Showing 3001 words to 6000 words out of 26686 words

Chapter 2 - Kasaita Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

30 Dec 2024

105

ya shigo, amma sai na ga damuwar fuskarsa ta gushe, wanda take kaɗan ya yin da Mamee ta biyo bayansa. A nan Mamee ta ce mu shiga ciki mu bar su nan. Na miƙe tare da satar kallon Yarima, saboda in karanto me ke fuskarsa. Cikin maganar raɗa ya ce, "Take care." Na lumshe ido alamar na amsa masa na wuce cikin gida.

Mamee ta zaunar da ni ta dinga yi mini ƴan tambayoyi kamar su, "Ba komai dai zaman ki da mijinki? Ya ya yanzu kun daidaita ko? Ya gida? Sarautar ba dai matsala?"

Duk na amsa mata da eh kawai. Saboda na san ni yanzu ba ni da wata matsala dama matsalata ɗaya ita ce Yarima, yanzu kuwa ni kaina na san ina son Yarima. To ballantana shi wanda na lura da zai iya rasa rayuwarsa idan har ya rasa ni.

Sai ƙarfe uku muka bar gidan, amma kafin in tafi tamkar ban taɓa yin komai ba, saboda sai da ma na ci abincin Mamee na ƙoshi. Lafiyata ƙalau muka yi sallama da su. Duk da sai da na nunawa Yarima ya bar ni gida tsayin ƙwana baƙwai,a lokacin muna falon Mamee. Wannan ne ma ya baiwa Yarima damar cije mini laɓɓana da harshensa kada ma na sake faɗar irin wannan mummunar maganar. Na ɗan narke masa tare da cewa.

"Gidan mu ne fa! Yanzu shi ne mummunar maganar?"

Bai ma ba ni amsa ba, sai dai ya ɗan kama hancina ya ja ya tafi falon Daddy,wato manufarsa baya son maganar ma.

Muna shiga mota na ƙwanta daidai lokon motar.

"I am tied." Har da ɗan canja yanayin fuskata. Bai fi minti ɗaya ba na ji Yarima na kiran sunana. Na juya na kalleshi, sai na ga ya ware hannuwansa, alamar in isa gare shi. Na ɗan kaɗa idanuwana na gyara ƙwanciyata sosai, alamar dai ba na zuwa.

"Honey please come on. Ina son jin ɗumin jikinki a kusa da ni."

Na matso na faɗa ƙirjinsa na ƙwanta tamkar ba ni ba, ina jin shi ya sumbaci goshina. "I love You Yasmin,I can't explain how much I love you. Amma ke kina ɓoye mini me ke cikin zuciyarki.

Yasmin kin san ba zan iya yin komai ba sai kina kusa da ni. Me yasa za ki takura mini in bar ki gida? Wallahi ba zan iya ba,in ba so ki ke inyi ƙwanan ƙofar gidanku ba, amma na lura ranki ya ɓaci don na hana ki. Yasmin ki yi tunani, ba ki da lafiya fa, ya zan iya ƙwatanta ƙwanan da zan yi a yau in na tuna haka?"

Jin maganganun za su yi yawa na san halin Yarima, yanzu zai iya shiga matsananciyar damuwa idan na yi masa shiru. Na ɗago nasa tsinin hancina a daidai bakinsa.

"Ka yi haƙuri ba zan ƙara ba. Wallahi nafi son ganin farin cikin ka fiye da nawa. Na fi kowa baƙin ciki idan na ga kana cikin shi. Ka yi mini afuwa,ɓata maka ran da na yi ba zan ƙara maimaitawa ba...."

Ya ɗago ni, "kin ci abinci?" Na ɗaga masa kai.

"Are You sure?" Na ɗaga kaina.

"Ai na yi wa likita waya, har ma na gayawa Mama na ce ta shaidawa Mai Martaba cewa ba ki lafiya za mu koma gobe."

"What? Haba Yarima, daga ɗan amai kuma sai ka damu haka."

Na sassauta murya, "Ka yi ƙoƙarin ɓoye sona a zuciyarka,fitowa da shi fili zai iya janyowa mutane su tsane ni."

Ya ɗago ni sosai, "Su tsane ki,su waye mutanen? Wa ya fara canja maki fuska? Gaya mini,kina so in sa duk a kashe su?" Na yi saurin rufe bakinsa cikin tashin hankali, kamar yanda na ga har ya rikiɗe mini ya koma Yariman farko.

Na yi sauri na sulale ƙasan mota tare da riƙe hannuwansa.

"Za ka yarda da duk abin da na faɗa?"

Ya ɗaga kansa.

"Wallahi ba wanda ya taɓa canja mini fuska, kowa na sona kamar yadda ka ke sona. Ina son cewa da kai ka rinƙa ɓoye na ka ne ka bar ni in dinga fito da nawa a fili."

Sai naga yayi ajiyar zuciya, amma kuma ya kasa magana, sai da ya ɗago ni ya rungume gam, tsayin minti biyu, sai na ji yana magana cikin sanyin murya.

"Yasmin ba ki san yanda nake jin ki ba a zuciyata. Kin ɗauka wasa nake ko?"

"A'a na san..."

Ta yi daidai da buɗe motar da aka yi, ya yi sauri ya rufe cikin ƙiftawar ido, jikinsa kuwa tun a lokacin ya kama rawa. Na gyara sannan na ji ya ɗan ƙwanƙwasa gilashin motar, cikin gaggawa aka buɗe mana ta ɗaya ɓangaren, na fito, shi kuwa ta ɓangaren da yake. Sai a lokacin na fahimci gidan Aunty muka zo,gudun kada in ruga in baiwa kaina kunya da uban gidana yasa na tsaya tafiyar wahainiyar da muke ni da Yarima.

Falo kawai muka isa na dinga kwala mata kira. A firgice ta fito daga ɗaki, na ƙarasa da saurin guduna na rungume ta. Ita kuwa sai dariya take yi,tana cewa in sake ta taryi baƙon ta.

Mun samu sama da mintuna ashirin a gidan Aunty Salwa,sannan muka yi sallama da ita, wanda har alƙawari ya yi mini a gabanta zai kawo ni in yini in mun huta. Na dinga murna. Ganin jikin Yarima a sanyaye yasa har na fara shiga damuwa, na matsa na kama hannunsa tare da durƙusawa a ƙasan mota.

"Honey,me ye ya tayar maka da hankali? Wa ye kuma? Nima fa zaka jefa ni cikin damuwa?"

Ya ɗago ni ya zaunar da ni a saman cinyoyinsa, sai da ya sumbaci laɓɓana, sannan ya cire gilashin fuskarsa.

"Ke ce Yasmin, hankalina ya tashi matuƙa a kan ba ki da lafiya, amma ki ka ƙi gaya mini. Yanzu me iyayen ki zasu ce? Bana kulawa da ke?"

"Wallahi ni kaina ban san dalilin yin amaina ba,ni dai na san lafiyata ƙalau. Ni dai zan iya cewa ƙamshin turaren Daddy ne ya saka ni amai, kuma yanzu ni lafiyata ƙalau, zan iya yin komai, zan iya cin komai."

Na koma na ƙwanta a ƙirjinsa, "Kada ka ƙara damun kanka a kaina."

Sai na ga ya ɗago ni ko kasa me zai yi mini ya yi, sai kawai na ga ya dungure mini goshina.

"Kada ki ƙara faɗa mini haka."

A take ma sai na ji ya ba ni dariya. Na sa dariya irin ta nutsuwa, ya rungume ni, shi ma ya yi tasa dariyar irin ta su ta mulki.

A hankali na ga gilashin motar mu na sauka, wannan yasa na yi saurin sauka daga cinyar mijina na gyara zamana sosai. Subhanallah! Jama'a ne tamkar su ɓall gidanmu, tun daga get ɗin gidajen har izuwa harabar gidan mu. Jinjina ake yi, gaisuwa, amma yau Yarima ya burge ni, saboda ɗaga masu hannu da yake yi har da murmushinsa, mutumin da ba ya ko motsi idan ya shiga motar nan, to balle ma an canja wata motar wacce za ta iya ƙara masa girman kai, amma abin mamaki yau har da murmushinsa.

Motar mu na tsayawa na hango wani mutum a tsaye,shi kam tamkar wani saboda yanda na ga an zagaye shi. Sakan ɗaya da tsayawarta aka buɗe mana,kirari irin wanda ake wa Sarakuna, shi aka dinga yi wa Yarima. Gaisuwa da sauran hidimomi irin na sarakuna.

Wani abin da ya fi burgeni, shi ne wannan mutumin da ke tsaye tsakiyar nasa dogarawan, shi na ga an yi saurin kawo aƙwatin kuɗi a gabansa, aka buɗe masa irin na matafiya,brief case. Yana ɗaukar bandir sai dai ya ɓalle ƴar takardar ya watsa su. Amma mutanen mu ko matsawa ba su yi ba, ballantana su san ana zuba kuɗi a gabansu. Sai dai ma dogari ɗaya da yake gabanmu yana share su gefe,gudun kada mu taka. Wannan kuma ina jin dokar Yarima ce,sai ma a lokacin na lura cewa ƴan ɗari bibbiyu ne ake wa wannan watsin da su.

A nan na saki da sha'anin Yarima, wato har dogarawansa ma ya san yanda yake tafiyar da su. Wani abin mamaki Yarima bai tsaya wajen mutumin nan ba, ya yi wucewarsa, sai me? Ai tun daga barandar gidana na ga gidana ya canja. Ƴan matan gidana kuwa, duk sun taru a barandar, suna hango ni sai murna. Ni kaina duk sai na ji na ƙara ƙaunarsu. Mansura kuwa har da gudunta, ta iso ta durƙusa gabana ta kama hannuna. Na yi murmushi na ɗago ta, sai tasa kuka. Na yi murmushi na kama hannunta muka tafi.


#####
[2/19, 22:29] Ummi Tandama😇: *ƘASAITA BOOK 3*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 3


Lallai Yarima " Na faɗa a zuciyata,ganin duk ya ƙyale mutanen da ke bin bayansa ya biyo ni gidana. Sai dai na ga ya yi wa wani dogari nuni da hannunsa. A take na ji dogarin na cewa.

"Yarima ya ce a jira shi ya huta. Yarima na gaishe ku. Nan da awa biyu zai fito."

Me zai faru? Ina kunna kai a gidana, na ji wani ƙamshin turaren wuta na tashi. Nan take kaina ya fara juyawa. Cikin ɗan sauri-sauri muka gaisa da jakadiya da jama'arta. Haka shi ma Yarima na ga yana gaisawa da su. Ko lura ya yi,ai muna hawa sama a guje na ƙarasa banɗaki. Yarima na bina shi ma tun kafin in kai ɗan wajen alwala,bath amai ya kubce mini. Alkyabbar jikina kuwa sai dai wata.

Yarima riƙe da ni na dinga ƙwaranya amai kamar dai yanda na yi a gidanmu. Nan take na ji Yarima na waya cikin mutanen shi na ji ya yi wa ɗaya magana. Wai ina likitan da ya ce ya zo gida ya jira shi?

Nan take na ji yana cewa,nan da minti biyar ya hayo sama da sauri yana son ganinsa. Ni kuwa har amai ya kai sai dai ruwa-ruwa, saboda abincin ya ƙare.

Ina gamawa Yarima ya kama ni wanda jikinsa har rawa yake, ya cire mini alkyabbar jikina, ya wanke min fuska. Ban da sannu da yake yi mini, ya ɗago ni idanuwansa sun yi ja, ban da hawayen da suka cika su, ya dinga shafar fuskata. Lallai na amince Yarima son gaskiya ne a jikinsa, saboda ya rasa me zai ce mini. Ya kama ni muka fito ɗakina, ina fitowa wani sabon aman ya taso. Na koma ciki da guduna. Ya biyoni ya yi tsaye a kaina, ina ta faman yunƙurin aman da ba komai a cikina.

"Mama Yasmin zata mutu ta bar ni. Ki zo Mama."

Wannan maganar da ya yi ita ta tabbatar min waya ce ya yi, duk da ban iya ɗaga kaina na kalleshi ba.

"Ka hawo kawai." Wannan ya tabbatar mini da likita yake. Da sauri na ga ya fita, sai na ji yana cewa, "Shigo nan ka ganta. Sau uku kenan tana yin shi a yau,kaga har ya zamanto ba komai a cikinta, kalli yanda take?"

Likita ya sunkuyo, "Sannu Madam." Na ɗaga kaina kawai."

"Me ke saka ki amai?"

Na ɗaga masa hannu alamar ya jira, suna tsaye,Yarima na ta safa da marwa a banɗaki. Har tsayin mintuna goma, sannan na ɗago, wanda a take na ji jikina na rawar zazzaɓi. Ban da jiri da nake gani.

Yarima ya riƙe ni muka fito ɗaki. Muna fitowa na yi saurin komawa banɗaki.

"Yarima bana son warin turaren wutar nan, kaina juyawa yake yi."

Nan da nan ya kuma ruɗewa, "Doctor, ya za'ayi?"

"Yallaɓai ko a tafi da ita sashenka mu gani."

"Haka za'ayi."

Da sauri na ga ya buɗe ƙofar, bayan wacce za'a fita barandar baya, wacce ke kallon ta gidan Yarima, sai da ya buɗe, sannan ya kamo ni. Muna fita madadin in ga fili kamar da, sai na ga an gine ta, ta yi wani zagaye kamar ƙaton fayif na ruwa, ga fulawoyi na gaske nannaɗe da jikinsa.

Ban iya tsayawa na lura da yanda aka yi ta ba sosai, ni dai na ga muna tafiya har mun ɓulla ƙofar barandar Yarima. A take na ga ya buɗe mun shiga, sai na ga ɗakin Yarima. Yana isa ya ƙwantar da ni a gadon shi, ya janyo bargo ya lulluɓa mini,sannan ya koma ga kaina ya zauna, inda likita ya matso ya tsugunna gabana.

"Madam kamar me ki ke ji yana yi miki ciwo.?"

"Zazzaɓi, ciwon kai, sai amai."

"Mara fa,ko ciki?"

"A'a."

"Yanzu za ki iya tuna ko ƙwana nawa rabon ki da al'ada?"

"Likita bana son irin waɗannan tambayoyin fa." In ji Yarima.

"To Yallaɓai an bar su, sai dai ina son fitsarinta, yanzu zan je in dawo. Awa ɗaya za ka bani."

"To ya za'ayi a ɗebi fitsarinta,in ba ya ga rashin hankali irin naka?"

"Allah ya ja da rai,ga ƴar ƙwalbar da za ta yi a ciki ta bani. Yanzu zan tafi da shi, zan yi wani ɗan aiki ne da shi. Wannan kuma jininta za'a ɗiba.

Ya fito da sirinjin ɗaga aƙwatin hannunsa, sannan ya ɗauko wani abu yasa a kunnanshi, sai na ga ya ɗaure mini hannu da wani abu kamar balt (belt).

"Ba hawan jini, Yallaɓai,a taimaka a bayar da jinin da fitsarin." Ya janyo sirinjin zai ɗauki jini. Yana sa allurar na ɗan yi ƴar ƙara.

"Ka bi a hankali fa,in har da ciwo ka barshi kawai."

"Ai an ɗauka ma, sannu." Ya kama ni ya kai ni banɗaki, sai da muka isa ya tsayar da ni, ya tallabe kumatuna, ya dinga shafa su. Da gani ya rasa me zai ce sai kawai na ga ya haɗa bakina da nasa yana tsotsa, ya sake ni.

"Ya zan yi Yasmin?"

"Bana jin ciwon fa."

"Ga jikinki nan da zafi, ga shi har jikinki ya yi laushi." Ya sake ni ya fito kawa.

"Ina fitowa da ƴar ƙwalbar fitsarin a hannuna ya yi sauri ya tarye ni ya karba.

"Tashi likita." Ya kalli agogon hannunsa, ƙarfe huɗu da rabi.

"Nan da biyar da ashirin ina son in ganka cikin gidan nan."

Da rawar jiki likita ya karɓa ya tafi yana cewa, "Insha Allahu Yallaɓai, alheri ne."

Ni ke ƙwance, lulluɓe da bargo, shi kuwa tsugunne a bakin gado, yana ta faman shafa mini fuskata da bayan hannunsa, na mayar da idanuwana na lumshe, sai na ji yana cewa.

"Yasmin." Da sauri na buɗe ido, sai na ga ya yi ajiyar zuciya.

"How do you fell?

"Da sauƙi."

Ana haka Mama ta shigo har da Hajiya Kilishi da wasu su uku. Ya yi saurin taryarsu.

"Mama ga ta nan,zo taɓa jikinta ki ji."

"To mu je." Suka iso gabana.

"Yasmin ya ya jikin?"

"Taɓa jikinta ki ji Mama."

"Na gani ma ba sai an taɓa ba, likita ya zo?"

"Yanzu ya tafi, amma yanzu zai dawo."

"To shi kenan, bari mu jira dawowarsa, sannu Yasmin."

Na ɗaga kai, dukkansu ma suka yi mini sannu, sannan na ji Mama ta ce bari su zauna a nan falo, shi kuwa cewa yake.

"Mama kada ku tafi fa, Mama mutuwa za tayi?.

"A'a."

"Za ta tashi."

"Eh." Ta juya suka tafi. Ko awa ɗaya ba a cika ba, sai ga likita ɗauke da wata ƴar talabijin ɗin ƙwamfuta da shi da wani ɗauke da wasu tarkace a hannunsa. Ya shigo, ya gama jonawa cikin mintunan daba su wuce biyar ba, sannan ya iso wajen Yarima da yake tsaye a kaina." Yallaɓai muna son za mu ɗauko hoton marar ta kawai."

"Bismillah."

"Tsaya ina zuwa." Ya iso ya janye rigata a hankali, tare da rigar ciki ta shimi. Cikin ƴan mintuna ya ce ya gama.

"Me ye."

"Bari mu yi magana da Hajiya, tana falo."

Ya juya ya fita. Cikin mintuna biyar ya leƙo ya ce zai tafi,yana fita su Mama suka shigo.

"Yasmin mu mun tafi, Allah ya bayar da lafiya."

"Mama me ye wai.? Me likita ya ce muku?"

Ko nima sai na ji gabana na faɗuwa da sauri da sauri,cutar me gare ni kuma? Na tambayi kaina. Tambayar da Yarima ya ƙara yi wa Mama ita ta mayar da hankalina gare su.

"Mama don Allah ki gaya mini?"

"Wai me yasa baka tambayar Hajiya ga ta nan sai ni da ka raina? Ku mu je ku ƙyale su." Suka yi gaba abinsu, sai ya bi Hajiya.

"Hajiya me ye?" Sai da ta kusa isa ƙofar fita, sai na ga ta tsaya. Bana jin abin da suke faɗa, amma ni tuni har gefen filona ya jiƙe da hawaye, balle yanda na ji amsar da Mama ta bayar.

Ina kallon su shi da Hajiya, sai na ga ya dafe ƙirji duk hannu biyun,can kuma na ga ya durƙusa ƙasa da gwiwoyinsa duk biyu.

Amma sai na ga yana dariya, ya ɗaga hannu sama, ita ma Hajiya ta yi waje tana dariya. Tana fita, na ga ya rugo a guje ya faɗa saman gadon, cewa yake.

"Allah kana ƙaunata, da za ka ƙara mayar da Yasmin ta zama tawa har abada."

Ya wuntsulo ƙasa ya tsugunna, sai na ga ya janye bargon jikina, ya ɗaga cikina ya shafa fatar shi, ya sunkuya ya sumbace shi. Ya ɗago ga fuskata, ya goge hawayen da yake ta ƙwarara a gare ta.

"Yasmin na rasa da wane baki zan yi miki godiya."

Ya sumbaci goshina, ya dawo ya shafa cikina.

"Yasmin abin farin ciki ya same mu ya ya zan yi miki bayanin shi?"

Ya ɗago ya ƙura mini idanuwan nan nasa masu firgita ƙaramin yaro. Ya ɗago cikina sosai ya rungume shi, tare da ƙwantawa a saman sa.

Ya ɗago, "Baby na ne a nan Yasmin. Na zama Daddy daga yau, kada ki ƙara kira na da Yarima, sai dai Baban Yarima." Ya kanga kunnensa.

"Lah! Yasmin,kin ji wai ƴan biyu ne."

Nan take na gano me yake nufi. Kunya ta yi saurin dirar mini. A take na tambayi kaina, kenan ciki gare ni? To ni ya zan cewa Daddyna,in ya ganni da ciki?.

Ya matso ya ƙwantar da fuskarsa a tawa,na rufe fuskata, ya yi murmushi ya sumbaci kumatuna, tare da faɗar.

"I'm proud of you." Ma'ana "ina alfahari da ke."

Sannan na ji ya miƙe tsaye, ina kallonsa ta tsakankanin ƙofar yatsuna ya fita daga ɗakin. Tsayin mintuna biyu ya yi, sai ga shi ɗauke da ɗan faranti a hannunsa, ya zauna bakin gado tare da ajiye farantin da tree top ya ɗago ni, sai da ya matsa mini na sha, sannan ya ba ni magani ƙwaya ɗaya na sha, na koma na ƙwanta.

Ƙwanciyata ta yi daidai da wata ƙara mai ƙarfin gaske kamar ƙarar bindiga. Ban da ihu da muka ji mutane na yi. Ba Yarima da ke zaune ba,ko ni dake ƙwance ina fama da zazzaɓi, sai da na miƙe cikin sauri. Gaba ɗayanmu sai ga mu tsaye jikin taga, ban da ƙura da ta turnuƙe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login