Showing 18001 words to 21000 words out of 23415 words
balle a kan uwar da ta haife shi.
Tukunna ma, shi shekarunsa nawa baya tare da su? Ya san irin rayuwar da suka yi cikin tsayin shekarun ne?
Da wannan tunanin ya mika hannu ya rungumo matarsa, ya kwantar da kai a kafadunta, zuciyarshi cike da nadamar saurin kai hannunshi ga lafiyar jikin wadda ta ba shi farin cikin rayuwar da bai taba tsintar kansa a ciki ba. A kuma ranar da ta ba shi farin cikin ko hutawa ba ta yi ba.
Jinta gaba daya jikin Ibrahim kamshin jikinsa na ratsata sai ta idasa narkewa, hawayen suka kara shimfidowa a kan kundukukinta.
“Ki yafe ni Rayhanah, kin yafe min Rayhanah?”
Ta daga kai….
“A’a, wannan bai gamsar dani ba, bude bakinki ki gaya mini….”
Ya fada a lokacin da ya dago habarta. Sai ya soma dauke hawayen da harshensa. Runtse ido ta yi, amma jin Ibrahim na neman zafafa al’amarin sai ta kwace.
“Malam yi a hankali, dinkin likita ce”.
Ibrahim yasa dariya ya sake kamo ta.
“Ba sai a sake dinkewa ba???”
Ya fada da muryar da ta gaya mishi hakan shekaru biyu a baya. A take ta tuno da first night dinsu. Ta juya masa keya cikin jin kunya tana jijjiga babyn.
Ibrahim ya sake binta ya ce,
“Ko kwaryar ba masaka tsinke ne inda za a sake soka allurar?”
‘Yar ta aje cikin ‘yar katifarta, ta dau filo ta danne shi tana bugu. Sai ya hantsilota ya koma samanta ya mamayeta yadda ko motsi ba za ta iya ba. Cikin dariya da shaukin bege mai yawa ya ce,
“Wallahi ki bini a hankali, in ba haka ba wannan dinkin farkashi zan yi yanzu”.
Ganin ya soma zarce Zaria ta soma lallashi, wanda ba ta san yaushe ta iya ba, har da su dadin baki, kirari da bambadanci.
“Haba dan Ibro na…. angon Rayhanah Baban Asma’u….. dan gaban goshin Baba Dacta.....likitan likitocin kodar Rayhanah......” Ibrahim dariya yayi yace
“har kin tunomin da Ado, oh su Rahane da yanzu fa anada ‘ya’ya goma” ta shaka tayi fus, kamar alkubus. A ranta tace “yanzunnan zan rama”.
“Ai dai duk da kaki bani shayin da Baba Dacta yace ka bani, ka turo inyamuri ya bani, kuma arzikin kalma ko ta sannu ce ban taba samu ba, na ganka kana mazari kana tsuma kana gwada ‘yar kashi da Adon don yana kokarin shimfidar ni.....”
Inda abin da ya tsana a tayar ko a tuna masa a duniya to wannan zancen ne. Ai kuwa a take ya koma serious. Fuskarsa tayi kicin-kicin kamar ba shi yake rahar da yake yi yanzun ba.
“Rayhanah zamu bata, uwar Asma’u zamu bata……”
“Na tuba….. na bi Allah na bika Baban Asma’u. I’m in nostalgia (ina cikin begen gida)”.
“Nima gidan nake so Rayhanah, amma bari Mamina ta yi dan kwari zuwa watanni biyar haka”.
Har cikin ranta ta gamsu da hakan.
******
WELCOME TO THE WORLD ASMA’U IBRAHEEM MANSUR
Rubutun da za ka fara cin karo da shi kenan a kasan tangamemen hoton da za ka fara cin karo da shi da zarar ka shigo falon nasu, mai kama da fadar wani gwamnan a Nigeria.
Uwar da Uban ne cikin ‘Native Hausa Attire (shadda da Atamfa) shi dinkin Mohammed na shudiyar shadda sheraton da hula Damanga shudiya mai duhu, sun sa buleliyar ‘yar tasu a tsakaninsu kowa ya rungumo bari daya, wadda ta washe ta yi haske ta zama kamar ‘yar Sudanese, dukkansu bakinsu a washe, fararen hakoransu a warwaje kamar masu tallan colgate. Itama ‘yar bakinta kamar ya tsage da dariya, cleft da beauty point din Mami da Ibrahim duk sun lotsa.
Hoto ne wanda Ibrahim ya turawa Baba Dacta copy dinsa cikin wayarsa, ta hanyar BlackBerry Messenger. A lokacin yana kan hanyar komawa gida daga wajen aiki.
Ya ji shigowar hoton amma bai bude ba, sai da ya shiga get Mal. Dahiru ya rufe ya adana motar a rumfar adana motocinsu.
Ya dauko kwat dinsa da bakar jakarsa tukunna ya bude. Sai da ya jingina da motar kada kafafunshi su kada shi. Kwallar farin ciki ta tsiyayo daga idanun Dr. Mansur. Ya tsura musu ido dukkansu ukun kamar ya hadiyesu don kauna.
Wannan rana yake jira, ya maidawa Asma’u martanin bakin cikin da ta kunsa masa shekaru uku da suka wuce. Ai bai shiga gidan ba, mota ya koma duk da gajiyar dake jikinsa ya sake fitowa ya nufi Arewa Studio dake Tarauni ya basu suyi mishi window size guda biyar zai dawo gobe ya amsa, bayan ya biyasu.
Wani abin mamaki a washegari bayan ya karbo hoton sai ya dasa a falonsu, daya a bed-room dinsa, daya a dakin su Abida, a lokacin duk basa nan. Jawahir tana Hurghada, Mimtaz ta sake haihuwar da namiji again. Mami na office, Abida da Aziza suna makaranta.
Bayan ya kakkafa enlargements din ya yi tafiyarsa office dinsa da nasa copy din da zai sa a office dinsa, zuciyarsa kal kamar madara. Duk inda ya gitta cikin ward din su an san Dr. Takai yau yana cikin farin ciki. Sai raha yake yi da likitocin da ke karkashinsa da marasa lafiyansa.
Dr. Kofar Mata ya kasa shiru ya ce, “Wai Dr. Mansur hala amarya ka yiwa Dr. Ma’u?”
Bakin Dr. Mansur har kunne ya ce, “Eh, kamar ka sani kuwa wallahi Dr. K/Mata, gata”.
Ya mika masa hoton da ya yi saving a fuskar wayarsa.
“Zo muje office ka ga amaryar tawa sosai”.
Ai kuwa ya mike ya bishi office ya nuna masa tangamemen hoton. Dr. K/Mata kamar yau bai ci abinci ba, haka ya bude baki yana ta kallon hoton.
Ya ce,
“Wannan kamar Ibraheem, ‘yar kamar Asma’u, matar ce ban sani ba”.
Murmushi ya yi ya ce,
“Ita ma ‘yata ce, ni nake rikon ta”.
Dr. K/Mata ya ce, “Masha Allahu, Allah ya albarkaci little Asma’u ya rayata cikin tafarkin Islama, amma ban san sanda Ibraheem ya yi aure ba”.
“Auren ne ya zo a kurace, amma abu wajen shekara uku”.
Haka suka yi ta zancen Ibrahim da iyalinsa, suka manta da patients dinsu.
A take Daddy ya turawa Hakimi da Haj. Karima da Inna Juma, wadda ba ta yarda ta zauna a Farm Center ita kadai ba, tana gidan Hakimi, can aka ba ta daki take zaune. A take kuwa suka hau kiran wayar Dacta suna neman karin bayani, baki har kunne Daddyn ke amsa musu.
Tafi-tafi zance ya yadu cikin gidan Hakimi da wajensa Ibrahim matarshi ta haihu, ‘ya kamar Asma’u. Wannan kadai ya isheta aya, idan fa har tana da hankalin tsinkayen hakan kenan.
Abida da Aziza ne suka fara dawowa gidan a gajiye tubis, suka baje a falo suka kure A.C. Kamar an ce da Aziza daga kanki ta yi arba da tangamemen hoton, ta hau zubawa Abida duka a cinya.
“Yaya Abida….. Yaya Abida ....sister…. Sister kin ga… kin ga”.
Abida ta juyo a fusace domin har ta samu barcin gajiya ya sureta Aziza ta katse mata. Tana niyyar mangare Azizah sai ta ji tana fadin.
“Kamar Ya Himu da RAYHANAH da ‘Cute Baby!”.
Abida ta daga ido ta kalli side din. Ai da sauri suka mike dukkaninsu suka runtuma ga hoton suna kallo sosai. Iyakar rikicewa da firgita Abida ta yi.
A take ta ja waya ta kira Mami.
“Mami ki taho gida maza – maza yanzu ki ga wani abin mamaki”.
“Mene ne?”
Ta fada da dan karfi.
“Ke dai ki taho Mami za ki sha mamaki, idan fa har baki suma ba”.
Ta kashe wayar ta kyale Mami.
Dr. Asma’u ta dade tana juya kan wayarta a hannunta. Ita ba ta son irin wannan sam, a ce ta yi abu, amma ba a gaya mata dalilin yin shi ba. Tana da ayyuka masu yawa a gabanta amma dole ta ture ta mike don Abida ba ta taba yi mata haka ba.
Abida jikinta bari yake, saboda kaduwa da razana. Azizah tsalle take, tsallen murna tana fadin
“A perfect match! Miskila, sai miskili dan’uwanta. Daddy the matchmaker! What a beautiful daughter I’ve….. wayyo ni dadi kashe ni.
Come soon baby Asma’u in goya ki in miki rawa in cillaki in café ki”.
Ta isa ga hoton ta sumbaci yarinyar daidai lokacin da Mamin ta fado falon. Abida ta janyota ta isar da ita ga hoton tana fadin
“Mami dubi rainin hankalin da aka miki, har aure Ya Himu ya yi da tsintacciyar yarinyar nan har sun haihu baki sani ba saboda an raina ki…..”
Ba ta kai ga rufe bakinta ba Daddy ya fito daga dakinshi yana ba ta amsa da cewa.
“An raina ta ko ta raina kanta annamimiya? Ba tun yau na kwana da sanin mugun halinki ba, to ki sani, ita wannan da kike kira tsintacciyar mage ta zama jininki, dolenki, uwar ‘ya’yanki ko ki mutu, ko ki yi rai ba abin da zai sameta da ikon Allah, wai don kun wulakanta ta.
Babu yadda za ku yi da ita, sai dai ku ci gaba da raina kanku, domin KAINUWA ce dashen Allah, kuma murucin kan dutse baka fito ba sai da ka shirya!!!
Idan kuna da hankali wannan ya isheku ishara. An gaya muku ana yiwa Allah shisshigi ne cikin al’amarinsa?”
Ya juya ya shige dakinsa.
Abida ta yi tsumu-tsumu, ita kuwa Dr. Asma’u sai ta zube a doguwar kujerar falon tana kuka, kukan da dukkansu basu san dalilin da yasa take yinsa ba, na bakin ciki ne ko na nadama? Allah kadai ya san me ke a zuciyar bayinsa.
Cikin zuciyarta Allah ya isa take wa Dr. Halima da ta goga mata bakin fenti a idanuwan wanda ya fi kowa sonta a duniya, ya yarda da ita, ya ba ta amanar gidansa. Ya yi mata kyakkyawar shaida a zuciya da bakinsa na uwargida ta gari. Yanzu wane bayani za ta yiwa Daddy ya saurare ta?
Babban bakin cikin Mami kullacin da Dacta Mansur ya yi mata a kan ikon da ta nuna a kan Khalipha da cewa da ya yi ta nuna masa yau ba shi ya haifi Khalipha ba….. tabbas ta dade da manta wannan tunda shi din bai taba nuna wata kafa da za a bambance ko a tuno hakan tsakanin Himu da Khalipha ba.
Kenan in da halacci bai cancanci butulci da rashin biyayyar da ta saka masa dasu ba.
A lokacin da babban mutum irin Dr. Mansur yake cikin fushi, dosar shi da ba da hakuri da karbar kuskure kamar izawa wuta fetir ne. don haka Mami tasa mishi ido har tsayin kwana uku.
Sai dai fa kullum cikin dare sai ta fito falo ta kurawa hoton ido tana shafa fuskar yarinyar, wadda Allah ya kinkimo wata gundumemiyar kaunar yarinyar ya saka mata a zuci.
Ta kan dade tana kallon Rayhanah wadda babu abin da ya sauya a halittarta sai santsin fata.
Da ka ganta ka ga matashiyar Bahaushiya ‘yar kimanin shekaru ashirin da shida, amma yanayin jikinta da canzawar fatar ta sai ka yi zaton daga kwai aka barota. Ta yi sumul ta yi mulmul har da wata ‘yar kiba ta samun perfection and contentment in life.
Shi kuma angon nata da ganinshi ka ga bakin Bature, kamanninshi da mahaifinshi sun sake fitowa sarari, da ka gansu za ka fahimci cewa komai na rayuwa ya yi musu dai-dai kamar yadda kowanne dan Adam ke burin samu.
Lallai Dacta Mansur ta yarda ba karamin hatsabibin dan boko bane. Wato ta hana da Khalipha tunda ta nuna ba nashi bane, sai ya yi mata lambo ta gama shuka tsiyarta, sannan ya fito mata ta bayan gida. Ta inda bata taba zata ba.
Ta tabbata ba ta isa in Ibrahim ne ta yi masa abin da ta yiwa Khalipha ba, don shi ba shi da hakuri ko kankani. Idan yana son abu fa kawai yana son shi, haka in bai so, jan ido da lallashi basu isa su sanya ya so abin nan ba.
Yau dai ga Rayhanah da take kora don tayi nisa da zuri’arta ta zama barin rayuwar Ibraheem. Da mafi soyawa a zuciyarta, ta hada zuri’ar da ba ta so din da ita, kuma Allah ya sanya mata so da kaunar zuri’ar, kamar ko ma fiye da yadda take son Ibrahim.
Dama an ce wai abin cikin kwai ya fi kwan dadi. Gaskiyar Dr. Mansur ne da ya ce ba a yiwa Allah shisshigi cikin al’amarinsa.
Dr. Asma’u ta yi nadama matuka, nadama irin wadda Ubangiji (S.W.T) ya yi alkawarin karbarta, wato nadama da tabbacin da bawa ya yi da zuciyarsa na cewa ba zaya kuma komawa izuwa zunubin ba.
*****
[1/1, 10:27] Takori: Karfe goma dai dai na safiyar litinin jirgin KLM ya sauke Dr. Ibrahim Mansur da iyalansa a filin jirgin saman Abuja, Khalipha ne yaje ya taho dasu daga filin jirgi, duk da cewa suma dawowarsu kenan a daren jiya daga Hurghada inda yaje ya taho da Mimtaz da Jawahir, wadanda suka kwashe watanni biyu a Egypt a dalilin haihuwar da Mimtaz ta yi ya kai su can suka yi biki. Khalipha bai yi kasa a gwiwa ba wajen radawa second born dinsa suna Ibrahim Khaleel.
Yau sai ga Rayhana da Yaya Khalipha, bayan gushewar a kalla shekaru uku da doriya. Ta kasa hada ido da Yaya Khalipha wanda ke rungume da Asma’u a kirjinsa. Shima Ibrahim rungume da takwaransa, kowanne ya kasa ajiye dan ya yi tukin motar.
Dukkansu suna gaba, ita da Mimtaz suna baya. Jefi-jefi Rayhanah kan saci kallon Yaya Khalipha, ya yi kiba ‘yar kadan ta hutu, ya kara murjewa. Da ganinshi za ka fahimci cikin kwanciyar hankalinsa yake, sannan likkafa ta yi gaba ko daga irin motar da ya dauko su a ciki da Balarabiyar da ya aje mai neman kashewa mutum ido don haske da hasken idanu.
Mimtaz ba ta da bakunta ko kadan, sai jan Rayhanah take da hira ta ji Hausa zau kamar (vedan) a dalilin rayuwa da su Jawahir, in ka ji tana Larabci to ita da iyayenta da danginta ne, amma ko Khalipha da Hausa suke magana.
Ta ce, “Yaya Khalipha aniyarka ta bika, ka ce ‘yar Dr. Ibrahim da Rayhanah muni za ta yi, gata nan ta fi duk iyayen kyau da haske”.
Ya ce, “Ai albarkacin sunan Mami ne shi yasa ta dan washe”.
Ya kara duban yarinyar cike da kauna yana fadin,
“Lallai Muhd. Mansur ya yi mata, zuki!” Ya sumbaci ‘yar.
Sai a lokacin ya juya ga Rayhana yana murmushi ya ce,
“Madam kinsha aiki, mun gode fah”.
Tana murmushi ta ce,
“Aikin me Yaya Khalipha?”
Ya mikawa Mimtaz Asma’u ya tada motar ya ce,
“Aikin haifo mana UWA, ba ta barota a komai ba”.
A ranta ta ce,
“Allah yasa kada ta yo halinta”.
Don dai ita har yanzu fargabar haduwa da Mami take, don ba ta san irin tarbar da za ta yi musu ba ita da ‘yarta. Tunda ita ba ‘ya ba ce annoba ce da ake neman guje mata, Allah ya kara manna musu.
Khalipha ya so suyi sati a Abuja su huta ya dan zazzaga dasu su ga sauye-sauyen ci gaba da Nigeria ta samu a Abuja, amma Ibraheem ya ki, ya ce a gobe za su wuce ya matsu da ya ga Mami don ya dade bai jita a waya ba, shi kuma in ya kira a ce da shi a kashe take.
Jawahir ta dawo daga asibiti cikin motar Mimtaz, ta kai Muhd Mansur asibiti ne yana fama da zazzabin sauyin yanayi, domin sun dade a Hurghada sosai har watanni biyu. Tun daga kofar falonsu ta fahimci lallai suna da baki.