Showing 6001 words to 9000 words out of 20783 words

Chapter 3 - Baniba Auren Talaka Complete Hausa Novel

01 Feb 2025

171

danyan lace ne baki jikinshi sai flawars din jikin lace din green da stones ajikin lace din green dinkin yamatukar kamata tsamtsam haka rigarnan takamata tsam tarangada daurinta me hawa hawa yayi mugun Kyau tamkar takasa hula dan mitsitsin mayafinta tadauka taninkashi biyu saita ratayeshi a kafadunta tadauki bakin takalmi da jaka tasaka tsarki ya tabbata ga ubangijinda ya halicci tsaleliyar cikakkiyar budurwanan tayi mugun Kyau sosai agogon hannunta ta kalla takwas hartayi kamun tace wani Abu wayarta tasoma ruri number Jidda tagani,'. ___"hellow Kawata ganinan fitowa ina zanganku?,' Jidda tace,'. ___"ke dan allah kifito munadan bayan layinku acikin adaidaita sahu kifito,' tasake rage volume din muryarta tace,'. __"kuna wuta bebs ganinan minty uku yayi yawa,' kashe wayar tayi sannan tafito tasakama kofarta makulli sannan tadan fita kofar gida tadan lalleka sannan tadawo Gidan sukaci karoda Umma,'. __"ahh harkinshirya kenan Hafsat dawurine haka dama?,'. Tawani yi murmushi,'. __"nagama Umma harna gama fitarda kayan Ai nizan wuce,'. __"toh Hafsat Allah yataimaka insha allah innasamu kudin zakiji aike,' ___"saidatakai kofar gida tace.'. __"to Umma'. Tawuce tana daria kasa kasa zurawa tayi aguje zuwa bayan layinsu tafada kekennan suka kara gaba me adaidaita sahun yasakarmusu kida ihu sukasa yayinda suka fara marming din wayar,' I don't get alert god win onomo πŸ˜ƒπŸ˜ƒπŸ˜ƒ```

*love u oll*
[11/27, 1:16 PM] β€ͺ+234 814 518 6542‬: *BANI BA*
_________
*AUREN*
________
*TALAKAπŸ‘¨πŸ»πŸ‘ˆπŸ»*
________________


*_______BY_______*
*_Badiat Ibrahim_*

*(episode)*
*36to40✍🏻*



``` shuraim ne yafito falon cikin shirinshi nazuwa office tsab yana sanyene cikin kananan kaya wandone ajikinshi blue jins tareda wata farar Riga polo wacce tamatukar amsarshi yasanya blue takalmi sinicars yanata tashin kamshi sumarnan tashi akwance abun shaawa affan yarugo da gudu yataho wajan dadynshi ya rungumeshi yanadan shafa kanshi,'. ___"gud morning affan,'. Tasaka daria,'. __"gud morning my Dady,' Dady bangankaba saiyanzu inata tambayarka,'. Murmushi yayi yadubi Rukayya wacce take zaune a daining table tana breakfast wata harara tasakarmai yayi murmushi yace,'. __"affan muje kakarasa breakfast katafi school karka makara,' yadauki yaron suka karaso inda Rukayya take yace,'. ___"gud morning my beautiful wife kintashi lafiya?,' kallon fuskarshi tayi yana murmushi tasauke idanunta akan lips dinshi tahango indata cijeshi gawajan haryatashi kuma yasaka ink awajan takauda kanta batareda tacemai komaiba yakasayin breakfast din yadan dafe kanshi da hannunshi yazuba mata idanu,'. Sallama direba yayi akofar falon tareda gaishesu yace,'. ___"hajia in affan yagama yatawo mutafi,'. Affan yatashi yaje ya rungume dadynshi da momynshi yafita dagudu shuraim yadawoda kallonshi wajan Rukayya yakura mata idanu datagaji tamike da niyyar tashi yariko hannunta yace,'. __"haba matata meyasa baki yadda daniba wlh bazantabayin abunda zaicutar dakeba janbaki dakika gani arigata wlh watace zata fadi mukaci karo wlh batasanma tagogamunba nima wlh banko ganiba kiyi hakuri plz ina rokonki,' hawayene suka sulalo akumatunta tajuyo ta fuskanceshi tana kallonshi tace,'. ___"wannan kirkirarren labarine shuraim domun kasake wata shawarar wannan bata karbuba yaya kiri kiri kakeneman rainamun hankali haba shuraim why why meyasa zakamun haka kasan ina sanka over wlh dazanga wacce ta kissing dinka saina yanke mata dukkan lips dinta,' kankameta yayi ajikinshi yana shafar bayanta fisgewa tayi taruga aguje zuwa daki yadafe kanshi idanunshi sukayi ja shiyarasa irin wannan jaraba da kishi,' haka shuraim yafice agidan ko breakfast baiciba sai a office yayi```

```dukyabi yadamu da fishinda matarshi takeyi dashi wayarshice tayi ruri yana dubawa yaga abokinshine Ahmed yake kiranshi yadaga,'. __"hellow Ango ango kasha kamshi kana kirana office dina yakaure da kamshin angwanci,'. ___"hahaha shuraim bakada dama ganan yaro naturoshi zuwa office dinka zaikawoma dinkinku nawajan dinnie ankawosu yau shine nace ararraba kawai tunda gobene,' yace '. ___"okry bawani Abu saiyazo dan allah kagaidamun da amarya Amina fa kamun muhadu goben,'. __"to insha Allah zataji nagode saimun hadun,' sukayi sallama ya ajjiye wayarshi yasoma aiyukanshi yanata ciccike takaddu,```

```rukayya ce tafita zuwa Gidan kawarta basira suna zaune afalo,'. __"Ahab mena fada miki Ai maza sunzama abunda suka zama Neman matan banza acikinsu ba'a magana kema Kawata kinsaki jikinki har wata tana miki wasa da hankalin mijinki harda yimashi kiss ,'. Tace,'. __"wlh Kawata bazan yaddaba company'nsu yanzu zaki rakani intara ma'aikatan wajan tsab saisun fadamun kirakani yanzu domun inasan sanin wacce ta kissing mijina domun innuna mata wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa Ai kayan kanfani daban Dana shago,'. Basira tace.'. ___"yes haka nakeso Kawata aibasanya muje kawai,' mikewa sukayi suka fita suna Mota Rukayya tanata jijjiga harsuka karasa masana'antar watace tazo wucewa,'. __"ke zonan jimana,' karasowa tayi gaban motar Rukayya tazare bakin glass dinta tace,'. __"sunana Rukayya bamalli Matar oganku shuraim gidado kinganeni yanzu,'? Cikin girmamawa ta tsugunna ta gaida Rukayya basira tace,'. __"kihado mana gabaki daya masu aiki a company dinna yanzu batareda bata lokaciba,'. Dasauri kuwa cinyare tashiga hado Kansu suna gaban Rukayya cib kowanne kanshi akasa,' tashiga zagayesu tanacin cingam ,'. ___"acikinku wacece jiya tature mijina harta rikemai Riga?,' gaban rahma yafadi tadafe kirjinta cikin rawar murya tamatso tace,'. ___"kiyi hakuri ranki yadade ni............ Kamun takarasa Rukayya tahada mata wani mari tasss tasake hada mata mari sannan tashaketa,'. ___"wacece ke waye ubanki a ina kikayi suna wayanki a ina ake kiran sunanki?,' to bari kiji mijina yafi karfinki domun nikadaice matarshi har abada zannuna miki ninafiki iskanci wlh zankawo karshen karuwancinki awajannan,'. Reza taciro kamun rahma tace wani Abu kuwa Rukayya ta zabtare mata lebe tayagashi ihu tasaka yayinda tadafe bakinta dayake zubarda jini duk jama'ar wajan sunkasa magana sabida tsoro , __"wannan shine last worning dazanyi miki karki bari insake tako kafata inganki agurinan aikinnan Na sallameki kodame magana?,'. Duksukayi kasa dakansu tace,'. __"kufadamai nice nazo yamasan aikinane wannan suka shiga Mota fuuuu fuuuu suna daria suka fice,"```


```aguhe akaje akasanarda shuraim yafito yaga a irin halinda rahma take kaitsaye yakaita asibity bashiri tanata kuka bakinta yana fidda JINI da yawu tayanketa sosai,' suna zuwa noses's suka amsheta tareda dubata wanke mata wajan akayi sannan akaimata allurar tetenous ,'. Amma shuraim gidado yakamata akulada yanayin shan maganinta domun asamu wajan yaciko harya hade sannan zatazo nakwana bakwai adinga wankewa anasa magani wadannan magungunan inkun fita saika siya shizata dingasha sau uku arana allah yabada lafiya,'. Yasauke ajjiyar xuchiya yace,'. ___"to mungode insha allah zatayi kikari tadinga zuwa ana wanke mata insha Allah,' sukayi sallama suka fito sunshiga Mota rahma tanata kuka gabakinta ya suntuma yanata mata zugi '```

```tausayi takebashi yashiga bata hakuri harsukazo gida yaisallama da mahaifinta yaimasa bayanin komai yadinga bada hakuri sannan tabasu uban kudi yashiga motarshi yana kada kai yarasa mekeyi mashi Dadi besanyazaiyi da rukayyaba tadameahi da wannan haukar datakeyi wai kishi ranshi ya bala'in bace idanunshi sunkada sundawo jajir dasu,"```

*love u oll*
[11/27, 1:16 PM] β€ͺ+234 814 518 6542‬: *BANI BA*
________
*AURAN*
_________
*TALAKAπŸ‘¨πŸ»πŸ‘ˆπŸ»*
________________

*_______BY_______*
*_Badiat Ibrahim_*
*(episode)*
*41to45✍🏻*




```adaidaita sahunsu yatsaya adaidai bakin get din tashar suka fiffito sunawani jida Kansu Jidda tamikamai Dari da hamsin yace,'. ___"ahh Hajiya yaxaki bani darida hamsin drop nadaukokufa Dari biyune da hamsin,'. Tace ,'. ___"inji ubanwa drop kadaukomu ninacema haka wayema kake tunanin zaibaka Dari biyu da hamsin mu ukun dallah Malam wuce daganan wlh konasa acikin tasharnan aimaka danbanzan duka wlh munfika tashanci,' sum sum Me adaidaita sahu Yakama hanyarshi sukuma suka shiga cikin tasharnan aikuwa akayo Kansu,'. ___"Hajiya inane Katsina ko Kaduna ko Abuja?,'. Hafkhas tanawani yatsina tace __"ina motar yola take,'? Yanuna mata wata Mota Sharon , ___"amm nawane Malam?,'. ___"dubu biyune tundaku naga manyan yarane kubada dubu da Dari biyar,'. Suka kalli junansu hafkhas takashe musu idanu kudin suka kirga suka mikamai yace,'. ___"kushiga bayan dama mutum ukune Mota saura mutum daya tacika,' suntaho anata kallonsu Yan tashannan sukuma sunatawani yatsina sunashan kamshi hafkhas dakyar take tafiya kasancewar akwai irin yashinnan acikin tashar harsuka karaso suka shiga cikin motarnan Kubra tanata kiran wayar Musa sai cewa yakeyi gashinan zuwa,' hafkhas tace,'. ___"guys karfa Musa yabamu kunya inbaizoba yazamuyi da Kubra dan allah gashi harmun biya kudin Mota yakenan?,'. Jidda tace '. __"nima tuntuni tunaninda nakeyi kenan wlh yazamuyi da Kubra kuma aibabu mutunci zuwa makka da kare acewai batayi ankonnan bayan munriga munce a dinka mana to meye abunyi?,'. Hafkhas tace,'. __"ga wannan kaddararriyar kuduba takita cika rana sai dukanmu yakeyi harnafara zufa wlh ,'. Kubra wayarta tayi kuka Musa ne kekiranta,'. ___"hello kuntafne kikuna tashar hanyanzu?,'. ___"muna tasha kainaketa kira wlh,'. ___"to aigani akusa tashar fito bakin titi danni Sauri nakeyi wlh,'. Tace.'. ___"to ganinan fitowa takashe wayar,' tafawa sukayi tana daria tace,". ___"gashinan yazo ina zuwanku,' dasauri tatafi hafkhas taja tsaki,'. ___"mtwwwwws meza ayi da soyayya da talaka menakasa yaci balle yajefoma Na kasa wlh Jidda bazan taba auran talakaba kiduba kakanninmu talakawane iyayanmu ma talakawane muma atalauci aka haifemu mukayi wayo atalauci muka girma atalauce saikuma inzo in auri talaka sai talaka yazo ya haifi talaka never wlh bani ba auran talaka,'. Daria sukasa tareda tafawa,'. __"wlh Kawata ina bayanki wayaki Dadi babu dan haka bamu ba talaka,' sukaita hirarsu har Kubra tadawo anbata kudin hardana Mota sunadai tasha har karfe uku, ```
`
```wayar hafkhas ce tasoma ruri tana dubawa taga Amina nuhu ke kiranta dasauri tace,'. __"ganan amarya tana kirana tajimu shiru bari muji mezatace,'. ___"amarya bakya laifi yaya akayi?,'. ___"yanzu hafkhas abunda zakumun kenan saidana Riga nafadama frnds dina cewar kawayena zasuzo saimukaji shiru sunatamun daria kowa yanaso yaganku haba guys meyasa zakumun haka?,'. ____"relax relax my dear karki damu sudena miki daria yanzunnan muka kamo hanya insha allah nanda awa uku masu Kyau munkaraso karki damu,'. Murmushi tayi tace,'. ___"harkunsa naji Dadi to allah yakawoku lafiya saikunzo plz inkunkusa isowa saiku kirani ko,'? ___"to to badamuwa ba bye,'. Kit kit takashe wayar saizuwa lokacinne. Motar tacika sannanfa aka kama hanya sunata shatata gudu kasancewar motar lafiyayyace tazo kuma tahaduda shinfidadden titi sai gudu jikakeyi suuuuuu suuuuuu,"```


*love u oll*
[11/27, 1:16 PM] β€ͺ+234 814 518 6542‬: *BANI BA*
_________
*AURAN*
________
*TALAKAπŸ‘¨πŸ»πŸ‘ˆπŸ»*
________________

*_______BY_______*
*_Badiat Ibrahim_*

*(episode)*
*46to50✍🏻*



``` misalin karfe bakwai nadare motarsu hafkhas tasauka agarin yola dake jihar Adamawa sannu ahankali suka fito daga cikin motarnan izuwa bakin titin Mota wayar Amina nuhu Jidda take kira tadaga inbanda kida babu abunda ketashi acikin wayarnan Jidda takashe hafkhas tace,'. ___"yadai metace?,'. ___"banajinta domun kodana kira kida kawai nakeji yana tashi,'. Text message ne yashigo wayar Jidda kamar haka ```
_guys anfara kamu inawajan yanzuma haka ba asakani a lalleba nace adan dakata manyan kawayena suna hanya kutsaya daidai bakin get din tasha ganan direba zaizo yakaiku hotel dinda kawaye suka sauka kuhanzarta kushirya kuzo,"_

```hafkhas tace,'. ____"omo guys abunnan nayinefa kekiji watoma kawaye basu sauka agidaba a hotel akaimusu masauki wow inasan harkar arziki komai ayishi babu karanta wata zukekiyar motace tatsaya agabansu Me bakin glass mutuninda ke tuka motar yazuge glass din motar yace,'. ___"sannunku da isowa dama nine wanda akace inzo indaukeku zuwa hotel inji Amina,'. ___"okey to kafito kasamana kayan a both,' inji hafkhas kenan sakkowa yayi dasauri yasaka sannan yadebesu suka wuce motarnan tanawani kamshi gawani a c dake tashi acikin motar sai zare idanu sukeyi harsuka karasa kerarren hotel din kallo saiya koma sama hotel ne Na manyan mutane yana daya daga cikin hotels dinda Yan yole keji dashi suka sakko sunatawani yatsina har dakin yakaimusu kayansu sannan yace,'. ___"zanyi jiranku amota hajia,'. __"to yanzu zamu fito,'. Hafkhas tace,'. ___"ma'aikin allah Na madina ni Hafsat khamis kuduba waje wai yau mune zamu kwana a wannan kerarren hotel din dankari.' Jidda tace,'. __"a gaskia sunkashema aurannan kudi sosai saida suka shirya hafkhas tace,'. ___"kodaya bawani shiri Ai mahaifinta mashahurin me kudine nasani kunsani to bawani shiri dasukayi dama kudine komai kuma akwaisu,'. Kubra tace,'. ___"yakamata mufara wanka tukunna,' aikuwa sukashiga sukayo wanka kowacce tayi adanta nakece raini hafkhas tana sanye cikin wani lafaya green yayi matukar yimata Kyau tasanya takalmi da karamar jaka milk Kubra kuma ita lafayarta blue ce tasanya takalmi dajaka yellow Saikuma jidda tasaka nata pitch colour tareda takalmi da jaka brown sunyi mugun Kyau kasancewarsufarare sol Sol sunata tashin kamshi suka sakko direba yawuce dasu wajan kamu```


``` amarya tanadai zaune yayinda aketa gudanarda bidia daya daga cikin kawayanne tataso taketo jama'a hartasamu karasowa , ___"Amina yanzu sabida kawai muhimman kawayanki basu karasoba saikice dole sai anjirasu kiduba mutane kowa ananwajanfa suyake jira sai kace wasu shararru alhalin kab cikinmu iyayanmu sunkasance manyan attajirai haba Amina kamun Amina tabata amsa sukajiyo tafin mutane rabbbb rabbbb take mc yasoma magana,'. ___"ahhh jama'a masu waje sunzo dole masu tabarma sunade allahu Akbar manyan bakinmu alafiyadai hajia hafkhas Yar gayu banraina girmaba manya manya maganin kanana angaisheki hajia Jidda tareda hajia Kubra barkanku dazuwa ina Yan uwan ango bismillah saisu karaso domun muyi abunda yataramu ahhh wato kamu bismillah su hajia hafkhas kukaraso daga kan gadanda amarya take dan asaka mata lalli,```

``` ahankali suke takowa ajere sunawani kasaita tareda TAKUN GIRMA harsuka karasa inda amarya take,' gabaki daya jama'_at wajan hankalinsu ya raja'a awajansu hafkhas yayinda kawayan amarya suka soma kuskus,'. __"dama wadannan hadaddun kawayanne aketa jira gaskia sungadu musamman me green kayan,' wato hafkhas,' dayar tace,'. __"daganinsu kuwa jikakkun masu kudine domun fatarsuma kadai tatona asirin hutun jikunsu gaskia,'. Aisha tace,' ___"Yan makarantarsune fa kai sunhadu over,' suna karasawa Amina ta rungume hafkhas tana murmushi,'. ___"kunsa jama'a saijira sukeyi wlh harna cire raina da zuwanku,'. ___"ahhh haba my dear gamu Ai munzo ina sauran kawayan dakuma dangin mijinki?,' karasowa sukayi dangin mijin Amina tareda ragowar kawayan Amina ,'. ___"to Yan mata kamar yadda al'ada yatsara gamu munzo gareku domun kuma amarya kara kufada mana Nawa kukeda bukata nasaka lalli?,' kowacce tayi shiru kawayan Amina sunyi shiru suna jiran amsarda su hafkhas zasu bada cikin wata hadaddiyar murya hafkhas tace,'. ____"dukkanmu dai bayara bane damma abun yazama da al'ada to kubada konawane it's okey ko?,' tajuyo tana kallon sauran frnds din cewa sukayi,'. ___"gaskia ne kubiya kawai konawane,'```


```suka miko musu bandir din dubu Dari,'. __"gashi kuyi hakuri to,'. Hafkhas tacema kawayan su amsa amma sukaki amsa sai Jidda ta amsa nantake akadinga fesama amarya turare akasata a lalli sannan akaci gaba da bidia saiwajan goman dare akatashi kawayan amarya suka koma hotel yayindasu hafkhas sukashiga gari chilling abinsu amarya kuma tana gida hartayi bacci sabida gajiya,'```


*love u oll*
[11/27, 1:17 PM] β€ͺ+234 814 518 6542‬: *BANI BA*
__________
*AURAN*
_________
*TALAKAπŸ‘¨πŸ»πŸ‘ˆπŸ»*
_________________


*_______BY_______*
_*Badiat Ibrahim*_

*(episode)*
*51to55✍🏻*




```matar shuraim tashigo cikin gidannan ahankali yayinda Rukayya take falo tanata jijjiga tacika tabatse kiris take jira tafashe yasakko rannan nashi abace yashiga falon suka hada idanu tawani zubamai harara karasowa yayi gareta afusace,'. ___"uban waye yabaki damar fita agidannan wakika tambaya kikazo company kikaci mutuncin rahma kika lalata mata lips dinta meke damunki domun wannan haukace ba kishiba,'. _______"dakata shuraimβœ‹πŸ» domun kai baka Isa kabudemun idanu akan wata karuwaba Mara daraja saika fadamun daman inkaje office abunda kakeyi kenan damata wayasan iya adadin yaranda ka lalatama nayi danasanin yadda dakai amstsayin masoyi why shuraim why kafiso sanka yakasheni kenan kasan zan iya aikata komai akanka wlh zan iya kisa indai akankane ,'. Tasss tassss ya gaureta dawani mari saidatayi xaman Yan bori kikukeyi tibb tibb tadafe kuncinta tana kuka yace,'. __"why rukayya kekanki kinsan ina sanki banida burin auren mata biyu sannan Neman Mayan banza basa gabana bakya tunanin ni babban mutunne sananne taya zanso in aikata aikin ashsha hw? Tana kuka tamike tamatso gareshi,'. __"nayima kaina alkawarin nikadai zanzauna azuchiyarka tareda gidanka kamar yadda naxauna acikin mahaifiyata nikadai shuraim karka fasa bin karuwai nima bazan gazaba wajan binsuba domun indauki hukunci,' fuuuu fuuu tawuceshi tareda bankado kofa,'. Kanshi yadafe zuchiyarshi tana suya yarasa yazaiyi da kanshi idanunshi suka kada sukayi jajir yayinda kanshi yashiga mishi ciwo kamar yadda yake aka'ida indai yayi hayaniya kokuma yasaurari hayaniya saiyayi ciwon Kai dakinshi yawuce yafada toilet yayo wanka kana yafito yaxauna akan gadon yana nazarin kazamin kishi irinna Rukayya yakada kanshi ya kwanta,"```

```amma me baccine ya kauracema idanunshi yayinda maganganunda Rukayya taimasa yadinga dawomai,'. ___"wlh zan iya aikata komai akanka sannan inbaka FASA binsuba bazan gashida binsuba domun daukan mataki shuraim nika Mara akan wata karuwa?,'. Hannu yasaka tareda to she kofofin kunnen dukka biyu πŸ™‰πŸ™‰ yaruntse idanunshi dakyar dakyar bacci yadebeshi yayinda rukayyama tanacan tanata kukanta tana birgima sabida tsabar kishi itama haka garin allah yawaye da'ita,'```

```yana falo yana wayada abokinshi ,'. ___"ahh haba ango wlh kayan sunyi allah dai yanuna mana daran bawani Abu Ai uhm,' yace,'. __"hakane abokina kashirya dawuri saikazo kadan ragemun wasu kawayan amaryar,'. Daria shuraim yayi tareda cewa, __"aa waneni bazayi wannanba nadaisan zanzo bikin but bazan dauki kowaba kasanfa halin Me dakina sarai koya akace mata gani angannk da mata daru zatamun Rukayya tacika rigima,'. __"hakane shuraim Na mantane nayima uziri tunda matarka bataso arabeka okey saidai munhadu kawai,' sukayi sallama tareda ajjiye wayar,'. Rukayya tafito daga daki ranta abace idanunta sun kunbura sosai yakada kanshi kawai tana zuwa dab dashi zata wuce yajawota tafado cinyarshi cikin tsiwa zatayi magana yasaka bakinshi acikin nata yahau tsotsa tanata fisgs fisge

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login