Showing 15001 words to 18000 words out of 27521 words
batasan lokacin da Safwan din ya tafi ba don a Malasia dare baya yiwa mutane sai dai idan mutum ne ya gaji da zirga-zirga ya je ya kwanta.
Kwanaki uku tsakani Sadiq ya wuce Egypt, kwananshi ɗaya acan suka dawo tare da Rahama. Ranar kusan kwana suka yi suna hira irin ta ƴan uwa.
Washe gari da safe dukkansu ukun suka shiga kitchen dan haɗa breakfast, sosai Sadiq ke zaƙewa wajen baiwa ƙannen nashi kulawa.
Bayan sun gama breakfast ne kuma suka hau aikin gyaran cikin gida har zuwa farfajeyar gidan, gabaɗaya Zarah da Rahama sun yi kaca-kaca da ruwa sun jika ko ina wai suna baiwa fulawoyi ruwa har abun ya koma suna watsawa juna.
Yana daga ɗakinshi ya ke hangosu ta window, sosai ƙaunar da suke wa juna take matuƙar burgeshi musamman yadda yaga dukkansu suna baiwa alawar zuciyarsa kulawa, murmushi yayi mai sauti saboda wani abu da ya tuna. Safwan kenan.
Wuni suka yi ranar cikin nishaɗi da kulawa da juna, yadda suke nuna ƙaunar juna kowa ya gansu sai sun bashi sha'awa.
Kamar wacce aka yiwa baki tunda Zarah ta kwanta bacci bata tashi ba, kasancewar tana fashin sallah shiyasa Rahama bata tasheta ba lokacin sallar asuba.
Sai wajen ƙarfe goma na safiya ta farka, da wasu haɗaɗɗun greeting cards ta fara yin tozali, da hanzari ta miƙe saboda tunawa da ta yi yau ranar zagayowar haihuwarta, cards ɗin ta janyo guda uku ta fara karantawa cikin jindaɗi sai dai guda ɗaya ya matukar tafiya da ita kuma ga alama ya fi duka kyau da tsada, duba suna ta yi taga an rubuta SMH bata gane ko na wanene ba tunda na Sadiq da Rahama duk sun saka sunansu bata wani damu ba ta miƙe ta nufin zuwa toilet, idonta ya sauka akan dressing mirro wani kwali ta gani dan haka ta yi saurin isa ta buɗe shi, wata haɗaɗɗiyar arabian gown ne a ciki kalar pink mai matuƙar kyau dai wani takalmi golden.
Da hanzari ta shiga bayan gida ta watsa ruwa ta fito dan tasan ƴan uwanta na jiranta.
Simple makeup ta yi a fuskarta sannan ta saka doguwar rigar wacce ta mata kyau matuƙa, veil ɗin rigar ta naɗa akanta sannan ta nufi falo.
Da alamun mamaki a fuskarta ganin falon gabadaya duhu mamaye shi, bata gama mamakin ba kuma haske ya gauraye falo ta re da suwar happy birthday to you, ido ta waro tana kallon mutanen falon cikin mamaki harda maƙotansu da matayensu, tuni ta ƙara rudewa ganin Jiddah da Saleem a gefe ɗaya, hawayen da ake kira na farin ciki ne ya sauko a fuskarta. Da sauri Rahama ta zo ta ja ta zuwa gaban tebur din da aka aje ƙaton cake kalar pink da fari, hannun ta kai da nufin yankawa Rahama ta yi saurin riƙe hannun, kallonta ta yi da alamun tambaya bata amsa mata ba sai ma zura hannayenta da tayi ta rufe mata idanu, kusan sakan goma sannan ta buɗe mata, sai da ta razana saboda abinda ta ga ni ta kuma ji, Safwan ne a durƙushe gabanta riƙe da ɗan ƙaramin akwati na zobe yana faɗin
"Will you marry me (Shin zaki iya aurena)"
Sam ta rasa a wata duniyar ta ke ciki, tana fata idan mafarkine ta yi gaggawar farkawa, kallon gefe da Jiddah ke tsaye ta yi, gira ta ɗaga mata tare da kashe ido ɗaya sannan ta rungumo Saleem a jikinta. Abin yaso baiwa Zarah dariya matuƙa yadda Jiddan ke yi kamar za'a kwace Saleem din.
Bata san ya akayi ta gyaɗa kai ba sai ji tayi kawai an zura mata zobe a hannu.
Tafi suka yi gabaɗaya sannan ne ta yanka cake ɗin.
Ƙaramin shagali suka yi sannan kowa ya watse sai su Jiddah da zasu wuce Dubai da daddare ita da Saleem zasu je siyayyar haihuwa.
Cikin ƙanƙani lokaci soyayya mai ƙarfi ta ƙullu tsakanin Safwan da Zarah, har wani lokacin suna mamakin junansu ta yadda basa iya ɗaukan awanni ba ta re da sun ji muryar juna ba, idan suka zauna hira kuwa da ƙyar Sadiq ke lallaɓa Safwan ya tafi gida ya kwanta idan dare ya yi, da ya shiga gida kuma zai kirata su ɗaura daga inda suka tsaya.
Harta su Daddy sai da suka san da batun soyayyar nan domin Safwan dai ya yi wa Abbansa maganar Zarah inda shi kuma ya aika Waziri da wasu wakilansa har garin Gombe su ka tambayowa Safwan auren Zarah tare da bada kuɗin nagani inaso da goron tambaya kamar yadda ya ke a al'ada ya tanadar.
Yau ma kamar kowani lokaci a ƙarshen mako sukan wuni tare ne harta ayyukan gidan tare suke yi, su na yi wani lokacin Sadiq na tsokanar Safwan mijin Hajiya, don shi Sadiq ba shi da wani girman kai irin na Yayu akan ƙannansu musamman idan su na soyayya da abokansu, ya na zama su yi hira sosai wani lokacin idan su ka yi faɗan masoya ma shi ya ke sasanta tsakaninsu idan bayanan kuma sai a kira Rahama ta video ta shirya tsakaninsu.
Yana zaune saman durowar kitchen ita kuma tana gaban fanfo tana wanke-wanke, hirarsu su ke yi cikin nishaɗi kamar waɗanda suka ɗauki tsawon shekaru su na soyayya. Tufa ɗin da ke hannunshi ya gutsira sannan ya ce
"Mrs. Safwan kinsan me ya sa ban takura anyi auren nan da wuri ba.?"
Ba ta re da ta juyo ba ta ce
"Sai ka fada"
"Saboda inaso ki gama ƙarasa wannan karatun don idan na aure ki nasan ba zaki nutsu ki yi karatun nan ba saboda yadda zan ruɗa ki da salon soyayyata sai kin daina fahimatar kowani zance idan ba nawa bane."
Dariya ta yi sannan ta juyo ta naɗe hannayenta a ƙirji tana kallon shi ta ce
"Saboda ina da ƙaramar kwakwalwa koh.?"
"A'a saboda soyayyar da zan nuna miki ta musamman ce kina buƙatar cikakkiyar nutsuwa don fahimtarta."
"Toh Allah ya kaimu lokacin yasa kada ka canza abinda ka fada."
"Bazan canja ba saboda ina miki ƙaunar da bana yiwa kowa irinta a duniyar nan."
"Uhmm" ta ce cikin murmushi sannan ta juya ta cigaba da wanke-wanke suna hira har ta gama ta gyara gurin.
Sai a lokacin ya sauko daga inda ya ke zaune ganin ta fara hada-hadar ɗaura abincin rana, kamar ko da yaushe idan yana nan yakan taya ta da ƙananun aiyuka kamar su yanka albasa, fera dankali, bare maggi da sauransu a haka har su gama girkin.
A haka Sadiq ya zo ya tarar da su a kitchen ɗin ya kalli Safwan ya ce
"Mijin Hajiya zo ka min wani aiki a falo."
"Haba babban Yaya baka ga ina taya ta aiki bane." cewar Safwan.
"Little ba shi umarni kinji abu zai min mai mahimmanci."
Dariya Zarah ta yi ta ce
"Ba ni na riƙe shi ba fa, jeka ta ya shi aikin mana"
Hannunshi Sadiq ɗin ya kama su ka fice ta re suna dariya.
Haka kullum suke kasancewa cikin farin ciki yayinda soyayyarsu ke da ɗa ƙaruwa.
Kwanci tashi asarar mai rai a haka kwanaki ke shuɗewa har suka zama watanni.
NIGERIA
A watannin da suka biyo baya duk wanda ya kalli M.J zai gane hankalinshi ba'a kwance ya ke ba gabaɗaya ya rame ya yi baƙi, abubuwan da Hajara ta ke masa ya ƙaro musamman yanzu da take ɗauke da juna biyu babu kalar fitsarar da bata yi mishi idan ya nemi ya tanka sai ta yi iƙirarin zata zubda ciki, gashi Allah ya ɗora mishi son cikin sosai musamman da su Daddy su ka sassauta mishi tunda suka ji labarin Hajaran na ɗauke da juna biyu, a gefe guda kuma tunanin Zarah da ke addabar zuciyarsa duk yadda ya so dainawa amma ya kasa nan ya fahimci cewa sonta ne ya mishi mugun kamu sai dai yana ƙoƙarin ɓoye hakan don har a wannan lokacin bai daina zargin cewa tana bin maza ba musamman idan yayi la'akari da yadda ya ganta a hotel ta re da wanda ba muharraminta ba.
Yana zaune a office ɗinshi cikin tunanin da ya saba ya ji ana kwankwasa kofar shigowa, umarni ya bada aka shigo sakatariyarsa ce riƙe da takarda a hannunta ta ce
"Yallaɓai wannan saƙo ne aka kawo ance a baka."
"Daga wanene saƙon?"
"Bai fada ba yallaɓai ya ce dai a baka ne yana sauri zaku yi waya."
Kan tebur ɗin ya nuna mata ta ajiye daga haka ta fice, hannun ya zura ya janyo takardar ya buɗe, wata irin zabura ya yi tare da miƙewa tsaye daga zaunen da ya ke.
Zufa ce ta karyo masa lokaci guda wasu hawaye masu ɗumi suka sauko daga idonshi, sambatu ya fara yana kiran sunan Hajara. A haka Abdallah ya turo ƙofar ofishin ya shigo ya same shi cikin wannan yanayi, a kiɗime ya ke tambayarsa abinda ya faru. Bai iya magana ba illa takardar da ya miƙa mishi cikin zubda hawaye.
"Innalillahi wa inna ilahi raji'un." shi ne abinda Abdallah ke maimaitawa bayan ya karanta abinda ke cikin takardar...✍🏻
*BY*
*JASMINE🌸🌸*
*ASP ZARAH*👩✈️
*BOOK 2*
*Page 10*
Fuska ba walwala ya ɗaga ido yana kallon M.J dake dube-dube a kan tebur ya ce
"Me kake nema ne haka.?"
"Abdallah gidan zanje naji ba'asi wallahi yau kome za'ayi sai na ci mutuncin Hajara a garin nan."
Duk da suna cikin wani hali amma hakan bai hana Abdallah dariya ba ganin yadda gabaɗaya M.J ya birkice yana neman key ɗin mota bayan ga key din nan a gefen tebur amma tashin hankali bai barshi ya gani ba, kai ya kaɗa sannan ya ce
"Muje na sauke ka a yadda kake din nan bai kamata kayi tuƙi ba."
"Muje muje Abdallah."
Fita suka yi M.J a gaba tamkar zai tashi sama, a haka suka shiga motar Abdallah ya tada suka ɗauki hanyar zuwa gidan M.J din, Abdallah ne ya kalleshi ya ce
"M.J ya akayi haka ta faru har yake ƙoƙarin maka ka a kotu.?"
"Bansani ba Abdallah, innalillahi wa inna ilaihi raji'un, a gidana ace har matata na ɗauke da cikin wani amma bansani ba. Wallahi sai yanzu na tuna sam bai kamata ace cikina bane don yanzu ne cikin ya shiga wata uku kuma rabona da ita na jima sai lokacin da aka ce tana da cikin nan sam zumuɗi bai barni nayi lissafi ba." M.J ya fada idonshi na zubar da kwalla.
"Ishara ce Allah ya nuna maka Jawwad shiyasa ake so mutum ya dinga kyautata zato akan ɗan uwansa."
"Me kake nufi ne.?"
"Abubuwan da kake zargin Zarah da su ne Allah ya tabbatar maka akan matarka."
"Ba zarginta nake ba tabbatarwa nayi."
Murmushi Abdallah ya yi wanda iyakarsa baki sannan ya ce
"Rana na tafe, sai dai kamar yadda nayi alƙawari duk randa ka gane gaskiya kada ka neme ni don taimaka maka. Yanzu ya za'ayi da batun Hajara.?"
"Abdallah zanje na tuhumeta sai ta faɗa gaskiya matuƙar da aurena ta ke bin wasu mazan wallahi sai na rabu da ita bayan na wulaƙanta ta, har ni za'a turowa takardar sammaci zuwa kotu akan bana kula da cikin da wani ƙato yayi har ana ikirarin idan wani abu ya same shi sai anyi shari'a da ni."
"Uhmm" kawai Abdallah ya ce daidai lokacin da yayi horn a gaban gidan M.J mai gadi ya buɗe masa ya shiga da motar, ko parking bai gama tsaidawa ba M.J ya fita a sukwane yana faɗin
"Jirani ina zuwa."
Rai ɓace ya shiga falon ganin bata nan ne yasa ya nufi hanyar ɗakinta, a fusace ya banka ƙofar ɗakin.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ya shiga maimaitawa, tashin hankali da ba'a saka masa rana, Hajara ce da wata babbar mata a kwance kan gado haihuwar uwarsu suna aikata masha'a. Sulalewa yayi a ƙasa ya rasa ma abinda zaiyi, sai lokacin suka farga dashi da hanzari suka miƙe matar ta rarumi kayanta zata gudu aikowa ya miƙe ya rufe ƙofar ɗakin sannan ya koma ya zauna, sun ɗau mintuna a haka lokacin duk sun maida suturunsu miƙewa yayi ya kwance belt ɗin da ke jikinshi ya shiga dukansu ba ji ba gani tun suna ihu da neman taimako har muryarsu ta daina fita, sai da ya tabbatar sun galabaita sannan ya tsagaita cikin fushi ya ce
''Kinci amanata Hajara wallahi yau bazan barki ba sai kin gayamin abinda na miki har kika nemi ƙuntata min haka, dama badan Allah kika aureni ba. Bayan zina har ƴan uwanki mata kike bi, ke kuma ki tashi ki ficemin daga gida tun kafin na halaka ki."
Da mugun sauri ta miƙe ta bude ƙofar ta fita, karo suka yi da Abdallah wanda tun sanda suka fara ihu ya jiyo su shine ya shigo dan ganin abinda ke faruwa, sai yanzu da M.J ya yi magana ya fahimci dalilin dukan na su. Kaɗa kai ya yi cike da takaici ya shiga ɗakin don fito da M.J kar ya yiwa Hajara wani illah.
Da ke Hajara matsoraciya ce gashi kuma ta ji jiki a hannun M.J tuni ta fara sakin zancen da batasan tana furtawa ba, tiryan-tiryan ta labarta mishi dalilin da ya sa ta aureshi har zuwa ranar da aka zo har gida aka duki Zarah, ashe da ita aka haɗa baki ta buɗe musu ƙofar falon dan ta kasance automatic ne ba da key ake buɗewa ba. Cikin kuka ta cigaba da cewa
"Ni bansan me ta yi musu ba, kawai sun same mu ne suka faɗa mana cewa ta yaudari wani da ke musu aiki har tayi sanadin da aka kamashi a garin bauchi shiyasa suke son ɗaukar fansa. Sai daga baya na fahimce cewa Diamond suke son karɓa a wajenta shiyaaa aka haɗa baki da ni don idan ta bayar nima a bani wani kaso a ciki."
Rigiji gabji! A yau Jawwad ji yayi ya fi buƙatar mutuwarsa saboda yadda yake jin zuciyarsa na suya tana barazanar fitowa a ƙirjinsa, tabbas bai cacanci yayi farin ciki ba a rayuwarsa a yadda ya ɗau tsawon lokaci yana ƙuntatawa marainiya.
Sai yanzu abubuwa suka fara dawo mishi dalla-dalla, a lokacin daya dawo daga ƙasar waje gabaɗaya sanda zai fara aiki a _M.J JEWELS_. ya tambayi Daddy diamond ɗin da ya siya a hannun turawa sai dai bai bashi cikakkiyar amsa ba sai cewa da yayi
"Son waɗannan Diamonds ɗin suna hannun wacce duk rintsi duk wuya nasan bazata taɓa bari su salwanta ba saboda tsananin ƙaunata da take yi da kuma riƙon amana da gaskiya da ta ginu akai."
A lokacin da Daddy ya faɗa mai haka yayi tunanin Momi aka baiwa ajiya ashe Zarah ce, sam a lokacin bai kawo ta cikin tunaninsa ba sai yanzu da Hajara ke mai bayanin nan. Wani abu da ya kuma zuwa tunaninsa shine batun Hajara da ta ce Zarah ta yaudari wani an kamashi a hotel a jihar Bauchi, kardai abinda ya fara tunani ya zama gaskiya.
Cikin zare ido ya kalle Hajara dake ɗar-ɗar ya ce
"Kince ta kama wani a Bauchi wane ne wannan."
"Bansan shi ba nidai kawai sunce min wai ta yaudareshi akan zata bishi hotel su kwana tare ashe shi baisan cewa ƴar sanda bace bayan sunje ne ta ga hodar iblis dama suna zarginshi shine ta kira jami'an da suke tare aka tafi dashi."
"Ya Hayyu Ya Qayyum" abinda M.J ya shiga maimaitawa kenan don ya riga da ya tabbatar da abinda yake tunani, sun jima cikin wannan yanayi Abdallah na daga tsaye a ƙofar ɗakin yana Hamdalar yadda zargin Zarah dake zuciyar M.J ya fara wankuwa a hankali.
"Ki tafi na sake ki saki uku Hajara, dama cikin jikinki ba nawa bane dan haka ki tattara ki ficemin daga gida, kuma ina tabbatar miki iyayen wanda kika cuta zasu tsayawa ƴarsu har sai an hukuntaki akan abinda kika aikata."
Kuka ta fashe dashi, zata fara roƙonshi ya dakatar da ita ta hanyar faɗin
"Kada ki kuskura don wallahi idan kika ƙara koda minti biyar ne a cikin gidan nan sai dai a fice da gawarki."
Ba shiri ta miƙe mayafi kawai ta iya ɗauka ta fice daga gidan.
Hannun M.J Abdallah ya kamo suka dawo falo inda ya bashi ruwa mai sanyi yasha sannan ya fara maimaita mishi kalmar innalillahi wa innailaihi raji'un. Kusan mintuna talatin sannan ya miƙe yace Abdallah ya kaisu gidan Daddy, kallo ɗaya zaka mishi ka tabbatar yana cikin matsananciyar damuwa saboda yadda jijiyoyin kansa suka tasa fuskarsa tayi jajir ga idanunshi har sun kumbura. Babu musu Abdallah ya mike suka fita yaja mota suka bar gidan, dake tsakaninsu akwai ƴar tazara yasa tun suna tafiya shiru har M.J ya nisa ya ce
"Abdallah kaji ashe ganin da muka yiwa yarinyar nan a hotel aiki ne ya kaita kamar yadda ka daɗe kana faɗa."
"Na daɗe da sanin haka ai." Abdallah ya fada kanshi akan hanya batare da ya waiwayo ba.
Cikin mamaki M.J ya kalleshi ya ce
"Amma shine baka taɓa fadamin ba Abdallah."
"Eh saboda naga kai ba mutum bane me yarda da mutane." Nan Abdallah ya labarta mishi abinda ya faru a waccan ranar lokacin daya tambayi wannan saurayin.
Abin mamaki sai ga M.J yana zubar da hawaye yana faɗin
"Meyasa baka gayamin ba, kabarni ina cutar baiwar Allah meyasa Abdallah."
Sauka akan hanya Abdallah yayi sannan yayi parking ya kashe motar ya juyo ya kalli M.J yace
"Na ɗauka idan anyi muku aure zaka nutsu sai naga ba haka bane, ba wannan ba ma saurari wannan kaji." ya ƙarashe faɗa yana danna wayarshi, sai kuwa ga muryar Baaba rangaɗau na fitowa a wayar da alama recording akayi bata sani ba.
"Audullahi ina sane da duk abubuwan dake faruwa a gidan Muhammadu, kasan Zara'u bata da wata abokiyar shawara da ta wuce ni, na dade da sanin cewa yana zarginta da aikata zina idan ta fita aiki. Wallahi duk da batare muke fita ba ko Qur'ani aka bani zan dafa nayi rantsuwar cewa Zara'u bata taba ko da tunanin aikata wani abu da bai dace da wani ba, nasan cewa tana yin basaja don kama masu laifi idan sun kasance masu neman mata. Sau da dama tana zuwa nan ta sameni akan ajiye aikinta saboda zargin da yake mata ni nake hanata, ba gori zanyi ba amma Zara'u ta bada rai da lafiyarta don kare dukiyar mahaifinsa. A sanadin wannan dukiyar ne akayi asaran rayuka takwas. Ita fa iyayenta biyu ta rasa, kasan zafin da mutum yake ji idan ya rasa iyayensa kuwa kuma a lokaci guda sannan ƴar uwarta da