Showing 3001 words to 6000 words out of 17701 words
Chapter 2 - Gangar Jikinsa Na Aura Book 2 Hausa Novel Complete
Unknown
25 Dec 2024
94
ga jakunkunanta nan awatse a waje dakin da
zata zauna ma yanzu yazama garari. Ahmad ya
matse hawaye yace'' hakikatuntuni munji irin
halin da mahaifiyarki ta shiga harta rasu mun san
kuma halin da yarta Hanne zata shiga amma da
yake ni ina yaro bani da ikon inzoin dauketa shi
yasa na hakura akwanakin nankuma na dinga
mafarki iri iri na 'yar uwatamarigayiya uwar
Hanne. Kullum na kwanta baccisai inga yayata
Habi tazo tana cewa Ahmad danuwana yanzu
baza kaje ka nemo 'yata ba Hanne kaga halin da
take ciki ba a duniya ba, ko darenjiya ma nayi
mafarkinta abu daya kuma takemaimaitawa don
haka yanzu daman nazo da niyyarmu tafi da ita
ko da mahaifinta yana nan zanrokeshi ya bani ita
idan batayi aure ba in tafi da ita.Balle kuma
yanzu da ya rasu dole in tafi da ita. Iya abu ta
tabe baki tace malam tunda ransa ya hanaakai
hanna wannan garin'' maigari da jama'arsa suka
yiwa abu caa suka rufetadafada suna cewa'' ba
yanzu kika gama mata watsida kaya ba? Bayan
bakar wahala da take sha tuntana karama ta
zamo tamkar baiwa a gidannan.Ahmad ya ce'' ba
saikun bata bakinku bama wajenbata amsa mu
dai zamu tafi da ita . Sai yanzu daya mutumin
yayi magana wato Bello Madu yace'' aianan kusa
muke a garin dashi muke. Dashi dababban
mutum ai border ce ta raba. Ni costom neina aiki
a border lokaci lokaci zan dinga kawomuku Hanne
kuna gaisawa. Ahmed ya katse shiyace ''duk
zancen ka lallashi matan nan bai taso ba kaga
kankat din gari wato maigari da jama'arsasun
bamu izinin mu tafi da ita to wacece kuma zatace
sai hanne ta zauna yunwa ta kashe ta. Iya
Abutaji wani dacin bakin ciki ya rufeta ganin
Hanna tasami wajen da zata je ta huta. Taso ace
da ta yiwaHanna watsi da kaya duk garin ta rasa
inda zata zauna. A haka dai aka rabu Ahmad da
abokinsaBello Madu suka yiwa mai gari da
jama'arsa sallamasuka daukarwa Hanna
jakunkunanta, Hanna tayafa gyalenta tarungume
iya salmai suna kukanrabuwa Hanna da kawunta
suka tafi.sun isa garin Dashi da daddare gidan
Ahmadsuka sauka. Ahmad yana da mata daya da
'ya'yabiyu , sunan matarsa Hajir itama irinsu ce
buzuwa.Hajir ta tari hanna cikin fara'a da murna
ta kaitadaki ta kawo mata ruwa ta sha sannan ta
zaunasuka gaggaisa sannan taje ta shirgowa
hanna tuwo. Hanna taci tuwo nan tamkar tunda
allah yahalicceta bata taba cin tuwo mai dadin
haka basaboda tsabar yunwa da take ji, taci tayi
nat sannantace a nuna mata bandaki zata yi
alwala Hajir tanuna mata. Hanna ta shiga ta
dauro alwala tazo tayisalloli tana idarwa taje ta
watsa ruwa tayi wanka ta kwanta. Hajir taji tana
son Hanna, tana sonta dakawa daga gani ma
sa'an nune, hajir ta zauna agefen shinfidar
Hanna na kwance suna ta hira kalakala,Hajir bata
bar dakin ba sai da taga Hanna tafara bacci
sannan ta hure mata fitila ta rufo kofa tafita ta
nufi dakin kwanciyarsu. Da asuba Hanna ta farka
taji ana kiran assalatu ta mike ta nufi ban
dakitayi alwalla tazo tayi salla ta zauna tana
Lazumi.Gyangyadi ne ya dinga daukar hanna ta
mike takoma kan katifa ta koma bacci tayi ta
barci har shadayan rana babu wanda ya tashi
Hanna sai da tayibarcinta ta gaji ta farka dan
kanta. Tana tashi tayi ido hudu da soye soyen
abinci kala kala Hajir tazota jera mata. Ba Hajir
kawai ba 'yar uwan uwarHanna fa yawa labari
yakai musu cewar hanna tazodon haka suka aiko
mata da abincin karin kumalloiri iri sunka ce
kafin suzo su ganta. Hanna ta fadawanka tayi
brush sannan ta saka kayanta tazo ta zauna a
gaban abincin burjik a jere a tsakar dakintaduk
nata ne sai taji wani farin ciki ya lullubeta
ba'asabanba, yau hanna ce da barcin safe ta
farka tagaabinci burjik an jere mata haka Allah
yake, duniyajuyi juyi. Tun kafin hanna ta gama
karin kumallo tajitsofaffi da mata suna sallama a
tsakar gida, yan uwan mahaifiyarta hanna ne
suka fara cinci rindonzuwa ganin hanna, sai koke
koke daga su harHanna taga dangin uwarta
cunkus amma suka cemata wadannan ma kadan
ta gani don tushenzuri'arsu Azbinawa ne [buzaye]
suna Agadas state .Sai dai wani abu guda da
hanna ta lura duk danginta talakawane sosai
suna cikin rashi wasuNono suke sayarwa rugage
suke wasu kumamanoma ne. kawu Ahmad ne
kawai dan Bokowayayye mai dan hali akan
sauran koyarwa yake amakarantar firamaren
garin har ya sami matsayinmataimakin
headmaster. Shima dai rufin asiri ne kawai ba
wani arziki gare shiba. Gidansa ginin kasane
dakuna uku ne, bandaki da zana aka zagayekicin
kuwa a tsakar gida aka dasa murhuna. Hakadai
Hanna taji ta shiga wata sabuwar rayuwa maidadi
fiye da rayuwarta da agidansu. A koda
yausheyana godewa Allah da yayi mata canji
daga ukuba da bakin ciki hantara ya kawo ta inda
aketarairayarta. Hanna da Hajir sun shaku sosai a
kodayaushe suna tare suna hira wasa da dariya.
Tunhanna na boyewa hajir wasu abubuwa
nadangane da rayuwarta har ta yaba da
hankalinta tafara gaya mata wasu abubuwa da
suka faru da ita ada na dangane da tsananin son
Haisam ranarrabuwarsu. Tace har yau kullum da
daddare sai tayikuka idan taje kwanciya barci
saboda tunaninsa.Hajir ta tausayawa hanna sosai
har hawaye tayimata ,daga karshe tayiwa hanna
nasihoho akantayi hakuri kaddara ce daga Allah
haka Allah ya rubuto musu.BAYAN zuwan hanna
da kamar wata guda kawuAhmad da sauran
manyan danginsu suka kiraHanna babban zauren
dake gidan. Bayan ta gaisheda kowannensu ta
koma gefe ta takure. BabaSha'aibu yace'' Hanna
kinsan dalilin da yasa mukakira ki nan? Hanna
cikin ladabi ta amsa musu a'a yace to a
matsayinmu na iyayenki da kakanninkimunyi
nazari mun kuma tsayar da shawara abindanake
nufi da munyi nazari shine bai kamata ba
muzuba miki idanu haka nan ba babu aure don
hakaya kamata kiyi aure a watannan kuma.
Gabanta yayanke ya fadi ras dajin kalmar aure
cikin rudani tace''....... Wazan aura ai ni bani da
kowa a garinmuanan garin ma babu wanda yace
yana sona.'' suduka suka kyalkyale da dariya.
Ahmad yace''hanna kwantar da hankalinki dole
mu aurar dakega mai sonki kece dai baki sani ba
amma zuwankigarinnan maza sun doshi goma
suka sameni suka ce suna sonki shawarar da
muka yanke ita cemuduba a cikin waye yafi
hankali. Addini. Sana'aasali wanda zai rikeki
tsakani da Allah mu aura mikishi tunda ke
bakuwa ce ba sanin halayensu kika yiba babu
kuma isasshen lokaci da za'a barki kinasoyayya
dasu har ki zabi miji mu baza mu zaba miki
wanda zai cucekiba . Hanna babu wanda ya
fadomata a rai sai Haisam, soyayyar da take yiwa
Haisamsai kara yabanya take a cikin ranta, Hanna
ta ciresha'awar auren wani a rayuwarta tunda ta
rasaHaisam shine ma hawaye yake zuba
dagaidanuwanta don tasan ta rasa wanda take so
duk duniyar nan ta rasa farin cikin kuma.
Wannanhawaye na hanna da yake zubowa
dagaidanuwanta yasa jikinsu ahmed yayi sani
kumamamaki ya rufe su yaya za'ayi hanna ta
fara kukatun kafin taji waye aka zabar mata ta
aura. Koakwai wanda ta kudira zata aura ne basu
sani ba ? Inna rabi tace'' Hanna kukan me kike
bafa cewamuka yi dole sai kin auri wannan da
muka zabarmiki ba idan kina da wanda kike so
fadi mu auramiki,daman ganin babu kowa ne shi
yasa muketunanin hadaki da wani. Hanna ta
share hawaye tagirgiza kai tace'' babu wanda
nake so zan aura dukwanda kuka zabar min zanyi
biyayya in aure shi kowaye kuma. Nasan baza ku
zabar min wanda zaicutar dani ba'' gaba daya
suka fara shiwa hanna albarka suna jinjina mata
bisa tsananin biyayya datake yi musu allah yayi
mata albarka. Kawu ahmadyayi gyaran murya ya
gyara zama yace'' hanna tunfarkon zuwanki
abokinna koma ince ya zama danuwana saboda
tun muna yara muke tare nasanhalinsa ciki da
bai fiye da uwar data haifeshi bata sanshi ba fiye
da yadda nasan yadda yake yana damutunci da
sanin ya kamata yace yana sonkitsakani da allah
zai aureki wannan aboki nawashine bello madu
abokina din nan da mukajenigeria garinku dashi
muka daukoki . Yana dasana'arsa kuma yana da
ilmi gaba daya boko da arabiya yanzu ma babba
ne ba laifi a aikinsa aikincostom yake sune suke
tsaye a bordar nigeriazuwa niger. Ni dai a ganina
bello masu ne kawai yacancanci ya aure ki ko ya
kika gani? Iya ma'idatace'' wanne irin yaya ta
gani bayan ta gamamagana tace ko waye muka
zabar mata tana so. Cancanta ma ai ba sai an
fada ba sun dace ai''hanna ta sukuyar dakai kasa
sai hawaye shar yasake keto mata. Bello madu
kam ya cancanci asoshi bashi da makusa kyau
kuwa kamar shi yayikansa dan buzaye asali
kamar balarabe, hankali datausayi kuwa ba'a
magana don da yaji labarin hanna hawaye ya
dinga yi don tausayinta bashi damakusa ko kadan
amma ita abun da ya kara satakuka shine tana
matukar ganin mutuncinsa donhaka bata so aka
ce shine zai aure taba don dukwanda ya aureta
sai yayi hakuri sabod bazai samisoyayyar taba
GANGAR HIKINTA zai aura zuciyarta na wajen
haisam har abada, hankalin hanna yasake tashi
sosao da taji sunan wanda zata aurakawu ahmad
yace'' ni wannan kukan naki ne yaketsoratani
hanna kiyi magana idan akwai wani abunda yake
damunki. Hanna tayi dan murmushi tagirgiza kai
ta ce'' babu kimai zabin da kuka yi min yayi. Inna
goshi ta dau buda kiwa ya hau cewa''allah ya
sanya alheri ya baku zaman lafiya. Hanna tamike
ta shiga cikin gida bata tsaya a ko!ina ba sai
adakinta ta rufe kofa ta fada kan katifa sai ta
budesabon shafin kuka mai tsanani taji a ranta
kamarwata sabuwar soyayyar haisam aka kara
zuba mata taji sonsa ya sake sartseta kamar zata
yihauka. Bayan anyi haka da kwana uku hanna
nazaune a tsakar gida tana tankaden gari da
yammatana taya hajir aiki, hajir kuma na wajen
murhutana kada miyar kuka, suna taba yar hira
hajir tace''hanna ina ganin kinfi sauran mata
sa'ar samun kintsatstsan miji a duk yan matan
garin nan sabodaduk yawanci yan matan garin
babu wacce batakaiwa bello madu hari ba farin
jini gareshi sosai.Kyawunsa ne ko kuwa illminsa ,
ko kuma jan ajinsane yake rudarsu oho? Amma
ke gashi kwatsam yadamu da sanki kinsan tun ba
yauba kawunki ahmad ya fadamin cewar bello
madu yana sonkiamma ya gargadeni da nayi
shiru kar in sanar mikihar sai ya sanarwa da
magabatansa shima. Hannata cije tayi dan
murmushi tace'' hajir kenan watonayi sa'a sosai
ashe dana sami bello madu ta sama.Ba tare dana
wahala ba? Amma ni a wajena sai dai ma ince
shine yayi sa'a sosai ma kuwa.Alhamdulillah
amma akwai matsala tabbas. Hajir tajuyo gaba
dayanta tana kallon hanna can tace'' bangane
akwai matsala ba. Wacce irin matsala
kumahanna ? Ko bakya sonsa ne? Hanna ta
girgiza kaitace ta ce a'a ni naki shi bayan shine
zabin iyayena ina sonsa mana. Muryar bello
madu ce tace.''assalamu alaikum''.Kai tsaye ya
shigo cikin gidan kamar yadda yasaba shigowa
daman. Kai tsaye wajen hanna yadosa. Hajir ta
amsa masa sallaman gami da yi masatsiya ta ce''
oh dan halak kaki ambato yanzuzancenka fa
muke yi ango kasha kamshi dagazuwanka ka
doshi wajen hanna da idan kazo wajen wa kake
dosa? Bello madu ya kyalkyale dadariya yace'' kai
hajir kin fiye tsokana kinsan da saiinyi sati biyu a
boda ban damu da zuwa garin nanba amma
yanzu kusan kullum sai nazo garin nanko banzo
gidan nan ba ina jin dadin garin sabodamatar da
nake so tana cikin garin. To yanzu an banu izini
inzo wajenta kina nufin sai in doshiwajenki duhu
bayan shigowata hasken fuskarhanna ne ya bugi
idanuwana. Kinsan ko a kabarihaske ake nema
ana neman tsari da duhu. Hajir tarike baki tace''
ah bello madu daina hadani daduhun kabari
allah ya baka hakuri'' wannan hira tasu ta bawa
hanna dariya bata san sanda tatuntsire da dariya
ba duk da wani kululun bakinciki daya dira a
ranta yanzun nan da bello madu yashigo haisam
kawai zuciyarta take haska matainama inama
aceda haisam za'ayi musu auren nanwata guda
ya rage ayi bikinta. Bello madu yace'' hajir yi
hakuri bada duhun kabari nake hada kibani na
isa? Ai nasan kokarin da kike min wajenturani
fadar zuciyar hanna tun dazu ina zaune atsaye
ina jin hirar da kuke yi. Kuyi hakuri ba labe
namuku ba ina doso kaina bello madu naji
anaambato shiya sa na dakata sai dana gama jin
komai'' hajir tayi dariya tace a'a baba bello ka
faralabe a gidan mutane dai kawai zaka ce min''
yakarasa wajen hanna ya jawo wata kujera a
gefentaya zauna a hankali yayin daya kafawa
hanna idoyana kallonta. Ji yake tamkar ya
hadiyeta sabodason da yake yi mata. Fargabarsa
daya yana tsoro kada hanna taki amincewa da
soyayyar da yake yimata haka nan bayan
abokinsa ahmad ya shaidamasa an bashi hanna
yayi farin ciki amma farincikin ragagge ne yana
gudun kada a takurawahanna ta aureshi yazo ya
rasa soyayyarta ammayau sai gashi da kunnensa
yaji hanna tace''ni na kishi bayan zabin iyayena
ina sonsa'' don haka yauyafi kowa farin ciki.
Hanna ta dago a kunya cetagaishe shi ya amsa
cike da fara'a ya mika hannu yakarbi rariyar dake
hannunra ya fara tankade. Hajirkuma tana yi
masa tsiya tana cewa'' wai bellowannan bamu
san wanne irin abu za'ayiwa hanna bayan anyi
aure tuwan ma kai zaka dinga tukamata. Bello
yace ke kin fadi kadan tauna abincikawai bazan
yiwa hanna ba saboda bazaiyu intauna mata ba
amma a baki zan dinga bata bayanna dafa mata
domin hanna tafi saraunoyar da takemulkin
duniyar nan idan ma akwai yadda nake jinta a
raina,Ga mamakinsa sai suka ga hawaye shar
yatsiyayo daga idanuwan hanna. Babu abinda ya
satakuka sai tausayin kanta dana bello madu
dominkowannensu son maso wani yake yi, inama
haisamne yake jinta a ransa haka kamar yadda
bello maduyake jinta a ransa. Shima ina ma
yadda yake sonta tana sonsa haka'' allah sarki
bello ka makara''hanna ta fada a ranta' sai bello
ya kurawa hannaido kawai yana kallo sai ya juya
ya kalli hajir wacceitama tayi kasake a tsaye tana
kallonsu. Ya miketsaye ya kade garin da yake
hannunsa yace dahanna ta taso suje zaure yana
son ganinta yana da magana da ita. Hanna ta
mike ta dauko ruwa tawanke hannayenta ta yafa
gyalenta tana biye dashisuka fita zaure.
Tambayoyom da bello madu yajerawa hanna sun
doshi goma dom son yaji meyeya sata kuka ko
aurensa ne bata so amma duk daa'a hanna take
amsa masa. Domin idan ta kuskura ta bayyana
abunda yake ranta ta sake shiga ukutasan bello
ba zai takura yace sai ya aure ta bahakura zaiyi
idan ya fasa aurenta wazata aurakuma tunda
bata da maganin ciwon da yakedamunta. Na san
na rasa haisam, na rasa shi kumahar abada na
rasa soyayyarsa na rasa farin cikin rayuwata,
meye ya rage mun a duniya kuma?Banda jiran
ranar mutuwa. Bello ya katsewa hannatunani
yace'' to tunda na tambayeki kince ba
komaiakwai wata magana guda da nake son muyi
dakehanna don allah kiyi hakuri ki sake yin hakuri
daduk yadda kika tsinci rayuwarki, abinda nake
nufi shine watakila hajir ta fada miki ina da gida
nawana kaina yanzi ma a ciki nake zaune nan
za'a kaikibayan anyi bikinmu, to kinsan halin
iyayemusamman ma mata mahaifiyata ta
kekashe kasatace lallai lallai sai dai a kaiki cikin
gidanmu ma'anagidan da take zaune da
kishiyarta wanda ba karamar takura bane dakine
kwaya daya jal ganata ga wanda za'a kaiki. Kiyi
hakuri ko bayanbikin zanci gaba da bata hakuri
akan ta yarda inmaida ke gidana'' hanna ta
sunkuyar dakai tacekawu wannan ba wani abu
bane da zaka damukanka. Kaabi maganar
mahaifiyarka domin abunda babba ya hango yaro
koya bishiyar rimi bazai ganoba, ita ta haifeka
tafika sanin dalilin dayasa tacemaka ka zauna da
matarka a kusa da ita . Allah yabamu zaman
lafiya gaba dayanmu ni da ita. Ni dakai kuma na
gode'' wannan kalamai na hanna yakwantarwa
da bello madu hankali don bai taba zaton hanna
ba zata damu ba idan taji yare dasurukai zata
zauna amma sai yaji ita take kokarin yimasa
nasiha, akan ya kwantar da hankalinsa
yabimaganar mahaifiyarsa. Kuma hanna ita ce
take yimasa godiya. Daga karshe ya yiwa hanna
sallamayace zai koma wajen aiki sai nan da
kwana hudu zai dawo an turashi tsakanin boda
dake tsakaninmaigatari da niger da zarar ya dawo
za'a kawo lefeinsha allah. Hanna tayi masa fatan
dawowa lafiya yatafi ita kuma ta shiga gida,Ta
iske hajir tana kwasar tuwo . Taje kusa daita ta
jawo kujera ta zauna. Hajir ta kalleta taceamarya
a gidan custom bello madu kinsha
kamshi,amaryar nan da wata guda. Wai ya naga
duk jiknkiyayi sanyi ne har koke koke kike yi?
Koda yakemuma fa duk munyi wannan don
gabanin bikina kurket na rame sai kuka ina zaton
auren waniabun tashin hankaline ashe babu
abinda ya kai shikwanciyar hankali, ke kuwa daga
ke sai masoyinkiku biyu a gida ku rakashe kowa
kokarin yafarantawa dan uwansa yake yi. Ke
gidanki nasiminti ne kewayayye ai bello madu ya
zuba sumunti a gidansa tal a lailaye da simunti
kamar abirnin. Mu da muke gidan kasa ma muke
jin dadinrayuwarmu balle ke'' hanna ta ce'' kai
hajir ai dagidan simintin dana kasar duk dayane
yanzu yakecemun mahaifiyarsa ta tubure lallai
lallai bata yardata kaini gidansa ba sai dai in
zauna a gidansu. Hajir ta zabura ta wurgar da
marar da take kwasar tuwota mike tsaye ta rike
haba da hannu tace'' hanname kika ce kina nufin
yanzu gidan su bello za'akaiki? Lallai mun shiga
uku mu masu kai amaryama balle ke da zaki
zauna da ita. Hanna ra jawohannun hajir ta
zaunar da ita tace'' hajir zauna mana muyi
magana daga zaune me yasa kika cemun shiga
uku wani abune ? Hajir tayi ajiyar zuciyata koma
ya ta zauna tace'' hanna bazan boye mikiba a
gaskiya innar bello bata da haki saboda dukgarin
nan babu wanda bai san bala'in inna hauleba
har tafi iya abu matar babanki da kike bani
labarinta don tun maigidanta yana nan bai rasu
batake azabtar da kishiyarta indo wahalar
duniyarnan yau idan kika je gidan indo da
yayanta tamkarbayi ne a gidan. Debo ruwa ma a
rafi ya ishekibayan zuwa gona da sassafe amma
shi bello meyasa zai yi mana haka bayan yasa
halin mahaifiyarsa ko da yake ba laifinsa bane
don idanta saka musu kara basun isa su tsallake
bamusamman bello yana yi mata ladabi sosai fiye
dasauran kannanshi shine babba a gidan. Ina jin
batsso yayi nisa da ita gani take komai ya samu
yanzuke zai dinga dankawa gaba daya'' kafin
hanna tace wani abu ahmed ne yayi sallama ya
shigo sukaamsa masa gami dayi masa sannu da
zuwa. Amurtuke ya amsa sannan ya juya ta kalli
hajir tadaka mata tsawa yace. Ke hajir ki iya
bakin kidanme kike kokarin rikita hanna akan
aurenta dabello madu akanta aka fara zama da
sirikai'' ya juya ya kalli hanna yace'' to saikin
toshe kunnuwankishi aure dan hakuri ne kiji kiki
ji ki gani kiki gani,ladabi da biyayya shi zai rabaki
da masifa datakurawar surukarki. Kada ki yarda
da 'yan zugamasu nuna miki kin hadu da masifar
suruka mutumko shaidan ne yasan mai kyautata
masa don haka idan kika bi inna haule sau da
kafa dole ta dagamiki kafa. Bawai nace hajir tayi
karya ba hakahalayyar inna haule take amma sai
kinyi hakurikindaure kin mata biyayya zaki ga
ashe duk abundaake fada maki ba haka take
bama'' hanna tasunkuyar dakai kasa tace'' to
kawu naji abunda ka fadamin zanyi amfani dashi
na gode madalla'' tamike ta shiga daki. Ahmed ya
juya ya kalli hajirwacce ta cika tayi fushi taf
kamar zata fashe'' yashafa kumatunta yace'' ke
kuma daga maganameye abun yin fushin'' hajir
tace'' haba ahmed mekake nufi da ka ce kada
hanna ta saurari yan zuga, kana nufin nice yar
zugar kenan zan hanata yinaure ko? Ya ce a'a
abunda naga laifinki shinemuddin kika sanar
mata halin innar bello madu aizata tsorata kuma
zata ji ta tsani surukarta daganan zaman lafiya
babu kuma ni bello ne yafi banitausayi har cewa
yayi ko zai fasa auren hanna ne saboda yasan
tabbas zata hadu da halinmahaifiyarsa shi kuma
a duniya abunda yaki jiniirin batawa hanna don
yana sonta kamar yaddayake son rayuwarsa.
Mun kada mun raya da innahauke ta hakura ta
bar bello ya tare da amaryarsa agidansa taki fur
wani uban ashar ta soka min ahe haushina take ji
wai na dauki yata na bashi, ashetana so ta
hadashi da wata shine yaki,Sum sum nayi na
ficedaga gidan. Kuma wani abun bakin ciki shine
belloyayi yayi ta yadda ya rushe bangarensa yayi
nasiminti ya zagaye da katanga tace bai isa ba
ana kasar zai saka amaryar tasa. Sai zana ya
suyo yadanzagaye dakin su kwaya daya