Showing 15001 words to 18000 words out of 28807 words

Chapter 6 - Rayuwa Da Macijiya Book 1 Hausa Novel Complete

Aisha MB   

30 Dec 2024

266

a fuskar Du'a ta ce." Mene kike faɗa ne aka? me ya same ki? Ni bana cutarwa kuma sannan Ni mutum ce kamar kowa, meyasa kuma zaki ji tsoro na?.


"Karya kike ke ba mutum bace, babu abin da kika sani sai shiƙa, kece nan bazan taɓa manta wannan fuskar taki bah".




@@@@@@@@@@@@@@@@@@@



*TUNATAR WA......, Free page dai ya kusan kare wa, fan's a fara tara kuɗi don biyan kuɗin wannan littafin Naira ₦400 complt babu tsada, ki siya ki mori karatun ki cikin kwanciyar hankali*.


COMMENT & SHARE PLS 🙏🙏🙏
ALKALAMIN ✍️
A'ISHA M.B
(Zinariyar🪙 Jajirtattu)



Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D80k1puBPBn6uJhojKKhK5

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


BISSMILLAHI RAHMANI RAHIM🌹

*🌸RAYUWA DA MACIJIYA* 🐍 🐍🐍

*PAID BOOK ₦400 complt*
kacal babu tsada
*9043687746 Hassana Aliyu Opay bank*
*Evidence of payment*
09130398321

FREE PAGE ️1️⃣1️⃣➡️1️⃣2️⃣
WRITTEN & DIRECTED ✍️ BY A'ISHA M.B💞
(Zinariyar 🪙 Jajirtattu)


*_______________________________*
"Nifa ban fahimci abin da kike magana akai bah" cewar Du'a. A ta ke budurwar ta faɗi ƙasa sumammiya.
Ganin akan da Maryam ta yi ya sa ta saurin jan hannun Du'a sannan ta nufi hostel da ita.

Barin su keda wuya Ahmad ya kalli ɗaliban ya ce. "Me kuka tsaya kallo? Kafin na irga uku gaba ɗaya ku ɓace min daga gani, koh ba ku san da cewa kuna da aji bane?".

Kamar haɗin baki gaba ɗaya ɗaliban suka bar wajan, a yayin da suka cinciɓi wacce ta tada aljanu.
Ganin gaba ɗaya sun wuce classes ɗin su ya sashi shima barin wajan.


"Me yasa kika janyo ni nan Maryam?, ina da tambayoyi wanda nake so wacce ta tayar da aljanu ta amsa min, gaskiya banji daɗin abin da kika yi bah samm". Cewar Du'a.


"Aba Du'a ke baki ga shugaban ɗalibai na makarantar nan ya zo wajan bah? Na san idan ban riƙe ki mun tafi bah komai zai iya faruwa. sabo da kin ruga da kin ɓata masa rai tun farko, muda muke so mu ba shi haƙuri kuma kije ki kara aikata wani abin da zai sa ya kara tsanar ki".


Murmushin takaici Du'a ta saki sannan ta kalli Maryam ta ce. "Wallahi kina ban mamaki, wai shin wannan shugaban ɗalibai mala'ika ne Koh me? Me yasa a koda yaushe baki da wata magana sai nasa. Ni na
*TUNATAR WA......, Free page dai ya kusan kare wa, fan's a fara tara kuɗi don biyan kuɗin wannan littafin Naira ₦400 complt babu tsada, ki siya ki mori karatun ki cikin kwanciyar hankali*.

gaji da jin wannan maganar".

"Allah na tuba dan kawai an bashi shugaban ɗalibai shi ne zai dinga wani jijida kai, toh wallahi duk taurin kansa bai kaini bah, duk wannan izza da yake takama da shi duk saina sauke masa su".


"Da na san inda office ɗin principal ɗin makarantar nan ya ke wallahi da saina kaishi ƙara. kawai mu fuskanci abin da ke gabanmu bawai mu tsaya muna tuannin wani mahaluƙi wai shi Ahmad bah".

"Shi kenen yanzu dai ki tashi kiyi wanka sannan na ɗora mana girki mu ci mu gabatar da sallah, saina zo na nunnuna miki ɓangare-ɓangare na makarantar nan".

Girgiza kai kawai Du'a ta yi sannan ta ce. "Dan Allah na tambaye ki mana?". Kallonta Maryam ta yi tare da faɗin. "Allah ya sa na sani "

Du'a ta ce da ita. "Shin ba ki san inda macizai suke bah a makarantar nan dan Allah?".

Kallon Du'a maryam ta yi mamaki lulluɓe kan fuskarta ta ce. "Kamar ya bansan inda macizai suke bah?, ban fahimci maganar ki bah, ina so ki ganar dani".

Du'a ta ce. "Eh abin da de kika ji na faɗa, nace kinsan inda macizai suke da zama a wannan makarantar?".

Wani kallon baki da hankali Maryam ta bi Du'a da shi sannan ta ce. "Kin manta har girki da wanka nake musu. Wato sabo da rainin hankali irin naki kike wani tambaya na nasan inda macizai suke".

"Shin ni jinsin su ce da zan san inda suke da zama? Hanya Du'a kalau kike kuwa? Ta ya ya zaki tsare ni ki dinga yi min wannan tamabayar, duk wanda ya jiki ma sai ya ɗauka koh kina da mental problem wallahi".

"Aba Maryam, ni fah nasan me yasa nayi miki wannan tamabayar. Su ɗin da kike gani abokai na ne sosai, na shaƙu dasu tun ina ƙaramar yarinya. kuma sannan har yanzu muna abota dasu ".

"Abin da ma yasa kika ga na tambaya shi ne, sabo da na fara kewar su ne. Kin san ya nake dasu kuwa? Su kaɗai ne idan ina kuka suke rarrashi na, su suke ɗebe min kewa idan ina cikin kaɗaici".

"Basua so su ganni cikin kunci, damuwar su ke sani ɗimuwa, murmushin su kuma ke sani dariya. Idan har ban gansu bah, banajin cewa zan iya bacci yau".


"Tabbas kina buƙatar ganin likita Du'a". Cewar Maryam. Sannan ta ƙara da faɗin. "Hanya Du'a bakida shafar aljanu kuwa? Ta ya ya za'a ce mutum yana abota da macizai wanda suke da illa wa lafiyar mu? Ni wallahi kin fara bani tsoro ma, karna je kema macijiya ce".

Ɓata rai Du'a ta yi ta ce. "Kada ki ƙara ce min macijiya bana so ".
Maryam ta ce. "Toh kema in banda abinki ta ya ya nima bazan yi tunanin koh kema macijiya bace, kin san yadda nake matuƙar tsoron macizai kuwa? Na tsani macizai a rayuwata. Ke bama ni kaɗai bah, kowane ɗan adam a duniya bazai so dabbar da zata cutar da lafiyarsa bah".

"Ni dan Allah abar ma wannan maganar, ki tashi muje mu yi abin da zai finshe mu".
Cewar Maryam.

Miƙe wa Du'a ta yi tsaye ta ce. "Shi kenen kada kiji tsoro in sha Allahu daga yau bazan sake ambatar sunan maciji bah kinji?".


"Shi kenen". Kawai Maryam ta furta, daga bisani ta ja hannun Du'a suka fita don neman ruwan da za su gabatar da alwala.


"Saina saka ta gane kuskuren ta, tun da har ta sake ta yi sa'insa dani toh saina sa ta gane Allah ɗaya ne. Ba'a min na ƙyale .saina saka wannan makarantar ya gagare ta da zama".


"Aba Ahmad this is not fear, bai kamata a ce ka dinga faɗan kalamai marasa daɗi haka bah, koh ba komai duk ƙanƙantar mace uwa ce ".

"Kuma sannan kaima mace ce ta kawo ka wannan duni.....
Maganar sace ta dakata sakamakon tsawana da Ahmad ya daka masa.

Zumbur Ahmad ya miƙe daga kan kujerar da yake tare da nuna Abdul da ɗan yatsarsa sannan ya ce. "Idan har ban gasa magana da kai bah, toh bana so ka saka min baki ".

"Dame take takama a wannan garin?, shin kasan maganganu marasa daɗi da ta faɗa min, idan da kana wajan ba zaka tsaya kana faɗa min story bah, kasan cewa na tsani na ja magana a ja ".

"Tun da ta ruga ta ta yi musayar yawu dani, toh walwala da farin ciki sun ƙare mata, don saina gallazawa rayuwarta a makarantar nan ". Yana kaiwa nan ya shige cikin mota tare da tada motan sannan ya bar cikin makarantar.

Baki sake Abdul ya bishi da kallo, sannan ya ce. "Ahmad ina fatan Allah ya shirye ka idan mai shiryuwa ne".


*9: o'clock na dare*
Mata wajan kusan biyar zuwa shida na hango kwance akan bonch ɗin kwanciya. Kowacce tanada wajan kwanciyar ta. Gefe guda kuma su Du'a ne kwance akan gado wanda mafi yawanci student ke amfani da shi wajan kwanciya.

Gaba ɗaya idanuwan matan ɗaƙin akan Du'a ya ke, duk inda Du'a ta juya sai ta ga suna kallonta.yayin da suke ganin irin tsananin kyau na halitta da Du'a ta ke da shi.

Juyarda da kanta Du'a ta yi tare da mai da kallonta kan Maryam ta ce. "Me yasa matan nan suke kallo na ne? Shin na aikata musu wani abu ne?".

Murmushi Maryam ta yi sannan ta ce. "Kema in banda abinki ta ya ya ba zasu kalle ki bah, farko kina da kyau, ga gashi har baya, kina da idanuwa da matsakaicin hanci masu ɗaukar hankali, gaba ɗayanki ma baki yi zubin yan Nigeria bah".

"Toh faɗa min ta ya ya ba za su kalle ki bah? Nida bani da kyau gashi nan babu ma wanda ta ke kallona sabo da bana gaban ta, kawai ki kwanta kiyi bacci ki daina waɗan nan saƙe-saƙen a ranki".

"Na ji shi kenan zan kwanta" cewar Du'a.
Sai da Maryam ta rabbatar kowa ya gama uzurin sa sannan ta kai hannunta kan fitila domin kashe hasken ɗaƙin.

Ganin aka da Du'a ta yi ya sa ta saurin riƙe hannun Maryam damuwa lulluɓe kan fuskarta.

Mai da kallonta Maryam ta yi kan Du'a sannan ta ce. "Mene ne haka kuma Du'a? Me yasa kika riƙe min hannu lokaci ɗaya?".

Girgiza kai Du'a ta yi sannan ta ce. "Dan Allah Maryam kada ki kashe fitilan nan, wallahi ina matukar tsoron duhu, idan kika kashe zan iya shiga wani hali wanda ke kanki saikin zo kina da na sani ".

"Bana son duhu maryam ki bar wutan a kunne dan Allah".

Ɗaya daga cikin yan ɗaƙin ne ta kalli Du'a ta ce. "Aba baiwar Allah, ta ya ya zaki ce kada a kashe hasken wuta. Toh mudai sabo da ke ba zamu iya kwana cikin haske bah gaskiya".

"Haka ne Du'a, maganarta gaskiya ne, bai kamata a ce mun kwana cikin haske bah gaskiya, sabo da babu ma kyau kwana da haske, sai dai fa kiyi haƙuri, ki lallaɓa ki kwanta a aka". Maryam ta ƙarashe maganar tare da kashe fitilan ɗaƙin.

Cun kushewa waje guda Du'a ta yi yayin da zuciyarta ya tsananta faɗuwa. Ƙaƙƙarwa jikin ta ya soma yi, yayin da haƙoranta na dukan na sama da ƙasa.

A ta ke hawaye suka fara zarya akan fuskarta, babu zato ƴan ɗaƙin suka ji ƙaran tsawa da walkiya. Mamaki ne ya kama su sabo da a sanin su dai wannan lokaci bana damuna bane, amma kuma alamu sun nuna kamar za'a yi ruwan sama ne.

gurnanin Du'a Maryam ta faraji ƙasa-ƙasa, saurin kunna fitila Maryam ta yi tsreda mai da kallonta kan Du'a.


Rass ta ji gabanta ya faɗi! Cikin tashin hankali ta nufi inda Du'a ta ke ganin yadda gaba ɗaya ta rikice numfashinta na neman sarƙewa.

Tashi suma sauran ƴan ɗaƙin suka yi tare da tallafawa Maryam ta ɗago Du'a. Ganin tadda idanuwan Du'a ke jujjuyawa yasa gaba ɗaya tsoro ya baibaye zuciyoyin su.

Saurin miƙe wa ɗaya daga cikin matan ɗaƙin ta yi, sannan ta nufi inda bokitin ruwa ya ke. Ɗaukar kofi ta yi sannan ta ɗebi ruwa kaɗan a cikin kofi ta nufi inda su Du'a suke.

A hankali ta fara shafa mata fuskarta da ruwan koh Allah zai sa ta dawo dai-dai, amma kamar ma abin da ɗa ƙaruwa ya ke.

"Na shiga uku ni Maryam!, dama na sani ban kashe fitilan nan bah, yanzu mai zamu yi ta dawo dai-dai?".

"Ɗaya daga cikin ƴan ɗaƙin ne ta kalli Maryam ta ce. "Ki kwantar da hankalin ki wannan abin da ke damunta nasan ba zai wuce shafar aljanu bane, dan aka kawai mafita ɗaya ce, shi ne muyi mata ruƙiya koh Allah zai sa su lafa".

"A'a ƴar uwata bata da aljanu koh kaɗan, bana so ki kara ce mata tanada aljanu ".
Tana kaiwa nan ta miƙe da zimmar fita don neman wa kansu mafita.

Ji ta yi an riƙe mata hannu, waigawa ta yi tare da ɗora idanuwan ta kan nata. Baki na rawa Du'a ta ce. "Kada ku tayar da hankulan ku a kaina, wannan bah sabon abu bane, bah yau ne karo na farko dana fara shiga irin wanann halin bah, zan dawo dai-dai nan bada jimawa, kudai kawai ku kwanta kuyi bacci nasan ta yadda nake dawo da kaina dai-dai".

"Kin tabbatar zaki dawo dai-dai ba sai mun nemi mafita bah?". Cewar Maryam.

"Kwarai ina da tabbaci akan maganar dana faɗa, kawai kuyi abin da nace".

Jin hakan da suka yi ya sa gaba ɗayansu kwanciya cike da fargaban kada wani abu ya samu Du'a.



"Mene ne ya faru Inna wuro? Ya naga hankalin ki a tashe?". Cewar mai gari .
Amsa Inna wuro ta bashi da cewa. "Gaba ɗaya hankali na ya'ƙi kwanciya zuwa birnin da Du'a ta yi, tun ɗazu gabana yake ta faɗuwa, kuma bansan dalilin akan bah".

"Kuma jikina yana bani cewa Du'a na cikin halin tsaka mai wuya wanda babu wanda zai iya taimaka mata bayan mu da muka san duk matsalolin da ke damunta, ina tsoron kada wani abu ya faru da ita".


Murmushi Mai gari ya yi sannan ya ce. "Babu abin da zai faru in banda alhkairy, dan Allah ki daina irin wannan saƙe_saƙen a ranki, Allah shi ne mai karewa, kuma ina da tabbacin cewa Allah zai kare ta domin tana tareda albarkar iyaye da kuma albarkar mutanen kauyen nan".

"Maza kije ki kwanta dare ya yi, in sha Allahu ma babu abin da zai same ta ƙunshi?.


"Na ji shi kenan Mai gari na gode, ni yanzu zan koma ciki, da safe zamu ci gaba da yiwa mahaifiyarta magani sabo da na fara ganin sauyi a tattare da jikinta, alamu na nuna cewa nan kusa zata tashi".

"Masha Allah". Mai gari ya faɗa sannan ya ce. "Allah yasa akan, ubangiji ya saka ta farfaɗo nan kusa, domin yarta na matuƙar buƙatar ta".


Washe gari sa sassafe jikin Du'a ya yi sauƙi, harta shirya zata tafi aji domin daukar darasi. Kallonta Maryam ta yi ta ce. "Du'a kamar ba keba wallahi, kinga yadda kika bamu tsoro a jiyan nan".

Mai da kallonta Du'a ta yi kan Maryam ta ce. "Kinga dan Allah abar wannan maganar, ki tawo muyi sauri mu tafi aji sabo da kada mu makara".

Murmushi Maryam ta yi ta ce. "Ke in banda abinki wazai yi miki lecture ƙarfe shida na safe, koh mune ƴan hallazi boko ai sai akan, gaggawan me kike? Ki bari bakwai ta yi tukun nan sai mu tafi ".

Ɗaukar jakarta na saƙa Du'a ta yi sannan ta ce. "Kinga tafiyata, ni bazan iya jiran har ƙarfe bakwai ya yi bah, sabo da ina so naje na kofi rubutun da aka yi bana nan".

Dakatar da ita Maryam ta yi da faɗin toh idan ma za kije, sai ki tafi da wannan jakar dan Allah, ai saiki sa a raina mu. Kalli fah jakar gaba ɗaya ta yi muni da yawa gashi kuma saƙa ta aka yi, kawai ki ɗau ɗaya daga cikin jakunkuna na ki tafi dashi".

Girgiza kai kawai Du'a ta yi sannan ta ce. "Babu wanda ya ajiye ni a makarantar nan, ni karatu nazo yi bah gayu bah, duk abin da nake dashi toh shi zan saka, idan kuwa bani dashi toh bazan takura wa kaina don mallakar abin da banda shi bah ".

"Idan ma kallona za suyi koh zagi koh akasin aka toh sun daɗe basu yi bah. Ni kinga tafiyata sai kin tawo". Tana kaiwa nan ta fice daga ɗaƙin.


Ɗaukar jakarta Maryam ta yi tare da bin bayanta da sauri.
Tafiya mai nisa suka yi kafin daga bisani suka isa wajan department ɗin su.

Shiga ciki suka yi suka tarar babu kowa a cikin ajin. chan sama Du'a ta nufa tare da ajiye jakarta akan kujera sannan ita ma ta zauna akan kujerar da ta ke ganin shi yafi cancan ta ta zauna.

Zuwa Maryam ta yi kusa da ita sannan ta ce. "Du'a me zai hana ki samu wani kujeran ki zauna, wannan kujerar da kika zauna akai, na su Jennifer ne kuma babu wanda ya ke zama in banda Jennifer".

"Dan Allah ki nemi wani ki zauna". Murmushin takaici Du'a ta saki sannan ta kalleta ta ce.

"Ni dai dana zo wajan nan banga inda aka rubuta cewa iya Jennifer ce kawai ke da ikon zama akan wannan kujerar bah, shin kujerar daga gidan su ta tawo dashi koh me? Koh an rubuta a jikin kujerar cewa kada wanda ya zauna a kan wannwn kujeran, dan aka dan Allah ki rabu dani ".


Shiru Maryam ta yi mata sannan itama ta samu guri ta zauna. A hankali ɗalibai suka fara shigowa cikin aji, babu bata lokaci ajin gaba ɗaya ya cika, yayin da suka dinga bin Du'a da kallo.


Chan Maryam ta hango tawowar su Jennifer daga windon ajin. Da sauri ta taɓa Du'a Tare da faɗin. "Du'a ki tashi gatanan zuwa fah, dan Allah ki tashi kada tazo ta tarar dake a kan kujerar zamanta".

"Murmushi Du'a ta yi wanda ya sanya dimple ɗinta lotsawa, sannan ta ce. "Allah ya kawo ta lafiya, wallahi daɗi na dake Maryam bakida jarumta, samm bakisan darajar ki ta mace bah, ta ya ya wata ɗaliba zata zo tana tsorata ki, kuma ke.....

Maganar ta ne ya tsaya chak jin muryar Jennifer na faɗin. "Waya baki izinin zama a waje na, kinsan kuwa wace ce ni a makarantar nan, toh maza- maza ki tashi kafin na nuna miki ɗanyen kaina".

Miƙe wa Du'a ta yi murmushi ɗauke kan fuskarta ta ce. "Keda wannan bahamagen wanda kuke kira shugaban ɗalibai baku da maraba, shima aka ya ke kuri amma banga har yanzu ya aiwatar da abin da ya ce bah".

"Kuma kema aka, dan aka ki samu wani gurin ki zauna, dan kuwa wannan gurin karfi ya cinye".

Ƙoƙarin magana Jennifer ke yi suka ji shigowar lectura, harara Jennifer ta watsa mata sannan ta samu wani kujerar ta zauna akai.

Gaishe sa gaba ɗaya ɗaliban suka yi, daga bisani kuma lecturan ya fara koyar dasu darasi.

Sosai Du'a ke fahimtar darasin da ake koyarwa, duda cewar bah duka abubuwan ta ke fahimta.

A hankali ya sanya kafufawansa a cikin ajin. Ɗaliban ajin na ganin sa gaba ɗaya suka mimmiƙe, tare da gaishe sa.
Banda Du'a wacce ke zaune kamar bata san da shigowar sa bah.

Ran Ahmad ne ya soma ɓaci, ganin gaba ɗaya ta yi kamar bata san da shigowar sa ajin bah. Gyaran murya ya yi sannan ya ce.

Wace ce Du'a a wannan ajin? Jin ya ambaci sunan ta yasata ɗago da kanta ta ce. "Nice nan fatan dai komai lafiya?".

"Kallonta lecturan ajin ya yi, mamaki ɗauke akan fuskarsa ya ce. "Ke baki ga shugaban ɗalibai bane, ba zaki iya tashi ki gaida shi bah, baki ga kowa ya tashi bane?".


"Eh na gani, naga ɗalibai sun tashi, ni kuma bai kai matsayin wanda zan tashi na gaida bah, idan ma mafarki ya ke toh ya farka, dan bazan taɓa gaishe shi bah saidai duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login