Showing 9001 words to 12000 words out of 23415 words
kudi ta barta, in dai kalarta ta amshi fatar jikin ta, saboda sanin sirrin atamfa ajikin matar bahaushe, atamfa ko wacce iri ce kyau take indai a jikin Rahane ne. Kuma ita ce favourite regular attire dinta.
Wannan ita ce, RAYHANAH MATAR IBRAHEEM!!!
Wadda ba kyale-kyale ne ke fizgar hankalin mijinta a kanta ba. Tsafta ce, da gyara. Don ko jambaki, bai taba gani a lebban Rayhanah ba, sai Avon lip Gloss.
A tsayin mintunan da Ibrahim ya diba yana bambance kamanni, halaye da dabi’un matar tasa, sai ya yardarwa kansa cewa wannan ita ce MATAR DA YA KE MAFARKI; mai kyakkyawa kuma sassaukan gayu na hankali da tunani, kuma ‘yar bokon data yiwa boko kyakkyawar fassara, though she's not wealthy but she has a great mind! Ba kamar yadda mata da yawa suka jahilci kalmomin guda biyu ba.
Turawa da larabawa da yawa kudinsu suke sanyawa suna sayen (Zaitun) don su rage hasken fatarsu. Black is beauty! And there's nothing worth respecting like naturalism!!! Fari ba shine kadai kyau ba, balle wanda akasa kudi aka sayo.
Mata da yawa sun gama amincewa cewa yin shampoo (kona gashi) da karin gashi, sanya tsadaddar suttura ta almubazzaranci ko mai zahirantar da tsiraici a wuce ana barbadawa duniya kamshi. A sanya dankwala-dankwalan ‘yan kunnaye, a lambata jambaki shine kwalliya ta wayewa da burgewa…. To ba shi bane a ra’ayin RAYHANAH RASHID TAKAI.
******
Da wannan Ibrahim ya sauke idonshi a kan Rayhanah, sai ya ga ta yi barci tana numfashi cikin nutsuwa, baccin da ba na komai bane face na wahala da azabar da ya gana mata. Shima da ya duba aika-aikar da ya yi mata sai ya ji kwalla ta ciko idanunsa.
Ya kasa sakinta, ya kasa aikata komai a kanshi ko a kanta, yana jarumtakar maida hawayensa amma sun ki hakan, sai da suka mirgina cikin gashin Rayhanah. Ya kankameta sosai.
Sauran abubuwan da yake tattaunawa cikin zuciyarsa na auratayyar da yayi a yau da Rayhanah, kuma al’amari na farko a tsayin rayuwarsa, da matsayin da hakan ya karamata a zuciyar sa, daga shi sai Ubangijinsa suka sani.
Shi da kansa ya fiddo kayan aiki da baka rasa likita da su a gida, don ya tabbata sai ya yi mata stitches, ya ji mata rauni sosai da hakan ya sa shi challenging (kalubalantar) kansa da selfishness (son kai) da rashin tausayi.
Bai san kuma ya zai yi ya yi mata ba tareda ta tashi daga barcin hutun da baya son ya rabata da shi ba. Sai ya maida ta kan sofa dake gefe ya yi mata allurar da ta karawa barcinta nauyi, sannan ne ya yi, ya gyara komai ya canza shimfidar gadon.
Ya yi wanka ya fita dining don ganin abin da Benjamin ya girka. Ya kai hannu ya bubbude dishes din yana gani; Lemon Ricotta, Pancakes with syrup, Quinoa, Poached-eggs, Sliced bacon, Sliced bread with jam. Abinda Benjamin ya shirya musu a dining kenan matsayin karin kumallo.
Yasa murya ya ce,
“Benjamin!”
Daga can kicin Benjamin ya amsa ya fito da hanzarinsa hannunsa rike da wuka da farar albasa katuwa. Ya ce,
“Jeka maza ka yo min farfesun salmon (kifi) easy chicken recipe da omelets ya isa, ina son su in ten minutes”.
Benjamin ya amsa cike da girmamawa ya koma ya fara aikin.
Minti uku ya kara akai daga mintunan da ubangidansa ya ba shi, ya jero a tray cikin ‘yan kananan bowls din karau (tangaran) zai soma jerawa a dining bayan ya kwashe wadancan maigidan nasa ya fito daga corridor din da zai sadaka da dakinsa yana sanye da farar shirt DKNY an rubuta DKNY din da ruwan kasar zare da dogon (brown jeans) ya debi wanka ya sharce gashin nan nasa da kumfar Arganavita. Shaidar sujjadarsa ta fito sosai a karshen goshinsa.
Ga mamakin Benjamin isowa ya yi gareshi da kansa ya karbi katon tray din ya sallame shi. Har sanda ya shiga bedroom din nata da abincin ba ta tashi daga nannauyan barcin da ya tsikara mata allura don ta yi ta yin shi ba.
Shima bai bi ta kan abincin ba computer ya kunna yana ci gaba da hidimar da ta kawo shi ta yanar gizo.
Ba wani abu ne ya kawo shi ba face tattara ajiyarsa da ke manyan bankunan Amurka daban-daban irin su J.P Morgan Chase, HSBC, U.S Bancorp, Morgan Stenly, Wells Fargo Don komawa gida kwata-kwata.
Gidan da yake ciki wanda mallakinsa ne kadai zai bari a Amurka ba zai sayar ba.
Jefi-jefi ya kan daga kai ya kallo Rayhanah wadda ta soma gyara kwanciya, sai ya sunkuya ya ci gaba da abin da yake yi. Yau jin kansa yake sakayau, kamar an sake haifo shi duniyar ne, new IBRHEEM! Babu nauyin komai cikin jikinsa da kwakwalwarsa har ma da zuciyarsa, sai abubuwan da zai loda musu yanzu. Duk wasu tensions sun fita.
Wanda ya tabbatarwa kansa ba komai ne ya haifar masa da wannan nutsuwar ba face rahamar dake cikin aure, da tarin lada da gafarar da Ubangiji ya sanya a cikinsa.
Daga lokacin da ka daura hannu a jikin matarka ta sunnah dukkan alhakin da ka dauka a rayuwarka na zina ko makamancin hakan Ubangiji ya juya shi zuwa abundant reward wanda shi kadai ya san adadinsa.
Juyi ta yi cikin gyara kwanciya kafin ta soma magana cikin gigin barci ne ko na allurar barci ne bai sani ba…..
“Ya Himu….. Ya Himu .... don Allah ka yi hakuri, na tuba na bi Allah na bika….Baba Dacta ka ceceni zai kasheni....!”.
Kalaman da take furtawa kenan wadanda a jiya ya hanata furtawa, sai yanzu suka samu sarari suke sakin kansu cikin magagin barci. Wadanda suka sa Ibrahim Takai, cikin wani hali mai kama da nadama, bai so al’amarin ya zo masa all of a sudden haka ba, amma ba regretting yake yi ba, tunda in a wajen Ubangiji ne baida wani laifi.
Shi Ya ce ku zowa matanku a duk lokacin da kuka so ko da suna a halin nakuda. Matanku gonakinku ne, ku zo musu a duk lokacin da kuka ga dama idan ba haila, ko nifasi suke yi ba.
Yadda bai yi tunanin cutuwarta ba sai na shi biyan bukatar shine abinda yake regretting, to shi kansa bai san yadda zai yi da kansa ba, samartakar, tashen balagar da tuzurancin ya hada duka ya saukewa Rayhanah a lokaci daya. Adadin kaunarka ga matarka, adadin karfin sha’awarka a kanta.
Sai dai ya yarda ya yi laifi, dole ya yi lallashi harma da banbadanci, in ma bai iya ba yanzun nan zai shiga makarantar soyayyah ya koyo. Ture laptop din ya yi, ya mike ya shige cikin bargon nata, ya mika hannu ya janyota gareshi.
Ai sai ta soma kokarin kwacewa tana rokonsa tana magiya cikin kuka, gabadaya ta gama tsorata da shi. Ko ganinsa bata son yi. Karfi yasa sosai ya riketa. Har tasoma gajiya da kokawar ta, jikinta yayi sanyi lakwas.
“Ka taba kashe abin da ka fi so a duniya RAYHANAH???”
Yadda ya yi maganar cikin sanyi, tarin so da kauna da kulawa, sai ta daina kokawar kwatar kan nata.
“Rayhanah idan ka kashe shi kai da wa za ka zauna? Wajen wa za ka je ka sauke son nashi da ya yi maka babakare a zuciya?
Ina rokon Allah ya kasheni ya barki, ki yiwa ‘ya’yana tarbiyya irin taki.
Madallah….. da shigowarki cikin rayuwata….. Maadallah... da Uba irin Babanki Dr. MANSUR. Mai so na da ALHERI..... da dimbin kauna mai yawa agareni. INA SONKI RAYHANAH! INA SONKI RAYHAH!! RAYHANAH I so much love you!!!.”
[12/29/2019, 19:10] Takori: Sai ta daga kai a hankali don ganin daga bakin da wadannan zakakan kalmomin ke fitowa, da babu wanda ya taba gaya mata kwatankwacinsu a zaki da gardi? Tana tababar ya zamo cewa daga bakin Ya Himu ne…. wanda in ya ganta bai iya cin abinci.
Fuskar da ta gani cikin hasken safiyar da ya keto fararen curtains din dakin barcin, ya fi gaban a kirashi Ya Himu.
Cikakken likitan Koda ne Dr. Ibrahim Mansur Balarabe Sardauna, mai matsayin (Nephrology Consultant) a babban asibitin Illinois, ba dan matashin dalibin nan mai girman kai da kwalisa a AKTH da gidan Dacta Mansur ba.
Wannan fuskarsa cike take da gargasa lallausa, da tarin hankalin da shekaru suka taimaka wajen karuwarsa. Idan aka kira shi Dr. Ibrahim Mansur Takai, zai fi dacewa da shi fiye da a kira shi Ya Himu.
Duk da cewa halayen basu canza ba, zuciyarshi ta yi laushin da bata da shi a baya, mijin da ko kyakkyawar surar jikinsa ta kalla kullum, ya ishi zuciyarta ta kasance cike da wadatar zuci, da godiyar Ubangiji. Ta kuma yi alfahari da zamantowarsa barin rayuwarta, kuma uban ‘ya’yanta.
Wadda ta fi kowacce mace a duniya samun alfarmarsa, har kuwa da uwar da ta haife shi sai dai a ba ta matsayinta na UWA a bar neman albarka, amma ba za ta taka wannan matsayin ba.
In haka ne bai kamata ta ji haushi, tsoro ko nuna gazawa a kan hakkinsa da Allah ya rataya a wuyanta ba. Har ta yi sake da wannan damar da Allah ya bata, wasu ‘yan iska a waje su kwace.
Masu iya magana suka ce, wai tsalle daya shi ke jefa mutum rijiya, abin nufi a nan, tun a lokaci na farko ta nuna gazawa wanda hakan zai sa ya yi baya-baya da ita don gudun bacin ranta ko bacin zuciyarta.
Ya soma tunanin hanyar da zai bi ya dinke barakar ta, wadda ba komai ba ce illa ya nemo wata, wadda za ta jurewa jarumtakarsa a auratayya.
Wannan tunanin da Rayhanah ta yi, ba wani ne ya koya mata ba, ba karantawa ta yi ba. Tsinkayen hankali ne kawai (foresight ).
An ce wai idan baka iya kuka ba, to iyayenka ne ba su mutu ba. Baki iya goyo ba saboda yana da wahala kuma zubewar aji ne, to baki haihu bane. Ko kece ‘yar Karuna in dai Bahaushiya ce ke, kuma cikakkiyar ‘yar kasar Nigeria.
Shirun da Rayhanah ta yi, da kukan da ta daina lokaci daya kamar daukewar ruwan sama, shi ya ba Doctor Takai, damar kara mamayarta (Needing for more…....).
Amma ga mamakinsa wannan karon bata nuna razana ba, shi din ne ya tuna da dinkin da ya yi mata ya hakura, amma fa ya kasa hakura da abin da ya fi so daga wadannan ‘luscious lips’ na Rayhanah, shi din ya ci gaba da yi cikin wani irin salo da Rahane ta kasa juyawa baya, lallashi da banbadanci har da hawayen neman afuwa, abinda ya gigita Rayhanah…. Ya Himu ne? (She is still doubting).
Alkawarirrikan da yake daukar mata ta san ba a hayyacinsa yake fadarsu ba, don haka ba ta kama ko daya ba.
Ba ta san lokacin da hannuwanta suka yi fitar bazata ba suka rungume Ibraheem, rungumar da bata taba yiwa wani abu a rayuwarta ba, bayan gawar mahaifinta.
Ga mamakin Ibrahim Rayhanah ta soma taya shi sumbar cikin nata salon mai bin umarnin zuciya da odar gangar jiki. Ta sakar mishi komai, ta yarda in mutuwa za ta yi ta mutun, in dai a kan farin cikin Ibrahim ne.
Shi din ne ya yi jarumtakar cewa,
“A’ah…Rayhanah ”
Yana yin baya-baya da ita kada cin zalin ya yi yawa. Ita kuma cikin kara iza shi take da tana fadin….
“Ba sai a kara dinkewa ba???”
Duk da halin da Ibraheem ke ciki bai fasa yin dariya ba saboda farin cikin da ya lullube shi. A kalla yau ya tabbatar Rayhanah na son sa, son da ba ta yiwa Khalipha.
Kalami ta yi cikin jin kan mace ga mijinta ba bisa tursasawa ba ko son fita hakkinsa, a’a, don tana sonsa. Tana son farin cikinsa fiyeda nata. Sai ya kwaikwayi ‘yar muryarta cikin dariya ya ce,
“A sake dinkewa don kin zama kwarya??????”
*****
Cikin wannan rayuwar da ta fi kowacce dadi da gardi ga kowanne dan Adam, Ibraheem da Rayhanah suka ci gaba da rayuwa a Chicago. Suna waya da Daddy da Inna Juma a kai a kai, shima Ibrahim yana gaisawa da mahaifiyarsa da Yaya Khalipha, sai dai bai taba yi mata zancen aurensa ko zancen Rayhanah ba, don Daddy ya gargade shi da kakkausan harshe da yin hakan.
An debi watanni biyar, duk abin da ya kawo shi ya kammala shi, ya auna komai da ya mallaka a Chicago bankunan gida Nigeria, wasu kuma daga ciki shipping dinsu yayi kamar motoci da furnitures da yake son kawata gidansa dasu.
Gidansa kawai ya bari bai kadar ba. A zuciyarsa ya ajiye shi ne ga first born din da duk Allah ya ba shi, mace ko namiji. Su zo su zauna ciki suyi karatu, in sunyi aure su zauna da iyalinsu.
Idan asibiti zai shiga, tare suke shiga, idan University of Chicago zai shiga yi lecturing, zama take cikin daliban ayi laccar da ita.
Ko tsura masa ido wata a cikin daliban ta yi, ta fara auna mata harara kenen. Ta hanashi motsin kirki ko doguwar hira yake yi a waya sai ta ce zance yake yi. Haka suke yawo cikin Illinois hannayensu sarke da juna.
Idan theatre za su shiga, Rayhanah na ofishinsa tana jiransa, shi Ibrahim maimakon ya ji haushi kamar yadda sauran maza ke ji in matansu na musu hakan, shi dadi yake ji. Domin ta rabashi da karnukan dake farautarsa, ko wata mu’amala ce ta hada shi da matan asibitin ko dalibansa, tana gefe sarke da hannu a kirji kafafu a sarke, tana dakon mai kawo wargi.
Ga Turawa da shegen tsoro basa son tashin hankali, ta fi ganin maita a kan Ibrahim daga mutanenmu mazauna can.
Mutum daya ta tsaya mata a rai dake yawan yi masa waya kuma su dade suna hira wai ita Sapna, bai taba ignoring kiranta ba, amma a cewarsa dalibarsa ce.
Kuma duk sanda ta binciki wayarsa babu hoto. Don haka take addu’ar Allah yasa wata rana idonta ya ga idon wannan Sapnar, sai yau Litinin a wani marece Allah ya amsa addu’arta.
******
Ibrahim na dakin ganawa da (Chief Medical Director) na Illinois TH, tare da manyan likitocin koda na duniya, tattaunawa ake yi a kan cutar (sars) tare da wakilan kungiyoyin AAPS, NAD, AMA, da Alberta. Ibrahim ya mike yana magana ta cikin ‘yar na’urar daukaka sauti dake makale jikin farar rigarsa ta likitoci, can karkashin rigar bakaken suit ne wuyanshi daure da bakin tie din da Rahane ta daura masa.
A lokacin ita Rayhanah tana can ofishinsa tana tsimayinsa, ya hadata da typing din wani record da yake son fitarwa a kan cutar ta sars, ba tare da sallama ba ko neman izinin sakatariya ko danna knocking na neman izini, wata farar yarinya kyakkyawa (ko da yake ba za a kira ta yarinya ba, domin a kalla tana da ashirin da takwas), ta murdo kofar ofishin ta shigo.
Kallon-Kallo ake tsakanin Rayhanah diyar Malam Rashidu Takai da diyar Ambasada Kabiru Abubakar Dogon-Daji. Rahanen, glasses ne prada a idanunta mai duhu wanda ya boye kwayar idonta. Tana sanye cikin traditional attire dinta atamfa ‘yar Holland koriya shar, yafe da mayafin da ya shiga da adon atamfar wato yellow, a kafafunta takalmi ne mai tsayin dunduniya sosai (heel shoe) shima yellow, babu kwalliyar komai a fuskarta sai ruwan hodar mary-kay sai lebbanta dake kyallin lip-balm mai danko.
Ita ma Sapnan ba wata kwalliya ta yi ba amma kallo daya za ka yi mata ka kirata da sunaye uku; ‘yar gata, ‘yar hutu, yar gayu.
Shadda ce getzner dinkin Senegal a jikinta dark pink wadda ba a cika zare da yawa wajen yin sirfaninta ba, wanda aka