Showing 9001 words to 12000 words out of 26888 words

Chapter 4 - Kasaita Book 1 Hausa Novel Complete

sai na ga ta kawar da kanta, na taɓe bakina na haye sama, zuwa ɗakina.

Bayan kamar mintuna goma sha biyar, sai ga Mamee ta shigo ɗakin da nake ta miƙo mini wasu riga da zani na ɗanyan ƙwatin less (Cotton less) mai launin kore wanda ya chiza wato ruwan kayan sojoji (Amry colour) da takalma ruwansa, amma mai haske (light green) da file ɗanƙwalin saƙi, da abin sagalawa a wuya, duk ruwan takalman. Da wani irin English Gold wai duk in saka a jikina.

Tambayar Mamee nake, amma ta ƙi ba ni amsa, sai dai faman shirya ni take yi hatta shimi da siket ɗin duk kalar kayan ne,ni kaina na san nayi ƙyau, balle raba gashina biyu da Mamee ta yi ta sakko mini su a gaban ƙirjina, wanda ya sauko mini har kusan rabin cikina.

Fuskata kuwa ta sha gyara,ni kaina ban san Mamee ta iya ƙwalliyar kece raini ba, sai yau, tun da ita Mamee ba ta ƙwalliya,iyakacinta ta murza hoda kawai da ɗan ƙwalli a idanuwanta. Ta umarce ni da in biyo ta,na bi bayanta a hankali wanda take ce mini taku ɗaiɗai zan dinga yi.

Dama ni sarkin iya ƘASAITA, shi na dinga yi. Mun isa falo na ga matan da ke zaune duk sun ruɗe, na yi zaton iya nan kawai za mu tsaya, amma sai na ga an nufi sashen (Sitting room) ɗin Dad,ɗakin shaƙatawarshi da ni.

Muna kai wa ƙofar ɗakin na ga Mamee ta ƙara fesa mini wani Desginer ɗin turare, sannan ta ce.

"In kin shiga da kin kai tsakiyar falon ki durƙusa ki gaishe su, amma da harshen Turanci, ban da sakarci, ban da shagwaɓar da ki ka saba yi wa My dear,kina ji na?"

Na ce, "To Mamee,wai su waye,me suka zo yi?"

"Baki da amsa yanzun sai sun tafi."

Na ɗan kaɗa kai na shiga.

"Tafiyar nutsuwa." Haka na ji Mamee ta ce.

Yawan mutanen falon Dad su suka sa na fara rikicewa wajen tafiya, amma tunanin kada in kunyata iyayena,shi yasa na yi saurin sanyawa jikina nutsuwa a take, hankalina kam ya tashi, sai dai ban yarda na nuna ba, saboda ganin dattijon mutum da na yi a hakimce a saman kujerar kishingiɗewa, har da sa masa darduma mai laushin gaske a saman kujerar.

Ban da mutane biyu da ke tsaye a kan shi, suna sama da ƙasa da wani ƙaton abu mai gashi, faɗin shi kamar ƙaton faifan bakacan masara, sai dai bazar gashin jikinsa da kalar ja da yalo da ke jikinsa da mariƙin da suka fito da shi, zai nuna maka mafici ne.

Amma na fi ganin shi a cikin talabijin, shi ma sai in an nuno wani sarki. A zuciyata na ce dan kinibibi duk A.C ɗin da ke falon Dadyna, amma sai an yi masa fifita.

Yanda Mamee ta ce inyi haka na yi,bacin duk dama hankalinsu ya dawo kaina tun da na shigo. Dad ɗina ne ya iso ya kama ni ya tashe ni tsaye, sannan ya fara magana.

"Your Highness this is My daughter Yasmin."

Ya tafi da ni har gaban wannan mutumin,ya tsugunnar da ni.

"Ɗiyata ɗago da kanki."

Na ɗago.

"Very fine lady,na tabbatar ɗana zai yaba da ita."

"Haka ne, haka ne, ai ba ja."waɗannan mutane na tsaye bayansa suka faɗa.

Sannan ya kama hannuna muka miƙe tare da shi, shi wannan mutumin ya juyar da ni na kalli ragowar mutanen da ke baje a ƙasa, sai dai wasu uku da ke zaune a kujera daban-daban.

"Wannan ita ce matar da na zaɓawa ɗana Faisal, ina fatan ta yi?"

"Ta yi, tayi."

"Waziri ta yi?"

Ta yi,ta yi."

Sai na ji wazirin ya ƙwala kira, amma ban ji yanda ya kira sunan ba, sai na ga wasu mata su huɗu sun shigo ɗauke da farantai lulluɓe da kaya a ciki, da wani farin gyale sun ajiye gabana.

"Ƙyauta daga waziri." Inji wani ya faɗa.

Aka dinga shigowa da kaya kala-kala,ni dai ina daga tsaye, daga a ce ƙyauta daga wa ne, sai daga wane, bayan kamar minti ashirin aka sallame ni na tafi. Raina a ɓace na shiga falon Mamee baƙin da na gani da waɗannan mata, shi yasa na ɗan saki fuskata, sannan na sunkuya na yi masu sallama na haye sama.

Komai cillar da shi nayi daga tsaye, takalma,tuntun saman kaina,sarƙar,awarwaron, na faɗa a gado.

"Me ye wannan?" Na tambayi kaina.

"Me su Dad ke nufi da ni,ƙyautar da ni suka yi ko kuwa siyarwa? Yanzun manufarsu in rabu da Anwar Proposed ɗina? Mutumin da nake ƙauna.

Mamee fa ta san yanda nake son shi, shine zata je ta yadda a haɗa ni da wanda ban taɓa gani ba, hawaye suka gangaro mini,shi kenan rayuwata ta raunana, tun da za'a aura mini wanda ba na so, yanzun ba za'a barni in zaɓa ba kamar yanda Aunty Salwa ta zaɓa?.

Kenan an nuna mini a gidan nan an fi son Aunty Salwa da ni, yanzu duk ƙaunar da na ga ana nuna mini,ashe duk ƙarya ne, ashe iyaye ma na yaudarar ƴaƴansu,anya kuwa ma su suka haife ni? Ban yarda ba,ƙila dai ruƙona suke yi, shi yasa za su haɗa ni da ɗan gidan sarauta ko sarautar wane gari ce ma? Oho. Ko dai cikin dangin Mamee ne waɗanda ba su Musulunta ba, na ga suma ƙyansu ya yi yawa irin nata. Tashin motocin da na ji, shi yasa na rarrafa daga gadona na ɗaga labule ina leƙensu.

Suna wucewa na sauko ina dire-dire na kuka, na shige banɗaki,dama na sani da ban tafi da wayata ba, duk ita ta janyo mini, da bata nan ai da ba za'a kira ni in zo ba. A banɗaki nake wannan tunanin da kuka mai fitar da sauti, to an fa tuno da Allah duk da dama muna kiyayewa mu a gidan nan.

Nan take na yi alwala na fito,ai sai sallah, kafin a kira sallar magriba na yi nafila ta kai goma, ina ji Mamee ta leƙo ɗakina ta koma,ganin ina sallah.

Ƙarfe taƙwas saura minti huɗu,Mamee ta shigo ta ce in je inji Dad.

Na ɗago kaina, na kalle ta kawai, na mayar.

"Ba ki ji ni bane?"

"Na ji Mamee yanzun zan je."

Tana fita,nima na bi bayanta. Bayan kamar minti biyar.

Yana kishingiɗe a inda ya saba hutawa, duk bayan sallar isha'i, Mamee na daga ƙafarshi zaune tana yi masa matsar yatsun ƙafa.

"Yauwa,autar Daddy zo nan."

Na isa na zauna ƙasa ɗan nesa da shi.

Ya ɗaure fuska, irin alamar in babba zai yi maka maganar da yake ganin so yake yaro ya ɗauke ta da muhimmanci na gaskiya, sannan ya kira sunana.

"Yasmin." Sai na ga Mamee ta tashi ta fita, sannan ya ci gaba.

"Yasmin,kin san kowanne uba yana son ya ga ƴaƴanshi sun fi na kowa ɗaukaka,ƙyau, asali, tarbiyya, miji nagari, idan mata ne,in maza ne mata nagari. To balle ku ƴaƴana da ku ke a zuciyata tun ranar da na haife ku har izuwa yau. Ku kanku kun san ba wanda nake so a duniya in har suka wuce iyayena sai kuwa ku da mahaifiyarku, kamar yanda nake ƙaunar Manzon Allah (S.A.W) haka na koya muku sonshi da ƙaunarsa,a matsayinku na ƴaƴana, na horar da ku tarbiyyar bautawa Allah da bin sunnar Manzon Allah (S.A.W).

Kamar yanda ku ka san ba wanda zai ba ka ladan bautar Allah,sai shi Allah, haka ba ɗan da ya isa ya biya iyayenshi ladan tarbiyya da haihuwarshi da suka yi sai shi Allah, amma ana son a yi masu biyayya, ga duk abin da aka ga suna so da wanda suka umarta idan dai har an tabbatar bai saɓawa shari'ar Muslunci ba, da abin da Manzon Allah (S.A.W), ya zo mana da shi.

Ko da kuwa sun zama suna masu tsanar abin da suka umarce su, da ƙiyayya mai tsanani to yin biyayya ga abin da suka faɗa ɗin nan, shi zai sa su sadu da rahamar Ubangiji, wata rana kuma su ƙaunaci abin,su yi wa iyayen godiya ta musamman da addu'a idan sun riga sun rasu.

Yasmin,kin san dai duk cikin ku ukun nan,ba wacce nake ƙauna da so, sai ke. Ke ce ƴar da take ƙwance a cikin zuciyata a koda yaushe,ke ce ƴar da nake ganin nan gaba za ki ƙaunace ni, ki kula da rayuwata.

Ki tuna na haife ki, nayi miki tarbiyya tagari, na baki ilmi, na wadata ki da abinci mai ƙyau, na kawo gida mai ƙyau na gina na saka ku,ya na same su, wacce wahala na yi? Oho,ni dai ku ji daɗi,yau rana ta zo ta ki nuna mini ɗaya daga cikin son da ki ke yi mini,ki nuna mini iri-irin biyayyar da zaki iya yi mini ko da bayan raina ne.

Ki sani Addini ya yarjewa iyaye su zaɓawa ƴaƴansu mazaje na gari, idan har ƴan mata ne, ko samari, amma in sun zama aure ne na biyu, bazawara,ko bazawari, shari'ah ta ce a bashi dama ya zaɓa, ba wai don ba zai iya zaɓa da farko ba, a'a saboda Allah kaɗai ya san hikimar da yake nufi a nan.

Yasmin yau na zauna a ƙasanki ina roƙonki wata alfarma ƙwaya ɗaya, amma girmanta ya fi ƙarfin Najeriya gaba ɗayanta, nauyinta kuwa ya fi ƙarfin teku, amma a gare ki in kin yi,abu ne mai sauƙi da rashin nauyi.......


*ƘASAITA BOOK 1*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 6


Kada kiyi tunanin na yi miki haka ne don in cutawa rayuwarki,a'a na yi ne domin ina ganin na isa a gare ki, kuma na san ke yarinya ce mai biyayya, mai ƙaunata, na yi ne domin in sakaki jin daɗi da annashuwa a nan gaba, ranar da hankali ya huda miki jiki.

Ke kin san dai yanzu nafi ƙarfin a kalleni ace zan je ƙwaɗayin wani abin duniya,ko zan kai ƴaƴana domin ƙwaɗayin wani samu na duniya ke kanki kin san nafi ƙarfin haka, sannan kin san na mallaki abin da zan iya ciyar da ku har ƙarshen rayuwarmu,ko na riga ku mutuwa, zan yi alfahari da cewa na bar muku abin da za ku tafiyar da rayuwarku har ku bini inda na tafi.

Yasmin na san kina son Anwar,na san zakiyi farin ciki yau a ce shi zan aura miki a matsayin miji a gareki, amma ki sani yawancin abin da ka fi so,in har ba ka same shi ba, to ba alheri ba ne a gareka, ta yiwu alherin na ga wanda ba ka son nan.

Yasmin ni mahaifinki nake son baki haƙuri a kan hana ki auran wanda ki ke so Anwar,Ina neman alfarma a gareki da ki yi mini biyayya zan haɗa ki aure da ɗan Sarki Jafar,ki yi haƙuri na san da takurawa. Yasmin ki taimaka ki fitar da ni kunya, sannan ki sani,ni ba irin iyayen da suke kai tallan ƴaƴansu ba ne ba, na fi ƙarfin haka nan.

Ko kuwa kuna da yawa a gabana, balle ku biyu ne, da kansu suka zo har gidan nan neman wannan alfarmar, ban sani ba, sai yau, ban taɓa jin labari ba, sai dai ganin su nayi sun zo, ban san abin da ke tafe da su ba, sai da suka faɗa,ban san wanda ya ba su labarin ina da ɗiya ba, sai da suka faɗa cewa wajen taron bikin gidan Alhaji Kabir suka ganki.

Shi ne Sarkin yasa aka dinga cigiyar ke ƴar gidan waye, ba su samu ba sai wannan satin, shi ne Sarkin ya zo da kansa wai gudun kada in ga da wasa ake yi. Ban san ko waye ba a cikin ƴaƴansa ba, sai dai ya ce zai turo shi cikin satin nan ya zo ku gaisa,ku daidaita kafin nan da lokacin bikin. Wannan da ki ke gani shine Sarkin nan garin na musulmi."

Gabana ya faɗi shi kenan gidan cin mutane ma za'a kai ni, saboda waɗannan mutane na gidan yarin in ba cin su ake ba,ai ya isa a sake su su koma gidajensu, da gani ma sai an shanye jininsu, sannan a cinye tsokar a yanda na ga sun bushe a tsaye.

Nan take na yi dana sanin kin gayawa Daddy abin da Yarima ya yi mini wata uku da suka wuce, da na sani wata ɗaya da wani abu da ya wuce da ban ɗauki fansa da kaina ba, da na faɗa an ɗaukar mini,na san da yanzu Dad ba zai yarda ya aurawa wani ɗan gidan ba ni ba.

Shi yasa aka ce ta yaro ƙyau take, amma ba ta ƙarko, ga shi dai ni yanzu ba damar in faɗa Daddy ya ga kamar zan tozarta shi ne a idon duniya.

"Yasmin na ji kin yi shiru."

"Dad ai na san ba zaka zaɓa mini abin da ka san zai cutar da ni ba, saboda haka na amince da zaɓinka matsawar in ka amince da in naga abin cutarwa zan zo in sanar da kai, kuma zakayi saurin ɗaukar matakin gaggawa a gareni,ka ba ni gudummawar ka ta uba."

"Na yi miki wannan alƙawari, sannan ni ma kin tunasar da ni zan faɗa masu da wuri tun kafin akai ki, na gode Allah ya yi miki albarka, ya baki ke ma ƴaƴan da za su yi biyayya a gareki,ki yi haƙuri na san na takura miki."

Na ce, "Ba komai." Na miƙe na koma cikin gida.


**** **** ****

Shi kenan,Rayuwata ta raunana, tun daga ranar da Daddy ya gaya mini maganar aurena, har zuwa yau,ƙwanaki tara kenan, ba ni da wata walwala,in ma naɗan yi ta, to gabansu iyayena ne,gudun kada su yi wani tunani na daban.

Amma ni a ɗakina,ko motsin kirki ma bana son yi saboda tsananin tunani da kuma rabuwa da masoyina Anwar,wanda muka rabu muna kuka ga junanmu. Ƙwanaki huɗu da suka wuce, amma har yanzu ɗin nan sai da ya bugo mini waya, kullum kuwa riƙe nake da kan wayata ina kallon hotanshi wanda shi ne (Screen Saver) ɗin wayata,hoton fuskar wayata.

Na kasa fita ko ina yawon da na saba, balle in isa gidan Aunty in gaya mata halin da nake ciki,ko gidan Fatima amarya da na yi niyyar buga musu waya kuwa, sai in ga matsalar tafi ƙarfin faɗa a waya.

Ƙarfe huɗu da rabi ina zaune a kan abin sallah ta, sai na ji ƙwanƙwasawar ƙofa, da ƙyar na ce a shigo. Yaya Habib, na yi tsalle na ruga na rungume shi, ina yi masa oyoyo, madadin mu koma ƙasa, sai na janyo shi cikin ɗakina na mayar da makulli na kulle ƙofata.

"Yaya zauna tambayoyi zan yi maka,dama ina neman ka, saboda ina cikin tashin hankali, amma kada ka gayawa su Mamee, ba na nunawa a gabansu."

"To ina jin ki."

Nayi saurin tsugunnawa a gabanshi, shi kuwa yana saman gado zaune.

"Yaya su Mamee kuwa su suka haifeni ko riƙona suke yi?"

"Kina da hankali kuwa, da tambayar taki kenan ta mahaukata?"

"Yaya don Allah ka da ka juya mini baya, kai dai ka amsa mini,zan gaya maka dalili."

"Eh,su suka haife ki."

"Kana da wayo sosai a lokacin da Mamee ta haife ni ina jaririya,kana ganin tana ba ni nono a gabanka?"

"Wai ke yau ko kin yi gamo da aljanu ne?"

"Wallahi Yaya da hankalina,kai dai ka amsa mini don Allah."

"Zan iya tuna lokacin da take shayar da ke, har ma nake cewa ki sam mini nono in sha, ana yi mini dariya, har in je in kai ƙararsu ga Daddinmu."

"Kuma ka ga suna so na?"

Ya miƙe tsaye, "bana son sakarcin banza, zan yi miki duka yanzun nan."

"Don Allah Yaya ka yi haƙuri."

Sai nasa kuka.

"Wai Yaya wai ɗan Sarki Jafar za'a aura mini,ban san ko waye ba a cikin ƴaƴan nasa, shi ma Dad wai ya amsa shi zan aura,ni kuma bana son shi, koma waye a cikin su, duk azzalumai ne fa."

Na saka kuka na miƙe na cakume shi.ina ji ya saukar da ajiyar zuciya, ya ɗago kaina.

"Haba Yasmin ƴar ƙanwata,ki yi tunanin irin son da Dad yake nuna miki yanzun haka in za ki buɗe zuciyar Dad shima baya so, Amma,zan je in tabbatar da me yake faruwa."

"Kada ka gaya masa cewa na ce bana so."

"Ba zan faɗa ba,kin ji ƙanwata."

Ya goge mini hawayen fuskata,sannan ya juya ya fita.

Bayan mintuna hamsin ne Yaya ya shigo, ya yin da ya nuna mini sai dai in ta addu'a kawai, saboda aurena ba fashi, yanda yake gaya mini ma har sun tsayar da ranar ɗaurin aure, da sarki Jafar,nan da wata biyu shi ma domin mu samu shaƙuwa da juna.

Iya bayanin da Yaya ya yi mini kenan, ya fita shi ma jikinsa a sanyaye, ban taɓa shiga tashin hankali ba tun da nayi wayo sai a cikin ƙwanakin nan tara, ban taɓa tunanin za'a samu abin da zai girgiza min zuciya ba, amma yanzu ga shi na samu wanda Yake neman kawar mini da tunanina.

Yau ƙwana goma sha bakwai da zuwan sarki Jafar kenan ya rage saura ƙwanaki arba'in da uku yinin bikina, sai yau ne aka ce ai ga Faysal wanda zai zama angona, duk da sanyin da ake yi, amma sai da na ji tamkar an watsa mini ruwan zafi.

Mamee ta shigo ta umarce ni da in shirya in isa falon Daddy na yi baƙo, lallashi, nasihohi,Mamee ta dinga yi mini na kada in nuna masa halayyar sakarcina. Ni kuwa ba ta san gani nake ma ba ta ƙaunata.

Dogon siket da riga ne,ƙirar ƙasar Japan nasa a jikina, dogayen hannu gare su har idon hannuwana,buɗaɗɗan wuya gare su tamkar irin ɗinkunan da ake ya yi yanzu a Najeriyarmu, sai dai tare yake da ɗan ziririn mayafinsu wanda za mu iya cewa iya wuya kawai ya tsaya.

Mamee ta lulluɓa mini shi, ta sako leɓe ɗaya a gaban ƙirjina,ɗayan kuwa ya nufi bayana, gashin kaina kuwa yana can baya aka tattara shi, sai ƴan ƙwayoyi da ta ɗan gyara mini su ta sako su gefen fuskata, wanda ya bi ƙirjina ya ƙwanta.

Na sha turare da gyaran fuska, abin ka da kalar ruwan ƙasa mai cizawa ne,siket ɗin sai ya yi mini ƙyau,rigar kuwa baƙa ce mai ƙyalƙali a gabanta, ɗan mayafin kuwa kalar siket ɗin ne,baƙaƙen takalma na saka a ƙafata, waɗanda suka yi daidai da rigar, na ɗauki baƙar wayar hannu na riƙe a hannuna.

Kafin in yi sallama in shiga, sai da na leƙa ta kafar labule,jiri ne yasa na koma baya da ƙarfina, na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login