Showing 9001 words to 12000 words out of 17701 words

Chapter 4 - Gangar Jikinsa Na Aura Book 2 Hausa Novel Complete

Unknown   

25 Dec 2024

97

GANGAR JIKINTA YA AURA ZUCIYARTA na
wajen haisam.Matsalar gara ta wuce tsakaninta
da surukarta saikuma matsalar da inna haule ta
dakko ta dorawahanna ita ce har yanzu hanna ko
batan wata batayiba balle ta samu ciki fada da
gori a wajen innahaule babu dare babu rana.
Bello yayi kokari ya wayar mata dakai akan cewa
ba laifin hanna baneciki Allah ke badawa amma
abu yaci tura inna hauletaki ta saurarawa hanna
cewa take ga sa'anninaurenta nan dukka ciki
garesu wata bakwaibakwai tunda yanzu watan
hanna bakwai da aure.Yau hanna tun karfe biyun
dare take kai kawo a tsakar gida bacci ya gagari
idanuwanta. Duk budeidon da bello zayyi sai yaga
hanna tana fita ko tanashigowa cikin dakin
kaman a mafarki yake ganinta. Can yaji ana
kiraye kirayen sallar asuba tayi. Yasahannu ta
laluba gefensa yaji hann bata nan. Yayifirgigit ya
tashi ya fito tsakar gida ya hango hanna a gaban
murhu tana hura wuta ya karasa inda takeyace.'
Hanna yau lafiyarkikalau kuwa tun dare kike
shige da fice kinki kikwanta yanxu da asubar nan
wutar me kikehurawa? Hanna ta danyi murmushi
tace'' kawu kamanta yau da duku duku oganka
yace zai aiko damota za kuje Agadas shine nake
dora maka ruwan wanka naji yau garin da sanyi
sanyi''Yayi murmushiya ce'' Ai jinsa nayi kawai
meye abun turo mota daduku duku sai kace
zamubar kasar'' Hanna tace''Agadas ai da nisa
shi yasa kuma wata kila bakwana zakuyiba ko ?
Yace' Gaskiya agadas da nisaba kuma cikin garin
zamu shiga ba local government zamu je ina
ganin wajen 450 Km nekuma bana jin zamu
kwana ziyarar aiki zai kaimucan mu kuma yan
rakiya'' Hanna tace '' Allah ya kaiku lafiya ya
dawo daku lafiya. Ina jin kiran assalatukafin
ruwan yayi zafi ga buta ka fara yin yin Sallah ?Ta
mika masa buta ta durkusa har kasa. Bello ya
tsaya yana kallonta kawai saboda wata
tsantsarsoyayyarta ce take kara sarke masa
zuciya.Musamman wannan kulawa da ladabi da
Hannatake masa, ya karbi butar ya shiga
bandaki, kafinya idar da sallar Hanna ta hada
masa ruwa wanka .Ya tashi ya shiga wanka. Kafin
ya fito ta debo wankakkaun kayansa data wanke
ta goge masa tadora akan gado ta goge masa
takalmin da zai sakamar yadda tasaba masa
kullum. Bayan yakammala yana goge gogensa da
yan shafe shafesai ya dauko kayan da Hanna ta
fitar masa ya saka.Tazo tana balle masa maballin
wuyan rigarsa. Yayi murmushi yace'' Hanna na
gode da irin wannahidima da kulawa da kike
nunamin wannan yasaina kara sonki dari bisa
dari, idan akwai soyyya datafi dari bisa dari ina
miki Hanna sai dai ni anyakuwa na sami kwaya
dayan nan kacal da nake so asanmin a cikin darin
da ake yiwa haisam ?Cikin kunya hanna tace''
Haba daya kacal ai kafiguda daya'' yace '' a.a
zancen gaskiya muke, nawaaka karamin ? Tayi
dariya tace'' kawu ka wucegoma ma zaka kai sha
biyar'' su duka suka tuntsireda dariya. Yace '' to
tunda a wata bakwai na samigoma sha biyar nan
da shekara bakwai zan iya tadda haisam'' suka
sake tuntsirewa da dariya.Muryar inna haule ce
ta katse musu dariyar da sukeyi tana bakin kofar
dakinsu tana cewa'' tun dazumagana nake muku
baku jini ba kun shige dakikuna tuntsira dariya
da duku dukun safiyar nan tomotar ofishinku ce
tazo suna ta kwankwasa gida . Daman Hanna
abinda kika sani kenan ki shiga dakida miji kina
dariya aikin kenan ciki fal kashi, babugurbin
kwanciyar Da sai gurbin tarin kashi'' Hannatayi
kasake yayi sanyi fara.ar da take yi ta koma
cikiranta ya baci damin da ana siyar da ciki da ta
suyohaka kuma da a wani waje ake nemoshi da
taje ta nemo duk wahala koda kuwa zata mutu
ne. Ko tahuta da zagin da gorin da ake yi mata.
Bello yayiajiyar zuciya yace'' inna gani nan zuwa
shiryawanake'' ta wuce ta tafi tana tsaki tana
cewa'' Kaje kadawo dai daga tafiyar kazo mu
zauna muyimaganar saboda bazai yuba, in zuba
muku ido haka kawai aure wata bakwai kenan
babu ciki baalamarsa kaina da kafafuwana
turawa yarinyaabinci nake sai dai taci tayi kashi
kawai. Ai ba dantazo ta cika mana shadda muka
aurota ba mumamuna so muga dan jariri a
gidanmu. Tunda tashanye ka ta asurce ka baka
ganin lefinta to ni bata asurceni ba dole ka karo
aure idan ma baza kasake taba, kai dole ma ka
sake ta ka auro maihaihuwa don daki daya
garemu a gidan nan'' Harinna haule tayi nisa ta
juyo ta dawo ta tsaya a kofardakinsu Hanna tace''
Hanna kiyi ki fito daga dakinnan yau duk ke zaki
yi aikin gidan nan shara wanke wanke surfe da
girki ki fara debo ruwatukunna idan kin cika
randunan gidan kakaf sai kifara aikin gida da
yamma kuma kije gona ki tsinkowake da gyada
dan sun nuna. Yau wacce kukeaikin tare indo
aikenta zanyi magarya wajenkawata. Tunda ba
ciki garekiba ba goyo ba ai wannan aikin bazai
gagarekiba, sai dai idan kinjikashi sai kiyi a gonar
tunda cikinki sai kashi babuhaihuwa. Kinga kuwa
kashin naki ya zamar mintaki a gonar kinga kin
taimaka kema'' Bello maduya fisata baisan sanda
yace'' Haba inna ki dainayiwa hanna gorin
haihuwa ba laifinta bane rashin haihuwa Allah ne
yake bayarwa inna dama haryanzu Hanna ce take
debo ruwa a rafi ina almajiriindana dauko aiki
nace zan dinga biyansa. Ita taji daaikin gidan su
kuna almajiran suje gonar. Hannatasa hannu ta
toshe masa baki tace '' yi shiru karkasa taji
haushina, mahaifiyarka ce babu komai duk zanyi
aikin. Inna Haule ta rike baki tace'' inyedannan
ka fara fada in fada dani akan matarkalallai abun
babba ne jeka ka dawo ka sameni donwallahi ina
ganin zamanka ya kare da wannanyarinyar mai
kama da tumatir ina ganin rabaka takesotayi da
kowa a duniya har dani dana haifeka . Ba'a
haiyacinka kake ba na sani bayinka bane. Tatafi
tana surutanta dai barkatai. Hawaye yana
zubashar daga idon Hanna. Bello yasa hannu ya
gogemata zuciyarsa cike da tsananin tausayinta
ammayafi jin tausayin kansa da kansa. Saboda
zaifi hannashiga wani hali,idanmahaifiyarsa tasa
ya saketa don shine yafi sontafiye da yadda take
sinsa idan ya rabu da hanna yarabu da farin cikin
rayuwarsa. Kalma daya ce yasanidan yafadawa
Hanna duk irin bacin ran da takezata yi dariya
idan ya ambaci sunan Haisam . Yayi dan
murmushi ya kalleta yace'' Hanna dama ace
ayanzu kina da ciki ki haifanmun da namiji in
sakamasa suna haisam. Hanna ta dago ta
dubeshiidanuwanta a cike da hawaye sunyi jawur
donkuka amma saida murmushi ya subuce mata
a taketaji zuciyarta ta fara dan hucewa daga
tsananin tafasar da take yi saboda kunar
maganganun dainna Haule ta fada mata. Hanna
taji wani dan sanyi aranta wani abu ya dasu a
zuciyarta da bello yace ''dama ace ana da ciki ta
haifi da namiji ya saka masasuna Haisam taji
dama ace hakan faru mana. Ammadata tuna
yanxu ma haka al'ada take don haka zancen ciki
ma babu shi sai ta sake rushewa dakuka. Bello
ya jawota ya rungumeta akirjinsa yanashafa
lallausan gashinta yace'' Hanna lallai yauranki ya
baci sosai har in kira miki Haisam ammakici gaba
da kuka kiyi hakuri ki yafewa innata mucigaba da
yi mata addu'a Allah yasa ta gane gaskiya Allah
ya cusa mata soyayyarki a ranta. Hannatayiajiyar
zuciya tace amin'' amma ka tayani addu'aAllah ya
bani ciki kafin karshen watan nan inaganin haka
zai saka soyayyata a zuciyar inna. Belloyace amin
ya Allah, zan dukufa da addu'a kema kiyiAllah ya
amsa mana. Ya goge matahawayen idanuwanta
ya sumbaci kumtunta yace'' Haisamsunan danmu
fa. Hanna ta kyalkyale da dariya tarufe ido sai taji
wani farin ciki ya lullubeta. Tatsugunna ta jawo
takalminsa ta fara saka masa akafa tana sake
goge masa da tsumma. Ta feshemasa jikinsa da
turare tace'' Kawu bello Allah ya kiyaye hanya
kuje lafiya ku dawo lafiya. Yace aminHanna Allah
yasa nazo na sameki lafiya cikin farinciki'' yana
tafiya yana waiwayan hanna, itama ta fitohar
bakin kofar dakin ta tsaya tana daga masahannu
har ya shiga dakin mahaifiyarsa sannanhanna ta
koma daki. A zaune a gefen gado Bello ya iske
mahaifiyarsa tana tunani tana gayda kai
yadurkusa ya gaisheta ta amsa a fusace ta fara
masfada tace'' to dannan abunda nake so dakai
shinekarka yadda kayimin musu akan duk
hukuncindana yanke akanka ina nemar maka
aure a gidandagacin garinnan yar sarauta ka dace
ka aura tubda ka makalewa Hanna baza ka iya
sakinta bato ta zauna anan gidan tare dani ita
kuma waccamidan anyi aure sai a kaita gidan ka.
Bello ya dagakai ya kalleta zuciyarsa cike da bakin
ciki.Gidan da yasha magiya ta yarda akai Hanna
takiyau gata da bakinta tana cewa yayi aure
yakaimatarsa can amma banda Hanna ba. To
ashe hannadin ta tsana kawai . Ya nisa yace inna
me zai hanamu tare mu duka da amarya da
hanna duk inhadasu acan din'' Ta girgiza kaia
tace '' nace maka karka yimin musu ko? Haka
naga dama, tashi kajeka dawo din mu karasa
maganar amma idan kamatsa akan sai ka mayar
da hanna gidanka zaka saince ka sake ta don
wallahi hanna baza ta tare awancan gidan va sai
dai idan bani na haifeka ba. Kobayan raina ka
kaita can Allah ya isa'' Bello ya rike kai don
takaici can yace'' Naji inna na gode, danAllah ki
yafemin duk abunda nayi miki, idan na batamiki
rai a rayuwata gaba daya''Tayi dariya tace ''Babu
abunda ka taba yimin wallahi ko musun madaka
tarka kake mun bayin kanka bane ta shanyeka ne
na yafe maka Allah yayi maka albarka Bello ya
mike ya fita hawaye ne shar yake fita
dagaidanuwansa . Yana fitowa hanna tana jika
gero tayisharkaf da hawaye daga gani ta gama jin
dukmaganganun da suke yi. Kallo daya yayi mata
yajihawaye ya sake kece masa. Yazo ya wuce
tagabanta yace'' Hanna kiyi hakuri, ki sake yin
hakuri, Allah yana tare da mai hakuri'' ta bishi
dakallo tana hawaye yana waiwayanta yana
hawayehar ya fice . Tayi shiru tana sauraren
karar motarsuhar suka yi nisa ta daina jin karar
motar, ta rushe dakuka tana cewa a ranta'' A
bakin ciki ashe zandauwama? Yanzu aure inna
zata sa kawu Bello zaiyi ya tareda amaryarsa
agidansa ni abarni anan, meyasa inna ta
tsaneni ? Me nayi mata tatsaneni? Meyasa
kowaya tsaneni a duniyarnan ? Ubangijinayana
sane dani, Allah kasan halin da nake ciki,Allahka
fitar dani, Allah kaine abin godiya. Bayanfitar
Bello madu da kamar awa guda. A lokacin hanna
tana surfa gero, inna haule tana tsakar gidatana
cin dumamen tuwo, indo kuwa daga wanka tafito
zata shirya ta tafi magarya inda inna Haule
zataaiketa. Suka ji ,Mota tururus ta tsaya a kofar
gidansu.Wani ma'aikacine mai sanye da kayan
'yan sanda,yayi sallama ya shigo ba tare daya
gaishe suba. Yace '' Nan ne gidan su custom
Bello madu ko @inna haule ta tsaya dacin
tuwonta tace '' Nan neamma baya na waye yake
nemansa? Yace inazuwa'' ya fice, gaban hanna ya
hau faduwa . Daf-daf daman tun jiya ta kasa
bacci saifaduwar gaba take. Jingine tabarya da
take surfe ta tsaya. Kawai ji suka yi ana cewa' ku
kamada karfiwajen kafadan zaku rike inna haule
ta zabura ta mike da gudu ta lekoHanna ma ta
biyota da sauri idanuwansu sukagane musu
wannan gagarimin tashin hankalin,Gawar bello
madu ce ake shigowa da ita. Allahyayi masa
rasuwa a sanadiyar hatsarin motar dayaritsa dasu
yanzu-yanzun nan suna hawa hanyarsuta tafiya
Agadas wata babbar mota ce tazo gwaramusu
suka kutsa ta tsakiyar motar cikin ikon Allahbello
ne kawai ya rasu, sauran sun sami munanan
raunika suna asibiti. Hanna ta fadi ta suma,yayin
da inna haule take neman tube kayan jikntadon
gigicewa sai da aka rirriketa. kafin kace
kwabogida ya cika yayi makil da 'yan uwa da
makwabtamaza da mata. Ani masa wanka, an
suturtashi ankaishi an binne kamar yadda sharia
musulunci ta tanada. bello ya tafi ya bar rikici
gidansa kuma shitasa ta kare a duniya domin
rikicin duniya da mairai akeyi duk wani rai saiya
dandana mutuwa Allahyasa mu cika da imani,
amin. hanna tayiwa belloaddu'ar har yawun
bakinta ya kame, idan ta ya gajida addu'ar ta
rushe da kuka tayi ta huta haka dai har akayi
sadakar bakwai 'yan zaman makoki sukawatse
aka bar 'yan gida. yayin da bacci yakegagarar
idanuwansu, kamar yadda inna haule takekuka
cikin dare haka hanna ma sai ta laluba kusada ita
taji ita kadai babu bello sai ta tashi tayi kukahar
ta godewa Allah. kaico hanneta rasa kowa a
duniya. hanna bata shiga. watamatsala
batabangaran ci ko sha ko aikin gida ba har ta
fitadaga takabarta.sai bayan ta fita daga takaba
an fara zancenrabon gado sannan inna haule ta
daka tsalle ta diretace babu abunda za'a bawa
hanna na gadondanta tunda hanna ba
haihuwatayiba da bello saidai ta hada 'yan
komatsanta ta bar musu gida.kawu Ahamed yaji
haushi sosai ya kuma lashi takobin ko sama da
kasa zata hadesai ya kwatarwa'yarsa hanna
hakkinta a tumuli takaba shari'ar shida inna
haule har kotin koli idn bata bari an rabagadon
nan da hanna ba. yace kuma babu indahanna
zataje a gidan zata zauna sbd bello yana dagado
a gidan ubansa, inna haule kuma tace ita kuwa
baza ta bayar da dukkiyar belloba sai dai suzuba.
makudan kudi kuwa aka kawo daga wajenaikin su
bello, gashi da filaye da wannan tafkekengidan
nan daya sha suminti da bulo. inna haulekuwa
tace duk natae banda hanna ko sisi baza tabata
ba tunda ko kwai bata saka a gidan ba. tashin
hankali ya tabbata a zuciyar hanna ta rasa
yaddazata yi da rayuwarta da kawunta zai hakura
ya bariinna haule ta rike dukiyar bello dukka ba
sai anraba da ita ba. duniyar nawa take wanda
yatara ma ya tafi yabarta kowa ma mutuwa zaiyi.
dukwani hango jin dadin. rayuwarduniya yagoge a
zuciyar hanna babu abunda take bege sai
mutuwatazo ta dauketa ta tafi ta hutaitama. daga
gidankawu ahamed dake aiko mata da abincin
dare darana. tafi tafiya suma wata rana basa
aiko mata donyau da gobe sai Allah. hanna ta
fara fitar dazannuwan daurawarta da
kwanukanta tana siyarwa snnn taci abinci. wata
rana da yamma daindo sunje rafi sun debo ruw
suna tafe suna hira saisuka ji hassan me yekuwa
yana sanarwa yanacewa "yekuwa. jama'a ga
wata sanarwa, mai girmadagacin garin nan yace a
sanar muku matawadanda mazansu suka rasu
suka barsu da suzo fadarsa yanzun nan.
ma'aikata daga nigeria sunzomusu da tallafin
taimako. gwamnatin jihar kano anigeria ta aiko
da taimakon kudi za'a raba musu jaridomin su
rike kansu da marayin 'ya'yansu. ammakada
wata ta kuskurataje idan ba mijinta bane yamutu,
sai wacce mijinta ya mutu idon ta zunguri hana
tace hanna muje wajen taron nan ko Allah zaisa
mu dace. hanna ta rike baki tace babu
ruwanmuyanzu idan mukaje ai mun shiga 3 a
wajen innnacewa zatayi munje. mun tona musu
asiri aci muka jemu tambaye tako zata yadda. a
hanya sukadingahaduwa damata wadanda
mazansu suka rasu suna ta tafiya gidan dakaci
don karbarwannan tallafi mai tsoka. kowacce
tagasu hannasai tace au, baza ku taho fada ku
karbiwannantallafi ba daga nig fa bakin suka zo,
indotace gaskiya hanna in baza ki ba ni zanje sbd
idanmukakuskuramukaje gida inna haule baza ta
barmu ba.amma idan mun riga munje mun
karbobabu yadda zata yi damu fada ne dai da
zagi yazama jiki. hanna tace to mu shigagidan.
adama muajiye ruwa muje din daman gudun
fadan inna nake,to kobabu abundamu kai ma
kullum zagin mu takemuje kawai, suka shiga
gidan adama suka ajiye ruwan da yake kansu
suka nufi fada wajen taron.mata ne makil akan
layi suma su hana sukajekarshen suka tsaya.
wata kyakkyawar mata ce azaune akan kujera da
tebur a gabanta an dorawasu fles akan teburin.
kallo daya zakayi wa matarkasan tana cikin daula
fatar jikintamulmul sumul. dukda matar ba fara
bace amma ba baka bacekalarta mai kyau kayan
jikinta kuwa ko ba'a gayamaka ba leshin zai doshi
dubu hamshin sarkargwal da dankunneta da
zubbunan gwal reras ahannunta guda hudu sai
sheki sukeyi.matar maifaraa'a gata bata kyamar
talakwa sai gaggaisawa dasu take suna yin hannu.
tace. kowacce tazogabanta ta rubuta sunanta don
asan yawansukuma nawa ya cancanta a basu.
kowacce ta hauzara ido sbd basu iya rubuta
sunanta. matar taceyanxu duk cikinku babu
wacce ta iya rubutu tazo ta taimka min mu
rubuta sunayenku?Hanna tayi shiru kamr tace ta
iya amma gudunsurutun 'yan garin nan kar ace
ta cika nuna iyawasai tayi shiru. Indo ta
zungureta ta hanna bakn iyarubutu baki rubuta
mana Hanna tace a'a indo baburuwana a samu
wani yazo yayi dan kar ace nazogarinku na zake.
Matar ta sake cewa To tunda babu wacce ta iya
rubutu ina ganin ba zaiyu mu aiwatarda aikin da
zamu aiwatar ba a yau sai mun nemowacce ta
iya rubutu sannan saboda da mata zallamukeso
mu kafa kungiyar dole mace ce zata zo tarubutu
mana sunayen indo da taga kiri-kiri zasurasa bata
san snda tace A'a ranki ya dade ga hanna ta iya
rubutu" sauran suka hau cewa hannataimaka
mana ke kuwa ashe daman kin iya
rubuturubutamana karmu rasa Matar tace
wacece hanna?Ta fito tazo nan Hanna taje gaban
teburin matar tatsaya tace gani ranki y dade.
Matr ta kalli hanna smada kasa wata burgujejyar
doguwar riga wacce aka dinkintada wani
wagambari mai kauri irin nddinnan itama kanwar
kkrta ce ta bata, gashintatufke a tsakiyar ki tai
gammo dashi da zasu deboruwa sai wani yalallen
gyale baki ta yana akanta datakalminta dan
madina akafarta. Matar tayimurmushi tace yaya
sunanki? Hanna tace sunana Hanna Abubakar
imam" matar tace HannaAbubakar kin iyarubutu?
Hanna tace na iya ranki yadade, matar tace ko
da yake ku anan french kukeyiba turanci ba ko
irin na 'yan nig? Hanna tace ni nafiiya turancin
nig, french din kadan-kadan na iyamijina yana
koy min mtar taace , ta jawo kujera kizo nan kusa
dani ki dinga rubuta sunayen su, ki fararubuta
sunan ki sannan ki rubuta sunayen sauran.Hanna
ta zauna tana rubutu sunayen matan nandaya
bayan daya suna tahowa a layi. Ta gamatubuta
sunayen sai magaruba tayi sai aka tsayar
dashawarar sai gobe da safe su kra taruwa dan a
raba musu tallafin sukanufi gidanjen su,
matarkuma gidan dakci aka kaita a can zata
kwana,namijin kuma da sukazo shima aka kaishi
wanigida aka suke shi tunda dare yayi dokin gobe
tayisu koma fada. Hann da indo kuwa sai suka
haufaduwar gab suna shirya kalmar da zasu furta
wajen kare kansu daga fadan inna haule.
Aikuwadaga shigarsu gida ta fara yi musu fada
donlabari ya kai mata cewar anga su hanna a
fadasunje karbar jari. Tana cewa dole Hanna ki
barmingidana sbd so kike ki koywaindo kinji da
fitinawanda da bata iyaba, ki tafi can gidan ku
acan ake yunwa ake neman jari mu nan Allah ya
rufa manaasiri,kema indo tunda wanda ya du
nuyinki ke da'ya'yankiya rasu bello ne damn
yace shi zai dingaciyar dku gashi ya mutu dole
kema asan yaddaxa'ayi idan bangaren gidanku
zaku siyarmin to,idan ma wani zaku siyarwa dai
duk daya ki karbi kudinki ki kada 'ya'ynki ku
koma can Tawa localgobernment grinku. Ba zaku
zo ban haife ku bakusamun hawon jini tunda kun
hallaka mazan nakuni dai ku kyale ni. Washe gari
da sassafe su hnnasuka tashi suka hu aiyukan
gidan,bayn sun gaamsuka leka ko ina basu ga
inna haule ba ta shiga makwabtasai suka debi
bokitansu suka cewamasa'ud dan gidan indo in
inna tazo yace mata suntfi deboruwa . A tamfar.
Maikyau hanna ta daurabasu tsaya a ko ina ba
sai a fada wajen taro, sunmadanmakara don ynzu
tar da rabi wjen taro, sunmadan mkra don ynxu
tara da rbi tayi suka ajiye bokitansu a lungu
sukaje wajen taron matr ta. KalliHanna tyi
murmushi tace hanna ke muke jira kifarakiran
sunaye in rarraba muku kudin . Hanna tagaisheta
faram faram da fara'a sannan ta krbitakardar ta.
Fara kirn suna tace Hanna abubakariman ce ta
farko, matar tace to ki kira sunayen daya bayan
daya suzo subi layi sai kwai in dingamimmika
musu kudin a layi Hanna ta fara kirnsunayen,
kowace tan zuwa tana shiga layi kamaaryadda
sunayen suke a jikin takrdar,byn hanna
takammala kiran sunayen sai matr t mike tace
tomadalla Assalamu Alaikum jam'a su duka
sukace wa'alaikussalm tce ni sunana Haj Hindatu
umardaga kano state nigeria. Nazo nan grin mai
sunaDashi karkashin karamar hukumar mgarya
a.Janhuriyar niger don in kawowa 'yan uwana
matatallafi da taimako yaddamatan da suke da
mazasuke samun taimako daga wajen mazajensu
to ku da baku damazasai kusamu san'ar da
zakutaimakawa kanku da marayin 'ya'yanku.
Sukasatafi raf'-raf suna cewa Allah ya saka da
alheri mungode hajiya hindatu. Ta cigaba da
cewa dagagwannatin jihar kno matar maigirma
gwamanjihaar kano ta bude wta kungiya wacce
za'a dinga taimakwa matan da mazansu suka
rasu sukabarsu. Shine taga ya dace mu shigo
makwabciyarkasarmu Niger suma mu hada kai da
gwiwamutaimaka musu saboda Abunda yayi
nigeria

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login