Showing 27001 words to 28807 words out of 28807 words

Chapter 10 - Rayuwa Da Macijiya Book 1 Hausa Novel Complete

Aisha MB   

30 Dec 2024

264

zai yi wa Du'a ya ji sauƙin abin da ta yi masa.

Abdul ne ya karaso inda Ahmad ya ke yana mai cewa. "Babban president bada kanka a sare, me aka yi maka naga ranka a bace?".

Kawar da kansa Ahmad ya yi ya ce. "Bana son takura Abdul, ka rabu dani ka yi abin da zai finshe ka, bawai ka tsaya ka dinga tsegumi bah".

Kallonsa Abdul ya yi ya ce. "Ahmad ni ka ke cewa ina maka tsegumi,Ahmad ni". Ya faɗa tare da nuna kan sa. Sannan ya kara da cewa. "Shi kenan Ahmad in sha Allah ba zan sake tambayar ka wani abu wanda ya shafi rayuwar ka bah". Yana kaiwa nan ya bar wajan.


Tsaki Ahmad ya ja sannan ya ce. "Ka ji dashi, shashancin banza kawai".
Wayarsa ya ji ta fara Ringing, dauka ya yi sannan ya shige cikin mota tare da jan motar ya bar makarantar gaba ɗaya.


"Ke Du'a gaskiya Umar ɗin nan yana da mutunci sosai, har namiji ya zo ya ce yana son ku zama abokai bana soyayya bah kinga mutumin kwarai ne. Gashi kyawawa amma fah bai kai Ahmad bah".

Takaici ne ya kama Du'a ta ce. "Ni fa idan muna tare da ke bana son ki dinga ambatar sunan wannan mutumin a inda na ke. Kuma shi Umar ɗin da ki ke magana akai ma ni ban yarda da shi bah wallahi , gaba ɗaya fuskarsa baiyi kalan mutanen kirki bah. Kin san ance, Kada ka yanke hukunci da littafin da murfinsa (don't judge book by it cover)".

"Haka ne Du'a ban musan dame ya zo mana dashi bah, koma mene ne aniyarsa ta bishi". Yanzu muje kawai mu fara shirye-shiryen exam na first semester, Na riga dana faɗa wa umma komai kuma ta ce in sha Allah za ta tura mana da kuɗin".

"Shi kenen" kawai Du'a ta furta. Yayin da kai tsaye suka nufi cikin hostel.

Bah dare bah rana su Du'a suke fafutuka wajan karatun exam. Yayin da suma sauran ɗalibai na course ɗinsu suke karatu sosai. Gefe ɗaya kuma tsakanin Du'a da Ahmad ba bu wanda ya sa ke haɗa ido da wani. Gefe ɗaya kuma ƴan ƙauyen su sun yi fafutuka wajan neman kuɗin da Du'a za ta rubuta jarabawa, aka suka dinga siyar da amfanin gonar su don cika muradin ƴa ɗaya tilo wacce za ta zamo jagoran ƙauyen. Inda a karshe da ƙyar da wahala suka samu suka haɗa dubu amsin kuɗin jarabawa.

Ya Inna wuro ce ta kira Du'a a wayar mai gari sosai suka gaisa da Du'a yayin da Inna wuro ta ce wa Du'a. "Ƴata kiyi min alƙawarin cewa ba za ki faɗi wannan jarabawar bah, idan ki ka faɗi toh ki sani cewa ba zamu kara baki kuɗin karatu bah sai dai kije ki nemi wanda zai dinga biya miki kuɗin jarabawa. Dan aka ki dage sosai dan bakisan irin wahalar da muka sha bah wajan ganin mu fidda wannan kuɗin".

Murmushi Du'a ta yi ta ce. "In sha Allah Inna ba zan taɓa yin rashin nasara bah, a koda yaushe zan kasance cikin yin nasara ne. Dan aka ku kwantar da hankulanku wannan jarabawar kamar naci ne".



Ranar Monday su Du'a suka rubuta jarrabawar su da kwarin gwiwar cewar za su yi nasara a wannan jarabawa.

Yau ne ta kama ranar Friday, wato ranar da jarabawar su ta fito.
Du'a na hango ita da Maryam sun ci hijabi onion colour wanda bah karamin kyau ya yi musu bah, bare ma Du'a wacce hijabin ya yi matuƙar karbarta.

Dafa Maryam Du'a ta yi ta ce. "Maryam ba zan iya karasa wa wajan da ake duba wa bah jarabawa bah, baki ga yadda ɗalibai suka cika wajan bah?. Kuma ni ina tsoro kada naje naga na faɗi, don zuciyata tana raya min cewa banci wannan exams ɗin bah".

"Aba Du'a an ce fah faɗi alhkairy ko ka yi shiru, in sha Allahu ma babu abin da zamu je mu tarar sai alhkairy dan aka tawo muje".

Tana kaiwa nan ta ja hannunta suka nufi wajan. Tsaya wa suka yi ganin sun isa wajan. Dubbuba sunanta Maryam ta fara yi yayin da ita ma Du'a ba ta yi jinkiri bah wajan duba na ta".

Ihuun! jin daɗi Maryam ta yi tans mai faɗin. "Du'a na aye alhamdulillah naci jarabawata duka bani da carry over".

Murna sosai Du'a ta taya ta, yayin da ita ma Maryam ta taya ta neman sunanta a jerin daliban da suka ci jarabawa.

Amma ina sunyi neman duniya basu ga sunanta bah. Hankalin Du'a bah ƙaramin tashi ya yi bah ganin ba bu sunanta. Kallonta Maryam ta yi ta ce. "Kiyi haƙuri Du'a".

Kallonta Du'a ta yi ta ce. "Me ya sa ki ke bani haƙuri kuma?".
Amsa Maryam ta ba ta da cewa indai bski ga sunanki bah toh akan yans nufin baki ci wannan jarabawar bah, kin faɗi Du'a".

"Ƙarya ne! Du'a ta faɗa da mugun ƙarfi. Sannan ta ce. "Duk karatun da nake yi bah dare bah rana kenen akan yana nufin ya tafi a banza kenen, wallahi ba zan yarda bah". Tana kaiwa nan ta nufi office ɗin HOD ɗinsu. Ganin akan da Maryam ta yi ya sa ta yi saurin bin bayan Du'a.

Da sallama ta shiga office ɗin hawaye shaɓe-shaɓe kan fuskarta.
Kallonta HOD ya yi ya ce. "Lafiya? Me aka miki ki ke kuka? Shin baki ci exam bane?". Tambayar da ya shiga yi mata kenen.

Cikin sheshekar kuka Du'a ta ce. "Na faɗi jarabawa ta kuma ina da tabbacin wani ne ya sa aka faɗar dani a exam saboda naji ance kuna karɓar cin anci a makarantar nan, dan aka ina son sanin wanda ya sa aka faɗar da ni a jarabawa".

Kallonta HOD ya yi sannan ya ce. "Me ki ke nufi da cews muna karɓar cin anci, shin ke bakya daraja manya ne, wato ni ne nake karɓar cin anci koh, Ni ɗan sanda ne kenen mai karɓar kuɗin mutane".

Haƙuri Maryam ta fara bashi tare da jan hannun Du'a. Wafce hannunta Du'a ta yi daga na Maryam sannan ta nuna Maryam ta ce.

"Kada ki kuskure ki kara taba ni, dan wallahi komai zai iya faruwa. Maida kallonta ta yi kan HOD ɗin ta ce tambaya na karshe waye ta baka kuɗi ka saka na faɗi a jarabawa bayan maƙudan kuɗaɗen da muka biya".

Amsa HOD ya bata da cewa. Ahmad ne. Shi ya faɗa min gaba ɗaya halayen ki marasa kyau. Ashe dama satar amsa ki ke yi bah ƙoƙarin ki bane, sannan kina google amsa a cikin wayar ki bayan an hana shiga da waya cikin exam hall. Dan aka ɗauki exams ɗin ki, ki fice min daga office".

Jikin Du'a ne ya mutu jin kalaman HOD. Rintse idanuwan ta ta yi cikin kunan zuciya ta ce. "Ahmad me ya sa za ka min aka? Me nayi maka da ka nemi gurɓata min suna a idon duniya, tabbas bazan kyale ka bah, a yau komai zai ƙare".

Tana kaiwa nan ta ɗauki takaddun tare da bangaje Maryam ta wuce. Da sauri Maryam da HOD suka bi bayanta yayin da suka dinga kiran sunanta.

Can ta hango shi kan motarsa yana latsa waya. Ba bu jinkirtawa ta karasa inda ya ke.

Hango ta da ya yi ya sa shi sakin murmushi sannan ya sauko daga motar.
Du'a na kaiwa inda ya ke, bata yi wata- wata bah ta watsa masa takaddun a fuska.

Ba bu ɓata lokaci gaba ɗaya ɗaliban makarantar suka taru suka zagaye su.

Cikin ɓaci rai da kunan zuciya ta ce"Gasu nan ka je ka cinye. Yanzu ai burin ka ya cika kasa na faɗi a jarabawa. Maza jeka haɗa shagali kayi murna". Ta karasa maganar tare da fashe wa da matsanancin kuka mai ratsa zuciya.

Cikin sheshekar kuka ta ce. "Kasan ta yadda aka samu aka biya min kuɗin wannan jarabawar? Kasan irin wahalar da ƴan ƙauyen mu suka sha kafin su fitar da wannan kuɗin, me ya sa ba za ka rama fansar ka akaina bah sai akan jarabawa da na dora rayuwata akai".

"Da a ce baka sa na faɗi jarabawa bah da yanzu nasan na riga dana faɗa wa ƴan ƙauyen mu, amma yanzu banida fuska koh kwarin gwiwa da zan iya fuskantar su nace musu na faɗi jarabawa".

"Da badan kai bah da yanzu ina cikin farin ciki da annashuwa. Shi kenan yanzu ka rusa min babban mafarki na, saboda ba zan iya ci-gaba da karatu a makarantar nan bah, tafiya zan yi na bar wannan makarantar".

"Na tsane ka, bana son sake haɗuwa da wannan fuskar ta ka wacce gaba ɗaya zuciyarta bushashiya ce. Ka sani cewa zan ɗauke ka ne a matsayin wanda ya taɓa tsayar min da farin ciki na".

Tana kaiwa nan ta juya da niyar tafiya. Cikin rashin sa'a ta ji ya fizgo ta jikin sa.

A fusa ce ta ture shi yayin da ta saki wani irin ƙara tare da buga kafarta na dama a kasa da mugum ƙarfi.

Cikin ƙanƙanin lokaci aka fara wata ieiyar iska da guguwa wacce ta karaɗe gaba ki ɗaya makarantar, wanda hatta kai ga bishiyoyin makarantar suna karyewa.

Ba bu ɓata lokaci suka ga macizai suka fara fitowa ta koh ina. Ihuuun ɗalibai ne gaba ɗaya ya karaɗe makarantar, yayin da kowa ya fara yin ta kansa.

Banda Ahmad wanda koh gizau bai yi daga inda ya ke, saima ƙara gyara tsayuwar sa da ya yi. Yayin da idanuwansa suka kaɗa suka yi jajir.

Gaba ɗaya ɗaliban ne suka ja da baya inda suka bar iya Ahmad da Du'a a tsakiyar makarantar yayin da kowanensu na fuskarta ɗan uwansa.

A ta ke macizai suka fara zagaye Du'a da Ahmad. Babu shiri jikin Du'a ya fara kakkarwa, yayin da fatarta ya fara saɓulewa.

Duk abin da ya ke faruwa akan idanuwan ɗalibai da kuma malamai na makarantar. Ganin akan da shugaban makarantar ya yi, ya sa shi saurin kiran jami'an tsaro.

Kallon Ahmad Du'a ta yi ta ce. "Jarumtar ka ba zai taɓa burgeni bah, domin a yau bah gobe bah za ka mutu, domin kuwa kashe ka za suyi.


Murmushi Ahmad ya yi sannan ya ce. "Kwarai kuwa ba bu tantama kece wacce na daɗe na ke nema kuma yau gani ga ki a gabana. a yau za ki san koh ni wane ne.


🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍🐍

YANZU WASAN YA FARA🏹🔪🗡️. SHIN AHMAD WANENE? ME YASA YA DAƊE YANA NEMAN DU'A, SHIN DAMA A CAN DA YA SAN DA ZAMANTA NE KOH Aa. KODAI SHIMA BAH MUTUM BA NE.

TOH KAWAI KUDAI KU BIYO NI DAN JIN YADDA ZA'A KAYA.



*END OF FREE PAGE*

COMMENTS & SHARE PLS 🙏 🙏


*MASU SON CIGABA DA KARANTA LITTAFIN RAYUWA DA MACIJIYA SAI KU BIYA KUƊI DOMIN A SAKA KU A ƊAYAN GROUP DIN WANDA ZAN CI-GABA DA KAWO MUKU RAYUWA DA MACIJIYA.*



IDAN KIN SHIRYA BIYA SAI KI BIYA DOMIN A SAKA KI A DAYAN GROUP NA PAID.

*PAID BOOK ₦400 complt*
kacal babu tsada
*9043687746 Hassana Aliyu Opay bank*
*Evidence of payment*
09130398321

KADA KU BARI A BAKU LABARI.


ALKALAMIN ✍️
BY A'ISHA M.B💞
(Zinariyar 🧝‍♀️ Jajirtattu)


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login