Showing 6001 words to 9000 words out of 26686 words
wajen.
Bayan kamar mintuna uku, sai muka ga ƙura na washewa a hankali. Ganin wani mutum muka yi a tsaye zagaye da shi, ana ta watsa kuɗi, jama'a na ta tsinta. Yarima ya juyo ya kamani.
"Zo ki ƙwanta, bari na sauka ƙasa na dawo."
"Ka turo mini jakadiya." Ya amsa da to. Ya yi waje.
Cikin mintuna sha biyar sai ga jakadiya a nan nake tambayar ta me ke faruwa? Bayan gaisuwar da ta yi mini,a nan take ba ni labari wai wani ɗan Sarki ne ya zo, tun ba mu daɗe da tafiya ba. Ba yaudarar da ba ya yi a gidan nan, shi ne rabon kuɗi, abinci da sauran kayayyaki, duk wanda aka kaiwa ya ƙi karɓa, to zai faɗa ne. Take gaya mini ko ita an bata magani ta zubawa Yarima a abinci da sauran wurare.
"Kin karɓa?"
"Eh, saboda in ka ƙi karɓa sai dai a wayi gari ba kai."
"Ɗan Sarkin wane gari ne?"
"An ce babban Yayan su Yarima ne,wai shi Abdulrahman."
Na yi shiru. A nan take na tunano labarin da Mama ta ba ni, ina cikin wannan tunani sai ga Yarima ya shigo da saurin shi.
"An kashe mutum uku a wajen can."
"Me ye dalilin kashe su?"
"Wai saboda sun ƙi ɗibar kuɗin da yake sa wa ana watsawa."
"Wa ye shi?"
Wai Yayan mu ne."
"Meye dalilinsa na yin haka?"
"Sarauta yake so."
Na yi shiru tare da faɗuwar gaba mai tsanani saboda tunanin kada a kashe mini mijina.
Canja alkyabbar jikinsa ya yi, ya ƙara sa turare a jikinsa.
"Ina za ka?"
"Wa je." Na miƙe da sauri.
"A'a kada ka fita ya harbe ka."
Ya yi murmushi.
"Ai mu ba'a kashe mu ta nan ɓangaren."
Ya nuna jakadiya da ɗan yatsa.
"Kin ga wacce za ki danƙawa amanar mijinki nan. Sai kuwa masu dafa mini abinci, ta sanadiyyar su ake yi mini komai."
Ya iso inda nake tsaye, ya tallafi kumatuna, cikin nutsuwa ya fara magana.
Kada ki tayar da hankalinki,ki yi tunanin cewa kina da yaron ciki, zai iya zuɓewa ta kowanne hali,ki ƙwantar da hankalinki."
Hawaye suka ƙarasa gangarowa.
"Ni dai ban yarda ba."
Ya yi murmushi, "Yasmin kada ki karaya mana. Ki tuna gidan sarauta fa ki ke. Haba Honey."
Na ƙwantar da kaina a ƙirjinsa, sai kuka sosai. Ya ɗago ni ya ƙura mini ido ba tare da ya yi magana ba. Ɗan tsayin minti ɗaya, sai kawai na ga ya mayar da ni ya rungume ni sosai. Ya ɗago ni da saurinsa ya sumbaci goshina, ya dawo ya tsotsi bakina,bai ce komai ba ya ɗauke ni cak ya ɗora a gado. Ya ja bargo ya lulluɓe ni, ya sunkuyo yana gyara gashin kaina, wanda ya zubo a fuskata,ko in ce wanda ya hautsine saboda ƙwanciya.
#######
[2/20, 13:07] Ummi Tandama😇: *ƘASAITA BOOK 3*
*NA*
*MARYAM KABIR MASHI*
Page 4
Ya ƙara sumbatar goshina, kawai ya juya ya tafi. Bin shi na yi da kallo, shi yasa idanuwana suka gane mini ba jakadiya a ɗakin nawa. Yana fita tana shigowa na mayar da kaina na ƙwantar,sai na ji hawaye sun ƙi tsayawa. Jakadiya ta iso ta tsugunna gaban gadona.
Allah ya ja da rai,ai ke ce ya kamata a ce kin ƙara ƙarfafa masa gwiwa tare da shawarwari, ke ce mace,kin fi shi tausayi, ke ya kamata a ce kin tsaya kin lura da tambayar me yakamata a yi wa talakawa,shin hukuncin da bai cancanta ba a yi shi?"
Na tashi zaune. "To yanzu jakadiya,kina jin ya ce an kashe mutum uku, wacce kuma daraja gare shi,ai kin ga bai dace ba ya fita, sai ya tsaya ya ga ya zata kasance."
Ta yi murmushi, "Yana shugaba? Ai shugaba bai ga ta zama ba, ke dai kiyi ƙoƙari ki koyi dabarun taimakawa mijinki da shawarwarin da zai sa jama'arsa ta bi shi, ta kuma ƙara ƙaunarsa."
"Kin san su ne ke? Saboda ni kin ga ba ƴar sarauta ba ce ba,haye min tayi da rana tsakiya. Kin ga kuwa ba zan san komai ba game da ita."
Jakadiya ta yi murmushi, ta ƙara gyara zama. Tun da ta fara magana nake tallaɓe da kumatuna, saboda al'ajabin abubuwan da take faɗa. Wannan ne yasa a take na ɗauki waya na daddana, domin neman Yarima, saboda fara gudanar da dabarar ta farko cikin dabarun da jakadiya ta koyar da ni. Amma ina! Hayaniya ta yi yawa,ko ƙarar ta ma ba ya ji. Wannan yasa na yi haƙuri sai ya dawo gida, na umarci jakadiya da ta je tasa a sa fanka a kori duk warin turaren da suka saka a gidana. Na bata room Freshner gidan Yarima na ce a sa mini ita.
Yariman bai samu shigowa ba sai ƙarfe tara da rabi na dare. Cikin nutsuwa ya zo ya zauna gefen gadon da nake ƙwance, ya sunkuyo ya sumbaci laɓɓana.
"Sannu da dawowa."
"Ke zan yi wa sannu, ke da na barki ba lafiya, na so shigowa in ga jikinki,amma ina, na so in gaishe ki ko da a waya ne, amma duk hakan ba ta samu ba, sai yanzu ma na ga kiran ki a wayata, missed call,ki yi haƙuri ban ji ba."
"Ba komai. Yaya komai dai ya tafi lafiya?"
"Eh, to hakan nake tsammani."
"Wai me ye ya faru?"
"Wani mutum ne ke neman tayar mana da fitina, shi ne na sa aka kama shi har da yaransa, wajen goma, bayan an kama su ne na turawa Mai Martaba Sarki da aiken cewa ga masu son tayar da zaune tsaye an kama. Kafin Mai Martaba ya iso shi ne nasa aka tara jama'a na basu haƙuri da dai bayanan da zai kwantar masu da hankali." Ya koma ya ƙwanta rigingine,saman jikina.
"Kin san ko waye mai son haɗa mana rigimar nan?"
Na ce "A'a." Cikin sanyin murya.
"Wanda na gaya miki ne wai shi Abdulrahman,wai ɗa ne ga Mai Martaba, amma baya son ma a na faɗa, saboda ko a yanzu ma bai bayyana ba,ba kowane ya ji ba. Ni ma waziri ne ke gaya mini."
Ya yi ɗan shiru. "Dama ni Mama ta taɓa ba ni labari cewa akwai su,su biyu ne ma har da Yayarsa. Yanzu dai Mai Martaba ya ja masa kunnansa cewa idan ya ƙara jin labarin ya zo garin nan sai yasa an kashe shi."
Na shafa gashin kansa, "Ka ƙwantar da hankalinka, ba ka tambaye shi cewa me yake so ba.?"
"Sarauta." Na ɗan yi saurin alamun tashi haɗe da tambayar.
"Sarauta ta me?"
"Ta Mai Martaba."
"To kai fa?" Ya yi murmushi, "kina son sarauta ne? Aƙwai wahala fa." Na ɓata fuska sosai.
Ya ƙara yin murmushi, "Yasmin kenan,ki ƙwantar da hankalinki,komai ya wuce, ina nan a matsayina na Yarima mai jiran gado, har da Babyna."
Ya faɗa yana lakatar mini hanci. Kunya ta kama ni. Na yi saurin tura kaina filo, shi kuwa ya kama ƴar dariya irin tasu ta sarakuna. Ya turo kansa cikin filon.
"Yauwa." Na yi saurin fito da kaina daga ƙarƙashin filon na yi alamar tashi da saurina.
Ya yi saurin mayar da ni ya zaunar, tare da riƙe min kunne.
"Kin manta ne ki ke tashi da sauri haka?" Ya ɗaga rigata ya sunkuya ya sumbaci fatar cikina, ya ɗago ya tallabi kumatuna tare da ƙura mini ido.
"Yasmin! Yasmin!!" Ya girgiza kansa.
"Ba zan taɓa iya ƙwatanta yanda nake jin ki ba a raina,son da nake miki yafi ƙarfin duk wani ƙaramin misali."
Na rausayar da idanuwana, waɗanda na ji sun aiko da hawaye. Mayar da su ɗin da na yi na runtse ya yi daidai da gangarowar su saman kumatuna,ni kaina ban san dalilin zubowar su ba, sai dai na ji zuciyata ta yi mini sakayau, ba nauyi. Na san ba abin da take so sai Yarima, mutumin da nake jin ya gauraye jinin jikina gaba ɗaya.
Hawayena kuwa sun tsiyayo ne ta dalilin wani abu da na ji yana yi mini yawo a tsakiyar kaina. Cikin sakan ɗaya na ga ya ruɗe,ruɗewar da take tayar mini da hankali. Gudun kada ya yi saurin fassara hawayena yasa na koma a hankali na ƙwanta a ƙirjinsa, zuciyata na son gaya masa cewa son da na ke masa yanzu ba zai taɓa misaltuwa ba, amma kunyarsa da nauyinsa sun hana ni sai dai na kurɗa kaina a wuyansa, na ce.
"I love You." Cikin sigar raɗa.
Ina jin shi ya ƙara matse ni a jikinsa,sam ban yi zaton ya ji ni ba, sai na ji ya ce "I love You too." Kunya ta sa na mayar da idanuwana na lumshe. Bai fi mintuna biyu ba na yi ƴar dabara na ƙwace jikina, saboda na san halin Yarima, sai mu ƙwana a haka. Na yi ɗan hanzari.
"Jira ina zuwa, na yi mantuwa." Na sauko daga gadona. Har na yi taku uku ya kira sunana, juyowar da zan yi sai na ji ya ce "I Fancy you."
Na yi murmushi na yi gaba. Faranti ne na shigo da shi ɗauke da abinci, har na ajiye farantin ban ga Yarima ya motsa ba, na yi sanɗa na iso inda yake, ya yi kwanciyar nan tasa, tausayin shi ya kama ni. Ganin kafin in je in dawo har ya yi bacci, na sunkuyo na sumbaci goshinsa, ya buɗe idanuwansa a hankali ya yi murmushi.
"Na gaji."
"I know,sannu ga abinci nan na kawo maka."
Na riƙe hannunsa duka biyun.
"Ta so ka ci." Ya miƙe tsaye a inda na yi gaggawar taimaka masa ya cire alkyabbar jikinsa.
**** **** ****
Lallai kam ni na zama ƴar gata gaba da baya, balle da cikin nan na jikina ya tsufa. Sarki, Mama, Hajiya, Daddyna, Mamee duk ba sa son abin da zai taɓa ni, wanda kullum sai Sarki ya aiko waziri ko jakadiyar sa tazo ta ga lafiya ta. Mamee kuwa, sai dai waya. Dad kuwa ya zo gidana ya kai sau uku, ba wai don ya ganni ba,idan ya ga Yarima sai ya koma. Shi kansa Yarima ya kasa gane kan Daddyna, saboda ko an ce ya shiga ba ya shiga, sai dai ya ce gaishe mu ya zo yi.
Shalelena kuwa, kullum ana manne da ni,ko fada ma sai na yi da gaske yake sauka, Kaɗan-kadan kuwa ya hayo sama balle in ina ɓangaren gidansa,in kuwa na gidana ne, idanuwana na ga barandar gaba wacce ta koma hanyar zuwa ɗakinsa.
Amma wani abu ƙwaya ɗaya da yake damun zuciyata, shi ne yanda gaba ɗaya suka raja'a da cewa namiji zan haifa, ba sa maganar mace ƙwata-kwata , wannan abu na tayar mini da hankali, ballantana idan na ga Yarima ya ɗaga cikin nawa yana sumbatarsa,yana faɗin ɗan shi ya kusa isowa duniya. A take sai na ji hankalina ya tashi, wannan ne ma yasa wasu lokuta na kan yi shiru tamkar na fita daga hankalina na ƴan mintuna.
Buɗe ƙofa da na ji yanzu ma ita ta dawo mini da hankalina, na gyara kishingiɗar da na yi a saman kujerar falon samana, na juya na kalli Yarima wanda ya fito daga ƙofar ƙuryar ɗakina,su Mansura suka yi saurin russunawa suka yi gaisuwa, sannan suka miƙe domin sauka ƙasa.
Ya iso ya tsugunna gwiwarsa ta hannu a saman cinyoyina, "Honey,na bar ki ko?" Ya ɗan yi tsaki.
"Wallahi Mai Martaba ya ƙi yarda, da yanzu muna can, tare da ke kullum."
Ya sunkuyo sosai, "My boy,how are you today?" Yasa hannu ya buɗe cikin kamar yanda ya saba, ya sumbace shi ya mayar da kansa ya ƙwantar a jikina.
Na sunkuyo na sumbace shi, gashin kaina duk ya rufe mu gaba ɗaya. Na ɗaga kaina sannan na ɗago shi.
"Yarima in tambaye ka mana?"
"Ƙwarai kuwa."
"Me yasa ba ka son a haifar maka mace?"
"Me ki ka gani?"
"Ban taɓa jin ka ambaci mace ba,ko ba ƙwa son a haifar muku mata?" Na yi shiru kaɗan.
"Yanzu in na haifi mace ba zaka zauna da ni ba?"
Sai kawai idanuwana suka ciko da hawaye. Ya miƙe tsaye ya zo ya zauna kusa da ni, wanda hakan yasa na saukar da ƙafafuwan ƙasa. Ya kamo hannuna ɗaya ya riƙe da hannayen shi duk biyun ya fara wasa da ƴan yatsun hannuna,a daidai lokacin da ya fara magana.
"Yasmin kin san dai mutum ba ya haihuwar wata halitta wacce ba mutum ba ko? Sai dai ya haifo nakasasshe ko marar lafiyar jiki,ko wanda halittarsa ba ta cika ba,ko kuwa ma ya mutu a ciki ko?" Na ɗaga kaina.
"To wallahi Yasmin a ce ki haifo wata halitta ta daban,ko ɗaya daga cikin abin da na lissafa, wallahi ni na san ma na so shi na gama,ko da kuwa jama'a za su ƙi ni a kansa, saboda kawai ya fito ta jikinki, ta balle mace mutum. Yasmin ya zan yi naƙi mace, alhalin kin san mu mata rahama ne a gare mu.
Ki tuna ke mace ke kika canja mini rayuwata, ta zame mini abin so da ƙauna, abin sha'awa ga kowa. Ke mace ke kika ƙwantar mini da hankalina lokacin da ya tashi, ke mace ke ce kika rungume ni a jikinki a daidai lokacin da na wuce mahaifiyata ta rungume ni a jikinta.
Ki tuna ke mace, ke ce wacce za ta haifa mini ƴaƴana,ki tuna ke ce tsanin rayuwata gaba ɗaya,in kin ga dama ki ruguza min rayuwata, wanda duk duniya babu mai baiwa ɗa namiji daɗin rayuwa sai Allah da matarsa tagari,in kin so kuma ki gyara mini ita.
Yasmin ki ƙwantar da hankalinki a kaina,ki dinga haifa mini yarana,ko da kuwa duk mata ne, ina so. Wallahi ina so,ni na san dalilin ki,wai sarauta? Ba dole ba ne a ce dama ɗana ya yi sarauta,ko da kuwa duk maza na haifa har guda ɗari,in Allah ya so sai ya ba ƴaƴan ƙannena,ƙila ma wanda ba'a ɗakinmu ɗaya ba da mahaifinsa.
Dakata ma ki ji, wallahi ni yanzun tun da na same ki a matsayin matata, na ji komai na duniya ma ba na son shi sai ke, ke kaɗai nake so. Baki san ma ni cewa nake dama a baiwa Ahmad sarautar nan saboda in zama free man in dinga zama da iyalina a kodayaushe muna hira,muna jin ɗumin junanmu."
Ya ɗago ya kalleni, ya juyo sosai. "No! No!! No!!!." Yasa yatsunsa manya biyu yana goge mini hawayen da suka gangaro.
"Shi yasa na liƙewa Mai Martaba a kan ya bar ni na tafi da ke London, muyi rainon cikinmu a can, ya ƙiya mini,ba don komai ba sai don in zamo kullum ina kusa da ke, da na samu haka da wannan tunanin bai ma zauna a zuciyarki ba."
Ya ɗago fuskata muka haɗa ido, sai na ga ya lumshe ido ya buɗe a hankali, ya kai bakinsa ga nawa.
Mintuna biyu ya ɗauka a haka, na yi dabara na cire bakina daga nasa, sanadiyyar wasu alamomi da jikinsa ya nuna mini. Sai da ya ɗauki tsawon wasu ƴan mintuna yana fitar da numfashi a hankali, sannan ya koma ya zauna. Ganin shirun da ya yi yawa.
"Yarima ka manta da ka baro jama'a?"
Ya ɗago ya kalleni sosai, ya lumshe idanuwansa tare da ɗan mayar da numfashi.
"Yanzu zan tafi, ke ce Yasmin,ke ce."
Ya miƙe tare da ɗan shafar saman kaina, sannan ya tafi. Ni kaina na san ina samun kulawa ɗari bisa ɗari a wajen Yarima, da jama'arsa gaba ɗaya. Ban da iyayenmu da suke zirga-zirga a kan ganina. Ni kam yanzu na riga na san Allah ya gama haɗa mini komai, sai dai in yi godiya gare shi.
########
[2/20, 18:49] Ummi Tandama😇: *ƘASAITA BOOK 3*
*NA*
*MARYAM KABIR MASHI*
Page 5
Tun kafin a kira sallar Asuba idanuwana suka bushe, sakamakon jin cikina ya naɗe ya tattare waje ɗaya, ya hana mini sakewa. Ina zaune lafiya ƙalau, Yarima ya tashi ganina a zaune yasa na ga ya tashi zaune a firgicen shi yana tambayata ko lafiya? Kafin in bashi amsa ma har ya ɗauki wayar hannunsa ya fara daddana ta. Na yi sauri na ƙwace ta.
"Haba Yarima."
"Me ke damun ki?"
"Ba komai."
"Yana gan ki a zaune, kuma sannan ki ce mini ba komai."
"Tun da na ce ba komai ka yarda,cikina ne kawai na ji kamar an ƙulle mini shi waje ɗaya."
"Na yarda, amma kin san dai daga ni har ke ba wanda ya san wata alama ta haihuwa, saboda haka ki yi mini haƙuri in kirayo Hajiya Kilishi."
"Na yarda, amma ka jira na yi sallah tukunna,ka ga yanzu biyar da mintuna ashirin."
Da ƙyar ya amince, sannan muka tashi muka yi alwala tare, wanda ya yi mini sallama ya tafi masallaci.
Shida da ƙwata na asuba Hajiya Kilishi ta iso gidanmu. Yanda Yarima ke bin ta a baya na yi imani shi ya je ya ɗauko ta har gida. Ya iso ya zauna ɗan nesa daga gefen gado,ni kuwa kallona da shi ƴar harara da take nuna alamun ya yi laifi, bai wani kulani ba na ga ya mayar da hankalinsa ga Hajiya da ke ɗan yi mini ƴan tambayoyi.
Dole tasa ni in tashi tsaye, amma tsayuwa ta gagare ni, ni kuwa ba wani ciwon da nake ji,iyakacina dai ƙuguna ya riƙe gam, cikin jikina ya naɗe waje ɗaya. Ganin haka yasa na ji ta ce wa Yarima ya bugawa Doctor Franca waya, wacce ita ce likitan gidan Sarki, sai kuwa Doctor Harisu, mai duba maza,ko wani ciwo amma haihuwa sai Doctor Franca.
Cikin mintunan da ba su wuce ashirin ba sai ga Doctor Franca ta iso. Ina jin Hajiya na tayi mata bayani kamar yanda na yi mata. Cikin ƴar hikima irin ta su ta likitoci ta aiki Yarima akan ya ɗebo mata ruwa a ɗan wani abu, yanda na ga sun kalli juna ita da Hajiya shi ya tabbatar mini suna son ya ɗan ba su waje ne.
Ai cikina kawai ta dafa ta ce haihuwa ce, sai dai kuma miƙewa tsaye ma ba zan iya ba, ballantana in iya tafiya. Ana cikin haka Yarima ya shigo da wata tasa a hannunsa, ya ciko da ruwa, har bakinta. A nan ne take gaya masa haihuwa ce, amma sai an samo kujerar tura ta zuwa asibiti. A zuciyata na ce yanzu a haka za a kai ni asibiti? Ban ƙarasa tunanina ba sai dai kawai na ga Yarima na shirin ɗauka ta.
Kunya kam ta kama ni, amma ganin Hajiya Kilishi ba ta yi