Showing 6001 words to 9000 words out of 17701 words
Chapter 3 - Gangar Jikinsa Na Aura Book 2 Hausa Novel Complete
Unknown
25 Dec 2024
95
jal kuma
abincinsu ahade dana yan gidan zasu dinga yi
allah dai yakyauta mana nan mun dukufa da
addu'a alah yadora shi akanta ta hakura ta
barshi ya zauna agidansa hajir tace''amin nima
zan taya hanna da addu'a amma caf wannan
suruka ta hanna. Ai kogidan bazan taba takawa
ba da sunan ziyara ni tunina yarinya tsoronta
na ke ko gidan bana shigaallah ya sani banasan
masifa. Duk hirar nan da sukeyi kakaf a kunnen
hanna wacce ke daki tana jiyosu. Tayi ajiyar
zuciya ta girgiza kai don tausayin kanta da kanta
tace a ranta. Haka allah yaso danihaka zan kare a
kunci, wahala da bakin ciki narabu da wahalar
iya abu na fada wahalat innahaule allah kana
sane dani, kasan halin da nakeciki kaine
majibincin lamarina la'ila ha illa antasubhanaka
inni kuntu minaz zalimin. Babana yayi gaskiya da
yace babu mijin da zan aura da zairikeni amana
in ba haisam ba. Baba baka sanyadda mukayi da
haisam ba ka mutu ka barni akaninje in cewa
haisam yazo ya aureni ka bashini, yayahaisam ya
auri wacce yake so yar barni, baba kabarni a
duniya baka san na rabu da haisam din bama. Ta
rushe da kuka mai tsanani. Ta koma takwanta a
tsakar dakin tana tunanin rayuwar dasuka yi da
haisam shine farin cikinta a makarantabaya so ko
kuda ta cijeta tattalinta wasa da dariyakullum har
ya zuwa ranar rabuwarsu. Hanna tayikuka har ta
gaji sannan ta mike don zuwa bandaki tayi alwala
magariba. Ashe ta dade dayi bata saniba. Kamar
yadda bello madu yace za'a kawo kefeda sauran
kudade na al'ada an kawowa hanna lefeakwati
uku kowacce a cike danma inna haule dukta
rarrage kayan amma duk da haka masha allahan
zuba mata kaya. A nan kauyen sai zancen kayan
ake yi 'yan uwan hanna sai murna ake
ammabanda ahmed domin ya tsorata da ganin
yawanlefen nan yasan dole za'a zuba ido aga me
kymaza'a kai dakin hanna.A matsayinsa na dan
karamin malaminmakaranta firamare mai daukar
dan karaninalbashi shi zai yiwa hanna gado, gara
da kumaabincin 'yan biki gashi kuma a kurarren
lokaci akasaka ranar bikin. Gashi duk danginsu
shine maidama dama duk a jikinsa damgi suke
nema. Yasan ko za'a taimaka masa da
gudummawa bai wuce ayimasa fantekar alkaki da
nakiya ba sai 'yankwanikan cin abinci wadanda
suka daddage nezasu bashi setin samira. Da cin
bashi da komaiahmed ya hada kudin gado mabi
lamba one damadubinsa. Dan kudin da hajir take
tarawa na dinkin hular da take ta bashi ya hada
da sauran yargudummawar da ya samu ya sayi
ledar daki dalabule shikenan sai kwanukan rabon
abinci dasamira seti hudu aka haka aka jerawa
hanna adaki. Bayan an sha biki an kai amarya
dakinta tsaftsaf daidai karfinsu sai dai wani
babban tashin hankali ahmed ta buga sama da
kasa ya rasa kudinsiyama hanna gara. Don haka
yace hajir da wasumatan suje su bawa inna haule
hakuri insha allahukafin ta haihu za'a kawo mata
gara don har ta farahabaici an kawo amarya
babu gara. Kwanan hannauku cur tana rusar
kuka bayan an kaita gidan miji . A ranar na
hudun ne bello madu ya shigo dakintada jakar
kayansa shi ma ya kauro gidan daga cangidansa.
Da misalin karfe goma na dare gari yayishiru
kowa yayi bacci abinka da rayuwar kauyeamma a
zaune a gefen gado ya tarar da hanna tayitagumi
tana tunani ido yayi mata jawur a kumbure , yayi
mata sallama ta shigo. Ta daga kai da sauri
tadube shi sannan ta amsa masa sallamar da
yayimata. Ya shigo ya ajiye jakarsa a gefen
akwatinantayazo kusa da ita ya zauna yana mai
yi matamurmushi da nuna farin cikinsa a fili, ya
dubikwayar idanuwanta yaga jawur don tsananin
kuka da tasha yi yace'' hanna kukan ne har ya
zamarmiki da idanuwanki haka ? Don allah ki
daina kuka,hanna ni mai kaunarki ne bazan cutar
dake ba'' tasake rushewa da kuka yasa hannu ya
jawotajikinsa sai yaga tayi sauri ta zabura ta mike
tsaye,Wannan zabura ta Hanna ta bawa
Bellomamaki kamar wanda ya dona mata wuta,
ya miketsaye yasa hannu zai rukota. Hanna tayi
sauri tajada baya tana kokarin ta fice waje. Bello
ya ce'' a.ahar waje zaki fice to na kyaleki zo ki
zauna bazansake taba ki ba'' sannan hanna ta
dawo tazo ta zauna a kasa kan ledar dake
shimfide a tsakardakin ta hada kai da gwiwa tana
kuka tamkarranta zai fita. Wannan kuka na hanna
ya tayarwada bello hankali ji yake tamkar tana
soka masawuka a zuciyarsa idan tana zubar da
hawayen nan.Ya nisa sannan yace Hanna kiyi
hakuri dan allah ki daina kuka meke damunki
ne ? Nifa yanxumijinkine ki daina guduna kuna
ina da hakkinakanki muddin kina guduna kuma
kina kuka kinatayar min da hankali.Nace kiyi
shiru kinki ki daina.Ko kina so inyi fushi dake
Allah yayi fushi dakeMala'ikun allah su dinga
la'antarki har sai gari ya waye? Hanna ta dago da
sauri ta kalleshi yace yayakike kallona? Gaskiya
nake fada miki ai duk macenda take gudun
mijinta Allah da mala'ikunsa zasudinga la'antarta
har sai gari ya waye ko kin yaddaki halaka ?
Hanna ta girgiza kai tace bana so nahalaka'' yace
''to in ba kyaso ki halaka zo nan kusa dani ki
zauna muyi yira. Cikin sheshshekan kukaHanna
tace"kawu na zalunci kaina, na kumazalunceka da
ban fada ma gaskiyar abunda yakedamuna ba.
Kawu na kasance ina cikin wani hali natsananin
damuwa wanda har nake tunanin bazaniya auren
kowa ba. To amma dole nasan za'a yi min aure
shi yasa na hakura na amince na aureka
atunanina zan iya daurewa in zauna amma
yanzubayan da akayi auren ciwon da yake
damuna yadawo min danye bana jin zan iya
zaman aure har insami aljannar da kowacce
mace take nema akarkashin tafin kafar mijinki ta
hanyar biyayyar aure. Kawu kayi hakuri ka
yafemin dan allah karufa min asiri. Ka
sauwakemin mu zauna haka batare da kowa ya
sani ba, saboda sai in halaka idanmuka zauna a
haka da igiyar auren ka. Bello yabude baki yana
kallon Hanna can ya taso yazogabanta ya durkusa
ya rike hannunta cikin yar siririyar murya mai
dauke da tsananin dimaucewayace'' Hanna.,
fadamin ni kawunkine mai shirintaimakonki ta
kowacce hanya kada kiji tsoronfadamin ko mene
ne '' ta janye hannunta a hankalita share
hawayenta tace '' idan bakamantaba a labarin
dana baku a garinmu nace nayimakarantar
sakandire da taimakon yaya Haisamson yaya
haisam ne ya zame min dafi a zuciyatawanda
dafin nan zai iya zamra min ajalina. Kawubello
inason haisam harni ma kaina ina mamakin
yadda kayi zuciyata ta kamu da sonshi haka
nayiaddu'ar don allah ya goge mun , nayi azumi
nayikukan kullum akan allah ya yaye min amma
kamarkaramin ake . Daga karshe sai nake
addu'ar allahya dauki raina da in dauwama a
haka amma kaganni har yanxu a haka na rasa
yadda zanyi'' ta rushe da kuka. Bello yayi shiru
yana kallonta shimacan ya nisa ya ce'l hanna me
yasa nazakiyi addu'arallah ya hadki da haisam ba
kuyi aure kike addu'arallah ya yaye miki sonsa ko
kua allah ya daukiranki? Hanna ta goge hawaye
tace:: haisam yayiaure a ranar da mahaifina ya
rasu'' bello madu ya gyara ya zauna a gaban
hanna ya lankwashe kafadon jin labarin wannan
rikirkitaccen al.amarin nahanna. Hanna bata boye
maiba ta bashi labarintadana haisam tun daga
ranar da babanta ya kaitamakaranta har ranar
gidansu ta iske shi zai tafidaurin aurensa, daga
karshe tace'' ashe yaya haisam ba sona yake ba
taimako kawai yayi min nikuma zuciyata ta kamu
da tsantsar kaunarsa donhaka ne a koda yaushe
nake addu,ar allah yayayemun sonsa bana
addu.ar haisam yazo yaaureni. Bello madu yayi
murmushi karfin hali yace''haisam yana sonki
yana kaunarki sosai fiye dani kaina da duk wni
mai sonki a duniya. Akwai watamatsalar da tasa
bai aurekiba hanna'' hanna cikeda mamaki ta
kurawa bello ido tace me yasa kacehaka me ka
gani daka fadi haka?'' bello yace''saboda ke
yarinya ce shi yasa baza ki fahimcihakan ba,
kuma nasan irin yadda kike hanna bawai haka ta
taba faruwa akaina ba a.a inakwatanta nima
rayuwata zata iya shiga irin wannanhalin da kika
shiga idan na rasaki saboda kecewacce na taba
jin ina so a duniya. Ni na yadda naamince zanci
gaba da zama dake a haka amatsayinki na
matata amma babu zancen saki a tsakanina dake
saidai mutuwa ta rabamu sabodasanda nake
miki, hanna da ace haisam yana jirankibayyi aure
ba da zan daukeki ina kaiki wajenshiinaura miki
shi don kiyi rayuwa cikin farin ciki, ni indawo gida
in zauna ciwon son da nake miki yakasheni na
yadda indai na ceto rayuwarki. Amma yanzu da
yake haisam yayi aure kiyi hakuri. A cikinkashi
dari bisa dari da kike yiwa haisam, ki daure
kibani kashi daya a cikin dari har
karshenrayuwarmu ta aure na gode. Hanna ki
daure kicigaba da zama dani a haka kada ki barni
ni dakeduka muyi biyu babu, kin rasa haisam ni
kuma in rasaki'' yasa hannu ya jawo jikinsa zai
rungumetatayi sauri ta mike tsaye ta juya masa
baya. Ya tashi asanyaye yaje ya rufe kofa ya
datse da makulli. Yayinda hanna taji wannan
rana tamkar ranar damahaifinta ya rasu ta kuma
rasa haisam yau gata adaki zata kwanta gado
daya da wani a matsayin mijinta ba haisam ba,
hawaye yaci gaba da tsiyayomata daga
idanuwanta. Bello yaxo ya rungumetata bayanta
yana mai sunbatar kunnuwanta dagefen
kumatunta cikin sanyayyiyar murya hannatace'' a
matsayinka na mijina akan babu yaddazanyi ka
sami GANGAR JIKINA amma ruhi, zuciyata na
wajen haisam.'' bai iya bata wannan amsan
bacimak ya dauketa ya dorata a tsakiyar gado.
Hannata shide tama fita hayyacinta saboda
tsananin bakinciki yau gani ga wani daban zai
fara saninta 'yamace kafin haisam wannan bakin
cikin ne yayimata yawa yasa ta fita hayyacinta
ma iya cewa suma tayi amma gogan naka baima
lura ba ji yakeyau tamkar an masa albishir da
gidan aljanna gashiya auri hanna harma ta
mallaka masa GANGAR JIKINTA.A ranar da hanna
ta cika sati guda ta fara saninhalin uwar mijinta
ashe da kara take yi mata. Dasassafe ko tashi
daga bacci basu yiba Inna Hauletayi dirar mikiya
a bakin kofan dakinsu tana bugunkofar da karfi
tana fadin a tashi haka baccin ya isaduk inda sati
yayi an gama cin amarci bakunta ta kare kin
zama 'yar gida fito ki dora dumame. Indozataje
rafi debo ruwa.Firgigit Hanna ta mike ta dirodaga
kan gado ta bude kofa ta fito. Ta durkusa
harkasa ta gaishe da Inna Haule. A yatsune ta
amsatace'' a tafi wajen murhu a dora dumame
ga dawada gero can idan kuka karya kumallo
keda indo ku surfa''. Bello yaji tamkar yayi ihu
saboda takaiciyasan Hanna kuma ta shiga uku ta
lalace kamanyadda amaryar Babansa Indo take
dandana wahalakullum kamar baiwa.Ya tashi
zaune ya rike kaitausayin Hanna zuciyarsa da
tunani ina zai samomafita kafin ta zama baiwa,
to amma babu wata mafita tunda har yau har
waye war gobe innaHaule taki amince masa ya
koma gidansa shidamatarsa. Da ya isheta ma da
maganar sai tace dukranar daya sake rokonta
akan wannan bukata tasaAllah ya isa kuma zata
tsine masa, don haka Belloyaja bakinsa yayi gum.
Haka hanna ta kasance tana yin iya kokarinta na
ganin ta farantama uwarmijinta tana binta sau da
kafa amma a banza innahaule bata gani. A koda
yaushe zagin hanna taketana cewa.A yaushe
zagin hanna take tana cewa aurendaba gara ma
ai bai cika aure ba. Wai hanna tamallake mata da
don da sai yayi sati biyu,uku baizogarin ba daga
wajen aikimsa amma yanxu bayasati guda,
zantuttuka barkatai marasa ma'ana daina nuna
tsana tsagoranta. To wannan al.amari yasa hanna
ta sake fitar da rai daga samun zaman lafiyaa
rayuwarta, inna haule halinta daya da iya
abukoma tafi iya abu ko uwarka ka yanka musu
kadafa ka basu bazsu gode maka ba. Sai dai
kawaiidan abun ya isheta ta shiga daki tayi kuka
ta gaji.Idan bello madu ya dawo ya ganta a
wannan hali sai ya shiga lallashinta yana bata
hakurin nan nasababu abinda yake karama
hanna banda takaici.Abu daya ya gano lagonta in
har yana so tayidariya a duk halin bacin ran da
take shine yacemata haisam. Haka yake sakata a
gaba yace dolesai ta bashi labarin haisam. A koda
yaushe hanna na kirga kwanikin yaushe bello zai
dawo dagawaje aiki saboda dashine kawai take
hira mai dadihar tayi dariya hirar ita ce hirar
haisam.. Hanna daindo ne suke surfe a yau, inna
haule ta fita unguwashine ma suka samu suna
yar hira. Duk da indo tagirmewa hanna amma
duk da haka bata fi shekaru ashirin da shida ba a
matsayin suruka take a wajenhanna tunda matar
baban mijinta ce. Amma doletasa suka zama
kawaye. Hanna na bakace dusar,indo tana tikar
dawa a turmi. Indo ta tsagaita dadakan tace''
hanna sai dai hakuri ni harna saba dawannan
bauta haka Allah ya rubuto mana rayuwarmu.
Hanna tayi ajiyar zuciya tace '' Allahyana barin
bawanshi a halin daya so ya ganshi.Amma duk
abubuwan da inna kemun bayadamuna irin duk
abunda muke yi mata bata ganidubi fa irin aikin
da mukeyi kamar zamu mutuyanzu idan tazo
cewa zatayi munyi ha'inci bata surfu ba. Ga zagin
da take yimin akan gara ni narasa yadda zanyi da
rayuwata. Indo ta ajiye tabaryatace'' ai waike
kina nufin duk abinda ake baki saniba a gidan
nan yau? Hanna ta ajiye faifan dakehannunta ta
tattara hankalinta gaba daya a wajenindo tana
jiran taji me yake faruwa. Indo tace '' ko da yake
kin tafi debo ruwa dazu da sassafe ni innahaule
tasa na shifa dakinki na miko mataakwatinan
aurenki guda biyu wadanda baki dinkakayan ciki
ba tasa almajiri ya daukar mata wai zatakai wani
gida ajiya tunda ba.ayi mii gara ba sumabaza ki
daura lefansu ba. Daman wata uku ta daukar
miki a kawo gara gashi yanzu kin shigawata hudu
da aure . Don haka da zarar bello yadawo zata sa
ya sakeki, lefen kuma ta kaiwa watayarinyar a
daura masa aure da wacce zata kawomata gara.
Kuma kinsan bello babu yadda zaiyiidan ta sashi
a gaba tace '' ya sake ki . Hawaye ne sur yake
zuba daga idanuwanta hanna ta mike dagudu ta
shiga daki ta tara wayan an kwasheakwatina sai
kwaya daya 'yar karamar kaya kalauku ne ta
dinka a lefen su suka rage sai saurantsofaffain
kayanta nada gasunan a kasa an watsarmata. Sai
ta kwanta a kan gado ta fara rusar kuka hanna ta
kware wajen iya kuka dan ko gasar masuiya kuka
akaje ta duniya ina ganin ita zata zo tadaya. Can
ba dadewwa inna haule ta dawo ta tarada indo
ce kadai take aikin abincin rana tace'' inahanna?
Indo tace'' ciwan ciki take tana daki. Taleka ta
tarar da hanna sharkaf cikin kuka sai tace.'' babu
wani ciwan ciki ba ciwan cikiba ko ciwannakuda
kike kin bar gidan nan bazan iya ba harkartalauci
anyi biki ko gara babu lefan dana dauke neshine
yasa bakin ciki ya kwantar dake. Haka hannata
yini cur a kwance babu ci babu sha sai kukaAllah
cikin ikonsa sai ya jeho mata Bello da yamma
kwanansa biyu ral da tafiya ba zato ba
tsammanihanna taji sallamansa ya shigo, furgigit
tayi ta tashizaune kallo daya yayi mata yasan
akwai abindaaka yi mata har tasha kuka. Yaje da
sauri ya zaunaa kusa da ita ya jawota jikinsa ya
tambayeta mekedamunta take kuka. Ta amsa
masa da ba komai . Ya ce yasan dole da wani
abu kar ta boye masa ta fadamasa gaskiya, sai
tace cikin tane ke ciwo, yayi shirushi dai ya jita ne
kawai amma bai gamsu ba. Sai canaka jima
hankalinsa yakai wajen akwatina yagabasa nan
yace hanna ina akwatinanki suke? Tayishiru can
tace inna ta kwashe takai ajiya wai tunda
ba'yimin gara ba wata zata kaiwa ta aura maka
itani ka sakeni. Sai ta rushe da kuka. Bello ya cije
bakidon tsananin bakin ciki yayi shiru ya kasa
maganasai yasa hannu yana goge mata hawaye
ya nisayace. Daina kuka kece baki sani ba na baw
ahmedkudin da zai saya mika gata kakaf yanzu
ma cikon kudin da zai karasa sayyar na kawo
masa. Damanyanzu zan koma wajen aiki tunda
ina da aikin dare.Daman inna bata ganni ba ance
tana makwabtabari inyi sauri in tafi baza ta san
nazo garin bamaballe tayi min maganar sai ince
Ahmed suyi kokarisu kawo garar gobe kinga an
kashe bakinta kafin in dawo. Ya rungumeta
hanna ya sambacikumatunta yace '' bazan sake
kiba hanna ina sonkida yawa ki kwantar da
hankalinki kinji ko, sannanya fice yana sauri ya
tafi. Hanna ta bishi da kalloyayin da zuciya kece
mata'' ba haisam kadai ba bello madu ma
maisonki ne hanna ki kaunace shi.'' haka kuwa
akayiwashe gari da misalin karfe uku na yamma
saihanna taji an doso cikin gidan kamar a
mafarkitaga kartan maza suna ta ajiye
buhunhuna a kofar dakin inna haule . Mata suna
ta shigowa dafantekun alkaki, nakiya dibulan da
sauransu.Wannan al.amari ya bawa inna haule
mamaki,nauyi da kunya saboda sunyi mata ba
zata duk tabigari tana fadin ba.ayiwa hanna gara
ba kuma bazasu iya yiba kwatsam sai ga gara
wacce ko 'yayan attajiran garin ba'a taba yi musu
gara mai yawanbuhunhunan haka ba. Nan dai
inna haule ta haufara.ar borin kunya tana cewa
ashe kuna tafe ku kaki sanar min nima in gayyato
yan uwana suxo sutayani karbar irin wannan abin
alhairi sannunku dazuwa ku shigo daki mana ya
zaku zauna a waje. Hanna dibo tabarminki dana
indo a shinfida baki.Ai da kun sanarmin zaku zo
da nasa anyi mukugirke girke da soye soye irin
wannan abin arzikihaka'' yan uwan hanna suka
ce'' babu komai ai bazama muka zo yi ba mun
kawo gara gata nan,zamu koma don yarmu ta
sami salama a zamanta na aure da mijinta''
suma suka yaba mata ba dadi.Washe gari inna
haule da sassafe taje ta debowahanna
akwatinanta ta kawo mata amma ankwashe wasu
kayan da yawa babu ta kumagargadi hanna kada
ta sake ta fadawa danginta komijinta tayi shiru da
bakinta. Da bello madu ya dawo faran faran inna
haule ta kira shi ta nunamasa gara har tana
cewa'' allah sarki ashe bakaramin shiri suke yiba
shi yasa basu kawo dawuri ba irin wannan yawan
gara sai kace yarsarkin noma ka auro '' bello yayi
dariya ya ce'' Allahya sanya alheri ya bamu
zaman lafiya'' ya nufi dakin hanna, bayan tayi
masa sannu da zuwa ta kawomasa abinci da
ruwa yasha sai ya jawo akwatinanya bude kamar
yadda ya zarga tabbas mahaifiyarsazata kwashe
wasu kayan haka kuwa ya gani takwashe kaya da
yawa. Ya waiga ya kalli hanna saita sunkuyar da
kanta kasa bata ce masa komai ba...
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
GANGARJIKINSA NA AURA 2 Part 2
Posted by ANaM Dorayi on 03:14 PM, 30-Apr-15
Under: Gangarjikinsa ta Aura
Yace '' hanna an kwashe miki lefenki ko?
Kiyihakuri zan suyo miki wasu insha Allah idan
muka yialbashi wani watan'' hanna ta dago cikin
ladabi datattausar murya tace'' ni na yafe duniya
da lahira basai ka biyani ba wahalar zata yi maka
yawa. Kawubello babu abinda zance maka sai
godiya da wannan gara daka yimin Allah ya saka
da alheridomin ka kwatar min yancina tun daga
ranar daaka kawo inna bata sake yimin gori ba.
Yanzu zanyizaman farin ciki a gidan aurena: yayai
murmushiyace'' farin cikin ki shine nawa Hanna,
Allah ya karasanya ki a farin ciki fiye dana yanzu''
tace amin na gode. Karshen wata nayi da bello ya
dau albashi saida ya sisiyawa hanna kayayyakinta
damahaifiyarsa ta kwashe cikin dare ya
kawowahanna a boye yace ai hakkintane dole ya
biya ta.Hanna tayi godiya ta karba haka hanna
da bellosuka kasance yana kyautata mata a boye
komai ya gani na sakawa kona marmari sai ya
suyo mata dadaddare ya shigo mata dashi ya
bata a boye ba taredaya bari mahaifiyarsa ta gani
ba. Bello yana karason hanna saboda ladabinta
hankali da nutsuwada uwa uba tsananin
hakurinta da tawakkali itakuwa hanna har yau
har wayewar gobe ta kasa masanya gurbin
haisam ta mayar da bello zuciyarta.Idan bacci
take yi tana kwance da bello ammamafarkin
haisam take. Idan tunani take yi haisamkawai
take hangowa a zuciyarta. Tana kokarin tamayar
da soyayyar da take yiwa haisam kan bellosaboda
ita ma ta saka masa da soyayyar, sabida irin
kyautata mata da yake amma abu ya faskara
hakadai take dagewa tana nunawa bello tana
sonsawanda a zuciyarta ba haka bane. Wasu
lokuta dayawa idan suka tashi da safe. Bello
yakan ce matayaya haisam? Don jiya kina kiransa
a mafarki.Hakika hanna duk sanda ta kwanta
mafarkin haisam take yi ashe har ambatonsa
take a fili.Saboda tsananin son da bello yake yi
mata ya yardaya amince kuma zai zauna da ita a
haka. Bai tabanuna mata bacin ransa ba. Ita
kuma hanna sai tajitausayinsa ya kama ta nauyi
da kunyarsa talullubeta. Amma yaya zata yi
tunda