Showing 21001 words to 23415 words out of 23415 words

Chapter 8 - Rayuwar Rayhana Book 4 Hausa Novel Complete

Unknown   

28 Dec 2024

327

Don haka ta shiga bakinta da sallama rike da hannun Muhd Mansur.

Rayhanah ta dago ido don jin muryar Jawahir, suka kuwa yi ido hudu da juna. Ai Jawahir cillar da jakar hannunta ta yi ta saki Mansur ta sheka da gudu ta rungume Rayhanah, ita ma ta rungumeta hawaye na zuba daga idon su. Hawayen kauna da TUNA BAYA……
(TUNA BAYA SHINE ROKO!) Inji Sumayyah Abdulkadir Takori.

Ita sam Jawahir ba ta lura da Ya Himu ba, balle karin ‘yar da falon ya samu. A lokacin ne Asma’u ta soma kuka tana zillo daga hannun Yaya Khalipha tana mikawa uwarta hannu, don ganin an shake mata ita.
Ibrahim ya ce,
“Kinga malama sakar min mata ta baiwa ‘yarta nono…..”
A firgice Jawahir ta juya don ta ji wata murya ne kamar ta Ya Himu, ta tabbatar shi din ne, ta kuma juya ga Yaya Khalipha wanda ya mikowa Rayhanah ‘yar, ta mika hannu ta karbeta.
Baki Jawahir ta bude tana kallon wani salon ba da nono na mutum biyu (uwa da uban). ‘Yar na shan nono amma uban ne ke rike da ita kamar shi zai yi breast feeding din, yana fadin,
“Kuma shi kenan don ta iya kamawa da kanta sai ki sakar mata? Salon ta yi katon baki irin na Jawahir? Hangangam!”
Jawahir ta bude baki (hangangam din kamar yadda yace) ta kuma kasa rufe shi. Sai ta kalli Rayhanah ta juya ta kalli Yayan nata, sannan ta maida idonta kan kyakkyawar jaririyar.
“Ki kwantar da hankalinki Jawahir na yi mata AURE!”
Ta tuna da kalaman Daddynsu a kan tambayar Rayhanah da ta yi. Shekaru uku da doriya a baya, ranar data wayi gari bata kara ganin Rayha a gidansu ba. Tun daga ranar kuma Daddy bai sake ba ta wata kofar da za ta yi masa zancen Rayhanah ba.
Wato Ya Himu ya aurawa!
Sai ta zube a kasa tana yiwa Ubangiji Sujjada, dama da mayafinta a kanta.
Jawahir ta fadi a ranta
“What a genius and examplary father they have?!”
“Bravo Daddy!”
Ta fada a hankali, idanunta na lumshewa. Kaunar mahaifinsu da mamakin kyakkyawar zuciya irin tasa ya cika mata zuciya. Irin su Daddy, V.C Baba Sa’idu (GIRMA YA FADI), Brigadier Bello Makarfi (SIRADIN RAYUWA), Alhaji Aliyu Dambatta (ALHERI), Tahir Usman Karaye (TUNA BAYA....), tsiraru ne a cikin al’umma.
‘Yan boko ne da basu fassara boko da defination din da sauran al’umma da dama suka fassara shi da shi ba, sun ba shi kyakkyawar fassara da ma’ana wadda ta yi dai-dai da addininsu wajen jin kan TALAKA da daukaka darajarsa ya tadda kafadar masu gata.
Sun kuma amince da ayar Ubangiji (SWT) ta
“inna akramakum indallahi atqaakum....”. Suna kuma aiki da ita. A cikin dukkan al’amuransu na rayuwar yau da kullum.
Jawahir tace
“How she wish za ta iya rubutu? Da ta bawa al’ummar Annabi labarinsu. Domin suyi koyi da kyawawan halayensu.
Ta mika hannu tana hawaye ta ce,
“Ku bani ita na dauke ta…..”
Rayhanah ta fizgeta daga nonon tana fadin
“Jeki wajen uwarki Asma’u…..”
Ai kuwa yarinya ta fasa kara, don bata koshi ba. A haka Rayhanah ta mannata a jikin Jawahir. Jawahir na daga cikin dai-daikun mutanen da ba za ta taba mantawa dasu ba cikin tarihin rahuwarta.
Ibraheem ya so ya yi bala’in an fizge masa ‘ya daga nono, amma ganin irin maternal rungumar da Jawahir ta yi mata tana shafa bayanta a hankali har ta yi shiru, ta ci gaba da dubanta cikin kauna, kwatankwacin kaunarta da dan’uwanta Ibraheem.
Sai ya fasa, ya dauke ido a kansu ya mayar ga amsa call din Daddy yana gaya masa sun sauka lafiya suna Abuja, sai gobe za su taho.
A ranar dai Baby Ma’u a jikin Jawahir ta kwana, kuma da yake ta fara cin abinci, ba ta farkawar dare. Da ta farka sau daya ta ba ta ruwa ba ta kara farkawa ba. A daren ta hada kayanta ta ce ita ma da ita za a Kanon, ba za ta iya barin ‘yarta ba.
Washegari basu bar Abuja da wuri ba sai da suka karya kumallo suka kintsa a tsanake, sannan suka dunguma dukkansu har Khalipha da nasa iyalin suka yo Kanon a jibgegiyar ‘BMW’ din Yaya Khalipha.
******
RAHANE A GIDAN DR. MANSUR
(Karo na Biyu)
Wannan karon, ta shiga ne da kafa mai kwari irin wadda Mimtaz ta shiga da ita. Ta samu karfin gwiwar hakan ne sakamakon hannunta da Ibrahim ya rike kam-kam cikin nasa har da matsa mata yatsun da karfi.
Asma’u na goye a bayan Jawahir ta yi barci tun a hanya. Shigar yamma suka yiwa Kanon, don basu taso da wuri ba. Ga tsaye-tsayen da Khalipha ya yi ta yi yana yiwa Mami cefane kamar yadda ya saba kullum zai je Kano. (Dankalin Turawa, Doya, Albasa, Kayan Miya, Manja da Plantain). Sanda suka shigo gidan, Daddy baya nan ma, amma sunyi waya ya ce yana kan hanyar dawowa ya samu emergency call ne.
Mami da Abida ido muzai-muzai abin tausayi, duk babu kintsi tare dasu, don Dacta Mansur ya dawo da bara bana, ya fita harkarsu da Aziza kawai yake harkokinsa, ita ta jagoranci kukunsu wajen girka abin da za a taryi bakin dasu.
Cikin Sallama a falon Mamin, wanda ke saman bene, bayan sun wuce falon kasa suka shiga falon, mazan da babbar murya suka yi sallama, matan har Jawahir mai goyo da karamar murya sukai sallamar.

Dr. Asma’u ta mike tsaye idonta cikin na Rayhanah wadda ke barin kafadun Ibrahim, hangawa kawai take don ta hango ‘yar. Can ta hango ta bayan Jawahir.
Ibrahim da Khalipha suka saki hannun matayensu suka hadu suka rungumeta, daya ta gaba daya ta baya. Don farin ciki sai tasa kuka tana fadin.
“Ka yafe mini Khalipha, ku roka min Rayhanah ta yafe mini. Na yi kuskure bisa son zuciya da ingiza mai kantun kawayen banza, don Allah ku roketa ta yafe mini, ina jin kunyar sake hada ido da ita a matsayin sirikata bayan na yi mata korar kare.
Ko cikin ‘ya’yana ban taba samun wadda ta yi min biyayyar da Rayhanah ta yi min ba…… ga shi Allah ya nuna min kuskure na a fili tun ban mutu ba, na kuma karba na yarda babu mai yi sai Allah….!!!”
Rayhanah ce ta je ta zube a gabanta tana fadin.
“Ba ki yi min komai ba Mami, ni ban taba rikeki a raina ba. Butulallen bawa shine mai manta baya idan gaba ta canza.
Mami na san baki taba kina ba, sai dan kuskuren fahimta da ya gifta a tsakaninmu, da kuma uzurin da na yi amanna da cewa, wani bai isa ya tsarawa wani dan Adam rayuwa ba, face Ubangijin da ya halicce shi.
Ban zata ba Mami, nima ban taba zaton al’amuran za su juye haka ba. In da na kuskuro nima ina baki hakuri…..”
Suka rungume juna sosai hawaye sharrr! A idon kowaccensu. A haka Dr. Mansur ya cimmasu, ko da yake ya jima a bakin kofa yana kallonsu yana sauraronsu, sune dai basu ganshi ba.
Sai da suka samu nutsuwa ne ta kama hannunsu ita da Mimtaz ta zaunar dasu gefe da gefenta, wato suka sakata a tsakiya a kan doguwar seater.
Mami ta mikawa Jawahir hannu ta ce,
“To sauko min ita sarkin iyayi da kankanba, ke kadai kin goye Asma’un, ko ta yi kama da mai suna Jawahir mummuna ne oho?’
Dr. Mansur ya karaso falon yana fadin,
“Basu ‘yarsu Jawahir dita. Jeki dauki dan Balaraben danki”.
Ya nuna Khaleel dake ta kuka a cinyar Ibraheem.
Ta ce, “Wallahi kuwa Daddy, dadin haihuwa sama da daya kenan”.
Ta sauko Asma’u ta dorawa Mami a cinya. Ta dade tana kallon buleliyar jikar tata, mai cike da tarin suma akanta da tsafta da koshin lafiya. Sai ta mike ta sanyata a bayanta ta goye da zanin Jawahir.
Rayhanah ta lumshe ido, hawayen farin ciki suka zubo mata. Muhd. Mansur yasa rigima shima sai Mami ta goya shi. Ta ce,
“Katoto da kai haka Daddy?”
Sai ta sure shi shima duk girmansa ta dora a kafadarta tana fadin,
“Miji na yin kishi ne dama da matarsa Mansur?”.
Ya ce, “A’a, Ni kece matata ba wannan Asma’un ba ta yi nauyi da yawa bana iya daukan ta”.
Kowa yasa dariya.
Abida da duk ta bi ta muzanta a falon, ba don komi ba sai don ba mai kallon ta a falon, ba wanda yabi ta kanta kamar basu san tana wajen ba. Ta rungume Yaya Khalipha tana kuka tana fadin ya roka mata afuwar Rayhanah.
Ya ce, “A’a, ni a suwa kuma? Ga mijinta gata da kanta”.
Ko giyar wake ta sha ta san itama ba ta isa ta doshi Ibrahim ba, wanda tunda ya shigo falon yake jefa mata harara. Ta kara kama kafar Yaya Khalipha tana kuka.
Dole ya dago ta ya zaunar a gefensa, dan’uwa rabin jiki. Ya ce,
“Rahane, an Rahane na! Ga Abida da kokon bararta ko Daddy da Himu sa daina kyarar ta”.
Ta murguda baki ta ce,
“Idan na ce maka Audu ai na rama…..!”
Tuno lokacin yasa Khalipha yin dariya. Dariya mai yawan gaske da ya manta rabon da yayi irinta. Ibrahim ma da ba kallon su yake ba hankalinshi na kan wayarsa sai da ya murmusa.
Ta ce, “Abida ai ni ban taba kin ki ba, ban taba kullatar ki ba daidai da rana daya. Allah ya yi mana afuwa baki dayanmu”.
Nan dai aka yafi juna. Dacta Mansur ya yafewa Maminsa, wadda dai-dai da rana daya son da yake mata bai taba canzawa da komai ba, illa dai ya yi kokarin nuna bacin ransa gareta don ta gane kuskurenta. Ta kuma gane hanyar data dauko rana tsaka ba mai billewa bace.
Aziza tuntuni tana makale jikin Rayhanah. Nan Daddy ya ja doguwar addu’a suka shafa, suka yi dinner tare cikin farin ciki marar misaltuwa.
Sai da suka share kwana uku a gidan (with nostalgia)cike da begen gida, sannan iyayen suka rakasu gidajensu da ke unguwar (Farm Center).
Washegari sun je Takai gaida dangi da Hakimi, inda suka tarar ana shagalin sunan Nabilah, ta haihu danta namiji tasa mishi suna IBRAHEEM….
Sai da kwalla ta fito daga idanun Rahane saboda tausayin Nabilah, wadda har yau kwayar idonta bata daina yiwa Himu kallon da take mishi tun farko ba, duk da auren nata a Lagos, inda ta auri wani ma’aikacin Custom Kabiru Dalhatu.
Sun sha gata wajen Hakimi da Haj. Kareema, daga nan suka tafi da Inna Juma, suka je Albasu wajen sauran dangi bayan motarsu shake da sittiru da kayan abinci. Sai da Zinaru ta yi ta kuka kamar ranta zai fita.
Bayan sun dawo daga Takai sunyi settling Dr. Ibraheem ya shiga sabon ofishinsa matsayin nephrology consultant cikin asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano. Har ila yau, malami a (Faculty of medicine) na jami’ar Bayero ta Kano.

MURFI
Likkafa ta ci gaba ga iyalin Dr. Mansur Takai, ta kowanne fanni daukaka ke binsu a gindi -a-gindi. Rayhanah ta samu komawa Jami’ar Bayero ta dora degree a (Computer Sceince), ta kuma fara koyarwa a bangaren nata (lecturing) matsayin (assistant-lecturer) albarkacin darajar kwali mai matsayi na farko data fito da shi, cikin nasara mai dimbin yawa.
Tun daga kai Asma’u yaye Mami ta kwace ta hanasu. Wai ita ma tana so ta ga dan karami yana gilmawa a gabanta. Daga ita sai Azizah wadda ke shekarar farko a Jami’a. Jawahir da Abida duk an aurar dasu shekaru biyu a baya.
Jawahir ta haihu. Abida na da karamin ciki. A shekarar da Rayhanah ta sake haihuwar Bilkisu, wadda ta sanyawa sunan Iya Bilki, a shekarar ne aka rantsar da Dr. Mansur a matsayin Ministan lafiya na kasa baki daya, saboda dimbin taimakon da yake bayarwa a fannin kiwon lafiyar al’ummar Nigeria, daga federal posting din ya fito.
Shekara na zagayowa ta sake haifo ‘yarta Jawahir, sai da ta jera mata biyar sannan Allah ya ba ta Da namiji, Ibrahim ya saka mishi sunan Hakimi Abdulkadir, tunda Khalipha ya yiwa Dacta Mansur takwara. Suna kiranshi Abdul.

Babu diya mace a idon Ibrahim duk duniya bayan RAYHANAH! Babu uwargida sarautar mata bayan RAYHANAH!! Babu sanyin idaniya a rayuwar Ibrahim sai RAYHANAH da ‘ya’yanta. Wannan shine labarin RAYUWAR RAYHANAH.

Masha Allahu la’quwwata illa billah.
Allahumma salli ala Dayyibil-mudayyibi. Wa ala ahlihi wa sahbihi wa sallim tasliman katheera!!!
-Maman Khazraji.

6
7
8

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login