Showing 45001 words to 48000 words out of 65321 words

Chapter 16 - Yar Sadaka Book 2 Hausa Novel Complete

03 Jan 2025

315

Har tana shidewa' jimm yayi kadan Yana tunani kafin ya koma gefen titi yayi parking Yana kallanta.


Ya Jima Yana qare Mata kallo' kishinta da tausayinta tare da haushin kukan da take Na qara taso masa' yace' Wai Dan Allah me kikeso ke idan ba ihu aka Miki ba kakyajin Dadi?

Girgiza masa kai tayi yace' tam kimin shiru haka ya isa' Ko kinaso kanki yayi ciwo?

Ah ah tace tana jinjina Kanta nan ya Tashi motan a zuciyarsa Yana cewa' zanga shegen daze qara cewa Yana nemanmu' Ni nayi iya yina Dan a zauna lafiya Nima a barni naci amarci na ya qare Magana Yana kwantar da ita a Kan cinyarsa Yana shafa Kanta tare da cigaba da tuqi da daya hannun.


Karfe 4:30 pm suka qaraso katafaren gidansu' Akan idon Yasmeen dalleliyar motarsa tayi parking da sauri ta koma ciki ta qara feshe jikinta da turaruka masu dadin kamshi'don ta Jima da tashi a bacci tin wurin karfe daya da rabi' tin tini takesa ran dawowar be dawo ba Dan ita ta manta da rayuwar nijlah a gidan duba da yadda mashkur ya rikice Mata a daren jiya ga wasu irin kalamai masu Sanya zuciya nishadi daya riqa kwararo Mata su Dan haka take tunanin ita dayace a cikin ziciyarsa' cikin sauri ta saki sabulan ta fito tana Taku qus qus qus qus..*Wannan shafin na kudine'karki karanta idan baki siya ba' ga mai so zata Biya 200 naira kachal ta karanta' Zaki Tura katin MTN ta wannan number 09038049272,,Ko ta account number, 0089110527, suwaiba Hussaini zakirai, access bank.idan Baki siya ba karki karanta..* o

*'yan Niger su tuntubi wannan number,, +22789520047.*



Suna tsayawa nijlah tayi saurin bude motan' hannu yasa ta Baya ya riqe gefen rigarta Yana binta da Wani irin kallo' a sanyaye itama ta juyo tana kallanshi' tare da narkemasa a shagwabe tace' ka sakeni bacci bakeji.

Be saketa ba saima binta da mayatancen idanunsa yayi' Yana qara kashe Mata su.


Daidai lokacin Yasmeen ta karya kwana zuwa hanyar da zata Sada ta da gurin parking motocin gidan' abinda idanunta ya gani shiyasata saurin tsayawa tare da murtsuka idanunta tanasan tabbatarwa da zuciyarta abinda idonta ya gani' su din ne ba qizo suke Mata ba.

Wani iri Taji zuciyarta Na Mata lokaci guda tafara dokawa da sauri da sauri' jitake kama zata fasa cikin qirjinta ta fito' kasa tsayuwa tayi dan bazata iyaba'

da dabara ta kai Kanta jikin Bango ta rumgume' hannunta dafe da zuciyarta Amma Duk da haka ta kasa dauke idanunta a kallansu' Saima qara budesu take tana Jin Wani Saban Kishinsa na qara shigarta.

A galabaice ta qara dagowa tana kallansu' daidai lokacin da mashkur ke janyo Nijlah jikinsa.

Saida Yasmeen ta runtse idanunta sabida bazata iya ganin wannan tashin hankalin dake dab da tarwatsa Mata zuciya ba'

ta qara gyara tsayuwarta tana kallansu' hawaye na wanke Mata fuska' abubuwa da yawa take aiyanawa a cikin zuciyarta.

Tinda ya janyota jikinshi take qoqarin kwacewa sedai be Bata damar Hakan ba Dan ba riqon wasa yayi masa.

Ki nutsu dallah' sallama zamuyi sabida bazaki samu damar ganina a ciki ba' wannan lokacin matata ne.

Batayi Magana ba" abinda Jin zafin kalamanshi'
hawaye masu zafi suka riqa rige rigen sauka akan kyankyawar fuskanta' binta yayi da kallo kafin ya zagaye qugunta da hannunsa yana lashe hawayen da murmushi dauke akan fuskarshi.'


nijlah Kam ta daskare a gurin Sai da ta dauki mintuna tana tinanin irin qiyayyar dayake mata kafin ta iya daga qafanta ta fito Daga cikin motan.

Cike da tsokala yace' au sallama ne bakiso muyi Zaki fita?

Batayi Magana ba ta fita da sauri Shima binta yayi da ido Yana mamakinta'


Ashe ni shashasha ne dana dauketa na kaina gurin Wanda sukayi soyayya da shi yanzu?
ko Dai ni bansan kaina ba?
da Har zata dauka irin wannan fishin sabida kawai nace matata.


Nijlah na fita ta nufi bangarenta zuciyarta da jikinta na Wani irin kyarma ga Wani tuquqin bakin ciki daya turniqe mata zuciyarta' ta gaban Yasmeen ta wuce Bata kula da ita ba.

Tinda ta qaraso inda take Yasmeen tayi kwafa tare da tsareta da idanunta hartazo daf da ita zata wuce.'
a fusace Yasmeen tace ke Dan ubanki Daga gidan uwar wa kuke?


Hararanta nijlah tayi ta cigaba da tafiyanta.

Ke 'yar kauye ba Magana nake Miki ba?

Da Sauri nijlah ta qarasa jikin kofan falonta Har tana tintibe sabida tashin hankali da take ciki yafi Wanda Yasmeen ke neman jefata Dan haka ta qara yimata banza ta cigaba da tafiyanta.


Ido Yasmeen ta tsura Mata Babu Ko kiftawa' a hankali zuciyarta ta riqa kitsamata abinda ya kamata tayi' juyowa tayi taga nijlah Na qoqarin Shiga falonta.

Dasauri tayi Kanta tana cewa' Ni sa'arkice ina Magana kina tafiya?

Girgiza Mata kai nijlah tayi'
ta kuma bude baki tana cewa'kiyi hakuri aiba Ni Zaki tambaya ba ki tambaya ya mashk''' Bata qarasaba Yasmeen ta sauke Mata lafiyayyan Mari' dafe gurin nijlah tayi tana kallan kofa' ganin ba kowa yasa tayi saurin juyawa zata gudu' Yasmeen ta qara dauketa da wasu Marin Har guda uku' Kuka nijlah tasa sakamakon daukewar jinta da ganinta Na Yan lokuta da tayi.


Jikinta Na rawa tace' Allah ya isana muguwa Kawai' Wanda Bata tsoran Allah.


Bige mata baki Yasmeen tayi tace'

Au nice muguwa ko' yanzu zakiga mugunta tinda ke yar iska ce Na tambayeki inda kukaje da mijina zakice kince Na tambayeshi' ga sa'ar uwarki ko' yasmeen ta fada tana dauko wayar charger.

Karkarwa jikin nijlah ya dauka ta saki qara a hankali'

Daga wayar yasmeen tayi zata tsula Mata mashkur yayi saurin riqewa ta bayanta tare da fizge wayan Yana binsu da kallo.

Sannu da zuwa Yasmeen tayi masa ya kafeta da ido kafin a hankali ya Maida kallansa ga nijlah.

Takure ya Ganta jikin Bango tana Kuka a hankali.

Yasmeen ya Kalla ransa a mugun bace yace'

Meyya hadaki da ita?

Cike da karairaya Yasmeen tace' baby rashin kunya zatamin Kuma.


Dakata nace' Kuma me?

Uwar tace ke Zaki daketa da wannan wayan?

Ganin yadda Yana yinsa ya chanza' tayi saurin cewa'

Baby banfa daketa ba' Amma gaskiya ka gayamata abinda banaso acikin gidan nan.

Ransa a bace yake kallanta' Sai kuma yayi Kan nijlah yasa hannu ya dago fuskanta' kumburi ya gani sosai Akan fuskan gefe guda ga yatsunta nan kwance Akan yar qaramar fuskan' kallan Yasmeen yayi Sai kuma yayi kwafa ya rungume nijlah suka Shiga cikin daki'.


Tsaki Yasmeen tayi ta juya zuwa nata Dakin tana cewa' indai irin wannan Zaman za'ayi Ni Kuma bazan basa jibgarki ba.

A kunnen mashkur tayi Magana be juyo ya kalleta ba ya shigar da Nijlah daki tana ta sauke ajiyar zuciya.

Kan gado ya zaunar da ita Yana cewa'

Kinga abinda taurin kanki yaja Miki Ko?
Nace kitsaya kinqi tsayawa gashinan kinfito an taba lafiyarki.

Jikintane yayi matuqar sanyi ta juya idanunta cike da hawaye tana kallanshi tare da jinjina maganganunsa' tabbas zata sha wahala a Zaman gidannan sedai bazata taba yadda da irin wannan ba.

Juyamasa Baya tayi ta kwanta tana goge hawayen fuskanta jikinta na karkarwa sabida bacin rai.

Wai ma meya hadaku Daga shigowanki?


Nima bansani ba Amma ka sani wallahi daba yanzu bane' Ni bazan zauna tana dukana Kamar ita ta haifeni ba' Dan haka Zan bar Muku gidan kuyi yadda kukeso tinda bakace Mata komai ba Kuma kana gani ta qare maganar da Kuka.


A hankali yace niban gani ba' Ko ina gurin abin ya faru' ke yanzu Na tambayeki kinqi gayamin.


Cikin Kuka nijlah tace'bani da burin hadaka da matarka saboda haka ka Tashi ka tafi gurin ta Allah shize sakamin.

Qoqarin rarrashinta yake taqi bashi Dama haka ya Tashi jikinsa ba kwari ya koma bangaren yasmeen.


Zaune take a falo tana karanta wani littafin sanadi na momn sultan Taji shigowansa' ajiye wayan tayi ta tafi da gudu ta rungumeshi tana Kiran oyoyo baby nayi kewarka.


Kissing kumatunta yayi Yana riqe da ita Har suka zauna Kan daya daga cikin kujerun.

Yana rungume da ita yafara shafa santala santalan cinyoyinta kafin ya bude baki a hankali yace' baby ya jikin naki? Ya warke Ko ya fada Yana tsareta da ido.

Dasauri Yasmeen tace ah ah ni yanzuma Wani Saban ciwo yakemin kuma kace Dr ze dubani Har yanzu be zoba kaima tinda ka fita Baka dawo ba Sai yanzu.

Eyyah srry Wani aikine ya tsareni shiyasa.

Turo masa baki tayi tana cewa'Kuma shine ka fita da nijlah Bayan kace Babu Wanda ze fita a gidannan Sai Bayan shekara?

Ah ah yace Yana Hura Mata iskar bakinshi' yana cewa' niba fita nayi da ita ba' ina dawowa Na Ganta zaune a can ta zuba uban tagumi shine tace Kanta Na ciwo' nace ta dauko paracetamol a Mota taje Bata gani ba shine Kawai naje da kaina Na dauko Mata Amma ba tare muka fita ba.

Dadi sosai ya lullube Yasmeen ta qara shigewa jikinshi' a hankali Kuma yace'

Yauwa waini mayya hadaku Na shigo Naga nijlah Sai Kuka take? Kinsan banasan tashin hankali Ko baby?


Tabe baki Yasmeen tayi tace' wallahi baby yarinyar Bata da kunya' Wai daga Na tambayeta inda kuke je shikenan ta fara zagina shine Na dauko wannan wayar Zan zaneta ka shigo falon ka hanani.

Eyyah Kawai yace' sabida yanaso a bashi abinda yake nema ya Tashi Yana cewa' muje ki tayani watsa ruwa yau a gajiye nake.


Bayan ya shirya suka dawo falo Yasmeen ta zuba musu abinci Wanda mummy ta Aiko dashi wurin karfe 6 na yamma

Suna gamawa ta kwashe kayan ta kai kitchen' daki suka koma Suna hira' Ko masallaci Bata Bari ya fita ba' a daki yayi sallah Suna hira Duk da yawancin hiran ita keyi Shi gaba daya hankalinsa Yana Kan nijlah tsoran abinda zesa ta hanashi Kanta yasa Shi kasa fita ya ganota' a haka Har qarfe 10 yayi Suna zaune Suna kallo kafin su koma dakinshi..


Daren ranar kasa bacci nijlah tayi Banda Kuka da juyi Babu abinda take Akan makeken dagon' dagadaya ta Rasa abinda ke damun zuciyarta' ji take kama tayi tsuntsuwa ta koma kauye gurin kaka' gashi Dai bacci take ji Amma data rufe idonta Sai ta riqa ganin photon Yasmeen tana sauke Mata lafiyayyan Maruka Akan fuskanta Kamar yanzu abin ya faru haka take gani.

Zaune ta tashi tana me tausayawa Kanta' na rashin Gata ga Kuma rashin soyayyar da mijinta be nunawa akanta' Kuka ta qara saki tana Jin Wani iri zafi a cikin idanunta girjinta Na bugawa.

A hankali ta sauko a gadon ta fada toilet' wanka tayi ta dauro alwala'tana fitowa ta Saka qaton hijab ta hau Kan sallaya.

Sallah ta riqa jerawa tana addu'a Akan lamarin ta kafin ta Tashi tana Jin dadin yadda zuciyanta tayi Mata sauqi ta koma Kan gadon ta kwanta nan da nan bacci yayi nasaran daukanta'.



Bangaren ango da amaryan kuwa Bayan sun sha soyayyansu Yasmeen ta Gama rigima bacci ya dauketa' Shima kasa bacci yayi haka ya raba dare a zaune Yana tunanin nijlah' be kwantaba Har saida Yasmeen ta farka tana masa shagwaba ya fara rarrashinta ahaka bacci barawo ya daukesu.


Yau Dadi Ko rashinsa ga yinwa dake yawan damun nijlah sedai ya siyo Mata bread da kayan ciye ciye taci ahaka Duk ta rame cikin 'yan kwanakin da sukayi a gidan' Dan Ko falo Bata iya fitowa sabida tsoran Yasmeen a cikin daki' take raguwanta sedai idan ya shigo su gaisa ya fita Dan Baya taba barin gidan ba tare daya Ganta ba' Yana yinta Na damunsa sedai bashi da cikakken lokacin daze tsaya yaji damuwarta acewar shi.


Yau kwananshi bakwai a dakin Yasmeen Dan haka yau yake Shirin komawa bangaren nijlah' Duk Da ba wani Shiri nijlah tayi masa ba Hakan be hanshi farin ciki da Jin dadi ba' yasan koba komai yau zeji damuwarta da abinda yasa take irin wannan rayuwar kama ba'a gidanta take ba.


Zaune take ya shigo Dakin Yana binta da kallo' sannu da zuwa tayi masa Kanta a qasa Dan ita bazata iya qirga kwanakinsu a cikin gidan ba' Dan haka batamasan yau ze dawo Dakin nata ba.






Nagaji haka mu Tara gobe idan Allah ya kaimu.*Wannan shafin na kudine'karki karanta idan baki siya ba' ga mai so zata Biya 200 naira kachal ta karanta' Zaki Tura katin MTN ta wannan number 09038049272,,Ko ta account number, 0089110527, suwaiba Hussaini zakirai, access bank.idan Baki siya ba karki karanta..*

*'yan Niger su tuntubi wannan number,, +22789520047.* P


Hannunsa ya rungume Yana cigaba da kallanta kafin a hankali ya gyara tsayuwarsa yaba tsareta da manya idanunsa.

Kallanshi takesanyi gabanta Na faduwa Taji Yana Magana da ita.

Kinmin sannu da zuwa Kuma kin dauke kanki'
Ko bakisan ganina ya fada Yana zuba Mata idanunshi.

Qirjinta na bugawa da qarfi ta fara girgiza masa kai' matsawa yayi jikinta yasa hannu ya dago fuskanta' a tare sukaja numfashi Mai sauti ya Dora hannunsa Akan boobs dinta tare da tsuramata rikitantun idanunshi yace.

Ba gaisuwa?

Bakinta na rawa tace' in ina kwana!

Qara hadata yayi da jikinsa yayi saurin hade bakinsu Yana tsotsar kowanne Sako da Lungu Na cikin bakin' Bata iya hanashi ba Dan a mugun tsorace take dashi.


Sai daya harya gaji kafin ya janye bakinshi a nata Yana sauke sansanyar ajiyar zuciya tare da zuba Mata idanunshi' hawaye ya gani kwance a fuskanta nan yasa hannu Yana goge Mata kafin ahankali yace.

Daga yau Daga ake gaida miji baki tsaya a tsaye kina turomin baki ina Kiran ina kwana'. Da ban kwana ba Zaki ganni???

Shiru tayi masa jikinta a sanyaye tana janyewa a jikinshi.

Matsawa ya qarayi da sauri ya taro ta ta qara dawowa qirjinshi' sunsunarta ya riqayi Yana shaqar kamshin dake Tashi a jikinta'' tana hawaye tace' Nika Bari banaso.

Beyi Magana ba yafara Daga qasan rigarta' tana turesa ahaka yayi sauri ya cafki nononta ya Kashi cikin bakinta Yana Wani tsotsa ta fashe da Kuka sabida zafin dataji a Kan nononta tana girgiza masa kai.

Ya cire nonon a bakinsa ya dago kansa ya sauke manyan idanunshi ya zubasu akanta yana binta da kallo.


Kukanta ta cigaba dayi ya Kira sunanta a hankali'

Nijlah!

Bata dago Kanta ba ya daka Mata tsawa.

Dallah hadiye kukanki kafin Na Bata Miki rai yanzu' yarinya Sai taurin Kan tsiya' ayi ayi dake ki saki jiki kiqi sakin jikinki' Sai Rama kike Kamar wacce muke yankan Naman jikinta muna chi.

Ko ni kikeso Na Shiga kitchen kullum ina dafa Miki abinda zakici'?

Dasauri ta girgiza masa kai tana qara qanqame jikinta.

Banasan wannan shirmen naki' nasan tinba yau ba kikasan waneni ni' bazan iya zuba Miki ido ba' Naga yanzu Dan wasan danakeyi dake nema kike ki hana' to wallahi kisani yanzu ba da bane nasan Ciwan kaina na Kuma gane cutar da nayiwa kaina idan Zaki shiryama amsar miji ki shirya.


Bakinta na rawa tace to.

Ko da Malam ya'u aka daura auren dake haka ze zubamiki ido kina abinda kikaga Dama?

Ah ah ta qara cewa idanunta cike da hawaye.


Saketa yayi ya tashi Yana cewa' nasan yauma bakici abinci ba' kinfiso kullum saina zo na hadamiki zakici' ya fada Yana aje wayarsa Kan kujera ya Shiga kitchen.

Mintuna kadan ya fito hannunsa riqe da cup da' ya dawo inda take zaune ta zuba tagumi qirjinta Na dokawa ya riqo hannunta da Dayan hannunsa kafin yace' ki bude baki yanzu ki shanye wannan shayin bansan musu ya miqa Mata cup din bakinta' budewa tayi tana sha a hankali sabida zafinsa' be kyaletaba sai da ta shanye ya rage saura cup a hannunsa.

Nan ya tsare ta da ido Yana Yana cewa' nijlah meyasa kike haka da wayanki Amma bakisan idan kinajin yinwa ki Shiga kitchen Ko tea ki Hada ba'
Allah ya sani idan aka zageni ke kika Jamin ya fada Yana Tashi tsaye.

Bata Kalli inda yake ba saijin maganarshi tayi Yana cewa'

Nina tafi office Kuma ki shirya yau a dakinki Zan kwana.

Gabantane Taji yayi Wani irin mugun bugawa Har saida tasa hannu ta dafe..

Wai bakiji abinda na gayamiki ba??

Qirjinta na bugawa da qarfi ta fara magana Kai tsaye'

Naji' Amma Nika zauna acan basai ka kwana anan ba ta fada qirjinta Na cigaba da dokawa.

Dasauri ya matso jikinta' jikinshi a sanyaye yasa hannu ya dago Kanta Yana kallan fuskanta' tayi saurin yin qasa idanunta shiko ya zubamata nashi Yana binta da Wani irin kallo daya fara saukar Mata da kasala a jikinta Duk da ba kallansa take ba.


Cikin nutsuwa yace' dago idonki ki maimaita abinda kika fada yanzu" Qin dagowa tayi yace' ki dago nace ki maimaitamin banji ba..


Turo masa baki tayi tace'


Nace kayi zamanka acan Ni Bana buqata.

Zaro ido yayi yace' Ni mashkur ne baki buqata kome?

Cike da qosawa da zancen tace eh...


Rasa amsar daze Bata yayi ga Wani irin bacin dayaji ya taso masa' Wai Ni mashkur ne ba'a buqatan gani Ko?

Acan wata Har Kuka take sabida bataso Na Barta Amma ke kina qoqarin nunamin iyakata.

Sai yanzu take ganin wautar ta data gayamasa haka ta bude baki zata bashi hakuri ya fice Daga dakin Yana banko Mata kofa tace gaaaaaraaa raammmm gammmmmm..


Sai da ta tsoshe kunnanta sabida qaran kofan tayi saurin Tashi tsaye ta biyo bayanshi' tana zuwa falo ta hangoshi rungume da Yasmeen tana zuba masa shagwaba' rintsu idanunta tayi ta dafe Bango tana yiwa zuciyanta fada Akan abinda ta aikata' tana nan tsaye Har Yasmeen ta rakashi cikin Mota tana Daga masa hannu ya tafi.


Daki da dawo jikinta ba kwari ta kwanta tare da dafe Kanta tana tunanin yadda itama zata dawo da hankalinshi Kanta.


Sallama ake Babu Wanda ya amsa' matar ta tsaya tana cewa' ina mutan gidan Ko sun fita?


Cike da gadara Yasmeen ta fito tana karairaya tana yatsina take kallan matar da shekarunta bazasu wuce 25 ba tace'

Baiwar Allah Daga ina Zaki shigowa mutane gida.


Murmushi matar tayi tace' sunana hidaya Ni makofciyarkice nace Bari Na shigo na muku Allah yasanya alkairi Daga Asan juna.


Kallan Sama da qasa Yasmeen tayi Mata kafin ta kyalkyale da wata irin mahaukaciyar dariya tace'

To angode iyayen shinshigi Zaki iya tafi' haka Kawai Dan kina makofciyar gidannan saiki shigowa mutane kanki tsaye' to wama ya baki Goran gayyata.


Riqe baki hidaya tayi ta kasa Magana tana cigaba da kallan yadda bakin Yasmeen ke motsawa Yana zazzaga Mata masifa.

Zaki iya fita idan kingama Naga kin tsareni da ihu saikace Zaki cinye.


Hayaniya nijlah Taji yaqi qarewa Dan haka ta aje tunanin da take ta fito falon' tsaye taga Mata Yasmeen Na cigaba da cewa.

Ki fita nace muba makofta muka zo nemana ba.

Juyawa hidaya tayi Ranta a bace sedai Bata abinda ta Isa tace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login