ya sunan sa.......???????
Fizge littafin ya yi ya keta shi gida biyu…. Bude baki ta yi cikin takaici, haushi da tsoro duka a lokaci daya, ta kuma mike tsaye da nufin fita ta bar mishi dakin tun da wuri, sabida ganin wani irin temper da ya samu kansa a ciki, sai ya fizgo hannunta da azama ta fado jikinsa. Shima bashi da kwarin, don haka gadon suka fada baki daya kamar jikakkun tsummokara.
Sai da ya tabbatar ya kanainayeta ya boyeta sosai ajikinsa, ya hanata yin koda kwakkwaran motsi don ta kwaci kanta, ya hanata yin kukan ta hanyar rufe bakinsa da nata. Kissing din da yake gudanarwa ga RAYHANAH zazzafa ne sosai, shi kansa bai san zai iya yinsu ba in real life ga kowacce diya mace a duniya saidai cikin kintace (imaginations).
Domin sumbace dake wanzuwa kadai a bisa umarnin zuciya da jagorancin so da kauna da kuma bukatar gangar jiki na miji ga matar da yake mutuwar so..... dying for her......!!!
Rayhanah ta rasa inda za ta sa kanta da sabon al’amarin da ya tunkaro ta a yau. Har sai da GIRMA ya risketa. Girman da take zaton shekaru sune shi, ashe basu bane. Girman diya mace daban ne.
A yau ta tabbatar ta bi sahun sauran mata, sai dai nata GIRMAN da wahalar da ta ci kafin ta same shi daban ne da na sauran mata.
Domin nata mijin ko a cikin MAZA sunansa MAZAJE….. ya kuma nuna mata bambancin sa da sauran maza….. ta hanyar sauke mata gaba dayan kauna da soyayyar shekara da shekaru da ya adanawa matarsa. Da shi kansa baisan wacece ba. Wanda ke nufin, ita din, ita tayi nasarar mallakar gurbin UWAR IYALIN.
Ko da za a karo wata daga baya, to ba za ta samu komai ba, sai burbushi ko ragowar IBRAHEEM MANSUR TAKAI (leftover). In ma akwai burbushin da ragowar kenan. Tayi amanna da cewa Ibraheem ya mallaka mata zuciya da gangar jikinsa gaba daya.
Ko da ya samu nutsuwa bai rabata da katafaren kirjinsa ba, domin shi kansa ya san ba karamar azaba ya gana mata ba. Sannan ya ki bada damar ta yi kuka, a doke ka a hanaka kuka!
Shi kansa ya san bai bi a hankali ba don shima al’amarin sabo ne a gareshi. Wanda ya jima yana tsimayen ranar zuwansa, ya sha kissima a yadda zai zo, da wadda zata amsheshi, would she be fresh on it kamar shi? Wani abu ne da ya fi karfinsa, ya fi karfin duk yadda ya zace shi.
Ya tabbata Rayhanah is his first luv..… ya so ta tun tana ‘yar Takai…. Ya so ta a sanda Daddy ya maida ta ‘yarsa….. ya so ta a sanda Abida ke wulakantata ta yadda har yau babu alaka mai dadi tsakaninsa da Abida…
Haka ya so ta a ‘yar Baba Dacta mai hearing-aid da har yau bai san ina ya tafi ba. Ya so ta son da ya tabbata Khalipha bai yi mata shi ba, domin daga dukkan alamu tausayi, jihadi da imani sune jigon soyayyar Khalipha.
Shi tashi babu wannan a cikinta, bai taba jin tausayinta ba daidai da rana daya, wai don ta rasa wani sashe na halittar dan Adam. Ya yarda babu nakasashshe sai kasashshe. You are only disabled if you truely believed you are....kuma da lalurar da Allah Ya dora matan ta kwarara zuciyarta ta kowanne bangare bata kasa ba.
As a medical student as he is a lokacin, ya kan fada a ransa dole ta gode Allah ma tana using hearing aid din yayi mata rana, wani duk gatansa, duk kudin sa bai samu alfarmar da (hearing aid) din da zai yi masa amfani ba.
[12/29/2019, 13:31] Takori: Otosclerosis muguwar cuta ce da sai mai tsananin sa’a zai samu kubuta daga gareta. Don haka ya yi hasashen, Rayhanah na daga cikin ‘ya’ya masu sa’a a rayuwarsu, kuma masu baiwa ta daban. Gaba daya halayenta da dabi’unta ba irin na sauran mata bane.
Cikin kwanakin da suka yi tare ne ya tantance hakan, sannan masani ne a ilimin psychology matuka. Cikin kwanakin da ya yi tare da ita zai iya dorar da wasu halayen ta wadanda suka taimaka kwarai wajen ribato zuciyarsa da ilahirin gangar jikinsa zuwa gareta, kadan daga ciki sune.
Ba ta yin kwalliya ko kyale-kyale wai don ta burge shi. Tana da tsaftarta a kan kashin kanta.
Tsaftarta ta kulli-yaumin ce; ba don shi takeyi ba don haka ta riga tazame mata jiki ta kama jikinta ko tayi ko bata yi ba she's luscious and sexy....
Tsaftarta kuma ba ta fuska da shafe-shafe ba ce ko tsadaddun sittiru, a’a, inner tsafta ce.
Manyan halayen da ya karanta daga gareta sune ‘pure heart’ wato tsaftar zuciya, da amsar kuskurenta daka nusashsheta, mai saurin yin afuwa da rashin kullaci ga kowanne bil adama, ko da kuwa ya bata mata uziri take yi masa da….
“Ai a baya ya yi min kaza….. ya yi min kaza…. Don yanzu ranshi ya baci ya yi min wannan ba zan kullace shi ba.”
Sannan da rashin manta wanda duk ya yi mata alheri ko da za a yi mata mummunar fassara a kansa. A misali, Yaya Khalipha. Idan ta bika ta lallami don ka fahimceta ka ki, to za ta kangare maka ka kasa sarrafata.
Sannan rashin yawan maganarta na da alaka da kasa fitowa fili ta fadi hakikanin abin da ke ranta.
Ita kuma inner tsafta, abin da Ibraheem ke nufi da ita shine, ma’abota wannan tsaftar a bandakin su take (toilet), a nan ne za ki gane abin da yake nufi ba a kan mudubinsu ko cikin kwabar kayansu ba.
Sannan they live a moderate life, yet a modest. Basu yarda suyi ta narkar da kudinsu wajen sayen lesussuka masu tsada da atamfofi masu tsada don su kece raini, da mayukan sauya launin fata masu tsadar tashin hankali don su zama kyawawan dole ba.
Sun yarda da yadda Allah ya halicce su and they will be beautifull as such......amma za su kashe ko nawa wajen sayen kayan tsaftar jikinsu da bandaki (toiletries) da turaren da za su shafa a jikinsu da wanda za su fesa a tufafinsu da muhallinsu.
Kayan wankan da take amfani da shi mai alfarma ne sannan wanda ta tabbatar (dermatologically tested) ne will in no way or the other change her skin colour. Sabulan wanke bakinta (maclean) shima na daban ne mai lasar manyan kudi, haka (mouth wash) da burshinta duka masu karfin kashe plaque ne accepted and approved by dentists.
Mai inner tsafta, har ila yau ba ta barin tsiron gashi ko kadan a jikinta, banda na kai da gira, domin akwai shower shave da wanka kawai za ta yi da shi kowanne tsiron gashi dake jikinta ya bi rariya.
Rayhanah hakoranta kamar kankara suke don haske, domin a kalla tana wanke su sau uku a rana, kafin karin kumallo, bayan lunch da lokacin kwanciya barci.
Tana kurkure su da mouthwashes (cavity fighters) masu karfi. In bata da halinsu, to bata wasa da yin siwaak da shan lipton data dafashi ya jiku da kanimfari.
Mai inner tsafta ba ta jin wahalar sayen turare mai kyau mai sanyin kamshi ba lallai sai mai tsada ba a’ah, daidai karfinta, domin mace wadda ta amsa sunan mace sai da turare, a jiki da muhalli, ba kawai na fesawa a suttura tana barbada kamshi don za ta fita ba, mala’ikun Rahma na rubuta mata zunubin yin zina.
Ita ko yaushe ka rabeta ma in har ba ka sunsunata ba, ko ta kusance ka sosai ba za ka ji tashin kamshin ba, sannan ya fi yawa a kayan barcinta.
Duk sanda maigidanta ya kusanceta baya iya jurewa sai ya raba jikinshi da nata, domin ya samu nasa kason na ni’imar kamshin fatar jikinta da kamshin bakinta, ya haska idonshi da hasken hakoranta.
Ya fahimci Rayhanah tana amfani da fararen kayan ciki ne (inner wears) kuma kulawar da take basu kullum ba ta bari su canja launi, domin ba sai sun nuna datti take wanke su ba, in har ta san ta saka, ta wuni ta kwana dasu, to lokacin wankanta da safe za ta wanke su da omo da bleach ta shanyasu.
Inda duk Ibrahim ya sa kai a jikinta baya iya mai da numfashinsa dai-dai ba tare da ya rabi ni’imar da Allah ya zuba a jikinta ba.
Ba ta ciye-ciyen kayan mata na shirme da lakatawa da mannawa da turawa, sai dai ta ci wadanda za su kara mata lafiya. Wadanda addini ya yarda su, kimiyyar lafiya ta yi amanna dasu.
A fannin sittiru ba irin atamfar da ba ta daurawa in dai kalarta za ta amshi bakar fatarta ta haskakata, ba sai ta dubunnan nairori ba. Ta nairorin ma sau dubu sai ta zabi mai rangwamen