Showing 6001 words to 9000 words out of 27017 words

Chapter 3 - Halin Rayuwa Book 2 Hausa Novel Complete

Sodangi   

28 Jan 2025

183

abin.
Su waye su Agogo? Ta sake bukatar sani, bai
ce komai ba sai da ta gaji da tambayar cikin
natsuwa ta soma yi cikin karaji da tashin hankali
sannan ya bata amsa ki tambayi Asabe tasan shi.
31
Da sauri Asabe ta daka mishi tsawa kai kul
kasa sunana a Cikin abin ku da waui ruba66en
bakinka.
Gaba daya kowa yayi shiru daga inda nake dai
ina jiwo mishin Sallau ba kuma san ba dadi ba ne
ya kawo hakan can cikin zuciyata kuma ina
tunanin Asabe da dan uwanta Sallau babu halin su
hadu wuri daya sai sun yi fada na tuna ni da Yaya
Dijah na ce to ko don mu ba mu da uwa ne yasa
muke son juna oho?
Zuwa can Sallau ya sake gajiya da tambayoyin
uwar ta shi ya ce, to in na gaya miki abinda yasa
Agogo suka yi min haka me za ki yi? Ba kin ce ko
sama da kasa zata hadu ba za ki daina dukan
Mairo ba, to wannan abinda a ka yi min ai ba
komai ba ne kan abin da ki ka ce, don haka gobe
ma ki sake dukanta.
Shawarar da na baki ba ki dauka ba ne yaja
min wannan wahalar gobe ma in kin sake za su
sake da har sun je sun kama mijin Babah Delu da
ki ke cewa wanki ne suka sake shi saboda ya gaya
musu babu abinda ya hada ku in ban da zaman
gidan baya, yanzu ma kuma bakwa tare don in sun
baki shawara ba kya dauka.
In ban da halin da Sallau ke ciki wata Rila da
Babah Lantana ta gwabe mishi bakinshi a dalilin

32
wannan bayanin nashi, nmaimakon haka kurma ihu
mai tsanani tayi, ta yi kuka irin na fitar hankali
bayan ta tambayi Sallau yanzu saboda wannan
shegiyar yarinyar a ka yi maka wannan azabar?
Bai musa ba bai ce mata uffan ba, to ai kuwa
ba zan daina dukantä ba, sai dai... kan ta karasa
taji ya ce mata to nuna min kawai inda dangin
ubana suke tunda shi kin ce min wai ya mutu in
dai da gaske ina da shi ai ba zai rasa dangi ba don
ni Babah Delu ta ce min duk abinda ki ke gaya
min kar..
Kan ya karasa tayi maza ta tarke shi da mari a
kan ciwon nashi, ni dama kashe ni kawai ki ka yi
da yafi min tunda dai duk wahalar da nake sha a
rayuwata ke ki ke ja min.
Wannan din ma ke ce na kuma san za ki sake ja
min wani tunda sun ce sau goma ki ka buge ta sau
goma za su rama mata a kaina, to ba gara kawai ki
nuna min in da ubana yake ba.
Ganewan da Babah Lantana tayi cewar
Mubarak ne yasa a ka yi wa danta irin wannan
matsanancin dukan duka kuma irin na rashin
tausayi, a matsayin kashe di mai karfi gareta kan
abin da take yi min na azabtarwa yayi matukar
tayar mata da hankali.
33

Ta rasa inda zata sa kanta taji dadi, don bakin
ciki ta rasa me zata yi ta dauki fansa kan wannan
abinda yayi mata? Tayi kuka tayi kuka har sai da
ta kwanta ciwo wanda ban taba ganin ta kwanta da
sunan ciwo ba sai a wannan lokacin.
Kwana biyu ita ma tana fama da kanta, rannan
ta samu sauki ta fito tana zaune a tsakar gida kan
turminta ashar take durawa Mubarak tana fadin
tana nan tana jiran dawowarshi yayin da ni kuma
take ta faman tsine min albarka.
Asabe ta gaji ta ce mata, to ya dai tsaya a kan
zagin kar kije ki sake jawowa mutane wata fitinar
don ke ba kya jin shawara.
Wani abin mamaki shi ne, Asabe sai ta kwaso
kowacce irin magana ta yabawa Babah Lantana
tana kallonta ba za ta ce mata omai ba, amma
Sallau duk da kasancewarshi da namiji kuma shi
ne babba bata yi mishi lamnunin hakan.
Jinya sosai Tanimu ya kwanta yayi kwana da
kwanaki yana yi Babana yayi ta dawainiya da shi,
amma tun bai gama warkewa ba sai naji Babah
Lantana tana cewa Babana wai yana gani ana
nema a kashe mata da a kan matsiyaciyar 'yarshi
amma ya kame baki yayi gum kamar na mai cin
najasa, gum din din dai ya sake yi mata bai ce
mata komai ba har tayi ta gaji tayi shiru.

34
Duk da kudin da nakeda su a hannuna rashin
Mubarak yasa nayi matukar. takura komai zan eii
sai na saya ban saba wannan rayuwar ba, abinda
nafi sabawa dashi a kawo min ne don haka kudin
da ke hannuna bai hana ni jin yunwa ba,
musamman ma da yake wani lokaci ana sayo min
in kasa ci, don bai gamsar da ni ba tunda in yana
nan ba irin wannan din nake ci ba.
Babah Lantana tayi girki ta raba ta baiwa kowa
nashi 'ya'yanta guda biyu da Babana yayinda ita
kuma take zaune a kicin tana cin nata, na mike
naje e same ta na ce Babah a bani nawa abincin.
Ta kalle ni a lalace ta ce in ba haka ba fa a kore
ni ko a yi ya ya? Shiru nayi na tsaya.ina kallonta,
yayinda ita kuma take bayani a nemi kashe min da
a kan ki sannan in yi girki in ba ki.ai ba zai yiwu
ba.
Daga bayana Babana ya ce min to zo ki dauki
wannan nawan kici, na juyo da sauri ta biyo ni
tazo ta fige kwanukan a hannuna in gadaranka kai
ka kawo ai ni na girka, ni baiwarta ce? Bata danye
itama ta girkawa kanta ai mace ce babu kuma
abinda bata sani ba wani abin ma ta fini sanin shi.
Wannan magana da Babah ILantana tayi ta in
girkawa kaina shi ne dalilin da yasa da gari ya
waye nabi bayan Babana zuwa wurin saida

35

tumatirinshi nace ya bani kayan miya, ya zuba a
leda ya miko min.
Na kalle shi cikin natsuwa na ce, to abin da zan
dafa fa? Akwai a gida, na ce ba za ta ba ni ba, bai
ce komai ba ya ciro kudi ya bani na wuce na shiga
shago na sayi taliya guda daya na juyo na kama
hanyar zuwa gida.
Ran 'yanmata ya dade, na jiyo muryar tashi
daga bayana na kuma shaidata ta Mansur ce, bàn
waiwaya ba na dai ja na tsaya ina jiran isowarshi.
Ai rannan na hango ki kina dawowa daga
Makaranta nayi ta daga miki hannu ina haba in
babu busa babu daga hann ne? sai na lura ma ba
ki ganni ba. Nayi murmushi tare da fadin eh, ka
kyauta min kwarai da kai da kanka ka gane
ganinka ne ban yi ba.
A'a haba ai nasan ba ki da irin wannan
wulakancin ke dai kawai ganinki ne yana wuya da
yake kin riga kin zama budurwa. Na ce, kai
Mansur ke nan, barkwancinka yana da yawa, can
cikin zuciyata kuwa mamakin dabi'arshi
kanbama 'yanmatancina nake yi.
Kullum muka gamu sai ya jaddada min ni din
budurwa ce ni din mai kyau ce, ni din daba ce da
saura, abinda kuma bai taba damun Mubarak ba ke
nan. Na dan yi shiru cikin nazari da tunanin ko

36
Mubarak. sya taba gaya min ifin wadannan
kalmomin? Kai bani tuna ba.
Kar dai a ce rashin lafiya ki ka yi bai sani ba?
Na ce eh amma ba mai tsanani ba ne, ya zuba min
ido yana kallona, kina nufin abinda yayi sanadin
wannan ramar ba ma tsanani ba ne? nayi
murmushi na cé. eh, ya ce to kuwa sai muyi ta
addu'a kar mai tsananin yazo, na ce to amin.
To mu ba yaran nan ledar cefanen mana don
kar mu 6ata muşu lokaci na ce a'a babu komai
cefanena ne, kina nufin kece za:ki yi girkin da
kanki? Na ce, eh, ya ce a'a to shiga ciki kawai ina
zuwa, bari in je in kawo cefane nayi maza na ce
a'a ka bari.
Ya daure fuska ya ce, to ai ba ke ki ka roke ni
ba, na wuce shi da nufin tafiya gida, ya sake biyo
ni ran yanmata ya dade, na dan rage takun da
nake yi don nasan wata magana yake son gaya
min, kina da bukatar wani abu ne? nayi maza na ce
mishi a'a na tafi.
Ina cikin tafiya sai ga Isiyaku da saurinshi, Anti
ai nazo ki ka ce babu aika, na ce eh Isiyaku wurin
Babana naje na karbo yasa hannu ya karbi ledar da
ke hannuna muna tafiya yana bani labarin wahalar
ruwan da ake yin da yanda suma matar Babansu ta

37

sanya dokar sai mutum ya ajiye bokitin ruwa goma
kafin ta ba shi abincinshi.
Ba ki ga fa inda muke tafiya diban ruwan ba,
na ce eb to wata rana ai zai wuce Isiyaku, ya ce
haka a ke fada, nayi tunanin shima yana da irin
manina kenan, da zuciyata ke yi min a duk
lokacin da a ka gaya min haka shi ne na in tambayi
kaina to yaushe ne wata ranar zata zo?
Cikin gida na shiga shima ya biyo ni duk da
yasan Babah Lantana ta tsani shigar da yake yi
cikin gidan kullum ta ganshi a ciki sai ta tambaye
shi kai baka san nan gidan, gidan matan aure ba ne
ba? Sai ya ce ya sani ye uce ta yayi abinda zai yi
ya fita.
Na shiga cikin kicin, tayi 2za ta biyo ni karki
shigar min kicin kar ki taba min komai a wurin
nan, don ba zai yiwu ni da ke a ciki ba, in kuma ke
ma matar gida ce sai ku zo ke da ubau i ku
gaya min."
Ban tanka ba nasa hannu na dauko risho tare da
tukunya mai murfi, ba na ce kar ki taba min komai
ba, na kalle ta na ce, kin gani? Wannan ai na Inna
ne, kadan ya rage ta kifa min mari saboda ambaton
Inna da nayi a gabanta, ban san yanda a ka yi ba
sai kuma naga ta fasa.

38
To juye min kananzir din ciki ko shi ma nata
ne? naje na juye mata, ina fitowa Isiyaku da ke
biye dani yasa hannu biyu ya karba ya bar ni ina
neman wani tsohon galan da na san yana nan a
cikin kicin din.
Na fito ina kwance bakin zanina da na daure
kudina don na daina ajiye su a ko'ina sai a bakin
zanin da ke jikina, na zaro abinda zan ba shi ya tafi
yaje ya sayo mana. kananzir, na rasa inda zan sa
risho din saboda iskar da ke kadawa.
Na wuce naje na kai shi dakina da nufin yin
girkin, à can nan ma ta biyo ni dakin ai ba naki ba
ne ke kadai, don haka ba za ki yi girki a ciki ba,
balle kije ki rine mata kayanta da hayakin risho.
Don haka ha koma cikin zaure na sa-shi a lungu
tunda ni dai nasan kawai zan yi girki ina bukatar
cin abincin, ga Isiyaku ma yana bukata, don tunda
Mubarak ya hada ni da shi wurina yake zuwa ya
karya ya kuma ci na rana, abinda Mubarak din ya
gaya mishi ke nan nima ko ban yi niyyar saye ba
in yazo sai in ba shi.
Shiga wurin Babah Sumaye ka ce wai ta bani
wuka da ludayin miya da kuma kwanukan cin
abinci, ya ce to.
Kai yau ga wani abin dadi, girkin ma a zaure a
ke yin shi? Alamar dai ke nan da girkin ba na

39

tsayawa yaci. Na waiwaya cikin murmushi na
Darowata ba ae mai wucewa a hanya ma zai iya
kalle shi, manya-manyan edoji ne guda biyu a
hannunshi a cike da cefane.
Na rike baki na ce kai Mansur wacce irin
hidima cekwannan? Ya yi maza ya daure fuska
alamar bai son maganar tawa, in wanke hannu dai
kawai kenan in yi shirin yankan attarugu da albasa
tunda nasan zafinsu ai kin ga ba zai yiwu in bar ki
ki taba su ba.
Nayi murmushi na ce ai an riga an yanka su,
sayayya sosaiaMMansur yayi na kayan tea daya ledar
kuma kayan ciki ne wanda hanta yafi komai yawa
a ciki, ga kuma a gada nono guca mai kyau da ita.
Isiyaku yana ganin ledar kayan cikin ya sure
shi ya shiga gidan Babah Sumaye yaje ya wanke
shi tas ya kawo ya nuna min. ina, dubawa yana yi
min magana naga gaushin da Babah Sumaye ta
sauke girkinta ko can zan kai wannan? Na ce to
kai Isiyaku in babu abinda zata dora a kai. Ko
akiwai, ma ai naga wani kurfon buhun gawayi ne
kuma da ita zan hura wata wutar, na ce mishi to.
A zaure na soya agada na hada mana tea muka
sha ni da Isiyaku bayan tafiyar da Mansur yayi a
kan zai je gida ya dawo.

40
Sai da muka koshi sannan muka zaune yin
girkin dafa dukan taliya mai hade-haden kayan
lambu a ciki nayi mana na zubawa Mansur a
karamin food flask na zuba mana namu ni da
Isiyaku saura na juyewa almajirai da suka zo
wucewa su biyu.
Farfesun kayan ciki yayi Isiyaku ya shiga ya
fito da tukunyar na zuba mana namu ni da shi, na
zubawa Mansur da Babah Sumaye na hada
baiwa Isiyaku duk yakai musu ya dawo.
Muka hadu muka gyara wurin ya kuma yayi
mana wanke-wanke ya kife ya dawo.
Wai dan girkin nan da nayi naci sai ya haifar
min da wata irin natsuwa da na dade ban samu
irinta ba, damuwa tayi min sauki naji dadi cikin
raina, don haka da na shiga gida ina ajiye kayan
tea na' da sauran abubuwan da na shigo da su, sai
kawai na wuce na shiga wanka don in kara jin
dadi.
Na fito daga wanka ina shafa mai na lura naga
kamar an taba kayan da na ajiye, na mika hannu
don jin ko da gaske ne an taba sai kawai naji an
juye babu komai a ciki sai gwangwanayen aka
bari. Cikin zuciyata na ce iko sai Ubangiji, na ci
gaba da harkokina.

41
Washegari da safe ina kwance kan shimfidata
ban motsa na tashi ba saboda nasan ko na tashin
bani da wani abinda zan ci na kuma daina aikin
Babah Lantana tunda ko nayi bani da rabo cikin
abincinta. Jiran shigowar Isiyaku nake yi don in ba
shi ya sayo mana abinda zamu karya dashi.
Jimawa can sai gashi ya shigo rike da kwano
mai shake da waina da wani kwanon kuma, miya
ce da kashi da man shanu, cikin fara'a ya ajiye
kwanon yana murmushi. ""Yaya Mansur ne ya bani
wai in kawo in na gama kuma in je in same shi na
ce mishi to."
Wajen karfe goma sha daya da rabi na safe sai
ga Isiyaku ya dawo dauke da cefane niki-niki har
da kaji da kuma busasshen manya-manya. A.zaure
rannan ma muka yi komai muka ci na zuba na
Babah Sumaye da na Mansur na aiki Isiyaku ya
kai musu na zuba mishi na Almajirai yaje suma ya
kai musu.
Sauran kayan kuwa gaba daya na sa shi ya diba
yaje ya kai wa Babah Sumaye ya ce ta ajiye cefane
ya zamo mishi wata ka'ida da ya dora wa kanshi
kullum sai yayi ko da kuwa na jiyan bai kare ba.
Kullum muka yi kuma zan zuba a kai mishi
sannu a hankali kuma sai Mansur ya maida zauren
gidanmu wurin hirarshi.

42
Rannan iną tare da Mansur a zauren tare da
Isiyaku, muna hirar ne ina yi mana girki sai ga
Babah Lantana tana ganin Mansur ta soma zagi da
fadin lalatattun maganganu irin wadanda ta saba yi
wa Mubarak.
Nan da nan Mansur ya maida wukar da ke
hannunshi wacce yake yanka min albasa, da ita ya
daga ido ya kalli Babah Lantana cikin natsuwa ya
ce mata ai ki na ambaton sunan 1yayena a cikan
maganganun naki za ki gane kin jawa kanki
matsala don ba zan bari ki zagan mun su ki
kwashe kalau ba, zan gwammace in biyo ki har
cikin gidan in sa dorinata in yi miki dukan tsiya.
In yaso duk abinda zai faru bayan hakan ya
faru zai fiye min sauki a kan kiyi wa iyayena zagin
wulakanci irin wanda ki ka saba yi wa mutane
suna kyale ki, kin taba ganin na shiga lamarinki?
Kin taba ganin na buda bakina na gaya miki
wata kalma ko da kuwa ta gaisuwa ce tunda ki ka
zo layin nan? Kin taba ganin,na shiga harkokin da
ki ke yi? Kin taba ganin na shiga harkar
'ya'yanki?
Amma shi ne ki ka zo kina zagina har kina
ambaton sunan ubana? To sake fadin kalma guda
daya ki ka ga ni? In ma nayi mata ciki sai me? Ina

43

ruwanki ai ba zan barta tayi ta yawo da shi kamar
yanda a ka barki kina yawo da naki ba.
Ban san yanda a ka yi ba sum-sum naga Babah
Lantana ta juya ta shige gida ta bar shi yana fadin
haka kawai mata kin zo unguwa kin samu mutane
kin tasa su a gaba suna kallonshi sun kyale ki? Ai
karyar iya shege ki ke yi.
Na shiga gida don taba ruwa sai kawai naji
Sallau yana cewa Babah Lantana na rantse miki
Mama in ki ka sake jawo wata fitina ta same ni sai
kin gaya min inda Babana yake. Tunda na ce zan
shiga duniya kin ce namiji don ya shiga duniya ba
komai ba ne, ga maigidan nan ma ai shiga duniyar
yayi ya bar danginshi da bai samu yanda ya ke so
ba.
Kuma ya bakura ya yafe su to na fasa shige
duniyar tunda don na shiga bai dame ki ba, zama
zan yi a inda ki ke iyaka in tara miki Jama'a su
rokar min ke ki nuna min in da ubana ya ke, a to.
Ya fadi a to din tare da gyada kai nuna alamar da
gaske yake yi zai iya aikata abinda ya ce din.
Rannan dai jikin Babah Lantana a sanyaye ya
wuni saboda rasbhin mutuncin da Mansur yayi mata
ga kuma kalaman danta wanda ko gama warkewa
bai yi ba, yanda ta wuni jiki a sanyaye haka Sallau
ma ya wuni yana mita ba fa gama warkewa nayi

44
ba har yanzu din nan ji nake kamar kasusuwan
jikina Agogo ce suke kuma wai kina sake shiga
sabgar wani saboda ba ke suke yi wa ba.
Ina jin su babu uwana takura ta dai tayi
matukar raguwa, gashi abin da nake so shi nake ci
na rabu da yunwar da ke yawan damuna a yanzu
kuma ina da yann hira ga Isiyaku ga 'yan
Almajiraina guda biyu wadanda in ba wani
muhimman abu za su yi ba basa barin gidan,
sannan ga Mansur abokin hira mai dadi mai fadin
kalamai masu dadi mai barkwanci, mai sanya
zuciya taji tanfar a kan gajimare take yawo, saboda
dadadan kalamanshi, ga shi kuma da yawan alheri.
Tun daga ranar da Babah Lantana tayi haka da
Mansur nima bata sake shiga harkata da yawa ba
balle Mansur din iyaka dai kullum zan ji ta tana
cewa Babana wannan yarinyar fa ba a rabu da
bukar ba wancan ya tafi ne wani kuma ya mayye
gurbinshi.
Ta kwashe bayani na karya da gaskiya tayi
mishi, rannan har tana yi mishi rantsuwar wai ta
ganshi ya matse ni a lungu in banda ta shiga
zauren da bata san abinda zai wakana ba.
Yana jin ta tayi shiru bai ce mata komai ba,
takaici ya kamata ta ce koda yake dai kai dama irin
wadannan ba su dame ka ba, ba ka tsoron shege ta

45


kalle shi ta tabe baki tare da mikewa ta nufi
dakinta tana tafiyar tana magana a hankali sai dai
hakan bai hana a ji ta ba, don rage muryar na iya
shege ne. Wa yasan abinda kayi ne ma Mallam
kafin ka baro gida nake damun kaina a kan 'yarka?
A zuciyata na tabbatarwa kaina raini ya kai duk
inda yakai tsakanin Babah Lantana da Babana,
tunda har zata iya furta mishi irin wannan maganar
a kan idonshi, bai iya ce mata komai ba, na gaji da
irin wadannan kalaman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login