Showing 21001 words to 24000 words out of 26686 words

Chapter 8 - Kasaita Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

30 Dec 2024

110

maka.

A saboda haka fushi da sa ido ga shuwagabanninmu ba na sarakuna ba ne, ba haƙuri da tausayawa talakawansu shi ne nasu, da hanyoyin da za su bi su ga sun gyara, sun dawo mana da jin daɗin da ya wuce, wanda muke tunanin ba zai taɓa dawowa ba,su yi mana bazata su dawo mana da shi. Allah ya taimake ku, ya sada ku da gidan Aljannar fiddausi madauwamiya, Allah ya raya maku zuri'arku, ya ƙara taimaka muku da haƙuri da mu,Amin."

"To yanzu wacce shawara za ki ba ni?"

"Shawarata a nan ita ce,ka fara yin amfani da abin da ke hannunka, ikon mallakar ka."

"Kamar me?"

"Kamar ɓangaren abinci. Ka ga yanzu haka a gidan nan zuwa gidan da muka baro, zuwa gidan Mai Martaba na ɗaya,aƙwai ɗakunan ajiyar abinci sun kai talatin (Stores), kowanne da kala-kalar abin da ke ciki,na yi imani in zamu shekara ɗari ba zamu nemi abinci ba, amma ka sani shi abinci ne ba zai kai shekara ɗari ba, da kuma mu da koyaushe Allah zai iya ɗaukar ran mu, sannan ko da yaushe abincin nan na iya lalacewa.

To me zai hana a taimakawa talakawa da shi, sannan kuma Allah ya hore maka maƙudan kuɗi, ba Mai Martaba na ɗaya ba, ba kai ba,ni kaina da nazo gidanka daga baya, na san na mallaki duniyoyin da zan iya taimakawa da su daidai gwargwado."

"Ai kuwa na gode, Allah ya yi miki albarka, ya baki ƴaƴa masu ƙaunar ki kamar yanda ki ke ƙaunar ubansu. Da kin haihu kuma zan fara."

"A'a ba ruwanka da haihuwata,ka cigaba kawai."

"Ai saboda matsalar mata sai ke."

"Ga jakadiya nan na amince da ita,ka yi tunanin ƙaunar da take yi mana, iyaka ni zan dinga tsara mata abin da ya kamata ta yi, ba ma sai na fita ba."

"Ni dama ai ba na son ki fita a gane mini ke,kin manta ke One in town ce?"

"Wallah Honey ka bar koɗa ni zanyi maka kuka."

"Na daina,ai ba na son inyi asarar hawayen nan naki masu ɗigon tawwadar ilimantarwa."

"Ka ƙarayi."

"Sorry My Beby na."

Na yi dariyar jin daɗi, tare da juya bayana na ƙwanta a ƙirjinsa, ya rungume ni.

Na godewa Allah da ya wadata ni da miji mai jin shawarata, mai ɗaukar duk kalamain da ya fito daga bakina,ko na iyayena. Wannan dalili ne ma yasa na sadaukar masa da nafila raka'a biyu domin ta zama kariya a gare shi, wacce nake zama musamman in yi masa ita shi ɗaya, da addu'o'in da ke cikinta.

Dalilina kuwa, shi ne duk abin da muka tattauna da Yarima ya aikata shi, duk unguwa idan suka isa, tun daga gidan farko har ƙarshe sai an ajiye masu buhun-hunan abinci da jarin sana'a, wanda na tabbatar zai wadace su. Sannan sai a tambayi matsalar ka ta rashin lafiya ko haihuwa,ko bikin ɗiya,ko gyaran gida, sai a taimaka maka.

Wasu buhun-hunan abincin kuwa, don ajiya har sun lalace da hunhuna, sai waɗanda ƙwari suka cinye suka koma gari. Kai Alhamdulillahi, saboda yanzu ni na san nayi jihadi mai tsananin lada, tun da har Islamiyoyi aka buɗe, ban da makarantu masu ƙyau, ban da ɗaukar nauyin ƴaƴan da iyayensu ba su da halinsa su makaranta.

Sai kuma ni tawa gudunmawar, shi ne taimakawa mata ƴan'uwana da koyar da su ilimin zamani da na addini, yanda za su zauna da mazajensu lafiya da tarbiyyar ƴaƴansu, ga sana'o'i ana koya masu. Abin da ya so ya bamu wahala ni da Mai Martaba na biyu, shi ne Musluntar da arnan da suke zagaye da Jos, waɗanda wasun su ko kaya ba su iya sakawa ba,wasun su ma nama danye suke ci, amma mun samu da ƙyar mun taimaka masu.

Dabarar da muka yi kuwa, shi ne duk garin da suka isa, sai su ɗauko shugabansu su taho da shi cikin gari ya samu wata ɗaya,ko biyu yana ganin yanda jama'a ke rayuwarsu, ana koya masa duk wata al'ada mai ƙyau da Addininmu, to idan ya koma garinsu, shi zai dinga koyar da ƴan'uwansa,idan ya ga suna da sha'awa sai ya dawo gari ya gayawa Yarima, daga nan sai a tayar da mutane kamar ashirin cikin su da malamai da masu taimaka masu da abinci, ruwan sha,wanki. Yanzu haka duk an tura su a matsayin zasu shekara a can.

**** *** ****

Cikin jikina dai har ya shiga wata na sha ɗaya a jikina babu zancen wata haihuwa, sai dai duk inda na zauna sai an taimaka mini nake tashi,don dai ma ni doguwar macece, da gajeriya ce da shi kenan sai an dinga saka ni a kujera ana turawa. Wannan abin yanzu shi ya damu duk wani masoyina.

Kai har da Mai Martaba Sarki ya aiko da cewa mu shirya zai turo likitocin da zasu duba ni. Shi kuwa Mai Martaba Yarima cewa yake gara mu bar ƙasar. Amma Sarki ya hana a je ko'ina ya ce saboda abin da tafiyar mu zata haifar, shi ne a shiga ruɗanin ya ya nake. Ni kuwa har mamaki suke ba ni, saboda ba na jin ciwon komai sai dai nauyin da cikin ya yi mini ya hana mini sakewa.

Likitoci turawa mata,su baƙwai suka iso gidanmu, ba wani ɗan rakiya sai Mai Martaba na ɗaya, yanda suka shigo falon ina tule waje ɗaya, shi ya bani kunya. Cikin matsananciyar kunya na samu na gaida su, daga nan kuwa suka umarce ni da in isa asibitin mu da ke cikin gidanmu.

Yarima kuwa kamar ya saka kuka, da ya ga likitocin nan, sai dai ganinsu tare da Mai Martaba yasa ya kasa yin magana.

Lallai na san an shiga ɗakin asibiti da ni, ɓangaren mu wato Emir's section.

**** *** ****

_Innalillahi wa'inna ilaihir'raji'un!” haka Mai Martaba yake faɗa yayin da yake riƙe da ɗansa Yarima, wanda ke zaune dirshan a ƙasa yana kukan mutuwar matarsa Yasmin. Wanda hakan ya faru ne ta sanadiyyar haihuwa da ta zo mata da gardama.

Babanta Alhaji Sani Sa'id shi ne ke da ƙarfin halin yiwa mijinta nasiha.

"Haba Yarima,ka yi haƙuri mana,ka yi tunani da Allah ne ya baka Yasmin,don ya ɗauke abin shi kuwa,ai ba a ƙi gode masa ba. Mu ma nan fa jiran tamu mutuwar mukeyi, saboda faɗar Allah Subhanahu wata'ala ce da yake cewa KULLI NAFSIN ZA'IKATUL MAUTI (Dukkan mai rai mamaci ne). Saboda haka ƙyau a ce godiya ga Allah ka yi, tare da yi mata addu'a.

Wannan nasiha ita ta ƙarasa rikita Yarima, sai dai aka ganshi zube a ƙasa sumamme,gudun kada hankalin jama'a ya tashi, yasa ba'a yi wata hayaniya da ƙarfi ba, sai dai ɗauke shi aka yi aka kai shi asibiti, wanda likitoci suka bi bayansa.

Maganar da na yi ita ta dawo da hankalin jama'a gareni, wanda ɗakin cike yake da mata ƴan'uwana. Cikin su kuwa har da Mamee, Aunty Salwa,ga Mama,da Hajiya Kilishi, ban da jakadiya da ke rakuɓe a gefe, duk na karanci hakan kafin na kai ga yin magana.

Maganar kuwa ta yi daidai da firgita duk wanda ke zaune, ganin yanda suka nuna.

"Mamee lafiya na ga kuna kuka?"

Tambayar da na yi masu kenan. Gaba ɗayansu sun firgita, wanda dukkansu sun yo kaina, kowa so yake ya rungume ni. Jin jakadiya ta fita da gudu tana kira, "Mai girma Yarima Gimbiya ba ta mutu ba,dogon suma ne."

Maganar ta ta iso a kunnena, ita ta gaya mini da jira ake gari ya waye a kaini kabarina.

Na yiwa Allah godiya da ya taimaka mini na farka kafin gari ya waye. Na yunƙura zan tashi, amma na ji jikina kamar an karya mini ƙafafuna. Sai dai ji na yi Hajiya Kilishi na cewa.

"Jira a taimaka miki. Ke kuwa ai dole jikinki ya yi tsami,a haihu tun safe amma ba wanka." Sai a lokacin na faɗa tunanin abin da ya faru da safiyar yau.

Zuwan likitoci da Mai Martaba Sarki, wanda suka yi mini wasu allurori sun kai biyar. Yarima har faɗa yake masu, shi kuwa yana tallabe da kaina a cinyar shi yana yi mini sannu, balle da na ji wani bala'in ciwo na jijjiga mini tsokar naman jikina. Ban fi mintuna arba'in ba a haka sai na ji kamar an zare numfashin jikina.

Daga nan ne ban ƙara sanin yanda aka yi ba, sai yanzu, amma na ji Yarima na yi masu faɗa. A can cikin tsakiyar kaina ina jin matsanancin ciwon da nake ji, sai na ji suna ce masa wai allurar naƙuda suka yi mini. Haka kurum ruwan da suka sanya mini a hannuna ma na naƙuda ne.

Jin Hajiya Kilishi ta kama ni yasa na dawo hankalina izuwa kallonta, sannu ta dinga ce mini haka ma duk waɗanda ke wajen. Amma Aunty Salwa sai ma sabon kuka da ta saka ana ba ta haƙuri. Mamee kuwa ko motsi ba ta yi ba daga inda take zaune.

Bayan Hajiya Kilishi ta taimaka mini na yi wanka da ruwa mai zafin gaske, wanda ta cika bahon wanka, ta ce in shiga. Bayan na shiga ita kuma ta zuba wani a wata tasa mai faɗin gaske (silba), ta dinga tsoma tawul a ciki tana gasa mini jikina. Ni kuwa kamar kada ta daina saboda daɗin da nake ji.

Ina fitowa aka ba ni kunnun goruba cike da ƙwano aka ce in shanye shi. Ban ƙi sha ba, amma ni na san ba zan iya shanye shi ba. Lallai dole na yi mamakin har yanzu a ce Yarima bai shigo ya gan ni ba. Shin ko dai tsorona yake ji? Ko kuwa ya daina sona yanzu?

Kasa ɗaurewa na yi da na kalli agogon bango na ga har baƙwai da rabi na safe ta wuce, amma Yarima ba wanda bai shigo ya yi mini sannu ba, har da Dad ɗina da yake nuna kawaici a kaina, sun shigo da shi da Mai Martaba Sarki. Ni dai kasa ɗaurewa na yi har na tambayi Hajiya Kilishi.

"Hajiya ina Yarima ne? Ko ya yi tafiya?"

"A'a yana nan, amma na ji Mai Martaba Sarki na cewa jikin nasa da sauƙi, yanzu haka suna wajen shi."

Hankalina na ji ya tashi matuƙa, da a ƙwance nake, amma sai gani na tashi zaune. Ya zan yi ni yanzu? Na tambayi zuciyata. Sai kawai na ji na miƙe tsaye. Hajiya ta yi saurin kama ni.

"Me ye?"

"Hajiya zan iya zuwa wajen Yarima?"

Eh,mu ma yanzu can zamu. Su Mamee ma na can tun ɗazu. Amma ganina da kinyi haƙuri sai Sarki ya tafi da mutanen shi,ki ƙwantar da hankalinki, ba abin da ya same shi, razana ce kawai ya yi."


#####
[3/1, 22:22] Ummi Tandama😇: *ƘASAITA BOOK 3*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 12


Ya ya zanyi? Dole na bi maganar manyana. Haka dole na koma na ƙwanta, amma hankalina duk baya jikina. Gudun kada a ce mini Yariman ya mutu, amma kaɗan-kaɗan na tambayi duk wanda na ga ya shigo, cewa, "Ina Yarima?" Sai dai su bani amsa da yana nan lafiya.

Ƙarfe biyu saura minti goma sha ɗaya na ga Yarima ya shigo cikin sauri. Yana shigowa ina ƙwance, ganinsa yasa na yi saurin tashi tsaye. Ya iso ya kama cinyoyin hannuwana duk biyun, ya zame hannayensa suka sauko ga ƴan yatsuna. Ya dawo da hannayensa ya shafi wuyana da su, ya tallabe kumatuna ya kalleni. Sai a lokacin na ga ya yi murmushi, ya mayar da ni ya rungume gam a jikinsa, ya ɗagoni ya zaunar da ni a bakin gado, shi kuwa ya tsugunna a gabana, da gani ya rasa ya zai yi mini. Sai na ga yasa ɗan yatsana a bakinsa.

A tunanina wasa zai yi mini,sai kawai ya cije ni, na sa ƙara irin wacce ke dawo da hankalin Yarima a gareni, sai kawai na ga yasa dariya. Nima ban san lokacin da nasa tawa dariyar ba. Sai na ga ya hayo gadon shi ma yana mai cigaba da dariya, ya mayar da ni ya rungume a jikinsa. Sai kawai na ji lema na tsiyaya cikin rigata ta bayana, na ɗago kansa.

"Yarima me ye kuma na fitar da hawaye bayan ga ni?"

"Yasmin da kin mutu da ya zanyi da ra....."

"Haba Yarima, kamar ba Musulmi ba,za ka dinga kawowa kanka irin wannan tunanin, ba ka san Allah mai rahama mai jin ƙai ne ba. Yanda Allah ya ɗauke maka ni, haka zai musanya maka da wacce ta fi ni."

"Ki yi shiru Yasmin,ke dai kawai ki taimaka mini da murna, da addu'ar godiya ga Allah da ya bar mini ke."

Hawaye ya tsiyayo a kumatunsa. "Ba zan taɓa iya ƙwatanta miki yanda na ji rayuwata ta koma ba a cikin ƙanƙanin lokaci."

"To ba sai..."

Jakadiya ce ta yi sallama, muka saki juna, sannan na ce ta shigo. Ta shigo tana rawar jiki da yaro rungume a hannunta. Har a lokacin ban fahimci me ta shigo yi ba, sai da ta durƙusa gabanmu tare da gaisuwar ta ta miƙo mini yaron hannunta. Sannan na tuna ashe fa haihuwa na yi,ni na ma yi tunanin abin da na haifa ya mutu, shi yasa ban ma neme shi ba.

Yarima ya miƙa hannu ya karɓa, ya ce da jakadiya, "Su Mai Martaba suna nan?"

Ta amsa da, "Suna fada,su Mama ne dai suka tafi."

Ya miƙo mini jaririn hannunsa ya miƙe.

"Tsaya ki kula da ita,in je in dawo"

Jakadiya ta ce, "To." Shi kuma ya sunkuyo ya sumbaci goshina sannan ya tafi.

Sai da na ga fitarsa sannan na dawo da kallona ga abin da ke hannuna, "Mace ce ko namiji?" Na tambayi jakadiya.

Ta amsa da "Namiji ne."

"Ina Suhailat?"

"Mama ta tafi da su ita da Ammar."

"Me yasa ba su zo yi mini sallama ba?"

"Saboda Yarima. Kai Gimbiya ki godewa Allah, Allah Yarima yana son ki,sumansa biyar da aka ce masa kin mutu. Ki duba taurin rai irin na Allah ya ja da rai, amma sai ga shi yana kuka a gaban kowa."

Na yi murmushi irin na wanda ya tashi daga ciwo, sannan na lalubi mama na sawa jariri a baki. Sai da ya kama maman, sannan na samu damar kallonsa sosai, abin ka da jariri sai na kasa gane da wa ya yi kama. Ina cikin ƙoƙarin gano hakan Aunty Salwa ta shigo.

**** **** ****

Rana ta zagayo aka sawa yaro suna Abdul Nasir,amma ba a yi wani taro ba, saboda jikina ya ƙara warwarewa, saboda haka Mai Martaba Sarki ya ce a barshi sai wani satin. Wannan yasa aka ƙara sa masu kulawa da ni su matso kusa da ni domin kulawa da ni sosai.

Su Ammar kuwa sun zama ƴan gidan Mama, saboda sai dai su zo da yawo su koma.

Bayan ƙwana uku da raɗin suna sai aka shigo falo na uku wanda nake zama domin hutawa, aka ce na yi baƙi. Ban tsaya neman ba'asi ba na ce su shigo. Sauran kaɗan in saki Abdul-Nasir ƙasa, saboda mamakin ganin baƙin su huɗu da na yi. Maza biyu, mata biyu,ba zancen koƙwanto na gane su, duk da sun canja kamaninsu. Cikin al'ajabi na kira sunan ɗaya daga cikin su.

"Mansura! Daga ina ku ke haka?"

Madadin su yi magana, sai kawai na ga Mansura tasa kuka, ƴar'uwarta Musulum na taya ta ko kuwa in ce suna taya juna.

"Su waye waɗannan?" Na tambaye su.

"Mazanmu ne, wannan mijin Mansura, wannan kuwa nawa."

"Daga ina ku ke haka? Ya aka yi ku ka san muna nan? Wa ya nuna muku gidan?"

"Mu ma labari muka samu, shi ne muka ce bari mu zo. Yanzu kuma muna ƙauyen Fembeguwa a zaune, saboda tsoron zama cikin birni gudun kada a sa a kamo mu."

Na kalli wacce ke kusa da ni, "A tafi da su wajen Sarkin gida ki ce baƙina ne a basu ɗakuna biyu, kowacce da mijinta. Ke kuma ki sa a basu komai da komai,ki tabbatar sun ci abinci.”

Na juya ga su Mansura, "Ku je a baku masauki zan neme ku in kun huta."

"Mun gode. Amma za mu koma mu ɗauko yaranmu."

"Kun haihu ne?*

"Eh, yaranmu bibbiyu."

"To shi kenan, amma da mazan nan naku su je su ɗauko su."

"To Gimbiya, haka za'ayi." In ji mazan.

Daga nan suka miƙe,. Har sun kai ƙofa na kira Sa'a.

"Ki ce wani ya kai su su ƙwaso har kayansu."

"Tanko direba ko Brown?"

"Duk wanda aka samu."

Suka juya suka tafi suna ta godiya.

**** *** ****

Yau garin Jos ya ruɗe saboda hidimomin bakukuwa ga taron sunana da nake yi, wanda gaba ɗaya taron gidan mu ake yin sa. Duk girman gida irin namu, wanda zai kai kilo mita uku, amma cike yake da mutane. Get uku ne a ƙofar shiga, kenan wacce ke kallon kudu a kowanne zagayen get gidaje goma ne na fadawa.

Get ɗin farko yaran gida ke zaune a cikinsa, kenan masu yi mana hidimomi da yi wa dawaki, fulawoyi. Kai aikin gidan gaba ɗaya. Get na biyu kuwa ƴaƴan dogarawa, wasu daga cikinsu, wanda shi ma gida goma ne. Get na uku ne ke da gida ashirin na dogarawa.

Idan an shiga daga ɓangaren gabas,ƙaton falo ne ƙwaya ɗaya, sai ɗaki ɗaya ƙaton gaske,an yi shi ne domin saukar Mai Martaba Sarki na ɗaya, sai ɓangaren yamma kuma barandun sama ne aka yi guda huɗu. Kenan kowanne ɓangare da aƙwai baranda sai ƙaton fili daga tsakiya,an tanade shi ne saboda wani gagarumin taro kamar na yau. Filin dai kamar filin wasan ƙwallon ƙafa (Football).

Ɓangaren Arewa ƙaton masallaci ne a cikin shi,aƙwai Islamiyyar yara da ta manya, wanda mata su yi da safe, da yamma maza su yi da daddare. A nesa da masallaci aka yi gidaje biyar. Limamin masallacin ke da ɗaya, ragowar huɗun malaman Islamiyya kowanne da matarsa da ƴaƴansa.

Idan aka iso ƙofar shiga gidan daga yamma kaɗan,ƙaton asibiti ne mai ƙunshe da ɗakuna taƙwas na jama'a kenan, sai ɓangaren manya aka yi wa likitoci hudu kacal. Dukkan gidajen ɗakuna biyu ne da falo a cikin shi, sai kuwa ɗakin samari a bayan gida, wanda yake tare da banɗakinsa.

Manyan falo taƙwas ne a gidan, uku na shi, uku nawa, dukkansu na karbar baƙi ne, amma ƙofa biyu ce ta shiga gidan da ƙofar shiga falona, sannan da ta shiga nashi falon.

Ɗaya cikin ɗaya ne, sai in da muke son zama.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login