Showing 30001 words to 33000 words out of 34512 words

Chapter 11 - Rana Daya Book 2 Hausa Novel Complete

19 Nov 2024

211

Anty Aliya sallama.

" Ya ce

"Yi sauri min ti daya da rabi.

Dan gudu ta kwasa, tare da tsalle ya girgiza kai

*Yarinyar nan da shirme bare taji ta a cikin

uniform me saka dalibi Kiriniya.

Ta samu Aliya tsaye a kusa da window tana

leke. Salma ta rusna ta gaida Aliya, sannan ta ce

sai ta dawo. Bata jira amsawarta ba ta juya don kar

ta shiga lokacin da Shatima ya bata.

Da dan tsallanta ta koma gurinshi.

Ya tada mota zata hau baya, ya ce "Kina son ki nuna ma

"Yan Makarantarku ni Direbanki ne ko?"

Tayi dariya tare da komawa gaba. Da suka zo fita, ta mika ma Maigadi kudin nama. Ta ce, *Yau na dari biyar ni ke so

Ya ce

"To."

Shatima ya kalleta

"Za'a soma adana kudin ne?" Ta ce Ai na dari uku ni ke siya duk kwanakin nan, yau da kana dakina ne zan kara.

Ya cE

"Au! Yau ina dakin baby ne ko?"

Tayi dariya,

"Kullum kana dakina Yaya sai ka manta,

" Ya CE

"Lokaci zai zo da zan tuna.

" Ta ce,

"Allah ya kai mu."

Ofishin Shugaban Makarantar •suka je, daga

nan aka nuna ma Salma aji. Ta daga mishi hannu

tare da fadin Bye-bye Yaya.

" Cikin murmushi yace

"Bye baby.

A cikin ajin an nuna ta a matsayin sabuwar

daliba, aka nemi da ta fadì sunanta. Ta mike ta ce,

"Sunana Ummu Salma A. Bashir.

Suka yi mata

sannu da zuwa. Malamin ya nuna mata wata yarinya.

"Ga waccan itama sunanta Ummu Salma, kije

kusa da ita na hada ku kawance.Cikin sakin

fuska ta kalli Salma,

"Zo mu zauna." Cikin turanci

tayi mata maganar.

Salma ta kan ji amma bata iya maidawa ba.

Umma Salma Sadi Dankasa ita ce Kawar da aka

yi wa Salma, tana da kokari ga salo da iya yi,

rawar kai kuwa ba a magana.

Suna shiga falo Amna ta ce, "Ko'ina ya yi kura

me aikin ta soma aikin shara.

Ya ce mata "Bari ya

duba Nafisa itama cikin ne.

Amna ta tabe baki

bata ce komai ba.

Ya samu Nafisa kwance bata jima da dawowa

dega amai ba. ya ce,

"Aman nan yayi yawa, ko dai

asibiti zamu je?" Ta ce,

"Ba za ta iya tashi ba.

" Ya dauki wayarshi, ya kira layin Likita ya fada mishi

halin da Nafisa take ciki.

Ya ce,

"Ya zo asibitinshi da mota ya dauki

Nurse ta saka mata ruwa, shine kawai abin da za'a

iya yi mata.

Ya CE

"To."

Haka ya dauki mota

yaje ya kawo Nurse ta zo da komai ta hada ma Nafisa ruwa.

Aliya da ke leke ta window ta ji haushin hakan,

dama tana cike da takaicin yanda yake ririta

Nafisar, ga Amna ma ta dawo. Ta dauki wayarta ta
tura mishi sakon korafi.

'Haba my love, ban zaci za ka yi min haka ba,

gani a gida sai ka dauko Nurse daga waje?

Gaskiya ban ji dadin haka ba.

Sakon na shigowa ya duba, guntun murmushi

yayi bai damu ba yasan Aliya tana da fahimta, da

ya yi mata bayani zata, fahimce shi.

Sai da Nafisa ta samu bacci sannan ya kira

Mama a waya yace Don Allah Hamida ko Momi

wani ya zo saboda dare, yanzun haka ruwa ake yiwa Nafisa kari.
Mama tace

"Jikin ne har yanzun?" Ya ce,

"Ciki ne da ita, sai wuya take sha, amai yayi yawa.

Mama cikin murna ta ce,

"Allah Ya bata

lafiya. Hamida sai ta zo tunda itace ba ta zuwa

Makaranta sun gama jarabawar fita.Yayi godiya

suka yi sallama. Ya tafi dakin Aliya don fahimtar da ita.

Tam! Ya same tacikin fushi, ya ce

"Haba

Aliya, keda ni ke gain kin fi su hankali, kuma za

ki fisu bani hadin kai?"

Tace

"Ai ni gani nayi ilimina bai yi min

amfani ba, in ba zan taimaki mijina da kuma

abokan zamana ba.

Ya kama hannunta

"Na

fahimce ki my love, amma kin san halinku na

mata, nasan ba za ta yarda ki sa mata ba ne.

Aliya ta ce, "To yanzun haka zaka sa mana ido

muna matanka babu taimako a tsakaninmu, babu

jituwa, ba za mu iya cin abinci kwano daya ba,

gaisuwa ma ta gagara tsakaninmu, ko dan su suna

jin su 'ya' yan wasu ne? Amma ni da Salma ai muna gaisawa, duk da

sakarcin kuruciya irin na Salma ta fi min su tunda

za'a gaisa. Ka iya tunawa fa ko makocinka ne

Musulunci ya gindaya sharadin makotaka

tsakaninku, bare matanka.

Wannan fa aiki ne babba a kanka, domin

kiwonmu Allah Ya baka, gashi za'a soma haihuwa

a gidan tun yanzun gara kayi digin hada kan yaranka.

Ya janyo ta zuwa jikinshi,

"Ina sonki sosai

gurin sa ni a hanya, ki taimaka min gurin hadin kan iyalina, ke ce ki ka fahimce ni.

" Aliya ta dan ji dadi, yanda ya nuna mata.

Salma kam bata da wata matsala, babu kowa da komai a gabanta sai karatunta, matsalarta daya in
an bata assignment bata samun me taimaka mata
in ta z0 gida, sai in ta koma Makaranta Salma

Dakanta ta taimaka mata.

Wannan Juma'ar an basu me wuya, gashi in

sun je ranar Monday babu lokaci bare Salma ta

taimaka mata don sai da ta bata shawara kan cewa

Yayan da ke sauke ki ya dinga taimaka miki.

Tace

"Ba shi da lokaci ne amma zata mishì

magana.Salma ta ce,

"To ki fada a dinga biya miki lesson, ko a nemo miki Malamin lesson agida.

" Salma tace

"Bari zata yi masa magana.

Cikin Nafisa me laulayi ne sosai, da tsarabar zan ci kaza, ba zan ci kaza ba. Domin wani abin ma sai an siyo shi tacì sai kuma ta sheka amai. Duk ta rame, ta kode abin tausayi kullum cikin

Karin ruwa. Yanzun dole ta yarda Aliya tana saka mata ruwa, tun lokacin da Aliya ta dage a kan sai sun je ta duba Nafisar, shi kuma yana gudun kada
Nafisar ta mata wulakanci ta ce ita dai suje.

Da yake Nafisar ta kanta take yi sai bata yi wata masifa ba. Aliyar ta gyara mata ruwa ta ce, ta gode. Shatima ya ji dadì sosai.

Tun daga ranar kullum sai ta-je gaida Nafisa, bare in ta lura Shatima ya shiga dakin. Amna kuwa ko ta shiga ta kan samu tana bacci, to da yake ba don Allah take zuwa ba, bata komawa sai kuma gobe in yana gida.

Shatima zuwa yanzun ya dauki Aliya ya sata a wani matsayi mai girma. Har yana ganin ta kai yayi kowace shawara da ita, kuma yana ganin zata iya zama wakiliyarshi a wasu al'amura na gidanshi.

Don tana da tsoron Allah, ga tsayawa a kan gaskiya da rikon amana.
[8/19, 12:22] Ummi Tandama😇: ________
*🏚️RANA DAYA BOOK 2 🏚️*


CHAPTER 15



*BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*


*Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻*

```ACT<<0700549935
Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925```

*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama👆🏻👆🏻ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana*

*Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki*



Nafisa ta tashi zaune, ta ce Hamida ta saka mata pillow zata jingina. Ta ce "Hamida yanzun Karfe nawa?" Ta ce,

"Tara na dare.Nafisa ta CE "Tabdi! Kin san wai me nike son ci?"

Hamida ta yatsina baki ta ce, "A'a

Ta ce

"Zogala! Ji wata fitina, ni da bai dame ni ba

Hamida ta ce

"Ni yanzun ina za a samu wani zogala?" Nafisa ta ce,

"Kira min Ya Shatima."

Yana dakin Aliya daidai lokacin da wayar tayi ringing, ya zo daidai da lokacin da Salma tayi sallama a dakin na Aliya, hannunta dauke da littafin ta wanda za"a koya mata,

Aliya ta amsa, sannan Shatima ya kalleta bayan ya dauki wayar yana duba suman. Zumbur! Ya mike tare da daga wayar ya ce, "Nafisa!"

Hamida ta ce,"Ni ce, ta ce kazo* Ya ce,

"To gani nan zuwa.Ya kalli Salma

"Ya aka yi?"

Tace,

"Yaya dama assignment ne za a nuna mini."

Ya kalli Aliya,

"Duba mata don Allah, bari in je gurin Nafisa in ji

Aliya tayi'yar dariyar yake tace

"Sai ka dawo, don Allah ka ce ina yi mata sannu.

Yana fita Aliya ta kalli Salma kallon sama da kasa irin kallon wulakanci da raini, ta ce "Aka yi sati da Lahadi duk ba ki tuna da assignment ba sai yanzun da ki ka ganshi a nan dakin? To bari in ja miki kunne, duk ranar da yake dakina na haramta miki zuwa.

Salma ta ce, "Anty don Allah kiyi hakuri, ina ta tunanin yanda zan ma Yaya magana ne,

" Aliya ta fizgi takardar tana dubawa. Salma ta ce

" Anty bari ki ga yanda aka ce….

Aliya ta katseta da cewa,

"Da Allah ni yi min shiru, ke ce za ki nuna min, tun kafin a haifi uwar me alli Balbela take da farinta."

Salma ta ce,

"Me ki ka ce?" Aliya ta ce,

"Tun kina^yar mitsitsiyarki ni ke zuwa boko, kuma muke rubuta maths.
Salma ta ce, "Yi hakuri."

." Don ta lura Aliyar tayi maganar cikin fushi ne. bata koya mata ba, saidai ta rubuta ta bata tare da cewa gashi nan ni bani da lokacin yi miki wani nune-nune.

Salma taje daki tana dubawa cikin kokwanto,tana tunanin gaskiya da kyar in haka ne, amma zata je da shi Makaranta ta nuna ma Salma Dankasa

Shatima ya shigo,

"Ina Salman?" Ta ce,

"Nayi mata ta wuce, yarinyar nan Allah Yasa dai tayi karatu, naga dan abin da ta kasa ganewa,ga takardarta duk ziro

Ya ce,

"To don Allah ki ke taimaka mata, sai a
hankali.Aliya ta ce,

"Har Lesson na ce zan ke yi mata." Ya ce, "To ai ko na gode. Yanzu ina zan samu zogala?" Ta ce, "Wake so?" Yace"Nafisa.Ce.

Tace

"Gashi dare ya yi. Amma ka tambayi

Maigadi, in za'a samu danye sai a dafa mata yanzun ayi mata kwado.

Ya ce,

"Haka ne.

Maigadi ya ce, "Can makotan suna da shi

Sai gashi an samu, nan da nan Aliya ta zage ta dafa, ta cE

"Sai kuma in da za a samu kuli-kuli

Nan ma Maigadin aka sake tuntuba. Shi ya bazu cikin unguwa sai kusan sha daya saura ya dawo. Kura-Kura aka samo. Aliya dai aka zage aka daka, ta kwadanta mata. Nan ya dauka ya kai mata. Tasa a gaba kuwa tayi ta ci, cikin ikon Allah kuma sai gashi bata yi amai ba,

Salma tana zuwa Makaranta, ta nuna ma Salma Dankasa, Salma ta ce

"Wa ya yi miki?"

Tace *Matar Yayana

Salma ta ce,

"To ba daidai bane.

Ta dauko littafinta ta nuna mata.

*Kin ga nIfa.

* Salma mamaki ya cikata, amma ta share tace "Bari ta sake kwalewa sai tayi kafin Malaminsu ya iso."

Amna cikin bacci taji karar wayar Shatima. Ta kalle shi yana ta bacci, da alamu yau ya gaji sosai,don sun je Abuja ne sai ma goma ya shigo gidan.

Ta kai hannu ta shafa fuskarshi,

"Honey ana kiran wayarka tun dazu." Ya bude ido da kyar, taCe

"Ka gaji ko?" Ya ce,

"Na gaji sosai."

Yana daukar wayar daidai lokacin kiran ya tsinke.

Yana dubawa yaga sau tara ana kira. "Nafisa!"

ya furta da karfi tare da mikewa tamkar bai taba bacci ba. Amna ta dube shi, "Wai ina za ka?" Yace,

"Nafisa, ina zaton jikin ne."

Amna ta sakko itama bata yi mishi magana ba,illa dai taje ta murda makullin kofa ta cire key din
tare da fadin, "Ba za ka fita ba. Na gaji da irin wannan abun, don ciki bai fi ciki ba.

Saboda salo bata tashi kiranka sai ranar da ka ke dakina? Sau biyu tana yi min haka, ba zan bari tayi na uku ba, tunda naga abin nata yana neman ya zarme.

Shatima ya ce, "Haba Honey, kin san fa cikinta ba irin naki ba ne.

Ta ce, cikin mamaki,

"Au!

Dama akwai wani ciki na musamman ne wanda kayi mata shi ni baka yi min ba?" Ya ce "Ba haka nake nufi ba, nata cikin me yawan laulayi ne. Don Shatima ya kira. Hamida ta ce,

"Tun dazun yake kira." Aliya ta ce "Bar shi kar ki daga har sai ya fito, in yana dakin wannan 'yar gwal din ba ya iya fitowa, yanzu dubi jikin baiwar Allahn nan amma ya wofintar da ita.Hamida ta ce

"Allah nima abin ya bani haushi,

na kira shi ya fi sau ishirin amma bai ko daga ba

Da ya daga ya ce min yana zuwa shine fa shiru Aliya ta ce,

"Sai ga shi ya kira ni wai inzo

Hamida ta cE

"Ai mun gode, Allah ya saka dabalkairi. Ai har Mamanmu na fada mata irin taimakon da ki ke mana.Aliya ta ce,

"Ai yi wa kai ne.
" Sai da aka kira sallar Asubahi sannan ta koma dakinta.

Shi ko Shatima zama ya yi a kan durowar gefen gado, yana ta kiran layin Aliya, ita kuma ta baro ta can dakinta domin da ta Nafisa ya yi ta kira yana tambayar Hamida ko Aliya tazo? Tana fada masa cewa bata z0 ba.

Bayan yayì sallah ya ce "To yanzun sai ki bude ni in dubo ta ko?"

Ta Ce

'"Ai ba yanzun ka ke zuwa ba.

Ya cE

"To yanzun kuma zamu iya samun matsala tunda gari ya waye

Ta ce,

"Mu samu mana, dama nasan ba zaka kula dani ba kaje ka rabo ni da gidanmu ina can cikin tattali
kaje ka dauko ni."

Ya ce, "Kin raina kulawar da nake ba ki? To kifada min abin da ki ke son in ke miki don ki tabbatar da ina kula da ke

" Ya fada ranshi a bace.

Ta ce

"Ga shi ka kwana zaune kana dakina
zuciyarka na gurin wata."

Ta ce, "Yiwa kai ne dai,kuma bana fata kema wata rana in haka ta faru zaki ji dadì in ta hana ni fitowa in wofintar da ke?"

Ta ce"Ni dai ba zan bude ba, dama ka shiga wanka in ba haka ba zaka yi lattin zuwa office."

Ganin da gaske ba za ta bude ba, ya bi shawarar ta ya shiga wanka. Kan ya fito ta bude sai ya fita zuwa dakinsa ya hau shiri.

Bai ko kalli karin da Ladi Mai aiki ta hada mishi ba, ya nufi fita. Kofar a damke take, ya waigo ta fito tana tsaye a falon. Ta ce,

"Ga abin karinka.

" Ya girgiza kai, "Bana jin yunwa.

Ta ce,

'"Ai ko ba za ka dakin wata ka karya ba.

Ta soma hada mishi shayi, Har gurin Kofar ta

Zota bashi. Ya amsa tare da fadin "In da ace za ki ke hada min ko shayin ne a duk ranar da nike dakin ki da na yi tasa miki albarka Ya kai

Karshen maganar tare da kurbar shayin

Da sauri ya watso shi domin suga ya ji har

cikin kwakwalwar kanshi. Ya mika mata shayin

"Ga abin ki, bude ni." Ta kalli agogo, duk abinka sai shida ta cika,

Ya ce,

"Amna har yanzun ina mamakin ki sosai, ashe kin iya mugunta har haka?"

' Ta ce,

Na daina bari ana raina min wayo."

Ya jingina da bango,

"Shidar dai saura minti hudu.

Ta ce,Inma minti daya ne sai ya cika."

Ya samu Nafisa a yan da take, ya kira Likita ya ce zai kawo ta asibiti don fa jikinta ya yi laushi Likitan yace

"Ko ka kawo ta babu abin da zamu ¡ya mata da ya wuce wannan ruwan. Amma zan

fita zuwa asibiti, ka fito bakin titi in same ka sai
muje in ga.jikin.Haka kuwa Shatima ya fita ya yi jiran kusan

minti biyar kafin Likitan ya iso. Shi kanshi Likitan

ya tausaya ma Nafisa, ya ba da wata allura ta

tsaida amai, ya ce ayi mata a gani. Amma ciki irin

wannan Kila sai ta kai wata biyar zata samu dan Salma tana ta jiran Shatima har takwas ta gota

Ta fito taje dakin Aliya nemanshi. Aliya ta ce an fada miki nan yake?"Salma ta ce,

"Ni wallahi yanzun bana tuna in da yake."

Ta ce,

"Yana dakin Amna.

" Har zata wuce sai

taga sun fito da Likita. Ta rusuna ta gaida su,sannan ta ce.

"Yaya mun yi latti.Ya kalli agogon

hannunsa. "Haka ne, ya ba ki tafi ba? Nafisa ce ba lafiya ban san lokaci ya tafi haka ba.

Ta ce,

"Anty ba lafiya, bari in dubata.

Sun gaisa da Hamida, sannan tayi wa Nafisar sannu.

Ranar latti taje Makaranta, sai da ya roka aka bude
mata don har sun ce ta koma.

**

Wata ranar Litinin misalin Rarfe biyu da minti bakwai. Salma ta sauka daga kan Mashin a bakin

Gate din gidansu. Ta ba mai mashin kudin sai taga bakuwar mota zata shiga gidan.

Maigadi yazo yana tambayar Direban gurin wa suka z0? Salma ta kalli Direban, kamar ta taba ganinshi a wani guri. Sun yi kama da Shatima kadan.

Taji lokacin daga bayan motar an ce,

"Uwar Maigidan ce

Gaban Salma ya fadi, domin ko a

ina taji muryar Hajiyar Shatima ba za ta manta ba.
[8/19, 18:44] Ummi Tandama😇: _________
*🏚️RANA DAYA BOOK 2🏚️*


CHAPTER 16 Karshen book 2


*BY HALIMA ABDALLAHI K/ MASHI*


Ta nufi cikin gidan gaba daya jiki a sanyaye,ta kasa bude kofarta,tabi motar da kallo har lokacin da taga motar ta tsaya daga cikin jerin motocin Amna da Shatima.

Ta bude kofarta ta shige,kasa cire kayan jikin ta tayi na makarantar haka kuma ta kasa dora girki,sai da tayi ta maza ta kunna risho ta dora tafasasshen nama.

Lokacin da su Hajiya suka shiga gurin Nafisa tana wanka,Hameeda tayiwa Mama da Hajiya oyoyo Aliya ta leko taga bakin Nafisa ne Dan haka sai ta yafa mayafi taje ta nufi wajen Nafisa da sigar duba jiki,tana shiga taga su Hajiya gabanta saida ya fadi tasan Hajiya ba kalar wasa bace, amma duk da haka saita cije ta zube ta kwashi gaisuwa a gabansu tana gaishe su yanda kasan zatayi masu sujada saboda girmamawa,Hameeda ne ta ajiye masu ruwa da lemu Aliya tace" Ya jikin Nafisa yau dai jiki da sauki? Hameeda tace "to gata nan ciki tana wanka".

Cikin kissa tace "Masha Allah naji dadi sosai,tasha magungunan ta kuwa?".

"Kinsan kuwa sai kinzo take sha,domin nidai nayi nayi da ita takisha"

Aliya tace "to bari ta fito inna lallasheta nasan zatasha haka za'ayi tayi hakuri da ita bansan inda zan samu tsakin nan bane bare ayimata abinda takeso amma ga rama can maigadi ya siyo mana".

Duk zubar da takeyi su Hajiya suna jin ta kuma sun yaba da maganganun ta musamman ma mahaifiyar Nafisa dan ance me da Wawa,Mama tace "Allah sarki kina dawainiya da Yarinyar nan Kullum Hameeda tana fadaman duk abinda ke faruwa har dare kina zuwa ki dubata."

Hajiya tace "haka akeso aishi zaman aure dama zaman tare haka akeson babba ya kasance,ita Yar'uwar takufa?

Aliya tace"Amna tana gurinta itama da sauki domin bacci takeyi,bari dai induba ta inaga yanzu ta tashi,Mama tace"Allah sarki kina dawainiya da wannan kiyi dawainiya da wancan kiyi da wannan Allah ya yi maki albarka.

Aliya ta amsa da"ameen" ta fita cikin jin dadi ta nufi shashin Amna domin dai burin ta kawai ta shiga ne gurin kowa taga yadda yake,hakan ne zai bata damar kunna wutar da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login