Showing 9001 words to 12000 words out of 28807 words
kanta kenen.
Basar wa tayi sannan tace. "Koh ma mene ne su suka sani, nidai na shigo dajin nan kuma sannan ina da tabbacin cewa zan fita lafiya". Tana kaiwa nan ta nufi inda bishiyoyin magunguna suke. batare da ɓata lokaci bah, ta fara tsinkar ganyayyakin. saida ta tsinki adadin yadda ranta yake so, sannan daga bisani ta nufi hanyar da take tunanin cewa ita ce hanyar futa.
Saida tayi tafiya mai nisa sosai sannan daga chan nesa ta hango wani abu mai sheƙi da haske. Karasa wa tayi wajan domin cire kwarkwatar idanuwan ta.
Zaro ido tayi ganin madubi ne wanda aka ƙayata shi da furenni masu kyau da daukar ido. Mamaki ta shiga yi domin ita tun da ta ke bata taɓa gani abu makamancin aka bah. Ƙoƙarin kai hannun ta take kan madubin.
Ta ke taji wani zuciya yace mata kada ta taɓa. Barin wajan tayi sannan ta ci-gaba da tafiya, hango wani karamin bishiya tayi daga chan nesa, da sauri ta karasa inda bishiyar take.
Rubuce_rubuce taga hanyi a jikin bishiyar. yayinda jini ke malala a jikin ganyayyakin ta. Tsoro da fargaba ne ya mamaye zuciyar Dua, yayinda ta ke ji kamar ta kawo kanta ga halaka ne.
Rintse idanuwan ta tayi, cikin kwarin gwiwa ta kai hannun ta ga wannan bishiyar. Babu zato ta fara jin muryoyi mara amo da daɗin sauraro ta koh ina. Yayinda suke faɗin. "Barka da dawo wa duniyar ki sarauniyar macizai, muna miki maraba da zuwa".
Cikin rashin fahimtar furucin su tace."su waye ku?, mene ne kuke nema a gare ni?, maza ku faɗa min hanyar da zan fita daga wajan nan ".
An gama shugaba taji sun furta. Babu tsanmani taga anyi sama da ita sannan aka fara tafiya da ita akan iska.
Saida aka yi tafiya mai nisa daga bisani suka isa baƙin wani kogi wanda launin ta ke jajir tamkar jini.
Sauke ta suka yi sannan suka ce da ita. "Halitta ɗaya ce a duniyar nan zata iya bin ta wannan kogin kuma wannan halittar itace sarauniyar macizai, idan har ke ɗin ce da gaske toh zaki bi wajan nan batare da wani abu na cutar wa ya tunkari inda kike bah".
"Amma kuwa indai ke ta bogi ce toh ki ƙaddara cewa kin zama gawa domin zaki yi mummunan mutuwa ne, sabo da wannan kogin halitta ɗaya ta yarda ta bi ta kanta, kuma ita ce shugaba na macizai ".
'Koh mu da muke Aljanu bamu isa mun bi ta wannan kogin bah, domin idan muka kwatanta yin akan zamu zama mutattu ne. Fatan nasara a gare ki". Suna kaiwa nan wajan yayi shiru.
Bin kogin Dua tayi da kallo, yayinda take ganin kamar duk abin da suka fada karya ne. Tsugunnawa tayi ta dora idanuwanta kan ruwan kogin. Sannan daga bisani ta saka ɗan yatsarta acikin ruwan.
Babu zato taga ruwan ya fara juyi, sannan ya farayin sama, saurin ja da baya tayi ganin yadda ruwan yake jujjuyawa tamkar mutum. Cikin kankanin lokaci taga ruwan ya raɓe yayinda wajan ya bada siririyar hanya.
Batare da tsoro bah ta fara bin hanyar wajan da sauri. Sosai ta ke mamaki ganin baƙon al'amari irin wannan.
Tana barin wajan ta kuma ganin ta a tsakiyar wani dajin daban. Namomin daji gaba ɗaya ta ke ta harba dasu. Yayinda kyawawan tsuntsaye suka fara hawa jikin ta.
Cicire su ta soma yi daga jikin ta, amma a yayinda ta ke cire su wasu na zuwa. Saida tayi da gaske tukunnan suka bar jikin ta. Kowane dabba na dajin binta yake da kallo.
Hatake taga namomin dajin gaba ɗaya sun tsuguna cikin gwiwo winsu tare da saukar da kai ƙasa. Mamaki ne ya kama ta. A yayinda take ganin mene ne akan da suke yi.
Ci-gaba da tafiya tayi, a yayinda suke mara mata baya. Juyawa tayi da sauri gani ko wace halitta ta dajin gaba ɗaya ita suke bi.
Alama ta fara yi musu da hannu dasu koma, amma ina kamar basu san tana yi bah. Ci-gaba da tafiya tayi, su kuma na biye a bayan ta.
Juyawa tayi a fusa ce tare da daƙa musu tsawa! Babu shiri gaba ɗaya suka ja da baya. Cikin ɓacin rai ta nuna su tace. "Maza_maza gaba ɗaya ku koma kafin na hallaka ku baƙi ɗaya". Ta faɗa tsoro fal cikin ranta
Kamar da wasa taga gaba ɗaya sun juya tare da koma wa. Baki sake tabi su da kallo, a yayinda take mamakin kanta. shafa jikin ta tayi sannan tace. "Ta yaya kuma ni na iya yi musu magana? Wacece ni? Me yasa ina ce musu su koma kuma naga sun koma?.
Wani zuciyar tata tace. "Inaga sabo da tsawar da nayi ne shi yasa.
Tafiya ta cigaba da yi inda a karshe ta hangi wani baƙin kofa wanda ba'a ganin ƙarshen ta sabo da girma da tsayin da ta ke dashi.
Murmushin jin daɗi tayi tace. "Babu makawa wannan ita ce hanyar da zanbi domin barin wannan dajin. Batareda wani tunani bah ta nufi wajan kofar da sauri.
Babu zato taji kifiyoyi na fitowa ta koh ina. Da sauri ta kwanta ƙasa, yayinda gaban ta ya tsananta faɗuwa.
Cigaba da harbo kifyoyin🏹 aka yi babu kagautawa. Ganin abun bana ƙare wa bane ya sata miƙewa da sauri.
Da mugun gudu ta nufi kofar da take tunanin ita ce hanyar futa. Cikin sa'a ta isa baƙin kofan batare da ta bari koh da ɗaya daga cikin kifiyan ya cake ta ba.
Hajiyan zuciya ta shiga sauke wa. Saurin Daga kanta tayi tare da dora wa akan wannan kofan. Rubutu taga anyi a jiki wanda ita kanta ba tasan me aka rubuta bah.
Sannan wannan kofar ba za ta taɓa bude wa bah batare da anyi kalmomin bada izinin wucewa bah.
Riƙe kanta tayi alamin tana yin nazarin wani abu, da sauri ta ɗago sannan tace. "Maza buɗe".
Shiru taji, taga kofa bai buɗe bah, cikin daƙewa ta cigaba da jarraba sa'ar ta,amma ina,koh gizau kofar batayi bah.
Soma gajiya Dua tayi, yayinda take ganin cewa nan zata karashe rayuwar ta. Maganganun aljanun dazu ne ya fara i mata yawo a kwakwal wa.
"Halitta ɗaya ce a duniyar nan zata iya bin ta wannan kogin kuma wannan halittar itace sarauniyar macizai, idan har ke ɗin ce da gaske toh zaki bi wajan nan batare da wani abu na cutar wa ya tunkari inda kike bah".
Buɗe idanuwan ta tayi, sannan ta miƙar da hannun ta tare da ɗora wa akan kofar tace. "A matsayina na shugaba da kuma sarauniya na macizai da sauran halittun boye, ina bukatar wannan kofar ta buɗe yanzu kamar yadda na buƙata".
Cikin kankanin lokaci kofar ta fara girgiza, hatake shima wannan dajin ya soma girgiza, faɗuwa Dua tayi ƙasa yayinda ganyayya kin hannun ta suka soma zube wa. Saurin miƙewa tayi ta kara faɗin. "Idan har niɗin ce da gaske shugabar ka, ina so ka buɗe min hanya yanzu".
a hankali kofar ta fara wangale, daga karshe kofar ta buɗe gaba ɗaya.
Farin ciki ne gaba ɗaya ya bayyana kan fuskarta, cike da farin ciki ta sanya kafar ta na dama tare da shi cewa cikin kofar.
Shigar ta keda wuya kofar ta rufe kanta.
Dua bata ganta a koh ina bah sai a cikin fadar Mai gari. Miƙewa tayi da sauri ta fara kwallah kiran Inna wuro.
Ba zato bah tsammani suka jiyo muryar ta, waigawa suka yi da sauri, hatake suka ɗora idanuwan su akan ta tana riƙe da magunguna.
A lokacin bah Dua suka gani bah, gobe mai haske suka gani a tattare da ita.
Da gudu ta nufi wajan Inna wuro tare da rungume ta sannan ta ɗago kai ta kalle ta tace. "Dama na faɗa muku cewa zan shiga kuma na fito lafiya batareea wani abu na cutar wa ya tunkari inda nake bah, yanzu dai kun tabbatar da cewa zan iya kare kaina batare da taimakon kowa bah koh ".
Kallon ta Mai gari yayi yace. "Babu wani ɗan adam da ya taɓa shiga wannan dajin ya fito a raye bah, amma ke kin shiga kuma kin tsinko magunguna sannan kuma kin fito bstareda kinji koda kwarzane bah ".
"Tabbas akwai wani ɓoyayyen al'amari game da ke, yanzu na yarda keɗin jaruma ce, kije na baki dama kije birni domin yin karatu kamar yadda kika bukata".
Kuma sannan zamu haɗa kuɗi baƙi ɗaya mu biya miki kuɗin da zaki je birni. Domin a yau ɗin nan kin sanya fuskar kowa murmushi, sannan ki mamaye zuciyoyin mu da farin ciki".
Maza kije ki shirya kayan ki domin yau ɗin nan zaki je birni karatu. Tsalle Dua ta daka tare da faɗin na gode sosai Mai gari, yanzu zanje na haɗa kayana, sai wani yayi min jagora ya kaini baƙin hanyar fita daga wannan ƙauyen".
Tana kaiwa nan ta shige cikin gidan su.
*KANO STATE BIRNIN TARAYYA*
Ƙerarriyar mota na hango kirar Mercedes Benz ta shiga makarantar Northwest university da gudu, inda gaba ɗaya dalibai idonsu akan wannan motar. Tabbas sun san da cewa mutum ɗaya ne yake gudu kamar ana gasan tseren mota a wannan makaranta. Gaba ɗaya ya zamana ya cika makarantar da ƙura.
Tsayuwa motar tayi . Lokaci ɗaya naga an buɗe kofan motan . Ganin wanda ke cikin motar yasa gaba ɗaya dalibai Jan jini jikin su. Sanin cewa tabbas president ɗin ɗalibai na makaranta ne wato Ahmad Yasir Bello, yasa gaba ɗaya nufan inda yake sannan suka fara kwasan gaisuwa.
Kafa naga an fito dashi, wanda ke sanye da canvas blue, daga bisani ya fito daga cikin motar. dukkan yabo su tabbata ga ubangiji Wanda yayi wannan kyakyyawar halitar. Fari ne amma farin sa irin yan black Americans ne. Fuskar sa a murtuke kamar bai taɓa dariya ba.
Yayinda yake ɗauke da madaidaicin hanci da baki wanda ke pink colour.
Sanye yake da jeans din wando blue sai t shirt fari da facing cap blue. Wannan kaya ba karamin kyau yayi wa Ahmard bah, wanda ɗalibai ke masa lakabi da A.y the school president.
Cikin lion voice ɗin sa yace. "Maza kowa ya ɓace daga nan, sannan bana son naga kowa ya wuce wani guri in bah department ɗin sa bah, understood?".
Yes gaba ɗaya suka furta,cikin kankanin lokaci kowa ya nufi class ɗinsa, duda cewar ba kowane class ne suke da lecture yanzu bah, amma saida kowa ya shiga sabo da sanin halin Ahmard baya raga wa kowa.
Wani mature guy na hango yana nufo inda Ahmad yaƙe. Karasa wa inda Ahmad ke tsaye yake tare da sakar masa murmushi yace. "Our president, kana aiki da kyau, chab wannan da kana shigowa makaranta jikin kowa zai fara kakkarwa kamar sunga mala'ikan mutuwa".
"Gaskiya ya kama ta ka rage wannan abu da kake yi gaba ɗaya abin da kake yi is not fair".
Haɗe rai Ahmad ya ƙara yi tare da kara murtuke fuska sannan yace dashi. " waya baka izinin fitowa daga class Abdul?.
Kallon sa Abdul yayi, lokaci ɗaya ya ƙyalkyale da dariya, saida yayi mai isarsa sannan yace. "Nima da nake abokin ka baka barni bah, lallai kamm Ahmad wuyan ka ya isa yanka, amma ina fatan wata rana wata ta saukar maka da wannnan jiki dakai da kuma taurin kai.
Murmushi gefen baki Ahmad yayi yace. "Babu ita, kuma ba zata taɓa bayyana bah, banga wacce ta isa ta saukar min da izza ta bah".
Kallon sa Abdul yayi sannan yace. "Idan kuwa Allah ya bayyana ta fah?
Maida kallon sa kan Abdul Ahmad yayi sannan yace. "Duk ranar da Allah ya bayyana ta, sannan kuma naja taja magana ta ba tare da tsoro kan fuskarta bah, ni kuma nayi maka alƙawarin cewa daga ranar, duk abinda kace nayi ni kuma saina yi. Wannan alkawari na ne ".
*TOH FAN'S MEYE RA'AYIN KU GAME DA AHMARD, SHIN DUA ZATA ZO BIRNIN NE KOH A'a. TABBAS AKWAI KALLO GABA*.
COMMENTS & SHARE PLEASE 🙏🙏🙏
ALKALAMIN ✍️
A'ISHA M.B💞💞💞
(Zinariyar🪙 Jajirtattu)
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🌹BISSMILLAHI RAHMANI RAHIM🌹
*🌸RAYUWA DA MACIJIYA* 🐍 🐍🐍
*PAID BOOK ₦400 complt*
kacal babu tsada
*9043687746 Hassana Aliyu Opay bank*
*Evidence of payment*
09130398321
FREE PAGE 1️⃣0️⃣➡️1️⃣1️⃣
WRITTEN & DIRECTED ✍️ BY A'ISHA M.B💞
(Zinariyar 🪙 Jajirtattu)
*_______________________________*
"Uhmm Ahmard kenen sarkin rigima, toh shikenen ni kuma nace maka wannan ranar saita zo, kaje ka rubuta zaka ce na faɗa maka".
"Ni abin da ma yasa kaga na fito daga class bah komai ba ne, illa kiran ka da Uncle Sharif ya ce nayi".
"Mene ne mutumin nan yaƙe buƙata ne? Na faɗa masa cewa bana son takura a rayuwata, yanzu ina zuwa gaba ɗaya zai cikani da warin baki".
Dariya Abdul yayi sannan yace dashi. "wallahi Ahmad kana da wuyar sha'ani, yanzu malamin naka kake wa wannan cin fuskar? Gaskiya kana buƙatar a saita ka ".
Fuskar Ahmad ne ya sauya daga walwala zuwa ɓacin rai, sannan ya kalli Abdul yace. "Go back to your class Abdul". Ya faɗa tare da kauda kai gefe.
"Shike nen ai zan tafi, ni na isa naja da maganar ka, kaga tafiya ta ma". Ya karashe maganar tare da barin harabar wajan.
Ganin akan da Ahmad yayi yasa shima ya nufi office din Uncle Sharif.
Ɓangaren Du'a kuwa, saida ta shirya tsaff ta haɗa gaba ɗaya kayan ta masu kyau sannan ta saka su a cikin jakar ta na saƙa, ta cinciɓe ta sannan ta fito da ita harabar ƙauyen.
Ɗaukar wayar sa Mai gari yayi tare da kiran ƙanwar sa Sakina, sannan yayi mata bayanin zuwan da Du'a zata yi gidan ta.
"Allah ya kawo ta lafiya kawai Sakina ta faɗa".
Sallama Mai gari yayi mata daga bisani ya katse wayar. Kallon Du'a yayi sannan ya mai da kallon sa ga maza biyu dake tsaye yace dasu. "Kune nake so ku raka Du'a har gidan Sakina sabo da kune ƙaƙƙarfan maza a wannan ƙauye, kuma inada tabbacin za ku ƙare ta ".
"In sha Allahu mah zamu kare ta duda cewar Allah ne mai karewa, amma muma zamu yi iya bakin ƙoƙarin mu wajan ganin babu wani abu na cutar wa ya nufi inda ta ke bah". Cewar ɗaya daga cikin mazan.
Miƙa wa Du'a kuɗaɗe dake hannun sa Mai gari yayi, Du'a ta karɓa, tana mai cewa. "Ina matuƙar godiya da bani damar zuwa birni, kuma nayi muku alƙawari bazan taɓa baku kunya bah, baza ku taɓa dana sanin bari na da kuka yi naje birni bah".
"In sha Allahu abin da ya kaini chan shi zan yi, kuma na gode da kulawar ku a gare ni ".
Ta karashe maganar tare da nufa inda Inna wuro ta ke, durkusawa tayi sannan tace."inna ina son ki saka min albarka, sannan kiyi min addu'a Allah ya bani abin da naje nema ".
Murmushi Inna wuro tayi tace. "Allah ya yi miki albarka ƴata, ya baki nasaran cim ma burin ki na alhkairy, yasa ki gane duk abin da aka koyar dake ".
"Ameen" Du'a ta amsa. Hajiyan zuciya Inna wuro ta sauke sannan tace. "Amma wani hanzari bah gudu bah, ina so kiyi min alƙawarin cewa zaki dawo gida kafin ki cika shekaru ashirin ciff a duniya".
Murmushi Du'a ta sakar mata tare da mai kallon ta kan Inna wuro tace. "Karki damu Inna in sha Allahu zan dawo kafin na cika shekaru ashirin a duniya, ai naji kuna faɗa a tsakanin ku cewa idan na cika shekaru ashirin a duniya, wani abu zai bayyana a jikina, kuma sannan rayuwata zai kasance a koda yaushe cikin hatsari ne".
"Yanzu inada shekaru sha tara ne a duniya, nasan za'a yi mana hutu a makaranta kafin na cika shekaru ashirin".
"Dan aka duk ku kwantar da hankulan ku baki ɗaya". Tana kaiwa nan ta cinciɓi jakarta tareda ɗora wa akan a malanke na saniya, wanda mai gari ya tanadar musamman dan suje bakin ƙauyen.
Saida gaba dayansu suka hau sannan dokin ya soma tafiya, lokaci daya fuskar Du'a ya sauya daga walwala zuwa damuwa.
Saurin dakatar da su tayi da faɗin. "Ku tsaya". Tsayar da a malanke ɗin suka yi tare da mai da kallon su kanta.
Da sauri ta sauka daga kan amalanken sannan ta nufi cikin gida da gudu. Kai tsaye ɗaƙin magani da mahaifiyarta ta ke ta nufa.
Shiga ɗaƙin tayi, sannan ta durkusa kan gwiwowin ta tace. "Mama inason ki saka min albarka, nima yanzu zan zama yar birni zan je birni karatun likitanci sannan na samo miki sunan maganin da zata farfado dake kinji".
"Ina so kiyi min fatan nasara". Share hawayen ta tayi da bayan hannunta sannan ta kara da cewa. "Shike nen na tafi kuma zan so ace kafin na dawo ki farfaɗo daga wannan baccin da kike".
Sannan ta ƙara da cewa. "Ya Allah ka kiyaye min mahaifiyata, kasa mata nutsuwa da kwanciyar hankali, duk wani cuta koh damuwa ka yaye mata su, ameen ya rabbil izzati".
Tana kaiwa nan ta fice daga ɗaƙin tare da ficewa daga gidan ta nufi inda amalanken yake sannan ta shige ciki tare da ɗaura mayafi a fuskarta, saida ta tabbatar ba'a ganin komai na fuskarta in banda kwayar idanun ta, sannan ta yi wasu Inna sallama.
Abinci kala_kala mutanen kauyen suka saka musu ganin cewar za suyi kwanaki a hanya batare da sun samu abin taɓa wa bah.
Addu'a inna wuro tayi musu tare da mata fatan sauka lafiya.
Sai da suka yi wa kowa sallama daga bisani suka ja amalanken suka bar harabar kauyen.
Tafiya mai nisa suka yi sannan daga nan suka isa wani garin, saida suka yi kwanaki biyar a hanya kafin daga bisani suka hangi wata siririyar hanya, babu bata lokaci suka fara bin hanyar.
Tafiya suke batare da wani ya kula ɗan uwansa bah, babu zato suka ji an rufa su da raga yayinda gaba dayansu suka shige cikin ragar tare da yin sama.
Hatake gaba dayansu suka kwashe da dariya gami da faɗin. "Babu wanda yake bin hanyar nan ya tafi lafiya, wannan yankin mu ne babu wanda muka bawa umarnin bin wannan hanyar".
Kokarin cire kanta Du'a take daga jikin ragar, amma ina akan ya cutura. Kallon su tayi a fusa ce tace. "Kune waɗan nan yan dajin masu karɓar haraji Koh?".
Ƙeƙeta dariya gaba ɗaya suka yi!. Sannan daya daga cikin su yace. "Kamar naso na gane wannan muryar taki, su waɗan nan mazan da suke mara miki baya basu faɗa miki mu yan daji bane?".
"Maza_maza ku kunce mu kafin raina ya ɓaci". Ta ƙarashe maganar tareda kokarin