Showing 18001 words to 21000 words out of 27521 words

Chapter 7 - Asp Zarah Book 2 Hausa Novel Complete

Unknown   

01 Jan 2025

111

zata lallasheta ta rasa hankalinta, amma duk da haka bata karaya ba ta cigaba da tsaron wannan kadara. Da ace zan shaida maka irin halin da ta shiga a waccan lokacin sai ka zubda kwalla amma duk da haka bata birge Muhammadu ba shi burinsa a kullum yaga ya ƙuntatawa rayuwarta duk da kasancewarta marainiya, ina sane da abinda ke faruwa da ita haka ma iyayensa duk sun san irin ƙuntatawar da ɗansu ke mata saboda na shaida musu duk da Zara'u ta gargaɗeni akan hakan, a ranar da mahaifiyarshi taji wannan batun da ba dan ni ba sai tsinuwarta ta tabbata akanshi, ni na hana hakan. Na so ace kafin rabuwarsu mu'amala ta aure ta shiga tsakaninsu don ya tabbatar da zargin da yake mata ba gaskiya bane amma hakan bai tabbata ba sai gashi daga ƙarshe ma ya mata saki irin na wulaƙanci. Ko ba yanzu ba Audullahi ko da ƙasa ce ta rufe mana idanu na tabbata sai Muhammadu yayi nadamar abinda ya aikata don laifine me girma ƙuntatawa maraya."

Ƙitt! Abdallah ya kashe wayar batare da ya kula da yanayin da M.J ke ciki ba ya ɗora da cewa

"Tun ranar da muka fara ganin Zarah a Abuja naji ta burgeni matuƙa musamman yanayin shigarta, idan baka manta ba bayan na ajiye ka a gida a waccan ranar na fita naje adireshin da muka ji Zarah na fada a waya, ba wani abu ya kaita ba wata abokiyar aikinta ce ta ɗauka suka wuce gurin wani taron ƙarawa juna sani da ake gudanarwa ba kamar yadda kayi zargi ba, ina wajen har sanda aka karramata na musamman a matsayin wacce ke baiwa ƙasa babbar gudumawa akan tsaro, na so kwarai na karɓi lambarta sai kuma kiranka ya shigo wayata na tafi da niyyar zuwa na dawo kuma muka tafi wani gurin, a ranar da muka ganta a hotel a bauchi kuwa ban bar wajen ba sai da na tabbatar ba abin banza ya kaita ba. Na barka ne kayi aiki da hankali da kanka sai gashi ka kasa. Dawowata ƙasar nan da banga Zarah a gidanka ba shine naje har wajen Baaba muka yi wannan hirar batare da na bari tasan ina ɗaukar muryarta ba."

Kuka wiwiii! M.J yake yi tamkar ransa zai fita har numfashinsa na ɗaukewa yana dawowa, rarrashinsa Abdallah ya fara yi yana gayamasa kalamai masu tausa zuciya ya ce

"Ba kuka ya dace kayi ba M.J tsawo lokacin nan kana ɗauke da zunubai manya akanka kamata yayi ka godewa Allah da ya ganar dakai tun waɗanda kayiwa laifin suna numfashi ta yadda zaka iya neman yafiyarsu. Zargi zunubi ne ko da ya kasance gaskiya, kaga a sanadinshi kayi manyan laifuka da har Allah ma yana fushi da kai, kayi zargi sannan ka ƙuntatawa marainiya ta hanyar hakan zunubi ne babba domin Allah yana fushi da duk wanda zai cuci maraya komin ƙanƙantar cutar, sanadin zargi ka saka iyayenka suna fushi da kai musamman mahaifiyarka da har tayi iƙirarin tsine maka wallahi kana cikin uƙuba da fushin Allah bazai taba dubanka da rahama ba harsai ta daina wannan fushin da take yi da kai. Tun farko sai da na gaya maka ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba amma baka ji ba yanzu wa gari ya waya kaine. Don haka tun wuri kaje ka nemi yafiyarsu."

"Wallahi Abdallah nayi dana sanin ƙin bin shawarwarin da kake bani tun farko gashi na saka kaina a halaka, gaskiya tsohuwar nan ta faɗa da tace sai nayi nadama kuma sai naga sakayyar abinda nayi, wallahi tun ranar dana furta kalmar saki ga Zarah Allah ya ɗaura min ƙaunarta tun ina ƙoƙarin kauda hakan a zuciyata har na fahimci cewa na kamo da sonta sosai. Bansan ya zanyi ba Abdallah ka kaini gurin iyayena na nemi gafarar su." ya ƙarashe maganar yana rushewa da kuka.
Sosai tausayinshi ya kama Abdallah don ya hango alamun nadama sosai a tattare da shi don haka ya kunna motar suka cigaba da tafiya, mintuna kaɗan suka iso gidan mai gadi ya buɗe musu gate suka kunna kai. Batare da ɓata lokaci ba suka fito don nufar babban falon gidan, tun kafin su ƙarasa suke jiyo muryar Baaba da alamu tana cikin nishaɗi don har dariya take ƙyakyatawa.
Da sallama suka shiga turus M.J ya ja ya tsaya saboda abinda yaji kuma ya gani...✍🏻

Uhmm lallai tsugunne bata ƙare ba Muhammad Jawwad angon Hajara.😅😅😅


*BY*
*JASMINE*🌸🌸


*ASP ZARAH*👩‍✈️

*BOOK 2*

*Page 11*

... Baaba ya gani kwance akan doguwar kujera sai Laptop kunne akan center table, cikin laptop din kuwa hoton mutane biyu ne wanda ya tabbatar musu video call take yi da wasu, sai dai abinda ya sanya M.J shiga ruɗu shine batun da yaji Baaba tayi na cewa

"Idan kaga ba zaka iya hakura da rashin ganinta ba ka biyo ta kawai kuzo tare idan kun gama hoton sai ku koma, ita ma nasan saboda kai ne take faɗin ba zata zo ba."

"Toh Baaba ai yanzu tare zamu taho." Safwan kenan dake zaune a kujera kusa da Sadiq suna video call da Baaba. Zarah ce ta ɓullo riƙe da kofi a hannunta wanda ke cike da fresh milk ta zo saitin computer din tana miƙawa Safwan tana faɗin

"Sweetheart ga shi kasha ka rabu da tsohuwar nan ba zata barka ka huta ba idan ta fara surutu." ta ƙarasa tana fuskantar Laptop din har da muguɗawa Baaba baki.

Tari mai ƙarfi ne ya sarƙafe M.J dake tsaye ƙiƙam kamar an dasa sa, sai a lokacin Baaba dake kishingiɗe ta miƙe tana faɗin

"Subhallahi me ya faru Muhammadu ai banji shigowarku ba ma."

Abdallah ne ya riƙo shi suka ƙarasa cikin falon ya zaunar dashi acan kujerar gefe ta yadda bazai iya ganin komai a cikin laptop din ba sai bayanta da yake gani kawai, hannu yasa ya dafe saitin zuciyarsa da yake ji tana barazanar fitowa, sosai ya yi mamakin irin canjawar da Zarah tayi ta zama kamar wata balarabiya musamman yanzu da ta yaga tana sanye da arabian gown sannan ta rolling kanta da veil din rigar, fatarta sai sheƙi take yi kamar a taɓa jini ya fito, ganinta ya faranta mishi da farko sai dai batun da tayi wa Safwan ya matuƙar ɗaga mishi hankali musamman da yaga irin kallon da suke wa juna hankalinshi yayi masifar tashi kar dai ace su Daddy aurar mishi da Mata suka yi, abinda yayu sanadin tarin nashi kenan.

"Sannu ɗan nan bari na kawo maka ruwa." cewar Baaba tana nufar hanyar kitchen, dawowa kuma tayi da hanzari ta isa gaban laptop din tace

"Zara'u ku kashe na'urar nan zanyi wani abu yanzu Muhammadu ne ba lafiya."

Baki Zarah ta taɓe dan ita har ga Allah ta manta da M.J kwata kwata a rayuwarta sai yanzu da Baaba tayi maganarsa, ko meke damunsa oho

"Toh" ta amsawa Baaba, da sauri Safwan ya ce

"Subhanallahi waye haka Baaba.?"

Shi kam Sadiq tunda Baaba ta ambaci sunan M.J ya mike ya bar Falon ya shige ciki.

"Ai ɗan uwar matarka ne shine ma mij.." bata ƙarasa ba saboda tarin daya kuma sarƙafe M.J wannan karon har yana faɗowa daga kan kujerar da yake, da hanzari ta nufi kitchen ta ɗauko ruwa daidai lokacin kuma Momi ta fito, dama suna zaune ne da Baaba su hira da su Zarah kiranta da akayi a waya ne ya sata miƙewa ta shige ciki.
Da sauri ta ƙarasa inda Abdallah ke riƙe dashi tana tambayar meya faru, bai kula da yanayin ciwo da yake ciki ba da kuma suya da ƙirjinsa ke masa tamkar a tsaga a saka mishi ƙanƙara, saukowa yayi ya riƙe ƙafar Momi lokaci guda kuma ya fashe da kuka mai taɓa zuciyar duk wani me sauraronshi, sosai yake kukan yana faɗin ta yafe mishi.
Tsakanin uwa da ɗa aka ce sai Allah, tuni tausayin ɗan nata ya kamata taji kamar hawaye zasu zubo mata amma ta kauda kai sannan ta kwace ƙafarta tayi tsaki ta ce

"Sakeni dan Allah, sai yanzu kasan da cewa kamin kuskure har kake nema na yafe ma ka toh bazan yaf..."

Salatin da Baaba tayi ne yasa ta kasa ƙarasa wa sakamakon M.J da ta gani kwance a ƙasa riris ba alamun motsi a tattare da shi, salati ta doka sannan ta tsugunna tana jijjigashi cikin tashin hankali.
Baaba ce ta kalli Abdallah da tsantsar tausayin abokin nashi ya sashi zubda hawaye ta ce

"Audullahi ɗauke shi mu tafi asibiti."

"Babu inda za'a kai shi yana nan a gida." Daddy da tun ɗazu yake tsaye a ƙofar shigowa yana kallonsu ne yayi wannan maganar. Ƙarasowa yayi cikin ya isa har gaban Baaba ya ce

"Ke mahaifiyace a gareni ban taba neman alfarma a gareki kin hana ba dan Allah karki dakatar dani daga abinda nayi niyya."

Faɗan da yafi ƙarfin ka aka ce maida shi wasa, don haka Baaba bata kuma tankawa ba ta nufi hanyar ɗakinta duk da tana tausayin M.J amma can ƙasar zuciyarta tana murnar sakayyar da ya fara gani, shima Daddy hanyar ɗakinsa yana faɗin
"Ban yarda ki zauna a inda Jawwad yake ba." daga haka ya shige, itama Momi miƙewa tayi tabi bayanshi fuskarta na zubar da hawaye.

Matuƙar tausayin M.J ne ya cika zuciyar Abdallah, jiki ba kwari ya miƙe ya ɗauki ruwan da Baaba ta ajiye a center table ya watsa mai a fuska, cikin sa'a ya ja wata doguwar ajiyar zuciya irin na wanda ya farfado daga suma. Miƙewa yayi zaune yana ƙara fashewa da wani sabon kukan duk da rarrashin da Abdallah ke mai amma bai dakata ba, dan haka ya barshi ya cigaba da kukan har yayi mai isarsa, a lokaci anfara kiraye kirayen sallar magriba dan haka suka mike don zuwa masallaci.
Sai da suka yi sallar isha'i sannan suka kuma nufowa gidan.
Sai da aka kai ruwa rana kafin Daddy ya sauraresu, nan Abdallah ke basu labarin abinda Hajara ta aikata, Momi kam taso a kama Hajara a kulle amma Daddy ya ce yanzu abu ya wuce ba za'a tada shi ba. Daƙyar da siɗin goshi suka yafewa M.J laifukan da ya musu sannan Daddy ya jadda mishi cewa lallai ya samu Zarah ya nemi gafararta idan ba haka ba kowa rayuwarshi tana cikin haɗari.
Abu da mai neman kuka jin Daddy ya ambaci sunan wacce yake muradin gani yasa yayi ta taɓa Abdallah kan ya tambayi Daddy inda Zarah take, gyaran murya Abdallah yayi sannan yace

"Emm Daddy ko za'a gaya mana inda ita Zarah take sai muje har can mu bata haƙuri. Bayan haka kuma muna so a sasanta inda rabo ta koma gidanshi."

"A sasanci me Abdallah?" Momi ta faɗa a firgice harda dafa ƙirji kamar wacce taga mugun abu.

Kai M.J ya sunkuyar shi kuma Abdallah ya fara sosar kai.
Murmushi Daddy yayi sannan ya ce

"Ai Zarah ba bare bace duk inda take ma ai zata dawo gida idan tazo sai ya nemi afuwarta, sannan maganar sasantawa banaso na ƙaraji dan babu aurenshi akan Zarah maganar da akeyi yanzu ma ƙarshen satin nan za'a kawo sadakinta daga masarautar Yola dan ɗan sarki ke nemanta na daɗe da bashi umarnin hira saboda sun kawo kuɗin nagani inaso. A taƙaice dai a janye wannan maganar banson kuma jinta kunsan babu kyau neman aure akan aure".

Daga haka Daddy ya sallamesu, M.J ji yayi gabaɗaya duniyar ta mishi zafi, Allah ba azzalumin bawanshi bane, a yanzu yana ji a ranshi lallai idan ya rasa Zarah ba zai iya cigaba da rayuwa ba.

A haka ya tattaro kayansa gabaɗaya ya dawo gidansu ya tare a tsohon sashinsa. Yawan rashin lafiya da yake fama da ita musamman ciwon ƙirji da matsanancin ciwon kai ne yasa ya yanke shawarar zuwa asibiti don duba lafiyarshi.
Gwajin farko likita ya tabbatar mai ya kamu da ciwon zuciya kuma ya kai matakin ƙarshe komai na iya faruwa da shi idan har bai kula ba, a haka likitan yayi mai gwaje-gwaje sannan ya bashi magunguna tare da shawarwari akan matakin da zai ɗauka na rashin sanya damuwa a rai. Da haka ya dawo gida.

Tsawon lokaci yana fama da jinya babu wanda ya sani sai Abdallah shima kuma ya hana ya faɗama kowa, haka yake fama da matsanancin ciwo, baya yin sati ɗaya cikakke batare da ciwon ya tashi ba saboda damuwa da ya sakama kanshi akan Zarah musamman yanzu da ya tabbatar tana gab da kubce masa. Yana galabaita sosai idan ciwon nashi ya motsa don aman jini yake yi sosai amma duk da haka bai sanar da kowa ba.

Watarana irin haka da ciwon nashi ya tashi lokacin yana gida a sashinsa, nan yayi ta aman jini har ya suma, a haka Abdallah yazo gidan ya same shi aikuwa bai ɓata lokaci ba ya sanarwa su Daddy nan aka ɗaukeshi zuwa asibiti hankali a tashe. Sosai Daddy ya ma Abdallah faɗa jin abinda likita ya faɗamai na cewa ya daɗe da cutar a jiki kuma suna zuwa karɓar magani.

Ko da ya nemi jin ba'asin ciwon daga gurin Abdallah kai tsaye ya shaida mishi cewa akan Zarah ne, duk da likita yace a nemowa M.J abinda yake so amma sam Daddy yace baisan wannan zance ba indai akan Zarah yake wannan ciwon sai dai ya ce Allah ya jiƙansa da Rahama dan kuwa ba samunta zai yi.
Nan likita ya bada shawarar sai anfita dashi ƙasar waje anyi mai aiki don kuwa a yanzu zuciyarsa na gab da bugawa, abu na kuɗi nan Daddy ya fara shirye-shiryen fitar da M.J zuwa ƙasar India don ayi masa aikin zuciya.
Hankalin Momi da Baaba ya tashi sosai jin abinda ya samu Jawwad din nan Daddy yayi ta tausarsu daƙyar ya samu suka ɗan kwantar da hankali.

*****************************

Duk yadda Zarah taso dawowa Nigeria hutu abun ya faskara saboda jarrabawar ƙarshe da zatayi don haka dole ta zauna ta fuskanci karatunta dan fitowa da sakamako mai kyau, watanni uku kaɗai suka rage mata ta gama wannan course ɗin mai mahimmanci dan haka tana buƙatar ta ƙara ƙaimi. A gefe guda kuma soyayyarsu da Safwan na ƙara ƙarfi sosai ta yadda har mutane na mamakin irin son da suke yiwa juna dan basa iya ɓoyewa ko a gaban wa suke.
Maganar aurensu tayi nisa dan har ankai sadaki kamar yadda Daddy ya faɗa sannan a tsaida ranar aurensu watanni huɗu masu zuwa, kenan wata ɗaya bayan Zarah ta kammala karatun da take yi a yanzu.

Ammi kuwa tunda aka saka ranar auren ta ɗauko mai gyara guda tun daga Maidugurin Nigeria ta kaita har ƙasar Malasia don gyara mata ɗiyar ta ta. Ai kuwa kwalliya ta biya kuɗin sabulu dan a cikin satin kafin Ammi ta wuce Egypt ita kanta ta yaba da irin canji da ta fara gani tattare da Zarah don haka gargaɗi matar akan kada ta bari Zarah da Safwan su dinga yawan haɗuwa gudun aikin shaiɗan. Da haka ta musu sallama ta wuce Egypt.
Gyara sosai Matar mai suna Hajiya Jamila keyiwa Zarah lokaci ƙanƙani ta koma tamkar wata baturiya ko balarabiya saboda tsananin kyau da sheƙi da take fitarwa.

Duk wani shiri na fitar da M.J ƙasar waje an gama shi, inda abokinshi na kwarai Abdallah yace dashi za'ayi tafiyar dan ya dinga kula da shi. Sati na zagayowa suka ɗaga zuwa ƙasar India, sai dai kafin tafiyarsu Daddy ya kira Sadiq ya shaida mishi halin da ake ciki, sosai Sadiq ya tausaya mishi sannan yayi mai fatan samun sauƙi sai dai bai faɗawa Zarah ba, ko meye dalili oho.
Dake sun riga sun gama komai ta internet yasa har airport motar asibitin ta zo ta ɗaukesu, babu ɓata lokaci kuma aka fara baiwa M.J kulawar likitoci, irin asibitocin nan ne da ba'a buƙatar masu jinya dan haka su Daddy na gama duk cukucukun asibitin suka nemi masauki dan hutawa.
Kullum sai dai su shirya su je da safe su dubashi su dawo sannan da yamma su ƙara komawa.
Satinsu ɗaya a ƙasar jikin M.J ya fara samowa dan har yana iya bude idon sannan yana motsi da jikinsa ba kamar a Nigeria ba da tunda ya suma bai ƙara motsawa ba saboda rashin isassun kayan aiki a ƙasarmu.
Kwanansu goma aka yiwa M.J tiyatar kuma cikin sa'a akayi lafiya ba tare da ansamu wata matsala ba sai dai fatan a kiyaye gaba. Sai da ya kwana tara cur! Kafin aka basu damar sake ganinsa kuma Alhamdu Lillahi yaji sauƙi sosai sai dai rama da ya yi. A ranar har video call sukayi da su Momi wanda tunda suka bar ƙasar kullum sai sun kira fiye da goma, har Ammi ma takan kira wajen sau biyar a kowacce rana don jin yanayin jikin Jawwad ɗin.
Wata ɗaya Daddy yayi a India ya tattaro ya dawo gida ya bar Abdallah don kulawa da M.J saboda shirye-shiryen bikin Zarah da za'ayi nan da watanni biyu da satikai ( Su Daddy manya kana namiji mai ya haɗaka da wani shirye-shiryen aure, kodayake ƴar so za'a aurar).
Kafin tahowarshi sai da ya zaunar da Jawwad ya mishi faɗa sosai tare da nasihohi sannan yace ya cigaba da neman zaɓin alkhairi a gurin Allah ya rabu da batun Zarah tunda dai ita Allah ya ƙaddara ba zasu sake zama da juna ba.

Kuma da alama nasihohi da tunatarwan da Daddy ya mishi sun shige shi don yanzu baya yawan tunani da sanya damuwa a rai sai dai sonta na nan danƙare a cikin zuciyarsa babu alamun zai ragu ko ya sassauta mishi.
Da haka suka yi sallama ya taho gida.

Sati uku tsakani aka sallami M.J nan suka tattaro suka dawo Nigeria da tsauraran ƙa'idoji da likitoci suka gindayawa M.J.

Alhamdulillahi jikinshi yayi sauƙi sosai a fili amma cikin ransa kam baiji sauƙi ba, wani lokacin yakan kulle kansa a ɗaki yayi ta kuka da nadamar abubuwan daya aikata ma Zarah gashi yanzu Allah ya bi mata haƙƙinta cikin lumana sai dai bai bari an fahimci halin da yake ciki ba duk da haka sai da Momi ta fahimta kuma ta tausayawa ɗan nata sosai, shiyasa duk abinda mutum zaiyi kada yasa son zuciya a ciki domin shaiɗan zai iya kaishi ya baro shi.


*******Duk da a gajiye take sosai amma hakan baisa can ƙasan ranta takejin daɗi sosai ba, saboda a yau ne ta kammala jarrabawarta na course din da aka turota

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login