Showing 27001 words to 30000 words out of 75868 words

Chapter 10 - Dubu Jikar Mai Carbi Book 1 Complete Hausa Novel

24 Sep 2025

953

titi yana share hawayen fargaba da tashin hankali.

Dubu sai da ta saita Ɗan'iya ya bi titi sannan ta bi wani layi bata tsaya ko'ina ba sai cikin wani sabon gini da ba a ƙarasa ba. Zama ta yi dirshan ta kwashi ragadada tana ci tana siɗar romo, kafin wani lokaci tuni ta cinye shi tas, saboda ba ƙaramin daɗi ya yi ba, ya ji farin magi zaƙwai ga ɗan yaji-yaji. Tana gama ci ta sa gefen hijabinta ta goge baki. Ta ɗauki bokitin ta cika shi da yaji ta ɓoye a cikin hijabi ta fice daga cikin kangon.

Dubu bata tsaya ko'ina ba sai ƙofar gidan Hansatu, Hansatu na tsaye a kan ƴarta Mairo da take ta zuba ragadada a ƙananan robobi, ta hango Dubu tsaye a ƙofar gida. Suna haɗa ido Dubu ta ƙarasa ciki kamar mutuniyar kirki ta ce, "A bani ragadada." Tana maganar tana sakin wani irin murmushi. Hansatu ta hangame baki tana yi wa Dubu kallon mamakin wato rashin kunyar Dubu ta bunƙasa haka. Balabare da ke bakin bishiya yana sharɓar ragadada ya yi zaraf ya ce, "Dubulliya ta nawa za a baki?" A fusace Hansatu ta ce, "Ta nawa za ki siya?" Ba musu Dubu ta miƙa naira ashirin nan fa Balarabe ya fara leƙenta yana kashe mata ido ɗaya. Dubu ta ɗauke kai kamar bata gan shi ba. A fakaice Dubu ta sunkuya tana gyara takalminta ta cikin hijabi ta dire mata bokitin ragadada, ta bayan ƙatuwar tukunyar ragadadar. Ta matsa can gefen bishiyar da Balarabe yake zaune. Hansatu mace ce mai matuƙar son kuɗi don duk abin da zai haɗa ku da ita muddin ka zo siyan abu wurinta bata zuciya. Tana da tsumulmula saboda ko ita bata iya zagewa ta ci ragadada idan ba mijinta Balabare da Allah ya jarrabeta da mutuwar sansa ba. Duk abin da Balarabe ya tambaya ba ta iya hana shi. Don haka a ƙa'ida kullin ta sauke tukunyar ragadada kwanonsa daban yake, kuma ko kara ya ajiye ba za ta iya tsallakawa ba.

Hansatu na ɗauko leda ta shiga wurgawa Dubu harara sanna ta fara zuba mata, za ta ƙulle ledar Balarabe ya ce, "Ke Hansatu ƙara mata ta hamsin." Ai kuwa kamar ya watsa mata ruwan zafi ta ɗago a zafafe ta ce, "A kan wane dalili za ka siya mata bayan ɗazun nan yarinyar nan ta gama ci mini mutumci..." Nan fa Hansatu ta zayyanewa Balarabe yanda suka yi, kamar ta rufe bakinsa shiru kake ji sai dai sam ba haka ya so ba, Dubu na karɓar ragadadarta ta nufi hanya za ta fita sai ga Ɗan'iya ya shiga gidan yana kwala ihu.

Da kallon mamaki ya bi Dubu har ta fice, Hansatu don sauri zaninta har faɗuwa yake. Ta fara jefo masa tambaya a hargitse, "Ɗan'iya ina bokitin ragadadar?" Tun bata rufe baki ba ya hau nuna ƙofa ya ce, "Dubu ce ta karɓe mini." Ai kuwa kamar wanda ya ɗanawa wuta haka Hansatu ta zabura tana cewa, "Buhun uban can, kai buɗe baki ka yi mini magana yanda zan fahimta." Dubu na jin haka ta fara zuba sauri bata tsaya ko'ina ba sai islamiyya.

Ɗan'iya ya zayyanewa Mahaifiyarsa abin da ya faru. Hansatu na jin ƙarashen labarin ta shuri takalma garin ɗaukan takalmi ƙafarta, ta shuri bokitin Ɗan'iya da ke cike da yashi. Hansatu ta nuna Bokitin tana faɗin, "Ɗan'iya ba wannan ba ne bakitin da ka fita da shi?" Nan take mamaki ya cika su. Hansatu ta suri bokitin ragadadar da ke cike da yashi, ko ta kan Balarabe bata bi ba ta wuce gidansu Dubu tana kumafar baki.

Lokacin da Yaya babba ta gama jin jawabinta, kallon sheƙeƙe ta yi wa Hansatu sannan ta ce, "Hansatu kura ko mayya kika mayar mini da Dubu da za ta iya cinye bokitin ragadada guda? Allah na tuba me ye ragadada abin da duk yaɗi da jijiya ne, me ye Dubu bata ci a gidan nan?" Takaici ya kama Hansatu ta yi ƙwafa sannan ta ce, "Dama ai sake ta samu shi ya sa take shuka tsiyar da take so, to wallahi daga kaina ba za ta sake yi wa wani haka ba." Tana gama masifar ta fice, Inna furai ta bita har soro tana mayar mata da martani.

"Aniyarki ta faɗa kanki, azzulama mai baƙin baki. Bayan zazzagar iya shegen da kika yi mata shi ne bai ishe ki ba za ki biyota har gida kenan." Sai da ta ga ficewar Hansatu ta juya ta samu Yaya tana faɗin, "Yaya an ya maganar yarinyar nan bata kan hanya, na san halin Dubu sarai za ta iya tare yaron nan ta karɓe bokitin ragadadar fa." Yaya babba ta yi ƙwafa cike da takaici ta ce, "Ai kuwa wallahi da na ɗebe mata falsafar albarka alƙur'an da babu ni babu ita."

Hansatu kai tsaye wurin mai unguwa ta wuce bayan ta kwashi gaisuwa ta zayyane masa abin da yake faruwa, ba shiri ya aika da kiran gaggawa gidan Marigayi mai carbi. Zuwan dogarawan ya yi daidai da zuwan Baba Abubakar shi da Aseem, wannan sammaci ba ƙaramin ɓata ran Baba Abubakar ya yi ba. Ya ci alwashin idan kuwa haka ta tabbata Dubu ce ta cinye ragadadar, tabbas ba ƙaramin hukunci zai ɗauka akanta ba don duk abin da Yaya babba za ta faɗa sai dai ya toshe kunnuwansa. Shi da Aseem suka wuce wurin mai unguwa ba tare da sun shiga cikin gidan ba. Suna zuwa aka aika kiran Dubu, tare da Dogarawan suka taho tana zuwa ta yi turus! Jiki a sanyaye ta zauna ta hangi Aseem na wurga mata harara sai Ɗan'iya da idanunsa suka yi wuri-wuri, saboda kukan da ya sha. Hansatu lokaci-lokaci take kallon Dubu tana ƙwafa cike da jin haushi.

Shiru wurin ya ɗauka Mai gari ya ƙurawa Dubu ido yana son gano gaskiyar lamari, don ya san sarai Dubu za ta yi abin da ya fi haka, bayan an gabatar da abin da ya tara su a wurin, Mai unguwa ya kalli Ɗan'iya ya ce, "Ɗan'iya ko za ka gaya mana yanda abin da ya kasance." Ɗan'iya ya fyace majina sannan ya zayyane duk abin da ya faru tsakaninsa da Dubu. Tun bai rufe baki ba Dubu ta yi caraf ta fara magana, "Alƙur'an ƙarya yake yi mini haka kawai zai yi mini sharri saboda ba ƙaunata ake..." Da sauri Baba Abubakar ya katse ta yana yi mata daƙuwa Hansatu ta tura ɗankwali gaba tana faɗin, "Allah ya taimakeka ka yi mini tsakani da Dubu wallahi muddin ta sake shiga gonata sai na yi ƙasa-ƙasa da ita. Ƙwaranƙwatsa kuma sai an biya ni kuɗin ragadadata." Mai unguwa zai yi magana Aseem ya zaro dubu biyar ya miƙawa Hansatu yana faɗin, "Shi kenan magana ta wuce." Dubu na gefe da ta ga maƙudan kuɗin da aka bawa Hansatu ta yi zaraf ta ce, "Wallahi ragadadarta bata kai da kuɗin nan bayan kafin na karɓi bokitin Ɗan'iya ya ce mini ta dubu ɗaya ce." Ta ƙarasa maganar za ta warci kuɗin da sauri Hansatu ta maƙe su tana cewa, "Ai irin wannan asara kullin ma Allah ya kawo ta." Baba Garba saboda ɓacin rai sallama ya yi wa Mai gari ya tafi ya tafi, shi kuwa Aseem hannun Dubu ya fisga suna tafe yana haɗa hannunsa da nashi yana murzawa. Ban da wash! Babu abin da take yi saboda yanda hannunta yake yi mata raɗaɗi.

Suna shiga cikin gidan suka wuce sashen su Yaya babba har lokacin hannun Aseem na riƙe da Dubu. Tun da Yaya babba ta hango su take sakin murmushi, don shi kansa Aseem har sai da ya saki murmushi saboda yanda ya ga kakar ta shi cikin farinciki. Tun kafin su zauna ta sake washe baki tana faɗin, "Allah ƙadiran alamanyasha'u. Ikon Allah! Allah mai sanin abin da yake cikin zuciya." Gabaɗaya ba su kawo komai a ransu ba sai ɗan murmushi da suka yi. Bayan sun gaisa cikin ɓacin rai Baba Abubakar ya fara yi wa Dubu faɗa, kasancewar mutum ne ba mai zafi ba ya sa bai cika faɗa ba, amma Dubu ba ƙaramin tsora ta yi ba. Saboda dama mai haƙuri bai iya faɗa ba. Yana gamawa Yaya babba ta dasa nata faɗan.

"Maganar gaskiya Dubu kin wulaƙanta ni ki rasa me za ki karɓarwa yaro sai ragadada?" Inna Furai ce ta shiga ɗakin tana girgiza kai ta ce, "Don Allah Garba ka ji wata muguwar ɗabi'a, ka gaya mana meye Dubu bata ci a gidan nan?" Yaya babba ta yi ƙwafa ta ce, "Gane mini hanya Furaira neman maganar fa. Garba ka rabani da Dubu tun takaicinta bai kashe ni ba, ba zan iya ba gaskiya ba za ta ƙara kwanar mini a ɗaki ba. Ina dalili ta kashe ni ta cuci iyalaina, ko da dai kun girama shi fa Maraici ba daɗi gare shi. Don Allah Garba idan babu ni ba kun zama marayu gaba da baya ba? Na gaji gaskiya, ka sa Dubu a gaba ka tafi da ita na bar maka ita halak malak."

Baba Abubakar ba ƙaramin daɗi ya ji ba, don dama ya jima yana san ɗaukan Dubu Yaya babba ce take hanawa. Ya gyara zama ya ce, "Dama Inno na daɗe ina yi miki maganar amma yanzu tun da kin amince zan tafi da ita." Madadin Yaya babba ta yi magana sai ta yi jim sannan ta ce, "Ni fa Garba ba raba ni da Dubu ne bana so ka yi ba, gaskiya a riƙa zalintar marainiyar Allah ne bana so. Wannan matar taka ba ƙaunar Dubu take ba, sai ta zo ta yi ta gallazawa marainiyar Allah, ina nan ban san halin da ake ciki ba. Kai kuma mutuwar sonta kake ballantana ka tsawatar mata. Gidan Ado kuma Fauziyya sai jaraba mace sai masifa ko ƴaƴan cikinta ba ƙaunarsu take ba bare kuma Dubu, raba ni da bawa Ado Dubu ana zaune ƙalau. Ita kuma waccan mai tausayin ƙasar komai nata ba kuzari ina dalili inkai Dubu ta riƙa barinta da yunwa? Ni inbawa Rahama Dubu ta kashe ta da yunwa Allah ya tsare ni. Don Allah Garba wacce riba suke ci wai Rahama basa karyawa sai goman safe, mu da anan ƙarfe goma an fara haramar na rana. A'a gara Dubu ta yi zamanta a nan ina ganinta ina jin daɗi." Baba Abubakar ya girgiza kai don dama sai da ya ayyana haka amma ya ci alwashin ko da dabara sai ya karɓi Dubu muddin ya dawo gidan da zama, don barinta a haka har girmanta akwai gagarumar matsala.

Yaya Babba ta kalli Inna Furai ta ce, "Furaira ki gaya masa mana ai kyayi mini kara dai ko?" Inna Furai ta washe baki ta ce, "Garba wani abin alkhairi muka hango kuma mun san da kai da kaya duk mallakar wuya ne. Mun yanke shawara ni da Yaya ya kamata a ci gaba da yaɗa zumunci." Gaban Baba Abubakar sai da ya faɗi don ya san wataƙila wani abin za su ɓallo masa.

Inna Furai ta karɓe zan cen da cewa, "Ka san dai bikin su Salisu da su Zulfa bayan babbar sallar nan ne kuma dududu bikin saura wata guda ina jin." Baba Abubakar ya gyaɗa kai ya ce, "Ai ina jin lokacinma mun dawo nan." Inna Furai ta yi dariya ta ce, "Ai za ku sha hidima tun da auren ƴaƴa shida ba wasa ba." Baba Abubakar ya yi murmushi don shi kansa idan ya tuna bikin har daɗi yake ji ace cikin gidansu za su aurar da ƴaƴa shida maza da mata kuma duk auren gida abin akwai farinciki.

Yaya babba ta katse masa tunani da cewar, "Ka ga da Zulfa da Bintu duka Dubu fa ta girme musu." Baba Abubakar ya gyaɗa kai ya ce, "Ai suma Yaya don kun matsa ne amma duka nawa yaran suke?"

Nan take Yaya babba ta ɓata fuska ta ce, "Yara dai Allah ya kawo musu mijin aure kar ka yi musu buƙulu, kai da ɗan'uwanka ba kun ɗorawa kanku bokon jaraba ba. To gaskiya bana son hassada Garba kuma na yanke shawarar haɗa Dubu da Soja don gaskiya ba za a zo ana yi mata gori ba tun da ƙawayenta kusan duka sun yi aure wasu ma sun haihu."
*DUBU JIKAR MAI CARBI*


©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*


FREE PAGE 10
https://youtube.com/c/DuniyarHausaNovels

Ku dannan👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼 subscribe tare da alamar kararrawa domin samun shirye-shirye da sauran littafai.


Baba Abubakar da Aseem lokaci guda suka ɗago suna kallon Yaya babba, da ta ci gaba da zayyano zance ko a jikinta. Dubu na maƙure a gefe sai raba idanu take don ita kanta ba ta san da wannan shawarar da Yaya babba ita da Inna Furai suka yanke ba. A madadin fushi sai ma wani murmushi da Aseem ya ke yi, wanda kana gani za ka tabbatar da murmushin mamaki ne da tsantsar baƙin ciki. Yaya babba da bata kawo komai a ranta ba ta ci gaba da cewa, "Allah ya sani dama wannan ne dalilin da ya sa na aika kiranka kai da Soja, don kune maganar ta shafa ba su Munkaila ba. Waye ya haifa maka Soja bayan kai da uwarsa Nafisa?" Yaya babba ta tambayi Baba Abubakar. Shiru ya yi yana murmushinsu na manya, sannan ya ɗago da kai ya ce,

"Inno na ji daɗin wannan maganar ta ki, kuma ni zan fi kowa farinciki da wannan haɗin domin abin da ya yi Dubu shi ya yi Aseem. Amma wani hanzari ba gudu ba..." Da sauri Yaya babba ta katse zancensa da cewar:

"Don Allah Garba ka faɗi alheri ko ka yi shiru. Wannan fa abin farinciki ne, kuma me ye aibun Dubu yarinya san kowa ƙin wanda ya rasa. Ƙwaranƙwatsa dubu babu abin da Soja zai nunawa Dubu, kyau ya fita ko tsafta? Yarinyar da sai ta yi wanka sau uku a rana ko ba haka ba Furaira?" Inna Furai ta taɓe baki ta ce, "Ina dalili tun ba a ji ta bakin yara ba Garba za ka kawo mana hanzari, wannan kamar zazzage albarkar da ke cikin auren za ka yi. Gaskiya karka ɓata auren yara tun ba a je ko'ina ba, yoo Allah na tuba wane hanzari gare ka da ya wuce ka sa albarka?"

Baba Abubakar ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin, "Inna ni fa baku fahimce ni ba. Ina nufin su yaran a fara ji ta bakinsu don kar ayi abu ba da son ransu ba. Amma idan kuna faɗin haka sai in ga kamar kuna nuna Dubu da Aseem ba ɗaya ba ne a wurina." Yaya babba ta washe baki ta ce, "Shi dai Soja na san ai ba zai ƙi ƴar uwarsa ba, ita kuwa Dubu kar ku ji ta, na san ta yanda zan shawo kanta." Aseem saboda takaici miƙewa ya yi ya fice daga ɗakin, Yaya babba na ganin haka ta saki dariyar farinciki tana faɗin,

"Ai na gaya muku wannan shiru-shirun da yake yi wallahi aure yake so, ja'iri ga shi nan kunya ta kama shi ya fita yana sunne kai, yoo waye zai samu Dubu bai yi farinciki na? Alƙur'an ana auren ku basu wata tara sai dai ku ji haihuwa, Soja wai mu zai yi wa hikima bai san na daɗe da gano lagwansa ba." Baba Abubakar ya yi shiru yana nazari domin ya san ba ƙaramin ruwa Yaya babba ta kunto masa ba, saboda ko makaho ya shafa fuskar Aseem ya san yana cikin yanayi marar daɗi. Saɓanin Dubu da ba za ka tantance ainihin halin da take ciki ba, na farinciki ne ko baƙinciki ba.

Yaya babba cikin murmushi ta kalli Baba Abubakar ta ce, "Yanzu dai Garba ka je ka shaidawa Nafisa halin da ake ciki don a fita haƙƙinta na mahaifiya, kar ta ji magana daga sama don ma bata da fushi ba kamar Fauziya Matar Ado ba, kai gaskiya Garba duk cikin ƴan uwanka akwai wanda ya yi dacen mace irinka kuwa? Allah ya sani Nafisa macen arziƙi ce idan na zageta sai dai na yi mata ƙazafi. Suma ƴan uwanka zan shaida musu abin da yake faruwa don kar su ji maganar aure bagatatan, na san Sule da baƙar zuciya sai ya ɗau fushi da ni ba gaira babu dalili. Yo ko auren na yi musu ban sanar musu ka ga laifina Garba? Kai ne dai uban soja halak malak, wani ne ya haifa mini kai? Ni ina na iya gaba halin ƴan wuta, ina masoyiyar Annabi (S.A.W) me zai haɗa ni da wuta ana zaune ƙalau? A'a rabani da wannan falsafar zan sanar da su da kaina, kar shaiɗan ya ɗebe ni idan suka ɗau gaba da ni na biye musu, ana zaune ƙalau na tsine musu su ɓalɓace." Baba Abubakar ya zaro kuɗi a aljihu ya dire musu a gabansu ya yunƙura jiki ba ƙwari ya ce, "To shi kenan Inno Ni bari na wuce." Cikin haɗin baki Yaya babba da Inna Furai suka fara faɗin, "Ka gaida gida Allah ya yi albarka."

Yana fita Dubu ta ɓata fuska ta ce, "Wai ke Inno ce miki na yi ina son shi bayan mugu ne, baki ga irin wuyar da ya bani ba rannan." Yaya Babba ta rungumo Dubu cikin lallashi ta ce, "Ke yi shirunki, kin san me ya sa na yi wannan haɗin?" Dubu zuciyarta ɗaya ta girgiza, Yaya babba ta ci gaba da cewa: "Allah ya sani Dubu idan ba mutuwa ba zan iya rabuwa da ke ba. Idan kika auri Soja a cikin gidan nan za ku zauna, ga wuri nan a gyara masa ku yi zamanku. Amma idan bare kika aura kin san dole ki fice daga gidan nan. Na san irin rayuwar da za ki yi a can gidan? Sam! Ba zan laminta ba a rabani da Marainiyar Allah ina ji ina gani." Daɗi ne ya kama Dubu lokaci ɗaya ta washe baki cikin farinciki. Lokaci ɗaya kuma sai ta ɓata fuska ta ce,

"Inno idan ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login