Showing 6001 words to 9000 words out of 26888 words
in samu Ibrahim a gida shi yasa na bari sai Asabar.
Cikin isa nake jan motata zuwa unguwar Ring Road,domin kai wa Fatima ziyara, daidai wajen bada hannu ne wajen unguwar Ahmad Bello way,na tsaya bai fi mintuna biyu da tsayawa ta ba ina jiran a ba ƴan layinmu hannu, sai kawai na ga ƙato ya buɗe murfin motata a gaba ya shigo, ina ƙoƙarin yi masa magana na ji buɗewar baya,waigawar da zan yi sai naga ƙarti uku zaune a cikinta, sun nuna mini bindiga, wanda na gaba ya ce mini.
"Kiyi shiru,ki ja mota kawai muke so!"
Ban tsaya gardama da su ba na mayar da hankalina ga tuƙina inda aka ba mu hannu.
"Titin hannun ki na dama za ki bi."
Haka ɗayan ya ce mini. Ni dai na san ba zan ɓata ba a garin nan sai dai in kashe ni za su yi, saboda haka ban razana ba.
Duk inda suka ce in nufa,nan nake bi da motata, har zuwa wani mahaukacin gida, wanda yake ɗauke da yawan fitilu, duk da safe ne ba kunna su aka yi ba, amma ganin su a tsaye shi ya nuna mini yawansu.
Titin get ɗin gidan muka miƙe, tamkar za mu wani garin, bayan mun shiga get ɗin gidan waɗanda yake ɗauke da sojoji sun kai goma sha biyar,ni kuwa ganin sojojin ma ya ƙara mini ƙwarin giwar in sakin jikina ma, sai da muka dinga wuce gidaje zan ce ko gine-gine, sun kai baƙwai sannan suka ce in tsaya a ƙofar wani gida mai bene,wanda saman shi yake zagaye da barandar sama.
Da gani zagaye yake kamar ƙwano kenan circle ta can sama na hango ƙyallin wani mutum ta labule ya ɗan ɗago masu hannu, daga nan sai suka ce in yi gaba na ja mota muka nausa cikin wani daji, duk fa a cikin harabar wannan gine-gine. Bayan tafiya ta kai ta kilomita uku, sannan na ga mun iso wani gida mai dogon gini kamar ginin Choci.
Nan aka umarce ni da in tsaya in fito daga motar, ba wanda ya taɓa ni cikin su, suka nuna mini hanya har cikin gidan nan. Mun wuce wurare da dama, sannan na dinga ganin ragar ƙarfe da mutane a ciki, wannan ya nuna mini gidan yari ne aka kawo ni,abin da ban gane ba,shin ziyara aka kawo ni inyi ko kuwa ganin wani,ni dai na san ban yi laifin komai ba......
*ƘASAITA BOOK 1*
*NA*
*MARYAM KABIR MASHI*
Page 4
Abin tausayi na gidan (Yarin) gidan maza, saboda duk sun bi sun rame, sun ƙare,ga su nan da ƙyar suke magana, masu ɗan ƙarfi ne ke miƙewa su zo su kama ƙarfen suna yi mana magana wadda bana ganewa.
Matattakalar bene muka haye ni da su, wanda nan naga mata birjik a ɗaure a zuciyata na ce laifin me suka yi waɗannan bayin Allah, har da masu tsohon ciki da masu ƴaƴa, ga su nan a kukkulle,ni dai ƴar kallo ce har aka kai wani ɗaki na ga an buɗe shi wai in shiga,ban musu gardama ba muka shiga tare da su.
Gado ne ƙarami irin na ƴan makaranta amma wanda bashi da sama, sai ɗaya a kusa da shi da wata ƙwance tana bacci. Ba su yi mini magana ba ɗaya daga ciki ya buɗe wata ƙofa,nan na ga ashe banɗaki ne, ɗaya ya buɗe famfo a kusa da ni, na ga ruwa ya zo, duk dai ban yi magana ba.
Sai da na ga duk sun fita suna shirin kulle ni a ciki, sannan na yi masu magana da harshen Turanci.
"Baku gaya mini komai ba har za ku tafi."
Ɗaya daga cikinsu ne ya ce, "ki zauna za a neme ki."
Ya juya ya tafi ban ce masu komai ba,nima na ɗan kalli gidan nan na zauna.
Tsayin awa ɗaya, sai na ga matar nan ta tashi, tana ganina ta taso a hankali ta iso wajena ta zauna.
"Yaushe aka kawo ki?"
Naji ta faɗa da Hausa. Na kalleta sosai.
"Ko baƙya jin Hausa?"
"Ina ji,ɗazun aka kawo ni."
"Me ki kayi?"
"Ba komai"
"To Allah ya taimake mu"
"Musulma ce ke?"
"Eh."
Daga nan muka dinga hira da ita.
Ina nan har ƙarfe tara na dare, sannan naga waɗannan mutanen sun buɗe in da muke sun shigo, ɗaya daga ciki ne ya ce in taso, na yi wa wacce muke tare sallama mai suna Mabaruka. Tana kuka na bar ta tausayinta ya kama ni. A motata muka kuma shiga na ja har gaban gidan da muka tsaya da rana.
Muna tsayawa na ɗaga kaina sama sai na hango mutum zaune a barandar saman bene ya miƙe tsaye sosai ya juyo tare da dafa majinginin barandar, cewa suka yi in fito, na fito na kalleshi sosai, cikin sakan uku na gane mutumin da ya kaɗe ni watanni huɗu da suka wuce.
Me zan ce masa ni kuma yanzu bai yi magana ba, nima ban yi masa ba. Na girgiza kaina na juya na koma motata har na tashe ta ɗaya daga cikin ƙartin nan masu sanye da fararan T.shirt, ya sunkuyo ta gilashin da nake tuƙi ya ce.
"An baki last warning saboda haka yana gargaɗinki da kada ki ƙara shiga layin gonar shi, balle har ganganci ya kai ki kice za ki ratsa tsakiyar ta, ina fatan kin fahimta?"
Na ɗaga masa kai kawai, na ja motata har na yi nisa na tsaya na leƙo da kaina na ɗaga masa babban ɗan yatsana ma'anata a nan za mu haɗu wata rana.
A mota ne na yi tunanin ba zan gayawa Dad kome ya faru da ni ba, amma ni da kaina zan ɗauki mataki wanda ko a hanya ya hango ni sai ya ce a sake wata. Har na isa gida ina tunanin hanyoyin da zan bi, amma na rasa su, saboda haka na ajiye lamarin, na dangana shi da ba aikin gaggawa ba ne.
Sai da Mamee ta ɗan yi mini faɗa a kan nayi dare, goma saura kaɗan, na san banida gaskiya na dinga ba ta haƙuri,gudun kada ta gayawa Dad shi kuwa ba wasa a lamarin sa, idan har ka taɓo shi. Kun san iyaye dai.
Bayan na yi wanka na shirya jikina ne na gabatar da sallolin da ake bina, daga nan ban iya yin bacci ba, saboda tunanin hanyar ramuwar gayyar da nake son haɗawa Yarima.
Wannan dalili ne yasa na tunano da litattafan novel na Turanci na shahararren marubucin nan (James H. Chase). Na san a cikin litattafan sa akwai idea zan iya samun wata hikima a ciki. Daɗi, murmushi, dariya, suka saukar mini a lokaci ɗaya, wannan ya sa na kashe fitilar gefen gadona na koma na ƙwanta, tare da tabbacin yanzu bacci zai zo mini. Haka aka yi kuwa,sallar Asubahi ma Mamee ce ta tashe ni.
Da ƙyar na shawo kan Mamee ta amince na fita, shima don na ba ta tabbacin iyakata Bookshop na nufa domin neman wasu littattafai, cikin saurin da bai fi na mintuna talatin ba na dawo,lode da litattafan James, sun kai goma sha biyar.
Tun da na haye sama ɗakina ko motsi na kirki ma bana son yi, abincin rana kuwa sai da la'asar na samu na ci shi. Sai da na ɗauki ƙwanaki goma ina nazarin litattafan nan da birona da zungureran littafina a gefe,in ta kama in rubuta in kuwa tawa muguntar ta faɗo in rubuta.
Wani lokaci a falon Dad,nake shigewa saboda kada a dameni, sai na ji dawowarshi, sannan in koma ɗakina, na gama karantawa saura haɗa ayyuka. To yaya kenan?.
Ƙarfe taƙwas saura na safiyar Litinin wacce ta yi daidai da ƙwanana biyu da gamawa, na je na samu Katung Maigadi nan na zauna na gaya masa buƙatata, a take ya ce ai wannan duk abu mai sauƙi ne, tunda da akwai shi, sannan akwai abokanansa,in zan tura da kuɗi kawai su zasu kawo mini aikin da suka shirya. Na yi murna ƙwarai da gaske, sannan na ce ya bani ƙwana ɗaya.
Saboda na jima ban fita ba, shi ne na tambayi Mamee zan je gidan Aunty,ta amince mini. Ina isa gidan na ce mata kuɗi nake so, na dinga narke mata kamar zan yi kuka, har sai da ta bani dubu goma, na bugawa Yaya Habib waya na ce masa kuɗi nake so ya ce zai turo ta account ɗina wato banki.
Sai da na haɗo dubu talatin, sannan na ɗauki ashirin a nawa (account) ɗin na haɗa, na zo wajen Dad kuma na dinga fadanci cewa litattafai zan siyo, ya bani, saboda ganin da yake ina yawan karanta su, ya bani talatin. To saura Mamee, na girka mata kuka tun da ita ba wasa.
Ganin duk ranar kuka kawai nake, shi ne ta tausaya mini ta dinga lallashina, har tana tambayar me nake so, shi ne na gaya mata cewa account ɗina ba komai a ciki, shi ne nake son kuɗi in siyi litattafai, shi ne Dad ya bani kaɗan ,nan ta ce nawa ne? Na ce ashirin, ta ƙirgo ta ba ni.
Bayan ƙwanaki tara, ya zo ya ce mini komai ya haɗu, amma aikin farko kenan,yau wajen ƙarfe biyar na yamma in bi ta hanyar Bank Road saboda ruwan da ake yi na san yanzu zai kai har nan da tsayin lokaci a yanda (weather forecast) ta nuna.
Cikin ruwan sama mai tsanani na bi hanyar Bank Road,hanyar da bata cika mutane sosai ba, sannan tana da haɗarin bi a lokacin ruwa, ga shi yau garin na Jos shugaban ƙasa ne ya kawo mana ziyara, saboda ganewa idanunshi tabbacin zaman lafiyar da aka samu yanzu a Jos, madadin rikicin da aka samu tsawon lokaci ana yi a baya. A cikin shekara ta ɗari biyu da uku (2003).
Wannan yasa sai motoci ɗaiɗai ke yawo a garin,na laɓe da motata a gindin wata babbar mota na ga motocin Yarima sun wuce cikin gudu sai da suka yi nisa, sannan na ji sun bugo mini waya da in tafi,nima in bi hanyar, cikin natsuwa na dinga tuƙina, balle kuma yanda ake tafka ruwan sama.
Ban fi tsayin tafiyar kilomita ɗaya ba, sai ga shi na same su motocin su sun tsaya, ga ruwa ana yi balle su samu damar ɗauko wasu,ga ba motoci masu giftawa, saboda ruwa da ake yi kamar da bakin ƙwarya.
Tun daga ɗan nesa na ga mutum a tsaye da lema yana ɗaga mini hannu, daidai motarshi Yariman, na tsaya na zuge gilashina,nan wannan yake mini bayanin zan bayar da motata za a mayar da Yarima gida.
"A'a ka ce masa sai dai ya fito in rage masa hanya,me ma ya samu motocin naku?"
"Kawai gani muka yi motarmu ta tsaya,mun ɗan tsaya gyarawa sai ta bayanmu ta kama hayaƙi, ba mu lura da ta Yarima tayoyin sun sace ba sai da muka ta da ita da sunan shi a isa dashi gida."
"Ka gaya masa in ya amince, amma gaskiya bana bayar da aron motata ni in tsaya nan har sai an kaishi an dawo ba,ka tuna ni macece."
"To Hajiya."
Mayar da gilashina na yi na zuge, ina kallonsu sun ɗan jima, sannan na ga sun zagayo da sauri dukkansu sun kara masa lema tare da baza babbar riga,wai gudun kada ruwa ya jiƙa shi,a haka suka kawo shi har motata, inda aka buɗe masa baya ya shiga.
Ya koma ya ƙwanta yanda yake yi, kafin wani ya zagayo ya buɗe gaba,ni har na ja motata, amma don ƘASAITA ko motsi bai yi ba, balle magana.
A Hill Station Hotel na yi fakin da motata a wajen harabar ajiye motoci, ina fita suna isowa da baƙaƙen kaya dogaye suka nuna masa bindigogi a cikin motar, mutane ne sun kai goma.
"Fito!" Haka ɗaya daga cikinsu ya ce, cikin taƙama ya fito a daidai lokacin da ni kuma na cire baƙin gilashin da ke manne a fuskata.
Tabbas ko ban faɗa ba na san mamaki ya dirar masa a lokaci ɗaya don dai namiji ne mai ji da mulki, shi yasa bai nuna razanarsa a fili ba. Duk fuskokinsu manne suke da safar fuska baƙa, wanda gilashi baƙi ne ke manne da fuskarsu.
"Alhaji doka ta ɗaya" wani daga cikinsu ya faɗa da harshen Turanci.
"Na farko za ka bi Madam zuwa sama, ba na buƙatar ka nunawa wani cewa kana tare da mu,in kuwa ka ƙi." Ya ɗago hoto duk dogarawansa ne tsare da bindigogi.
"Zamu ɗauki rayukansu a yanzu, sannan mu ɗauki naka."
Sai a yanzu ya samu ya yatsina fuska ya yi magana cikin isa a hankali.
"Okey,no problem."
Na yi gaba yana biye da ni, na waiga na ce masa.
"Ka je ka biya kuɗin ɗaki ni nayi gaba."
Bai ko kalleni ba, ya yi wajen biyan kuɗi ni kuwa na haye sama.
Tsayin minti sha biyar sai ga shi ya miƙo mini makullin da aka rubuta No.120, ɗaki na ɗari da ashirin, ina tafe yana biye da ni har ɗakin. Na buɗe na shiga ya biyo bayana, sannan na juyo na fito na mayar da ƙofar na kulle. Na sauko na bawa Katung makullin.
"Ku ƙarasa sauran aikinku, amma kada ku yi masa komai, kuyi komai cikin mutunci,kun san babba ne ku ƙarasa haɗa komai, ina fatan kun gane?" Suka amsa eh. Na miƙa masa dubu talatin a biya a ɗan ci abinci.
Bayan ƙwana uku na dira a hotel ɗin da ƙarfe goma na dare, wanda su Mamee ma basu san na fito ba, na sa makulli na buɗe shi yana kishingiɗe a gado yana karatun mujalla ta Turanci (Tell) da ido ɗaya ya ɗago ya kalleni.
"Za ka iya tasowa mu tafi yanzu."
Bai ce komai ba ya miƙe ya zura babbar rigarshi da ke gefe ɗaya ya biyo bayana.
A motata har wannan gidan da yasa aka kai ni, amma inda yake da alama dai gidansa ne,kafin in shiga sai da na rufe fuskata da wata baƙar fuska mai tafe da kitso, sannan na ɗaga wata ƙatuwar ambulan na ce masa.
"Ko baƙar magana ka gaya mini sai na kai wa Sarki wannan ambulan ɗin da ba zaka san ko meye a ciki ba, sai nan da ɗan wani lokaci."
Ya buɗe murfin motar ya fita ba tare da ya ce mini ƙala ba,ya juya ya tafi abin sa, nima na ja motata sai gida.
Duk da na yi masa haka, amma ban ga alamar razana ba a jikinsa, wannan ta sani kaina na ce lallai wannan ya cancanci ya hau gadon mulki, saboda ba a san matsoracin Sarki, ga shi kuma da iya ƘASAITA, na yi dariya ni kaɗai, nayi murmushi kuma sannan na haye gadona na ƙwanta.
Bayan ƙwana biyu ne na taka da kaina har get ɗin gidan sarautar nan, wajen sojojin nan muka gaisa amma a cikin ɓatacciyar fuskar nan, sannan na kawo ƙatuwar ambulan (envelope), na miƙa masu na ce.
"Saƙon Yarima ne daga ƙasar Sudan."
Suka ɗan dudduba ni da motata, sannan suka ce sai na zazzage kayan ciki, na ce masu ba zai yiwu ba, amma su buga masa waya su sanar da shi cewa yana da baƙuwa ta kawo masa saƙo amma kun ce sai na buɗe....
*ƘASAITA BOOK 1*
*NA*
*MARYAM KABIR MASHI*
Page 5
Nan take suka buga masa, sai ya ce a karɓi saƙon kawai a kawo masa, ya san da shi,ni kuwa na juya na yi tafiyata gidan Auntyna.
Ɓangaren wajen Yarima kuwa,kaset ne aka kai masa da hoto ƙwaya ɗaya. Ya sanya kaset ɗin,lallai ya san na isa, hoton ƙwance yake ba riga a jikinsa da bargo lulluɓe daga ƙafafunsa zuwa ƙugunshi, sannan ƙirjinsa yarinya ce ƙwance a daidai lokacin da yake rungume da ita, ya kai bakin shi ya sumbaci goshinta nan aka ɗauki hoton.
Kaset kuwa daga inda ya ɗauki yarinyar ne har zuwa hotel ɗin da shiga ɗakin hotel ɗin duk dai yarinyar ɗaya ce, da takarda wacce na gaya masa, idan har ya ƙara sawa aka kama ni ko ya yi ƙoƙarin sawa a yi mini wani abu zan kai wa Sarki kaset ɗin da hotunan da kaina, na yi sallama.
Tabbas ni kaina na san na gama da Yarima, saboda yanzu ba shi da wata hanyar yi mini wulaƙanci,sai dai ni inyi yanda nake so a garin nan, da ya nemi takura mini da na tona masa asiri da ƙundin kaset ɗin da na ɗauka a matsayin ɓata masa suna. In kuwa haka ta faru, sarauta kuwa shi da ita har abada.
**** ****
Yamma ce yanzu wacce ta nuna ƙarfe biyar har da wasu mintuna goma, yanayin sanyin daminar garin sun haɗa sun mayar da garin tamkar dare ya yi, sanyi kuwa mai shiga cikin tsokar jiki.
Motocin da na gani a harabar gidanmu a lokacin da na shigo da motata, shi yasa na ɗaga hannuna na kalli agogon da ke maƙale a tsintsiyar hannuna, tabbas waɗannan koma su waye baƙin Daddy ne, da gani ka san manya ne na gaskiya, saboda ganin manya-manyan (Jeep) da na yi har wajen biyar,ban da ƙananan (Pegeout 406) ga zungureriyar motar nan irin ta Yarima Limousine Cadillae.
Don dai kalarsu ce ba ɗaya ba, kuma wannan mai murfin ƙofa huɗu ce, kenan babbar ta Yarima ce,na samu na raɓa tawa motar daga gefe ɗaya, sannan da Katung ya iso nake tambayarsa su waye? Nan ya nuna mini bai san ko su waye ba, amma manyan mutane ne (Big Men).
Mamee na falo ita ma da wasu mata har biyar, ina isowa na sunkuya har ƙasa na gaishe su, sannan na isa ga Mamee, na sumbaci kumatunta alamar na dawo kenan har zan wuce sai na ji Mamee na cewa.
"Ai itace wannan."
Wata mata wacce take zaune ita kaɗai a doguwar kujera wacce da ƙyar take motsi, ita ta yi ƴar dariya ta ce mini in zo.
Ina zuwa na zauna ƙasa kusa da ita, sai na ga ta shafi gashin kaina wanda yake a buɗe ta ce.
"She is beautiful, she deserves to be the Prince's wife,amma daga yau ki dinga kula da rufe gashin kan ki, saboda yanzun kin zama babba."
Ta faɗa da harshen Hausa, sannan ta ce in tafi. Ina tashi na kalli Mamee kallo mai alamar tambaya, amma