Showing 9001 words to 12000 words out of 26686 words

Chapter 4 - Kasaita Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

30 Dec 2024

109

masa magana ba, yasa na lumshe idanuwana kawai. Jin an ɗan tsaya da tafiya yasa na buɗe idanuwana. Labulaye kawai na ga an janye, sai da na waiga ma sannan na gane falon sama muke,babu wata alamar ƙofa a wajen da suka buɗe labulan. Hajiya Kilishi kawai na taɓa wani ɗan makunnin kunna fitila, sai kawai na ga ƙofa ta buɗe.

Mamaki biyu ya dirar mini a daidai lokacin da muka shiga ɗakin, ban gama mamakin ƙofar ba sai kuma gani na dasa na ɗakin da muka shiga. Ɗaki ne wanda ba su da maraba da na asibiti. Gado biyu ne a ɗakin irin gadajen asibiti, sai daga can gefe ɗaya an saki wani koran labule. Abin ka ga ƙaton ɗaki, ban ƙarasa gani ba naji an ɗora ni saman gado, wata irin kunya ce ta saukar mini a take sanadiyyar sumbatar goshina da Yarima ya yi a gabansu Hajiya.

Madadin in ga ya fita, sai na ga ya zauna gefen kaina,ya sa hannu yana gyara mini gashin kaina, da ya baje fuskata,ko in ce ya baje ko'ina. Madadin in ji sun ce ya fita, sai dai na ga an sako wani ɗan koren labule, wanda ya sauka saman cikina, ma'ana ya raba tsakaninmu da su. Ni kuwa ta kwance sun raba ni biyu suke nufi kenan, kaina da gangar jikina ta sama ta wajen Yarima, daga cikina zuwa ƙafafuna suke wajensu.

Sam ni ban wani tsorata ba, saboda dama ita ke zuwa yi mini awo duk bayan sati biyu, sannan kusan duk ƙwana uku sai ta zo ganina, ballantana ma da cikina ya tsufa sosai. Shi kuwa ganin an yi haka, sai na ga hankalinsa ya tashi matuƙa, har da wani irin gumi da ke tsiyaya daga saman kansa. Ganin haka yasa na sa hannuna ɗaya na shafo kumatunsa, ya juyo sosai ya kalleni cikin sanyin murya, na ji ya yi mini magana.

"Da ciwo ko?"

Gaskiya ni bana jin wani ciwo ko ɗaya, saboda haka na girgiza masa kai alamar a'a. Hannunsa ɗaya da ke maƙale da nawa ya ɗago ya sumbata,ni kaɗai nake jin abin da ake yi mini,amma ba ni da damar nunawa, ganin yanda hankalin Yarima ya tashi.

Ba afi minti ashirin da kawo ni ɗakin ba na haifi yarona namiji, amma ni kaina na san cikin mintunan na fita daga kamannina, shi kuwa Yarima ya sha cakuma tamkar zan karya shi.

Ni kaina ban san duk jama'a sun san ina ɗakin haihuwa ba, sai da na fito. A nan ne na ga falon sama cike da jama'a. Ina fitowa kuwa bakuna suka dinga haɗuwa wajen yi mini sannu, ban da jakadiya wacce ta rangaɗa guɗa tamkar ta yi hauka don murna. Yarima ne ɗauke da yaron naɗe cikin jakar tawul ɗin jarirai, amma sai da jakadiya ta tsugunna ta karɓe shi daga hannunsa.

Ni kuwa na sha gayuna tamkar ba ni ce na haihu ba. Tun daga ranar kuwa shagali ya tashi, amma kuma Yarima yana liƙe da ni,in ka ga ya fita daga ɗakina,dangin mahaifiyarshi ne ko nawa, shi ma yana yi yana zagayowa.

Ana saura ƙwana biyu suna aka kai wa Mai Martaba jariri har gida, domin yi masa huɗuba, wanda taro suke yi na musamman idan za'a huɗubar nan, duk da dama ba ganin farko ba ne ba ga Mai Martaba, domin jakadiya ta kaiwa Sarki jaririn da Mama tun ranar da aka haife shi. Haka kuma Daddyna shi ma an kai masa shi gida.

Wani abin mamaki kuma shi ne yaron kamar su ɗaya da Mai Martaba Sarki, ba ni da wani bakin magana sai dai kawai na yi wa Allah godiya, na yarda aka nuna mini ƙauna.

Shi kuwa Yarima tamkar yau aka kai ni gidansa, saboda irin yadda yake liƙe mini. Maganar mai taya ni zama kuwa, Yarima sam ya hana mata sakewa, saboda sai ta yi barci, sai kawai na ji shi rungume a jikina,ko da kuwa zan kulle ƙofar barandar bayan ɗakina, sai yasa mukullin ya buɗe.

Tun saura ƙwana biyu suna gida ya ɗauki cika, duk da Mai Martaba yasa a buɗewa jama'a gidan baƙi. Daren suna kuwa, abin har tsoro ya ba ni, irin yawan jama'ar da ke ƙwararowa gidanmu, ban da kaya da aka dinga shigowa da su,wai duk nawa ne ni da jaririna.

Ba zan iya gane ko ƙarfe nawa na dare ba, amma tabbas na san dare ya soma yi sosai. Cikin ɗan sauri na tashi zaune, ina lalubar gabana inda jaririna ke ƙwance, amma ban ji kowa ba,gudun kada in kunna fitila mutanen da ke ƙwance ɗakina duk su farka, yasa na yi amfani da fitilar wayata, amma ban ga jaririna ba. Na haska gaban Aunty Salwa da take ƙwance kusa da ni, sai ƙaton goyon ɗanta a gabanta.

A hankali na miƙe na dinga haska gabanta ina haska gaban baƙin da ke ƙwance a manyan katifu a tsakar ɗakina, duk da ƴaƴan ƙannai da matan yayye da ƴan uwan Mamee, amma duk ba jariri a tare da su.

Na bi a hankali na buɗe ƙofar shiga sama, saboda duba su jakadiya da mata biyun da suke taya ni ƙwana da ƴan hidimomi ni da jariri. Duk na haska gabansu babu alamar ƙaramin yaro a tare da su.

Sam ni ban ruɗe ba saboda na san da wuya a sace yaron nan, sai dai abin da na yi tunani ko dai suna wata al'adar ne wacce sukeyi da tsakiyar dare. Har na koma na ƙwanta sai na ji na kasa bacci ni kaina, ban san ina son jaririna ba sai yanzu. Na miƙe cikin sanɗa a hankali na buɗe durowar da alkyabbobina ke rataye na sanya ɗaya saman rigar barcin jikina.

Ban yi wani motsi da ƙarfi ba har na samu na buɗe barandar ta wacce zata kaini dakin Yarima, domin in sanar masa abin da ke faruwa. Ina buɗe ƙofarshi da makulli ba abin da na ci karo da shi sai ɗan sayon sayon safar jaririna ɗaya. Na sunkuya na ɗauka, sannan na ƙarasa cikin ɗakin.

Fitilar wayata dai na yi amfani da ita ina duddubawa, na yi murmushin da ya ratsa har zuciyata, saboda jin daɗi. Na lallaba na isa inda suke ƙwance. Ƙwance yake a rigingine ya ɗora yaron a ƙirjinsa, fararen kayan sanyi ne ya sakawa yaron,zaman da na yi a gefensu wannan yasa na kunna fitilar gefen gadon da suke ƙwance. Ƙyau Yarima ya ƙara yi mini. Na sunkuya na sumbaci goshinsa, tare da shafa gashin kansa.

Gani na yi ya buɗe idanuwansa a hankali, "Ka firgita ni fa."

Ya yi ƴar miƙar nan ta masu bacci, sannan ya tallabe yaron, ya miƙe zaune tare da sa ɗaya yana murtsikar idanuwansa alamar tashi daga bacci, har da ƴar guntuwar hammarsa. Zolaya ta sa nayi alamar tashi in tafi, sai a lokacin ne ma ya yi magana.

"Ina za ki kuma?"

"Ɗakina."

"Da me ya kawo ki?"

"Neman yarona."

"Shi kaɗai ya dame ki,ni fa? Ko yanzu ba'a yi da ni?"

"Na isa."

"Zo nan."

Ya nuna kusa da shi da hannu ɗaya. Na iso na zauna.

"Dama na ɗauko shi ne saboda ina son yin magana da ke,kin ga da wuya gobe mu samu ganin junanmu da zamu iya tsayawa mu yi magana, saboda jama'a.

Dama game da sunan yaron nan ne. Mai martaba ya mayar masa da sunansa, shi ne na ce bari na tambaye ki in ya yi miki,kin san shawara tana da daɗi."

"Yarima ba ka gajiya,in ba ya ga zolaya irin wacce ka saba yi mini,ya ma zaayi in buɗe baki in ce bana son sunan da Sarki ya sa. Kai dai ka faɗi maganar da ke damun ka, ba dai wannan ba."

"Ita ce mana, sai kuwa maganar zuwa gida wanka, gidan mu fa ake kaiwa, ma'ana wajen Mama za'a kai ki, gidan Sarki, amma za'a tambaye ki ra'ayin ki."

Ya kama hannuna ɗaya, "Don Allah ki ce nan za ki zauna,a kawo miki masu kulawa da ke kawai,kin san Allah ko jakadiya kawai sai ta kula da ke, ballantana daga gobe kin gama wankan ganyen, magunguna zaki cigaba da sha."

Na yi shiru, tunanin ya za'ayi in ce bana zuwa. Na girgiza kaina.

"Ba zan iya ba, kunya nake ji."

"Kunyar me, ba gidan mijinki ba ne ba."

"Saboda me kai kuma ka ke son in Zauna nan gidan."

"Saboda ni."

"Ba ka da lafiya ne?"

"A'a,in dinga ganin ku."

"Ai can ma zaka dinga ganin mu ko?"

"Yasmin, Please understand me."

Na miƙe tsaye, "bari in tafi kada wani cikinsu ya farka bai gan ni ba, kaga kunya zan ji."

Bai ce mini komai ba, ya koma ya ƙwanta. Ni kuwa na juya na nufi ɗakina, amma sai na ji duk jikina ya yi mini nauyi.

Da na ƙwanta kuwa har gari ya waye ban yi bacci ba, saboda tunanin maganar Yarima ina son in ga jakadiya in gaya mata, saboda ko tana da dabarar yi, amma jama'a sun yi yawa.

"Subhanallahi!" Na faɗa a zuciyata, saboda ganin yanda jama'a suka yi yawa, har sun fi duk taron da aka yi. Cikin gidan kuwa jama'a mata da maza,cin abinci akeyi ban da kayan sha,kai abin ya yi mini yawa, har na zamo ba na iya gane komai.

Daɗina ma ɗaya ba yawo ake yi ba, zaune nake a saman kujerar mulkina a falon ƙasa, sai dai kowa ya zo ya kawo tashi gaisuwar,in kuwa na miƙe tsaye, to kaya zan je sakewa. Jariri Jafar Bn Jafar,yana hannun yayar Mamee Ruƙayya a riƙe, sai dai a leƙa a gansa, wanda kuwa yake da buƙatar ganinsa sosai sai dai ya kalli ƙaton hotonsa da ke manne a falona, wanda Mai Martaba ne ya aiko da shi.

Ƙarfe huɗu na yamma kuwa duk jama'ar da ke gidan mu ta dawo waje, ana gama sallah kowa ya nemi wajen zamansa, tamkar dai yanda suke yin kayansu, amma yanzu ya sha bamban da na baya, tunda na baya za ka ga jama'a bayan mu, yanzu kuwa daga ni sai Yarima, sai kuwa dogarawa guda bakwai da ke zagaye da mu.


#####
[2/21, 08:11] Ummi Tandama😇: *ƘASAITA BOOK 3*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 6


Yaro Jafar Bin Jafar na hannun jakadiyar Sarki, tsaye wajensu Mama da Mamee da Hajiya Kilishi, ban da ragowar mutanen da ke bayan su. Dad ɗina kuwa ga kujerarsa ga ta Sarki.

Wasan ƙwallon dawaki aka fara yi (Polo), sai kuwa ɗan hawan Daba, sai wani wasa da shanu ke yi (Hawan Ƙaho), ban da wasanni da raye-raye da yare kala-kala suka yi. Saboda Yarima dai shi ne baya magana, amma ta hannu da ta ƙafa yake yi mini magana, shi ne yatsun hannuna ɗaya na riƙe da nashi yana ta wasa da su, ban da idan na gaji na ƙwace ya koma tsokanar ƙafa.

Duk bayan an gama wannan hidimomin ne wanda za mu iya cewa ƙarfe biyar da rabi ta yi, sai na ga wasu irin ƙartin mutane guda biyar sun shigo filin, kowanne ɗaure da bantai a jikinsa, ma'ana ba riga sai wata fata mai ruwan jinin kare ɗaure a ƙugunsu, ga shi iyakacinta cinyarsu.Waziri ne ya miƙe ya fara magana.

"Yau ne ranar da Allah ya kawo muka ga jikan Mai Martaba Sarki, rana ce ta farin cikin kowa. Duk wani wanda yake gidan nan ya san sunan yaron shi ne Jafar Bin Jafar, wanda ya gaji sunan Sarki kenan. Yanzu za mu ƙara tabbatar da cewa yaro namu ne, jinin mai girma Yarima ne, duk kuwa wanda ya tashi a gidan nan ya san ƙa'idarmu ce hakan, saboda haka jakadiya Bismillah."

Ni dai na sa ido in ga ikon Allah, na san kuwa ba ni kaɗai ba, har danginmu gaba ɗaya, shi ne ƴan uwan Mamee da Daddyna.

Jakadiyar Sarki ta sauko daga sama riƙe da jariri a hannunta sanye da kayansa masu ƙyan gaske. Tana shigowa tsakiyar filin nan sai na ga ta miƙawa ɗaya daga cikin ƙartin nan ɗana. Na ɗan yi alamar zan miƙe, Yarima ya riƙe min hannu. Ban ko kalleshi ba, amma na san dai na koma na zauna.

Ina kallo aka tuɓe (cirewa) yarona kayansa gaba ɗaya, ya zamo tamkar yanda aka haife shi. Ganin ƙaton nan ya cilla jaririna sama yasa na yi saurin cakume cinyar Yarima da hannuna ɗaya. Sai a lokacin na ji Yarima ya yi magana, sai da ya jefa shi sama sau uku yana cafewa, sannan na ga ya miƙawa tsohon cikinsu.

Me zan gani? Gani na yi ya saka mini yarona a cikin ruwan nan da ke cike da uban bahon ƙasar nan,ai ban san lokacin da na miƙe tsaye ba na ce "Yarima kalli ka gani, za'a kashe shi." Da sauri na ga Yarima ya fizgo hannuna ya zaunar da ni.

"Yasmin ki ƙwantar da hankalinki, kada ki ba ni kunya. Ni nayi imanin Jafar ɗana ne,ni ne mutumin da ya fara sanin Mamansa,ni na san...."

Ai kuwa wannan tsohon mutumin yasa yarona cikin ruwan nan ya barshi ciki bai ɗauko shi ba. Yarima ya matsa hannuna sosai, "Kalle ni." Na juyo na kalleshi.

"Me ki ka gani?"

"Ba komai." Na juya na kalli inda aka jefa mini yarona.

"Ka gani ko,ka gani ko." Jin ya yi shiru ya ƙyale ni yasa na yi saurin kallonsa.

Fuskarshi ba wata walwala da ya juyo ya kalleni. Ni kuwa har firgita na yi don tsoro, wannan yasa na yi shiru na zauna sosai, sai kuma hawaye da na ci gaba da zubarwa. Ba wani mai ƙwaƙƙwaran motsi a cikin mutanen da ke wajen nan, wajen ya yi shiru kowa yana kallon ikon Allah, tamkar a ce wani shugaban ƙasa ya iso wajen taron,an tashi za'a yi taken ƙasar su.

Abin ka ga uwa, sai na ji na kasa haƙuri, sai da na ƙara kamo hannun Yarima,ko kallona ma bai yi ba, na juya na kalli Dad ɗina,amma ban ga alamar hankalinsa ya tashi ba, kowa na kalla sai in ga hankalinsu ƙwance yake, sai dai alamun su da ya nuna suna jiran ganin abin al'ajabi.

Sai da aka ɗauki tsayin mintuna wajen sha biyar, sannan na ga yasa hannu ya ɗauko shi. Yanda aka yi masa da farko, haka ya yi masa yanzu, shi ne cilla shi sama sau uku. Inda na ga kamar hankalin Yarima ya tashi, shi ne a inda aka cilla shi na farko, sai na ga Yariman ya ɗan yi alamar miƙewa tsaye, na biyu sai na ji yasa kuka irin nasu na jarirai, sai na ga Mai Martaba ya miƙe tsaye.

Gaba ɗaya mutane suka miƙe tsaye aka dinga ihu da tafi,sai a lokacin na ga Yarima yana dariya, ya juyo ya kalleni, kallon da ni da shi kawai muka san fassarar shi. Hankici ya miƙo mini, ma'anar shi na goge hawayen fuskata, tare da cewa.

"Na gode." Cikin sanyin murya.

"Wata al'ada sai mu masu ita."

A nan na ga jakadiyar mu ta gangara tsakiyar filin nan, jakadiyar Sarki na karɓar yaron sai na ga ta baiwa tamu jakadiyar. Murna kuwa da jakadiyar mu ke yi kamar zata kifa don sauri.

Daga nan dai jakadiya ta ɓace mana, sai kuwa Sarki da ya tashi ya yi wa jama'arsa godiya tare da ni kaina da iyayena.

Ana haka aka miƙo mini jariri Jafar,wai zan kai wa Sarki shi. Kamar na yi ihu don kunya. Ganin na kasa tafiya yasa Yarima ya karɓa, ina kallo ya miƙawa Mai Martaba, shi kuwa ya ɗan tsaya yana nunawa jama'a shi, sannan na ga ya miƙawa wazirinsa.

Jafar ya yi lamo cikin baƙaƙen kayan sanyi, waɗanda aka ɗorawa ƙaramar alkyabba a sama. Waziri ya miƙawa Hajiya Kilishi wacce suke rukunin mata Iyaye. Ina kallo ta baiwa Mamee. Mamee da ƙyar ta karɓa,ni dai na san kunya hana ta karɓa tun farko.

Bai fi na mintuna biyu ba ta miƙawa Mama. Mama ce ta kaiwa Daddyna, inda na ga Daddyna ya karɓa yana dariyar farin ciki, irin wannan dai aka ci gaba da yi har lokacin sallar Magriba ya ƙarato, aka rufe taro da addu'a aka tashi.

**** **** **** **

Gama arba'in ɗina da ƙwana uku, ya yi daidai da hidimar bukukuwan barorin gidanmu,ƴan mata da samari, wanda su Mansura tun da biki ya matso take kukan rabuwa da ni, duk da an ce wa mazajen su mai so zai iya barin matarsa ta yi aiki, ana biyanta kuɗin aikinta.

Bayan ba kuɗin mota za su dinga biya ba, gidaje ne aka gina musu a cikin dajin gidanmu, sai dai na san muna da ɗan nisa da su.

Ana gobe kai amarya ne na taka gidan yari tare da ɗana Ammar, wanda yake ɗauke ga kafaɗar Mansura amaryar Isma'il.

Gaba ɗaya na sa aka jera su layi, na dinga tambayarsu. Yawanci laifi ɗaya gare su, shi ne rashin kunya, wasu kuma sun tarewa Yarima hanyar fita,babu dai wani taƙamaiman mai laifi, sai mutum tara,su ne aka haɗa baki da su za'a sawa Yarima guba a abinci, Allah ya toni asirinsu.

Macen da na samu lokacin da Yarima ya kawo ni gidan yarin, ita kuma laifinta shi ne ta aiko da takarda tana son Yarima, shekarunta ba su wuce ashirin da huɗu ba, sai dai ƴar wahala ce ta mayar da ita baya kaɗan.

Gaba ɗaya mazan na sallame su,ban da taran nan, kowanne daga cikinsu na bashi jarin dubu ashirin da kekunan hawa. Su kuwa matan keken ɗinki da dubu goma-goma. Mubaraka ce kawai na ce a kai mini ita gidana da sauran tambayoyin da zan yi mata. Mazan nan tara kuma na ce a tsare mini su, sai na yi bincike a kansu.

Wata ɗaya na baiwa Mabaraka akan ta fito da miji a yi mata aure,in kuwa ba haka ba duk abin da ya biyo bayan haka, ita ta janyowa kanta. Na kawo dubu biyar na bata ta sayi sabulu kafin ta fito da miji.

An yi bukukuwa lafiya, taro kuma ya tashi lafiya, amma inda Allah ya ba ni sa'a har yau ina tare da yarana na gidana, duk mazansu sun bar su, sai dai wasu biyu da aka kawo mini saboda ƙwana. Ammar kuwa ya zama abin ƙauna ga kowa. Yarima kuwa,ni da shi tamkar amarya da sabon angonta.

**** **** ****

Ƙwanciyar hankali tana neman gagarar mu ni da mijina, da duk wani masoyinmu, sakamakon juya bayan da Sarki ya yi mana,a cikin wata biyu kenan. Dabara,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login