Showing 15001 words to 18000 words out of 26888 words

Chapter 6 - Kasaita Book 1 Hausa Novel Complete

ni daga jikinsa. Ganin yanda nake yi ne yasa Daddy ya ce su tafi, zai kai ni da kanshi daga baya. Hakan yasa sai dai aka lulluɓa wata abokiyar wasata aka fita da ita a matsayin amarya.

Ni kuwa har goma da rabi na dare,Daddy nata lallashina da ƙyar na amince, shi ma sai da ya yi mini alƙawarin gobe tun da safe zai je gidan,in ya ga ban haƙura ba zai dawo da ni, kai ni kaina na san dai wayo kawai ya yi mini.

Duk da na san dai shi kanshi dole ta sa zai rabu da ni,kari da ganin hankalin Dad ya yi mugun tashi har yana zubar da hawaye ganin yanda nake kuka, har da neman shiɗewa.

Da lallashi da ban magana,Daddy ya kaini har gidan Faysal, shi da kanshi ya rakani har cikin ɗakin da yake nawa bayan nan ma sai da ya ɗan zauna ya ƙara yi mini ƴan maganganun da za su ƙwantar mini da hankali, wanda sai da jama'a suka ɗan ba mu fili, saboda yawa, amma duk da haka da zai tafi sai da na ji hankalina ya yi mugun tashi.

Abu ɗaya ya hana in bi shi, ƴan'uwa da ƙawayena da sauran waɗanda suka isa a kaina, kamar ƙannan Dad da na Mamee,da suka riƙe ni suna lallashi, dole dai ta sa na haƙura. A wannan rana sai da aka bar mini mutane daga gidanmu suka ƙwana, har da ƙawayena,ganin Aunty Salwa ta ƙwana,shi ma ya ƙara taimaka mini.

Sabuwar hidima ce ta ɓalle da gari ya waye,taro a cikin ariyar (area) gidan Sarki tamkar yau aka fara bikin, tun daga get kuwa har izuwa cikin gidana, wani sabon biki ma ni zan ce ake yi. Yamma na yi kuwa, sai hawan Daba ya tashi ranar Litinin kenan.

A al'adarsu,wai amarya da ango ke fitowa saman gidan Sarki, Sarki da tawagarsa a gefe ɗaya, ango da amarya a gefe ɗaya a sama. To sai a dinga kawo gaisuwa, dole ta sa na shirya, saboda Aunty na nan, ban da sauran dangin iyayena,ƴan Syria,kuwa suna can wajen Mamee suna taya ta zama.

Sai da muka kai gaisuwa wajen Sarki, sannan muka wuce ni da Yarima muka zauna, baya ga ƴan bi baya da muka samu, tun daga fitowata, kafin ma in iso inda Yarima ke jira na,a nan zaune har sai da aka yi kiran Magriba, tsakani da Allah na ga girmamawa da ƙauna a wajen jama'a. Wannan tasa ma na saki jikina.

Ranar Talata kuma amarya da ango ke zuwa gidan Sarki na cikin gari, amma iyakacinmu fadarshi aka gabatar da mu ga manya-manyan hakiman Sarki.

Daga nan kuma sai zuwa gaishe da iyayensa, shi Sarkin wanda dangin amarya ne ke raka ta, kuɗi,ƙyaututtuka kuwa,wai na sha su,ni kaina na sake da irin ƙaunar da ake nunawa Faysal, na san kuwa iyayenshi suka fara nuna masa ita.

Ranar Laraba,a ranar ango ke yin tashi walimar da abokanansa, saboda gabatar da amaryarsa a gare su, ita ma ta san su, sannan da ƴan ƙawayenta ko su goma ne,a wani babban wajen taro na manya. Iyakaci na da Faysal wajen hidimar auranmu, da mun iso gida, kowa hanyarshi yake nufa,dama kuma ba mota ɗaya muke shiga ba,ni da motocina, shi ma da nasa.

Ranar Alhamis ita ce ranar da na ga kowa na tafiya, wasu da safe, wasu kuwa sai yamma, amma ni ƴan'uwana, sai da dare suka tafi, cikinsu kuwa har da Aunty da Fatima amarya, zan ma iya cewa su ne na ƙarshen tafiya, wajen taƙwas da rabi na dare, saboda sai da suka gyara gidan duk inda aka ɓata,turaran wuta da sauran kimtsa amarya da ake yi kafin ango ya shigo ɗaki, shi da abokanansa, wanda ake kiranshi siyan baki, sai da suka sa na sake wani wankan na sake kaya, sannan suka umarce ni da in sauka ƙasa,in zauna ga wata kujera ta nan ita ɗaya, idan sun tafi.

Huɗuba, ba wacce ban sha ba a wajen Aunty,daga nan muka yi sallama suka tafi, da sunan ba zata dawo da wuri ba, saboda gidan sarauta ba a yi masa zirga-zirga,ganin na narke zan yi mata kuka ta ce wai jibi za ta dawo,ni dai na san tsarani kawai ta yi.

Na sauko daga sama a daidai lokacin da agogon bango ya buga ƙarfe tara na dare, na shigo falo na yi tsaye a inda nake tunanin an bar ni ni kaɗai kamar mayya, na tuna irin jama'a da suka taru a gidan nan,yau gashi rana ɗaya kamar an ƙwashe su.

Na samu ƙwanar kujerar kishingiɗa na ƙwanta gefe, ita kaɗai ta sha shimfiɗun sarauta,ƙasan ta ma zagayayyan kafet ne (Circle) mai taushin gaske, da gani ka san ita ce kujerar zama idan mulki ya taso. A hankali na dinga bin ɗakin shaƙatawar da kallo, ba inda idona ya kai, sai ga ƙaton hoton Faysal wanda zan iya cewa ya fi ƙarfin taga, sai dai ƙofar mutan da.

**** **** ****

Ban ce ƙala ba, har ta gama, ina kallonta suka jera layi ita da ragowar ƴan matanta suka yi waje sai guda biyun nan su ne suka yi saurin dawowa gefena suka zauna a ƙasa, na yi murmushi na juyar da kaina gefe, sai na ji hawaye sun gangaro mini,saboda tunanin tausayawa yara ƙanana da aka jera mini su,ni ina aure su suna bauta, Allah ya kiyaye.

Na ɗan motsa na tashi zaune, amma na ɗan kishingiɗa, cikin sauri duk suka miƙe tsaye ɗaya ta ɗauki ƙafata ta gyara mata mazauni, na kalle su, ba laifi duk suna da ƙyawunsu.

"Ku zauna na gode."

Suka yi saurin zama, na kalle su.

"Ya sunayenku?"

Ɗayar ƴar wacce ta fi ƙyan ta ce mini, "Mansura." Ɗayar kuma Musulum.

"A wane gari ku ke?"

"Nan gidan Sarki."

"Na sani,iyayenku nake cewa."

"Can cikin gidan Sarki, babban gidan kenan."

Nayi shiru, ina tunanin me suke nufi da haka, ban kammala tunani ba, sai na ji sallama, na juyo a hankali na kalli masu shigowa. Jakadiya Dela ce da wasu mata biyar ɗauke da wasu abubuwa a rufe suna biye da bayanta, tana zuwa kusa da ni, ta ƙara zubewa a ƙasa,su kuwa suka matso gaban kujerar suka ajiye kayan, suka ja da baya, suka zube ƙasa, sannan suka ce.

"Gaisuwa muke, gaisuwa muke."

Na ɗago masu hannu.

"Gimbiya ta amsa." Na ji jakadiya ta ce.

"Gimbiya ayi mana afuwa,muna damun ki da zirga-zirga."

"Ba komai."

"Abin da ki ka ce ba ƙarya." Inji ɗaya daga cikin matan da suka shigo tare da jakadiya. Ta miƙe tsaye ta iso gaban abubuwan da suka shigo da su, sannan ta tsugunna.

"Allah ya ja da ran Gimbiya wannan saƙo ne daga Yarima, ya ce in kawo gaisuwa a gare ki."

Na miƙe zaune, inda su Mansura suka miƙe da sauri za su kama ni, na yi saurin ɗaga masu hannu, ina zama sosai, sai na ga jakadiya ta fara buɗe kayan ɗaya bayan ɗaya.

Faranti ne ɗan dogo, mai ruwan zuma (golden color) kayan marmari ne a ciki,lemon zai kai goma,ayaba nono ɗaya, sai tuffa (apple) da dabino a tsakiya, amma fa na alfarma, dole ne ma su ba ka sha'awa, saboda ƙyawunsu, daga saman dabinon wani ɗan faranti ne shi ma mai zagayewa.

A warwaraye ne cikinshi, tsakiyarsu da sauran kaya rakwacam, na sunkuyo na ɗauki ɗan farantin na ɗaga awarwarayen (ƴan hannu) sai na ga su shida ne, da sarƙa ƙatuwar gaske, zobuna huɗu da ɗan kunnayensu na zinare ne ƴan Dubai ɗin asalin (Daham).

Na miƙawa Mansura ta yi saurin karɓa ta ɗora a kai, sannan aka buɗe ɗayan,Faranti ne shi ma kamar tsayin na farko, sai dai shi kalar ruwan silba (Silver colour) kayan sawa ne a ciki, amma da gani na bacci ne, da faranti ƙaramin sama.

"Mansura miƙo mini." Na faɗa.

Awarwaraye ne ƙwaya huɗu da sarƙa da ɗan kunne, da zobuna biyu kacal, amma Diamond,sun bala'in burge ni, ta dinga ɗagawa,sama rigunan bacci ne a ƙwalinsu guda bakwai, kala-kala, sai tawul ƙasa da silifas, amma masu ƙyan gaske, dukkansu a ƙwalaye suke irin ƙwalayen ƙasashen tsallake,su kansu ƙwalayen abin kallo ne.

Na miƙa mata ɗan farantin hannuna ta karɓa, sannan aka buɗe ɗayan duk fa kalar faranti kalar ɗan yankin da ke rufe da shi, leshi na gani na faɗa, da takalmansa,jakarshi,mayafinshi,a samansu aƙwatina ne masu ƙyau guda huɗu sai ɗan ƙarami a sama.

Aka miƙo mini ɗan akwatin na buɗa, ɗan zobe ne, mai ƙyau na Diamond da ɗan ƙaramin zanen abin sarauta a jikinsa, ya yi mini ƙyau sosai, na ajiye shi gefe, aka dinga miƙo mini ƴan aƙwatinan duk turarurruka ne a cikinsu desginer na miƙa musu, sannan aka buɗe na cikon na huɗun,kaji ne gasassu har guda huɗu masu rai da lafiya,ko a ido ka gansu sai ka yaba.

Sai ƙamshi ke tashi sai sheƙi suke yi, da wuƙaƙe biyu ƙanana a gefe ɗaya,ɗayan gefen kuma cokula masu yatsu ne (Knife and fork) nayi murmushi na koma sosai na jingina.

"Gimbiya Allah ya ja da rai, waɗannan kayan siyen baki ne inji Yarima." Sannan ta buɗa na biyar ɗin bandiran kuɗi ne ƴan ɗari biyar biyar sun kai guda goma.

"Allah ya ja da ran Gimbiya idan har baki ya siyo wannan leshin Gimbiya zata saka, sai mu tafi tare can gidan shi Yarima ɗin, tare da dukkan farantan nan, saboda ko za'a buƙata a can."

Na miƙe tsaye, a daidai lokacin da jakadiya ta gama tata maganar cikin ƘASAITA na haye matattakalar bene zuwa ɗaki inda na ce su Musulum su zo.

Na basu umarnin da su ɗauki kayan da ke saman gadona su ma lulluɓe da fararan yanki, ina isowa falo, sai da naga na daidaita wajen zamana, sannan na ce da jakadiya.

"Ga waɗannan ki kai masa,ki faɗa masa baki ya siyu, amma Gimbiya hutawa take yi sai nan ƙila da sati biyu."

Na umarci Mansura da ta ɗauko mini faranti a kicin,ta miƙe da sauri. Faranti ɗaya kayan sawa ne, riga da wando da babbar riga, waɗanda aka ɗinko su daga ƙasar Sinigal,aƙwalinsu, sai dogayen riguna guda huɗu, sai gajerun wanduna huɗu, duk a ƙwalayensu da silifas, da turarurruka huɗu da tuwal ɗaya a samansu ne ke da zobe ƙwaya ɗaya na azurfa.

Ɗaya farantin kuma alƙur'ani ne da abin ɗora shi, ɗan katakon nan da dardumar sallah mai beza mai ƙyan gaske, da carbi da littafin ibada da hukunci ƙwaya ɗaya.

Farantin da Mansura ta ɗauko mini kuwa, na sa hannu na ɗauki kaza ɗaya, na ɗora a saman shi, cokali mai yatsu ɗaya, gefe ɗaya na sa tufa biyu,lemo biyu,ayaba biyu, na ɗauki dabino huɗu na zuba, na bayar da umarnin a ɗauki yanki ɗaya a rufe.

*ƘASAITA BOOK 1*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 9


Sannan na ɗauki kaza ɗaya na baiwa ƴan kawowa, tare da bandir ɗin kuɗi.

"Jakadiya ku je ku raba,ke da abokan rakiyar ki, waɗannan kuma na gaya miki ki kai masa,ki ce Gimbiya na gaishe shi baki ya siyu, amma tana hutawa har nan da sati biyu."

"Maganar ki ita za'a bi, godiya muke."

Na koma na ƙwanta jikin kujerar da nake zaune, ina kallonsu suka bi layi suka fita kamar yanda suka shigo, bayan nan kuma na umarci su Mansura da su ƙwashe kayan su ɗan ɗibar mini kayan marmarin,su ɗauki ragowar, haka kajin na ce su ɗauki ɗaya.

Cikin girmamawa da biyayya suka aikata yanda na faɗa, tun daga lokacin kuwa sai na koma sama,a inda na umarci su Mansura da su ɗauki daki ɗaya a ƙasa su ƙwanta,ni sai da safensu.

Baƙin ciki, takaici, suka saukar mini a daidai lokacin da na tuno da Anwar,na yi tunanin da shi na aura,muna can ya shigo ɗaki a sunanshi na ango, ina can yana tarairayata da nuna mini kulawa ɗari bisa ɗari, wannan tunanin yasa na sha kayan baccina, na buɗe ƙofar da za ta fitar da kai barandar da take a gaban gidan.

Na dafa ƙarfen barandar, wanda na mayar da idanuwana na lumshe,a daidai lokacin da wani ni'imtacciyar iska ta kaɗa, iska ta dinga ɗaukar gashin kaina tana juya shi a hankali, hawaye masu sanyi suka tsiyayo mini a kumatuna, a lokacin da tunanin rayuwata ta raunana ya faɗo mini,anya kuwa zan amince in dinga irin wannan zaman jakadancin? Komai ke tsakaninka da mijinka sai wata ta sani.

Na buɗe idanuwana tare da ware hannayena tamkar ina jiran wani ya rungume ni, kamar an ce in kalli barandar sama wacce take kallon tawa barandar,sai kawai na hango mutum a tsaye, shi ma ya dafa ƙarfen barandar ya sunkuyo yana kallona.

Da ɗan nisa, shi ya hana ni in gane ko waye, kuma ga iska tana kaɗawa, natsuwa na yi sosai na ƙura masa ido, ba abin da idanuwana suka karanta mini sai angona Faysal.

Tsanarshi na ji ta ƙaru a zuciyata a take ban san lokacin da na juya na shige cikin ɗakina ba, na mayar da ƙofa na kulle, na wuce na faɗa gadona a inda na kasa tunano komai sai Dad wanda da ya san rayuwar da ya jefa ni ciki, na san da bai fara ba.

Ni ce har ƙarfe biyun dare zaune a abin sallah ta, ina roƙon Allah ya kawo mini canjin rayuwar da ta fi alheri a gareni,ni kam na san ba zan iya wannan auran ba, na yi tunanin wai yau ne daren farko (first night) ɗina,amma gani nan a zaune ko kalar ango ma ban gani ba.

Ƙarfe shida na safe na farka, hakan yasa na yi saurin saukowa daga gadona, domin gabatar da sallar Asubahi ɗin da na makara ban samu yi ba. Ƙarfe tara na safe har na gama komai na sauka ƙasa domin nemawa cikina abin da zan ci.

Wani abin mamaki da na gani, shi ne yanda har an gama gyara ko'ina na falon, sai ƙamshi ke tashi, sannan kuma gaba ɗayan gayyar ƴan matan nan sun hallara waje ɗaya ni kawai ake jiran fitowata. Tausayinsu ya kama ni,a zuciyata na ce bayin Allah, insha Allahu sai na raba ku da wannan ƙangin na bauta,a take na ji ina ƙaunarsu, sannan ya zama dole ma in ɗan saki jikina da su, saboda su ji daɗi su ma.

A take na yi murmushin dariya, "A'a Mansura har kun tashi?"

Cikin sakan ɗaya har sun gama isowa bakin matattakalar benan da nake saukowa sun zube ƙasa.

"Haba, abokaina, ya zaku dinga yi mini haka, tamkar wata wacce ku ke bautawa, na san dole ne ku ba ni girma, amma irin wanda nima zan ji daɗinshi ba irin wannan ba.

Sai na ga wannan ya kalli waccan, waccan ta kalli ƴar uwarta, na sauko na dinga dafa kafaɗar na kusa da ni.

"Ku zo muje." Suka biyo bayana. Ina zama gaba ɗaya suka zube ƙasa.

"Gimbiya mun gaishe ki. Barka da ƙwana?"

Na amsa masu da lafiya ƙalau. A nan na dinga tambayarsu sunayensu, ɗaya bayan ɗaya, wani abun in yi ƙoƙarin ba su dariya, amma bayin Allah nan sai na ga sun kasa yin dariya, ga ta kuma suna son yi. Na waiga na kalli Mansura.

"Mansura, har yanzu ban fahimci waɗanda ke kicin ba."

"Allah ya ja da ran Gimbiya ga mu nan."

A take na ga ƴan mata masu ƙyau suma.

"Yaya abinci?"

"An gama shirya shi a wajen cin abinci, na Yarima fa?"

"Ai can ake haɗa masa shi ma."

"Su wa ke haɗa masa?"

"Yana da masu yi masa."

*Maza ko mata?"

"Maza ne."

Na taɓe baki, sannan na miƙe na bada umurnin a kai ni wajen cin abincin. Kai wata duniyar ma in ka shige ta, sai ka ga tamkar yau aka haife ka, saboda ganin sabon yanayi da sabon tsari.

Duk a cikin falon muke, amma da muka bi ta wata hanyar sai na ga tamkar mun fita ƙasashen turawa, wani ɗan rukuni ne mai kama da ɗan ƙaramin wajen shaƙatawa an saka masa wasu labulaye masu kama da rumen kitso, da ka buɗa sai ka ji sun yi kankacakau, madadin tebirin cin abinci da muka baro a falo.

Sai na samu shi kuma wajen shafe yake da kafet, mai ƙyan gaske ga wani tsakiya mai zagayewa, sannan na ga an shinfiɗa wani yanki mai ƙyan gaske,fari mai zanen jajayen fulawoyi, shi ma zagayayye ne,saman shi aka jera kayan abincin,ga tuntayen alfarma guda uku gefunansa.

Ina zama jakadiya na isowa, ta zube gabana ta kai gaisuwa.

"Allah ya ja da ran kilishin Gimbiyoyi jakadiya na yi miki barka da Asuba."

Na yi murmushi, "Gimbiya na amsawa jakadiya,kin ƙwana lafiya?" Sai na ga tana sussunne kai.

"Jakadiya ba a amsa mini."

"Lafiya lau, Kilishin Gimbiyoyi."

"Dama Yarima ne, ya aiko ni ya ce a gaya miki yana jiran gaisuwarki, sannan yana gayyatarki karya kumallon safiyar nan,zuwana na huɗu kenan a lokacin dai baki fito ba."

"Ki gaya masa ina amsawa, amma ki ce kin same ni har na Zauna saman in da zan karya nawa kumallon,sai dai ya jira wata safiyar sai ya ƙara aikowa."

"An gaishe ki." Ta miƙe da hanzari ta yi gaba,ni kuwa na buɗe kayan cin abincina, amma a cikin sauri ƴan matan nan masu girki suka karɓe ni. Farfesun naman kai ne da sinasir a gefe ɗaya, sai soyayyan dankali mai ƙwai a ciki, ga kunun gyaɗa a gefe ɗaya, ban da ruwan shayi da yake a gefe, da cinyoyin kaji zalla an soya su.

Bayan na gama ne na umarci su Mansura su zo su raka ni in zagaye gidan, har waje saboda sanin yanda yake duk da ƙwanana biyar kenan a gidan, amma a tare nake da jama'a ƴan biki.

Samana dai falo ne babban gaske, wanda ya sha kujerun alfarma har kala biyu, kowanne rukuni,kalar kujerun su daban, amma irin na gidan sarauta, sai ɗakuna ƙwaya biyu kacal, wani gado ne ƙwaya ɗaya a tsakiyar ɗakin zagayayye mai kama da ƙwano (Circle), ƙaton gaske,an zagaye shi da wasu labulaye farare, wanda sai dare ya yi ake danna wata na'ura wato remote sannan sai ya sauko.

Gaba ɗayansa shinfiɗe yake da zanin gadon da ya bazu ƙasan shi, wanda kafet mai laushin gaske ne ƙasan shi, shi ma a zagaye yake, sai daga can gefensa kujeru ne masu zagaye aka yi masu rukuninsu daban, har ɗan tebirin tsakiyarsu (Centre table), sai daga kusurwa tebirin rubutu ne har da kujerunsa biyu.

Daga ɗan nesa da gadon kuma kujerar kushin ce doguwa, ƙwaya ɗaya, wacce ta sha shinfiɗar dardumar sarauta da filillikan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login