Showing 18001 words to 21000 words out of 26888 words

Chapter 7 - Kasaita Book 1 Hausa Novel Complete

ta biyu. Gefe ɗaya kuwa wani irin kafet ne, amma ba wai irin wanda ni kaina na sani ba, tabbas wannan ya fi kafet ɗin tsakiya laushin gaske.

Bangon gidan kuwa ɗaukar ido kawai yake yi, wanda na yi imani da Allah ba tayal ba ne ba saboda yanda yake ɗaukar ido. Ɗaya ɗakin kuwa, shi ma an zuba masa wani irin gado, wanda kan shi kawai ma abin kallo ne, sai kujeru ƙwaya uku da ke gefe, sai kuwa rukunin tebir ɗin kayan Na'ura mai ƙwaƙwalwa (Computer).

Banɗakin ɗakunan kuwa shi ma wani sabon gida ne, saboda shiga ka ke yi ƙwamin wanka tamkar ka shiga ramin wanka (Swimming pool) saboda ƙasa ya shafe, kuma sam ba ka ganin mai ke ƙasan ƙwamin ne,ko kuwa irin abin da ke manne a bangon gidan ne? Oho, sai dai zaka ga yana ta gudu, tamkar ka shiga ƙorama.

Sannan an rubuta zafi da sanyi a jikin wani bango da yake tsaye shi kaɗai a can tsakiyar kusa da ramin wanka, shi kan shi ramin wankan ka tattaka matattakalar bene,amma shi sai mu ce kamar za ka gidan ƙasa, sannan ka shiga ciki.

Wasu green da blue ɗin abubuwa ne liƙe da ɗan dandamalin inda za ka ajiye hannuwanka in ka shiga, wanda aka rubuta sabulu da soso, ma'ana su za ka danna su fito da kansu,in ka gama ma su koma da kansu.

Ƙaton madubi ne wanda za mu iya cewa ya kai rabin bangon banɗakin, shi ne ke kallon ka in ka shiga, da in ka fito. Tsayawa ƙarasa bayanin ma na san abu ne mai ɗaukar lokaci.

Da ka buɗe ƙofar da ke cikin ɗakin,za ka ga gaban gidan, wanda yake kallon gaban wani gida wanda na ga Faysal tsaye jiya da daddare,da ka gangaro matattakalar benen,sai ƙaton falo, wanda zan iya cewa tsayawa fassara shi ɓata lokaci ne, sai dai aƙwai ɗakuna biyu shi ma a ƙasan da banɗakinsu.

In ka fita cikin gidan,za ka samu bene ne zagaye da shi kamar ƙwabo, sai filin tsakiyar,in ka fita ƙofar shigowa kuwa za ka samu ragowar rariyar gidan, waje kenan inda ke da lambu in ka dawo ta gaban gidan kuma doguwar baranda ce kamar ta asibiti, amma wannan yanayinta kamar ƙaton fayif ɗin ruwa.

Tun da zagaye take da shukokin fulawoyi,in kana ciki kamar kana cikin inuwa, ita za ta ɗauke ka har ka shiga gidan Faysal, wacce kamar nan naɗe take da wayoyi, sai dai akwai ƙofa biyu in ka zo tsakiyar ta.

Ɗaya ƙofar za ta fitar da kai filayen wasa na gidan, wanda gaba ɗayan zagayen gidan ciyawar nan ce ƙwantacciya mai kama da kafet ɗin ƙasa, filayen wasa ne kala-kala, akwai na ƙwallon ƙafa, ƙwallon raga, ƙwallon ƙwando, ƙwallon hannu,ƴar ƙwallon rami da sauran wasanni kala-kala.

Daga can nesa da wajen kuma wani dutse ne wanda ƙasanshi duk ƙananan duwatsu ne, ga ruwa mai ƙyau yana gudanya a ƙasansa, wanda za mu iya cewa wajen shaƙatawa, wajen ya yi mini daɗi da sanyi-sanyi. Ƙaton dutsen kuwa malale yake, tamkar an shinfiɗa a kai wanda sai ka taka kamar ƙananan duwatsu uku, sannan ka haye shi.

Ba zan iya cewa ga inda wannan ruwan ke nufa ba, saboda gabanshi duk daji ne,wato dogayen itatuwa ne, masu kama da iccen turare,ko ko iccen fulwaya za mu ce, shi kuwa ruwan kana hango ƙasanshi garai-garai, wanda ƙananan duwatsu ne ke aiki.

Muna isa wajen kuwa, na tattaka na haye saman dutsen nan,a nan take sai na ji ai ni na samu wajen zama in dinga hutawa, duk da an keɓe wajen hutawa a cikin wajen filin wasan. Ɗaya hanyar kuwa, ɓangaren lambu ne,babu abin da babu,a cikin wajen, wanda sai da muka zagaya shi sosai, sannan muka fita, shi ma a cikin shi akwai duwatsu, sannan an tanadi wata rumfar gargajiya a ciki, wacce ta sha shimfiɗu a inda daga nesa da ita akwai wani ɗan ƙaramin gida mai ƙyan gaske, sai dai sun ce gidan hutawar Yarima ne.

Saman dutsen nan mai ruwa shi ne ƙarshen zagayen gidana, tunda ni ba abin da zai kai ni gidan Yarima. A nan na umarce su da su ɗan kawo mini darduma,zan zauna a saman dutsen,dama ni ba gwanar ɗan ƙwali ba, sannan ga ni da son ƙananan kaya (English wears) duk da dama ƴan Jos haka muke,mun fi baiwa ƙananan kaya muhimmanci a kan kayan gargajiya.

Doguwar riga ce kuwa jikina, wacce take ɓalalliya daga ƙasa, ba ta wuce ƙwaurina ba, sai dai ƙaramin hannu gare ta, iya cinyar hannuna, na sa suka ɗebo mini ƴan ƙananan duwatsu don kawai in dinga jefawa a cikin ruwan.

Na samu tsayin awa ɗaya a wajen nan,ni da Mansura da Muslima, sai ga jakadiya cikin hanzari ta zube a can ƙasa, sannan ta nemi iznin hayowa, na bata,a inda ni kuma na kishingiɗa a ɗan tuntun da suka kawo mini.
*ƘASAITA BOOK 1*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 10


"Allah ya taimaki Gimbiya,Yarima ya ce a ce miki yau ƙarfe huɗu na yamma ki same shi gidanshi,za ku gaishe da Sarki, da mahaifiyar shi,dama haka al'adar take, domin su ga ya ku ka ƙwana."

Na yi shiru, sannan na nisa na fara magana.

"Ki ce masa ina da ƴar hidima a gidana, amma shi in ya shirya yazo ta gidana mu tafi in kuma ba damuwa ma iya haɗewa a can, ina da ƴar rakiya." Sai na ga tana rausayar da kai.

"Shikenan jakadiya."

"To,to,to, Gimbiya ai ba gardama, abin da ki ka ce shine."

Ta miƙe ta gangara ta tafi,ni kuma na cigaba da harkokina, wanda suke yi mini daɗi, ga ba rana ko kaɗan a ganina sai ma iska da ke ratsa jikina, irin ta sanyin damuna.

Ƙarfe biyar na yamma na farka daga baccin da ya ƙwashe ni a kan abin sallah ta wanda na tashi da mamakin jikina ba hijabin da na saka na yi sallah, sannan an ɗora mini kaina a saman filo.

Cikin ɗan hanzari da faɗuwar gaba na miƙe, saboda tunawa da na yi cewa mun yi da Yarima za mu gidansu. Banɗaki na shige na watsa ruwa da saurina, ina fitowa ɗaure da tawul na leƙo ta barandar sama, ta cikin falo, na kira Mansura,wai dama in tambaye ta cewa Yarima ya aiko,ko ya zo? Ai sai kawai muka yi ido huɗu da shi.

Ya yi tsaye a maimakon in kira Mansura, ganin ya cire gilashin da ke manne a fuskarshi, ya ƙara ɗago idanuwanshi a kaina, ya tuna mini cewa jikina ba riga, na yi saurin shigewa cikin ɗakina, tare da ƙwallawa Mansura kira.

Ta shigo da sauri, "Ya daɗe da zuwa?" Tambayar da nayi mata kenan.

"Eh, ya daɗe."

"Tun yaushe ya zo?"

"Tun ƙarfe huɗu, na zo gaya miki sai na same ki kina bacci, shi ne na gaya masa,ni dai na ga ya hayo saman da kanshi, sai ya sauko ya zauna a nan,mun kawo masa kayan marmari da lemu, amma bai ko kalle su ba."

Na yi tsaki, "maimakon ki ce masa ya tafi zan zo daga baya?"

Na ga ta zaro idanuwa da sauri.

"Allah ya huci zuciya,ai ba a mayarwa da Yarima magana, yanzun ka ƙwana a yari." Nan take sai na tuno yarin nan,nima na taɓa zuwanta, ta tsawon awa goma.

"Ke ki ka cire mini hijabin jikina ki ka sa mini fulo a kaina?"

"A'a"

Haushi ya kama ni, "wa ya ce ki ka barshi ya shigar mini ɗaki?"

Ta yi saurin sunkuyar dakai, ba ta ce komai ba, "fita ki bani waje ki turo mini masu kula da kayana!"

"Ai sun ajiye Gimbiya, Allah ya huci zuciya,ga su nan sun fito da su." Ta nuna saman kujera da ɗan yatsa, sannan ta yi waje.

Boyal ne mai ruwan makuba (Coffee Color) wanda ya amsa sunansa, wanda ya sha aikin surfani a wuyansa da hannayensa, amma hannun bai wuce cinyar hannuwana ba, sai rigar kuwa da kaɗan ta wuce ƙuguna, amma buɗaɗɗiya ce, wacce ake kira da Stella Style.

Zanin kuwa ya sha ado, wanda zai ɗaukewa jama'a hankali,ni kaina mai kayan sai da na ji sun birge ni, na zauna a jikin madubin da ke kusa da gadona, na gyare fuskata.

Takalmi da jaka ruwan ƙasa ne nasa a ƙafata, wacce jakar iya silin hannu kawai ake rataya ta, da gani ka san desginer ce,wata siririyar diamond na saka a wuyana,inda zobunan hannuwana da ɗan kunnan duk kalar sarƙarce, zobe ƙwaya biyu kacal ne a hannun nawa.

Ɗan ƙwalin Boyal ɗin ne aka naɗo shi, tamkar naɗin gwaggwaro, amma a matsayin ɗaurin ɗankwalin yake. Turaren (Network) na zuba a jikina, ban tsaya wani make-up ba a fuskata,saboda gaishe da sirikan dole zan je, sai dai na san dole ta sha farar hoda da Wetlips mai sheƙi,farcena kuwa sun sha fenti ruwan ƙasa suma.

Taku ɗaiɗai nake yi na sauko daga ƙafar bene inda takalmin ƙafata ke fitar da sauti cikin nutsuwa, saboda malalen kafet da ya baje gidan, shi ya hana su ƙara mai fitar da sauti da ƙarfi.

Babu kowa a falon sai Faysal shi kaɗai da jarida a hannunsa,jin takuna yasa ya ajiye jaridar, amma ba tare da ya kalli inda nake ba, har sai da na iso daidai da shi, sannan na ga ya ɗaga kai ta gefe ɗaya ya kalleni,mayar da kan da ya yi ya sunkuyar ya yi daidai da fitar maganarshi a hankali.

"Something is missing."

Na ƙara kallon jikina sosai, ban ga abin da na manta ba.

"What?" Na faɗa cikin jan aji.

"Mayafi,ko kin manta yanzu ke matar aure ce?"

Na tsaya na ƙare masa kallo, amma shi ko motsi bai yi ba,a hankali na nufi inda na san zan ga su Mansura, sannan na yafito ta, ta iso da gudun saurinta, sannan na umarce ta da ta ɗauko mini mayafi wanda yake iri ɗaya da takalman da jakata, cikin rawar jiki ta ce to.

Ko kallon inda yake ban yi ba, na wuce zuwa waje abina,bai ce ƙala ba, shi ma na ga ya taso ya biyo bayana. Wani abun al'ajabin kuma shi ne dakarun tsaron shi suna nan tsaye ƙam suna jiran shi, a zuciyata na ce lallai wannan mutumin da mulkin masifa yake.

Limousine motar nan mai ƙofa uku, wacce ta bugeni a titin Ahmad Bello Waya, ita aka buɗe mini na shiga cikin takaicinta, ta gefe ɗaya na ga ya shigo shi ma,a inda bai fi sakan biyu da zama ba, na ga labulaye baƙaƙe sun sauka da kansu, kenan an rufe mu,ko direban ma bana gani.

Kujerar gefenmu ba kowa, sai tsakiyarta naga ƙaramar talabijin na aiki,sanyi na ji ya sauka a lokaci ɗaya, tare da wata fitila mai kalar duhuwa ita ma a zuciyata na ce lallai dole a dinga kaɗe ƴaƴan talakawa ba a sani ba.

Yanda ya shige ƙwanar kujerar da yake,ni ma haka na ƙwanta linkif a cikinta,tsawon mintuna goma sannan na ga ya cire gilashin fuskarsa da ƙyar, sai ga wani ɗan tebir ya ɓullo daga ƙasa da ƙwalaban lemu amma ba irinsu fanta ba,da kofunansu, wasu ƙwalaben ne abin kallo, don ma ina ƴar gidan masu da shi, da sai in ce giyoyi ne ba lemo ba.

Ya ɗora gilashinsa a sama, sannan yasa hannu ya janyo gaban tebirin, sai na ga ashe ɗan firji ne ya zaro robar Ice Cream da Chukulat, ya ajiye a gabana, sannan ya ɗaga ƙwalba ya tsiyaya lemo a kofi, ya ajiye a gabana, sai na ga shi ma ya tsiyaya.

Sai da ya kurɓa sau biyu, sannan ya ajiye ni kuwa sai bin shi nake da kallo ta wutsiyar idanuwana.

"Na aiko da gaisuwata ɗazu, amma ban ji gamsasshiyar amsa ba, wanda ke ce mace a ƙarƙashina ki ke,ke ya cancanci ki aika mini da ita,ko kizo ki gaishe ni." Ya yi shiru ya ƙara ɗaukar kofin ya kurɓa lemun.

"Ki sha mana,sarkin shan zaƙi."

Na ɗago na kalleshi a zuciyata na ce wa ya gaya masa ina son waɗannan kayayyakin, ban amsa masa ba sai naga ya ɗan sunkuyo kaɗan ya ɗauki Ice Cream ɗin ya buɗa ya miƙo mini.

"Karɓi."

Na girgiza kaina alamar a'a, saboda mamaki da al'ajabi ya hana ni motsi, ashe ya iya magana mai sanyin gaske ko don bai cika yin magana ba.

"Yasmin!"

Na juyo sosai na kalle shi domin mamakin yanda aka yi yasan sunana, ya ɗan yi murmushin ƘASAITA, ya ƙara miƙo mini,na sa hannu zan karɓa, sai na ga yasa ɗayan hannunsa ya riƙe hannuna, ya kama ƴan yatsuna, sannan na ji ya yi magana.

"Daga yau don Allah kada ki ƙara shafa irin wannan fentin, ina son kisa a yanke miki faratan gaba ɗayansu,ni ba na so, Allah ma baya so."

Na zame hannuna, "Dole ne ki bi umurnina, saboda ina mijinki, ba ki da wata hanyar rabuwa da ni, tunda kin zo hannuna."

Na yatsina fuska. "Ka manta da ina da abin da zan iya tona maka asiri da shi?"

Ya yi murmushi, "Ai yanzun kan ki zaki tonawa asiri, tunda duniya za ta kira ni da mijin Yasmin ne ɗan iska mai bin mata. Amma duk da haka ina roƙon ki ƙonasu,bana so mu ɓata ran mahaifanmu."

Na yi murmushi na juyar da kaina gefe ɗaya.

"Zan ƙona su, amma sai ka bi dokokina."

"Bama za ki same su ba,ki yi shiru kawai."

Bai yi wata magana ba, na ga ya koma ƙwana ya ƙara gyara ƙwanciyarsa.

Ni dai ƴar bi ce kawai, saboda ban san ko'ina ba a gidan, har muka iso wani falo. Wata ƙyakƙyawar mata ce kishingiɗe a saman wani tudu kamar na katifa, wanda ya sha shinfiɗun dardumai wanda kalolinsu ba sa ƙirguwa. Sai da muka isa kusa da matar, sannan na ga na ma taɓa ganin ta. Ƙasa na ga Yarima ya zauna cikin ladabi, nima sai na yi yanda ya yi.

Cikin ɗan lokaci ƙanƙani, na ga matan da ke zagaye da ita suna kawo mana gaisuwa,suna ficewa waje.

"Barka da yamma Mama."

"Barka ka dai yarona."

Nima sai na faɗi yadda ya ce, "Barka da yamma Mama."

"Ɗiyata barka da yau, ya baƙunta, ina fata baya ɓata miki rai?"

"A'a Mama, lafiya ƙalau."

Sai na ga ya tashi ya haye shinfiɗar ya zauna, ya fara wata magana irin ta shagwaɓa, mamaki ya kama ni,nan take na ce lallai iyaye, iyaye ne ashe da wanda Faysal ke wa magana lafiya ƙalau ba taƙama.

"Mama ni har yanzun Sarki ya hana ni zuwa Malesiya,Mama don Allah ki sa baki ya bar ni in tafi gobe."

"Ba fa zai yiwu ba,in dai ka tashi zuwa Honey Moon ne to na san ba zai hana ka ba."

"Mama don Allah." Ya ƙara matsawa kusa da ita har da riƙe mata hannu.

"Kana da naci Yarima a kan abin da ka san ba zai taɓa yiwuwa ba. Yanzun ka tashi ka je ku gaisa da Sarki naji an ce ya shigo, kuma na san saboda kai kawai ya shigo. Baby Yasmin ku je ku gaishe da Babanku, ga shi can ya shigo gida,ki ƙyale wannan shagwaɓaɓɓan mijin naki,kin gan shi nan kullum bai girma ji yake kamar a mayar da shi ciki ma."

"Mama, kada ta raina ni,ni bana yi mata wasa."

"A'a,lallai ni tashi ka wuce ka ba ni waje,marar kunya."

"Mama." Ya faɗa a daidai lokacin da shi kuma ya sauko muka tafi.

Tabbas sarauta sai ɗanta, Sarki kam yana mugun ƙaunar Faysal, saboda yanda ya nuna lokacin da muka shiga. Mun shiga Faysal ya sunkuya har ƙasa ya gaishe da Sarki,a inda ni ma na yi yanda na ga ya yi, sannan muka zauna gabansa.

"Faysal na ji aikenka har karo biyu, amma na bayar da amsa ɗaya, ita ce a'a, yanzun ma a gabanka na ce a'a, ba wai don in ɓata maka rai ba, a'a saboda yanzun ba da bane ba, yanzun kana da nauyin iyali a kanka, ya kamata a ce ka tsaya ka kula da su na tsawon lokaci kafin ka yi wata tafiya.

Faysal ban haɗa ku aure da sunan in zalunce ku ba,mu iyayenku mun haɗa ku aure ne, saboda muna ganin ku ƴaƴa ne nagari masu tarbiyya, hakan yasa ni nayi tunanin wacce ta dace da kai ta ɓangaren ko'ina rayuwar duniya nan, har izuwa lahira, na ga ba wacce ta dace sai wannan yarinya.

Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! Ɓacin ranta zai iya shafar tsakaninmu da kai,ko da kuwa labari na samu,ka riƙe ta tsakaninka da Allah, shi so da ka ke gani, a hankali yake shiga cikin zuciya, har ya ratsa gangar jiki,in kuka yi haƙuri da juna, wata rana sai kun yi murna. Saboda mu ma duk haka aka yi mana,ga shi yanzun ya zame mana alheri."

Daga nan ya ci gaba da yi mana nasihohi, sannan ya sallame mu.

Muna fitowa daga ƙaton falon Sarki,Yarima ya yi gaba ya bar ni a baya,a zuciyata na ce ni dama cewa ka yi in tafi gidanmu,ni ya fiye mini alheri, tunda nima saboda mahaifina kawai nake zaune a gidanka.

Ina isa falon mahaifiyarsa na ga ban gansu ba, sai na nufi wata ƙofa nima in nemi inda suka shiga sai na jiyo muryar Yarima.


*ƘASAITA BOOK 1*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 11


"Mama wallahi yarinyar nan ba ta sona ƙwata-ƙwata, nima har yanzu ban ji ta ƙwanta mini ba sosai. Mama taƙama gareta ga jiji da kai."

"Kai ka fara yi mata,ka manta labarin da ka ba ni a baya cewa yi fa tana burge ka,tun ranar da ka fara ganinta."

"To Mama ai burgewa ba so bane ba."

"To yanzun me ka ke so inyi maka?"

"Mama ki yi mata faɗa, ita ma ta rage jiji da kai."

"Kai ka yi mata."

"Wallahi Mama tun da ki ka ce kada in yi mata wallahi ba na yi mata."

"Haba Faysal na san ka fa."

"Mama ko yanzun fa da zamu zo nan ni na je har ɗakinta, sai da ma na jira ta tashi daga bacci. Mama ai kuwa na yi."

"Shin wai waya gaya maka rana ɗaya so ke shiga,a hankali in kuna tare zaka ji kana sonta, amma na gaya maka dole kai ne za ka yi ƙasa ka dinga lallashinta,ƙiyayyar mace ba ta da tsanani."

"Mama ni wallahi da an bar ni nayi tafiyata kawai."

"Bana son haukan nan naka fa,kullum ana koya maka hankali, amma ka ƙi ka koya." Jin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login