Showing 21001 words to 24000 words out of 28807 words
ni Allah na tuba kwata-kwata bana son namiji ya fiye kyau da yawa, sabo da idan na je na aure sa hankali na a koda yaushe zai kasance a tashe ne. Dan aka ki gode wa Allah da ya cire miki son wan can jarabbaben a ranki".
Nannauyan ajiyan zuciya Maryam ta sauke sannan ta ce. "Wallahi har yanzu ina jin sonsa a raina, ban taɓa jin dai-dai da rana ɗaya sonsa ya ragu a zuciyata bah, kawai dai ina danne zuciyata ne akansa sabo da ire-iren abubuwan da ya ke yi wa mata Waɗan da suka ce suna sonsa".
Kwanciya Du'a ta yi akan gado tare da yin mi ƙa sannan ta kalli Maryam ta ce. "Kinga kizo mu kwanta gobe muna da darasi karfe tara bana so na maƙara".
"A'a ki kwanta kawai ni ba yanzu bah sabo da bana jin bacci". Cewar Maryam.
Girgiza kai Du'a kawai ta yi ta ce. "Allah ya ya ye miki yar uwa". Tana kai wa nan ta ja pillow tare da kwanciya a kai sannan ta fara lumshe idanuwanta alamun bacci na san ɗibanta. Babu ɓata lokaci barcin barawo ya sace ta.
Ƙarfe ukun dare.
Ganinta ta yi a tsakiyar daji mai matuƙar abin tsoro, a ya yin da ta fara waige-waige tana neman hanyar kuɓuta, chan ta hangi wani ƙaramin halitta a gaban ta. Ba ta re da jinkiri bah ta nufi inda halittar ya ke.
Gaba ɗaya wajan zagaye ya ke da macizai kala-kala masu matuƙar girma. Ya yin da ta ke tafiya macizai na mara mata baya.
Sai da ta je gaban wannan halittar sannan ta tsuguna tare da fuskantar sa. Kallon sa ta yi ido cikin ido a ta ke ta yi wani irin muguwar zabura ganin yadda sufar sa ya ke da matukar munin gaske.
Cikin daƙe wa ta kara kallon sa a karo na biyu sannan ta ce. "Wane ne kai? Me ya sa ku ka kawo ni cikin wannan baƙar dajin?"
Amsa ƙaramin halittar ya bata da cewa. "Mun kawo ki ne sabo da ki na da halaƙa da wannan dajin. ke ɗin jinin mu ce kuma kece sarauniyar wannan dajin gaba ɗaya, me ya sa ba za ki dawo ki ci gaba da mulkar dajin ki kamar yadda ki ka saba yi a da bah? bai kama ta a ce ki ci gaba da kasancewa cikin mutane wanda ke kan ki kin san da cewa ke bah jinsin su bace".
"Har yanzu ke mu ke jira don ga kujerar ki na sarauta chan yana jira ki dawo gare sa.
Koda yaushe wannan kujerar ku ka ta ke yi. dan aka yanzu ba ki da wani zabi da ya wuce ki dawo duniyar ki, domin shi ne zai zamo alhkairy a ga re ki".
A fusa ce Du'a ta miƙe tsaye sannan ta kalle shi cikin ɓaccin rai ta ce. "Karya ka ke makaryacin banza kawai, Ni ɗin mutum ce ba macijiya bah, har kai waye da za ka ce Ni ba mutum bace"
"Idan har ni ɗin macijiya ce da gaske toh me ya sa bana sauya kammani? Na ga ji da jin ire-iren waɗan nan tatsuniyoyin da ku ke yawan faɗa, wannan ya zamo na farko kuma na karshe da za ku ƙara cewa ni macijiya ce".
"Kuma shin kana da hujja akan abin da ka ke faɗa?".
Amsa aljanin ya bata da cewa. "Ba za ki san da cewa ke macijiya bace sai lokacin bayyanar baiwar ki ya yi tukun nan, kuma ba za ki ji komai a baki na bah, aka zalika hujja ma ba za ki ji daga waje na bah, amma ita asalin mahaifyar ki ta san ko mai, ita za ki je ki tambaya domin ita keda cikakkun bayanai ga me da rayuwarki".
A fusa ce Du'a ta shaƙe masa wuya tana mai cewa. "Makaryancin banza wato kana so ka shiga tsakanina da mahafiyata koh, yau bah gobe bah zan ga bayanka.
Babu zato ta ga macizai sun fara hawa jikin ta, a ta ke ta saki wani irin razannaniyar ƙara!.
Ihuuu! Maryam ta yi ganin yadda Du'a ta maƙure ta ta re da shaƙe mata wuya.
Zabura gaba ɗaya ƴan ɗaƙin suka yi, ganin yadda Du'a ta shaƙe wuyan Maryam tana surutai.
Babu ɓata lokaci kowannen su ya kai wa Maryam ɗauki. A firgice Du'a ta farka daga mafarkin da ta ke.
Da sauri ta cire hannunta daga wuyan Maryam ganin yadda ta shaƙe ta. Tari Maryam ta soma yi babu sassauci.
Ganin akan da Du'a da ƴan ɗaƙin su ka yi ya sa hankali su ya ƙara tashi!.
Da sauri Du'a ta tashi tare da nufan inda ruwa ya ke. ɗebo ruwan ta yi a cikin kofi sannan ta nufi kan Maryam da shi.
Ɗaya daga cikin matan ɗaƙin wato Khadija ce ta wafce kofin da ke hannun Du'a sannan ta yi magana cikin ɓacin rai ta ce. "Baki da hankali za ki shaƙe mata wuya? sabo da me za ki aika ta mata aka? Ki dubi yadda ki ka sa ta gigice duk sabo da ke".
"Naga alamu tun da ki ka shi go cikin makarantar nan abubuwa mara sa kyau suke faruwa. Farkon shigowa ki makarantar nan wata ta tayar da aljanu, kin ce bakya iya kwana cikin duhu sabo da kina jin tsoro, aka muka haƙura muke kwana cikin haske, yanzu kuma kin zo kin maƙure ta kina son ki kashe ta Koh? Nan gaba ma abin ba'a iya nan zai tsaya bah harda mu za ki haɗa".
Girgiza kai Du'a ta yi ta ce. "Ni samm bada sane na aikata mata akan bah, mafarki na ke yi shi ya sa ban san na shaƙe mata wuya bah".
"Ka ji munafuka algunguma, wato mafarki ki ke shi ne aka ce ki shaƙe mata wuya koh?". Cewar habiba. Sannan ta kara da cewa. "Wallahi babu tantama yarinyar nan mayya ce, in bah mayya bah mene na shaƙe mata wuya wato so ki ke ki zuƙi jininta Koh? Toh ki sa ni jinin mu ɗaci ne da shi babu wata mayya da ta isa ta ce za ta sha mana jini".
Girgiza kai Du'a ta fara yi ta ce. "Na rantse ni ba mayya bace kuma ni bana shan jini, kawai kun yi min gurguwar fahimta ne shi ya sa, amma ni samm bah mayya bace".
Ture ta khadija ta yi ta ce. "Dalla ware dangin mayu kawai mai fara ƙafa, daga yau kada mu sa ke ganin kin kusanci inda Maryam ta ke, in kuma ba aka bah, sai kin gane kuranki.
Tana kaiwa nan ta bangaje Du'a. A ta ke Du'a ta faɗi a wajan a yayin da hawaye suka fara zarya a kan ƙun cin ta. Da sauri ta ta shi tare da yin hanyar waje da gudu.
Gudu ta ke yi babu ƙagautawa sai da ta yi tafiya mai nisan gaske ba tare da tana ganin gaban ta bah, bakin bishiya ta samu ta zauna sannan ta fara ku ka.
Ku ka ta ke tamkar ranta zai futa. Ɗago idanuwanta ta yi wanda su ka yi jajir ta ce.
"Me ya sa akan ta ke faruwa dani? Mene ne tsakani na da macizai, me ya sa na ke irin waɗan nan munanan mafarkan? Shin ko dai da gaske ina da halaƙa da macizai?".
"Me ya sa ma banyi zama na a kauye bah? Da nasani ban zo birni bah na yi zama na a ƙauye domin nafi samun farin ciki a chan".
Miƙe wa tsaye ta yi tare da share hawayen ta ta ce.
"Ni wace ce? Me ya sa nake iya mu'amala da macizai bayan kuma ni ɗin mutum ce? Tabbas maganar su khadija gaskiya ne. kenen da gaske ni mayya ce? me ya sa zan kasance mayya bayan a dangi na babu mayu, toh kodai mamata mayya ce?".
Ji ta yi gaba ɗaya ku kan tsuntsaye ya gauraye wajan yayin da aka fara iska mai ƙarfi wanda ya ke haɗe da guguwa. a ta ke ta fara kalle-kalle, tare da juya wa.
Juyawar ta ke da wuya ta ga wani jibgegen baƙi maciji wanda ya zalalo da harshen sa wanda ke a tsage gida uku.
Zaro ido ta yi waje sannan ta sa ki wani irin ihuu da sauri ta fara ja da baya-baya, sannan ta fara ƙoƙarin guduwa, kafin ta yi wani yunkuri, macijin ya nannaɗe ta tare da ɗaga ta sama.
Ƙoƙarin kwace kan ta ta ke amma akan ya cutura. Rintse idanuwan ta ta yi don ta gama sallame wa cewa yau ne ranar mutuwar ta. Jin shiru babu abin da ya same ta, ya sa ta buɗe idanuwanta a hankali tare da ɗorawa akan na macijin.
Sauke ta macijin ya yi sannan ya shafa gashin kan ta da jelar sa na macijin daga bisani ya yi tafiyar sa.
Baki sa ke Du'a ta bi macijin da kallo sai da ta tabbatar idanuwanta sun daina ganin sa sannan ta ce. "Shi kuma wannan macijin daga ina ya fito? Me ya sa kuma zai zo waje na? Sannan fuskarsa ya nuna shiɗin ba ya da cutarwa".
Babu zato ta ji an dafa mata kafaɗa. A firgice ta juya da sauri ta ɗora idanuwanta akan na ta.
COMMENTS & SHARE PLS 🙏 🙏 🙏
ALKALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
(Zinariyar🧝♀️ Jajirtattu)
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/D80k1puBPBn6uJhojKKhK5
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🌹BISSMILLAHI RAHMANI RAHIM🌹
*🌸RAYUWA DA MACIJIYA* 🐍 🐍🐍
*PAID BOOK ₦400 complt*
kacal babu tsada
*9043687746 Hassana Aliyu Opay bank*
*Evidence of payment*
09130398321
*DA nayi niyar bar muku free page a aka, amma insha Allah zan kai muku shi twenty free page 🙏🙏🙏*
FREE PAGE ️1️⃣4️⃣➡️1️⃣5️⃣
WRITTEN & DIRECTED ✍️ BY A'ISHA M.B💞
(Zinariyar 🪙 Jajirtattu)
*_______________________________*
Rass gabanta ya faɗi! Yayin da jiri mai karfi ya fara ɗibanta, ta saki wani iriyar razannaniyar ƙara!. Da sauri ta fara ja da baya-baya sakamakon harba da ta yi da wata mai kama da ita sakk.
Riƙe kanta ta yi sannan ta nuna ta da ɗan yatsa a tsorace ta ce. "Wace ce ke? Me ya sa ki ke matuƙar kama da ni? Dan Allah na roƙe ki kada ki cutar da ni".
Murmushi aljanar ta yi sannan ta ce. "Ni bah cutar da ke na zo yi bah, ai idan na kwatanta taɓa lafiyar ki ni ce zan mutu bake bah. Dan aka ki tsaya ki saurari abin da zan faɗa miki". Ta faɗa tana nufar inda Du'a ta ke.
"Kada ki matso kusa da ni, bana so ki rabu dani dan Allah kada ki cutar da ni". Cewar Du'a.
Girgiza kai aljanar ta yi ta ce. "Na faɗa miki bah cutar da ke zan yi bah, ina so ne na sanar miki da wata muhimmiyar magana wacce za ta sa ki iya kare kanki a Koh ina, wanda koh mutum koh aljan bai isa ya tunkari inda ki ke da mugun nufi bah".
Kuka Du'a ta soma yi sannan ta ce. Yayin da hadari ya tashi aka fara yayyafi.
"Ni bana so, ki rabu da ni dan Allah". Ta ƙarashe maganar tare da juya wa da niyar tafiya. Babu zato taji ta yi tuntuɓe da dutse.
Luuu ta tafi tare da faɗuwa a kasan wajan. Jin takun takalmin mutun yasa aljanar ta ɓace daga farfajiyan wajan.
Karasawa wajan Maryam ta yi tare da kwallah kiran sunan Du'a. Jin shiru da ta yi ya sa hankalin ta ya yi matuƙar tashi. Da sauri ta fara waige-waige koh Allah zai sa ta ci karo da Du'a.
Can ta hango ta a yashe a kasa. Babu jinkiri ta yi saurin karasawa wajan. Saurin ɗaga Du'a Maryam ta yi. Yayin da ta fara jijigata tana mai kiran sunanta.
A hankali Du'a ta fara buɗe idanuwan ta yayin da ta dora su hakan na Maryam. Saurin miƙe wa ta yi sannan ta fara waige-waige.
Kallonta Maryam ta yi cike da mamaki ta ce. "Meyafaru Du'a? Me yasa na ganki a yashe a wajan nan.
Girgiza kai Du'a ta yi ta ce. "Babu abin da ya same ni, ina cikin ƙoshin lafiya sannan ta ce.
"Maryam kin samu lafiya, babu abin da ya same ki Koh?". Du'a ta ƙarashe maganar tare da tattaɓa wuyan Maryam.
Murmushi Maryam ta yi ta ce. "Kada ki damu ba bu abin da ya same ni, yanzu ina cikin ƙoshi lafiya kin ji. Amma me ya sa na ganki a nan ke ɗaya?, keda waye ku ke a nan?".
Amsa Du'a ta ba ta da cewa. "Ba bu kowa Ni kaɗai ce hanan wajan". Tana kaiwa nan ta ja hannun maryam sannan ta nufi kujerun da ke garden ɗin da ita.
sai da suka isa wajan sannan Du'a ta zaunar da Maryam ta ce.
"Maryam ina so na yi miki wata tambaya. Shin mutum yana iya zama maciji koh kuwa karya ne?".
"Mamaki ne ya kama Maryam jin abin da Du'a ta furta. Amsa Maryam ta bawa Du'a da faɗin. "Kin taɓa ji koh koh ganin inda mutum ya zama maciji? Duk wacce ma ta fada miki cewa mutum yana iya rikiɗa ya koma maciji toh karya ta ke domin tatsuniya ce kawai bah wani abu bah. sai dai na taɓa jin wani labari da ummata ta taɓa bani akan wata macijiya".
Da sauri Du'a ta kalle ta sannan ta ce. "faɗa min dan Allah ina so na ji".
Kallon ta Maryam ta yi ta ce. "Me ya sa na ga kin bi kin damu? Ki bari bah yanzu bah
, kinga yanzu asuba ce, kuma kinga ya kama ta muje mu ɗauro alwala domin gabatar da sallah".
Riƙe mata hannu Du'a ta yi hawaye na sauka kan kun cinta ta ce. "Inaso ki fada min dan Allah, wannan abin abu ne da ya shafi rayuwata gaba ɗaya, ina so na san ko mai ga me da macizai dan Allah". Ta faɗa tare da haɗa hannayen ta guri guda.
"Ni wallahi ban san ta ina zan fara baki labari bah Du'a. kiyi haƙuri nan gaba za ki san ko mai ga me da macizai tun da aka ki ke so". Cewar Maryam.
"Shi kenen Maryam tun da baza ki faɗa min bah, zan samu masana wanda suka sani na san za su faɗa min".
"Kuma sannan dan Allah da ga yanzu mu daina tafiya tare, saboda ƴan ɗaƙin mu gaba ɗaya aushi na suke ji akan abin da ya faru da ke ɗazu".
Murmushi Maryam ta yi sannan ta ce. "Duniya kyakyawan guri ne, guri ne mai matuƙar kyau mutanen ciki masu kyawawan zuciyoyi ne, dan aka ki dunga kai zuciyar ki nesa kada ki bari sheɗan ya ci galaba a kanki".
Kallon ta Du'a ta yi tare da faɗin. "Ta ya ya gaba ɗaya mutanen ciki suka zama gaba ga masu kyawawan zuciyoyi? Duda cewa koh wane ƙarni sai an samu azzalumi koh sheɗani, shi ne kuma ki ke cewa masu kyawawan zuciyoyi ne, dan Allah kiyi shiru ki rabu rani".
"Da ace kowa addini ɗaya ya ke yi a wannan duniyar, da ba za'a samu kafirai bah, da kowa sai ya fi samun ƴancin kansa". Amma yanzu aikata zunubai da alfasha sun yawaita, Sheɗanci yanzu sune suka zama ruwan dare a cikin zukatan mu".
Murmushi Du'a ta yi tana mai cewa. A duk lokacin da Sheɗanci ya kai makurar tsananta, adalci ne kaɗai ke iya yin maganin sa, kamar yadda idan duhu ya mamaye rayuwar ɗan adam toh haske ne ke iya yin maganin wannan duhun".
"Duda cewar a makarantar nan ina ji kamar akwai sheɗanu, amma ni samm bazan yi wani abu a kai bah domin bah abin da ya shafe ni bane, amma da ina da halin dakatar da su da kuwa ba bu tantama sai na kawar da su".
Murmushi Maryam ta yi ta ce. "Koda ya shafe ki ma ba za ki iya bah, keda bah kowan kowa bah shi ne za ki ce wai za ki dakatar da sheɗanu makarantar nan, kuma bara kiji na faɗa miki, a makarantar nan ba bu sheɗanu. dan aka ki dinga kiyaye harshen ki dan Allah domin ba bu wanda ya san me zai zo ya biyo baya".
Girgiza kai Du'a ta yi ta ce. "Koh kare ya zama sarki, toh kura ta fi karfin haraji. Idan na faɗi abu toh ki yarda cewa sai na yi, a ƙauye mu har dajin da ba bu wanda ya ke iya shiga ta fito a raye na shiga kuma na fito batare da na ji koda kwarzane ne".
"Ƙauye da birni Du'a suna da banbamci, ke ƙauye ki ka sani bakisan birni bah, abin da ki ke gani a kauye bah lallai ki zo birni ki tarar da shi bah, aka zalika abin da ki ke gani a birni babu tabbacin ki iya gani sa a ƙauye".
"Ni Allah na tuba ma daji nawa ne ban shiga bah, koda yaushe a makarantar nan muna cikin zuwa excusion, kuma ba bu inda muke zuwa sai daji, domin samo magani cututtuka. Amma bah gashi bah ba bu abin da ya same ni".
"Shi kenen" Du'a ta faɗa. Tana kaiwa nan ta miƙe tsaye tare da nufar cikin hostel. Bin bayan ta Maryam ta yi da kallo tare da sakin murmushi ta ce. "Allah ya yaye miki Du'a".
Tana kaiwa nan ita ma ta miƙe tsaye tare da bin bayan Du'a.
Ƙarfe takwas ya yi musu a cikin hostel, kafin daga bisani suka fito cikin shigar su ta alfarma. Sanye Du'a ta ke cikin abaya milk colour wanda umma ta aiko a ba ta.
Kayan bah ƙaramin kyau ya yi mata bah. Gaba ɗaya ɗalibai idanuwansu akanta.
Murmushi Maryam ta yi ta ce. "Du'a kinga yadda ɗalibai maza da mata suke binki da kallo?".
Amsa Du'a ta bata da cewa. "Wannan su ya dama, sun daɗe basu kalle ni bah, ni buri Na yanzu shi ne muyi sauri mu isa inda Ahmad ya ce mu haɗu dan wallahi bana son koma wa ƙauye" ta faɗa tare da fito da sarƙar ta daga cikin kayan ta.
Zaro idanu Maryam ta yi ganin sarƙar da ke wuyan Du'a. Baki na rawa ta ce. "Du'a ina ki ka samu wannan sarƙar? Na tabbata wannan sarƙar lu'ulu'u ne kuma zai kai makudan kuɗaɗe kuma naga kamar harda tambarin masarauta a jiki. Du'a a ina ki ka samo shi?"
Kallon sarƙar wuyarta Du'a ta yi sannan ta saki murmushi ta ce. "Wai kinq nufin wannan sarƙar? Toh ai