Showing 15001 words to 18000 words out of 27017 words
gama in karbi
kwanon ya wuce ya shiga gida kafin in bi
bayanshi.
A haka har Azumin yazo karshe muka shiga
kwanaki goma mafiya daraja kwanakin neman
daren Lailatul Kadri daren da AIkur'ani mai
75
girma ya ba mu labarin cewa darajarshi tafi ta
watanni dubu, haka alkairorin da ke cikinshi.
Ubangiji yasa mu dace, kullum abinda Umma
ke fadi ke nan in taji Mallam yana ta nanata fadin
alherin daren 'Lailatul kadri ni kuwa sai in ce
mata anmin Umma.
A wannan lokacin zan iya cewa ban taba
samun kaina cikin hali na kunci da farin ciki
lokaci daya ba irin wannan karon, ina cikin farin
ciki saboda alkhairori da suke ta zuwa min daga
wurare daban-daban.
Kusan kullum gari ya waye sai an zo min da
sako na kayan sallah daga wani wuri. Yakumbo
Halima da ba wani karfi ne da ita ba ma atamfa
'yar Holland ta dinka min a dalilin wai na zama
budurwa, Yaya Dijah tsalelen leshi gami da
takalmi da Jaka da gyale.
Umma atamfa da leshe itama da takalmi da
Jaka da gyale mahadin takalmin duk da dai tace
wai da kudin bankina ta saya min amma dai nasan
alherin Umma bai kwatantuwa a wurina.
Mansur yayi min kala biyu masu kyau shima
tare da takalmi da Jaka tare da gyale, sai kuma a
ka kawo min na Mubarak, Isiyaku ya aiko ya kawo
min. Na zauna ina kallonsu suma kala biyun ne sal
dai shi komai nashi daban ne da na saura, bai taba
76
mancewa da wani abu ba in dai har aiken zai yi
min yadika ne masu kyau masu laushi kala biyu
mai ruwan madara da kuma baki na rike su a
hannuna ina kallonsu ruwan da suke yi ya kara
tabbatar min da darajarsu.
An yi musu adon zare a wuyansu kalan zaren
ya dace da kalan takalma guda biyu da ya saka a
cikin kayan kenan kowanne da mahadinshi gyale
biyu sai kayan shafa da under wears ga kuma wani
dan karamin akwati mai dauke da wata 'yar sarka
mai dan madaidaicin 'yan kunne da zobe a wata
yar takarda kuma wasu siraran wararai ne da
agogo babu yanda za ayi a kushe hidimar Mubarak
in dai zai yi ta matsalarshi guda daya ce ita ce ta
ban san in da yasa gaba ba.
Kuncin da nake ciki da takura kuma shi ne na
tasa ni a gaba da Mansur yayi in bar shi ya tura
iyayenshi wajen Babana magana ta wuce tsakanina
da shi har yaje ya hada ni da Yakumbo Halima, ita
kuma ta kira Yaya Dijah ta gaya mata cewar lalle
ne ta gaya min in bar Mansur ya tura iyayenshi
wajen Babana ayi maganar aurena in kuma ba shi
nake so ba to in turo wanda nake son daga nan
zuwa watan Sallah in har ba so mu nuna mata ba
ita ta haife mu ba, amma ina amfanin wannan
zaman da nake yi a gidanmu?
77
Shi karatun boko ai ba dole ba ne wurin 'ya
mace, na Addini kuwa na same shi daidai
gwargwado a gidan mijina ma kuma zan iya yi
tunda neman sanin addini ne shi aure ai suturar 'ya
mace ne.
Yanda naga Yaya Dijah ta dauki maganar da
karfi na tabbatar zai yi wuya a ce watan Sallah
yazo ya wuce ba tare da an titsiye ni na fitar da
mijin ba, to ya ya zan yi? Ba da sunan Mansur din
zan yi shi da yake son a bada sunan nashi ko kuwa
wata hikima zan yi da Mubarak zai san abin da
nake ciki?
Cikin hanzari na kawar da wannan tunanin
saboda sanin da nayi cewar ba zan taba nuna mishi
wani abu ya dame ni game da shi ba, ba zan taba
karya 'yancina na kasancewata halitta mai daraja
da Ubangiji ya karramata da kunya ba, wato
halittar da aka yi min na zamowata 'mace
Haba, mace ta rasa kunya? Ai kuwa dai tayi
rashi mai girma, kalaman Yaya Dijah ke nan
kunya ai adon 'ya mace ne, a bakin Umma na saba
jin hakan, don haka na kara kudurawa raina babu
wani abin da zai sa in nuna mishi wani abu in dai
yaga ci gaba da yin shirun nashi yafi mishi to yaje
yayi tayin shiru.
78
Aka wayi gari a gidanmu da ma sauran gidajen
Musulmi na garuruwa daban-daban, hidimar sallah
a ke yi, Jama'a sai kaiwa da kawowa suke yi cikin
walwala da farin ciki ga dukkan alamu kuma an yi
sallar ne cikin walwala da wadata.
Tasa kayan sallar tawa nayi a gabana gaba
dayansu ina binsu da kallo daya bayan daya, kafin
zuwan sallar niyyata in sanya kayan da Yakumbo
Halima tayi min ne ranar sallah don girmamawa a
gareta, amma a yau da aka wayi gari ana hidimar
sallar ga kuma kayan sallar tawa a gabana sai naji
bazan iya kaucewa sanya daya daga cikin kayan
sallar da Mubarak yayi min ba duk kuwa da niyyar
da nake da ita ta daina mu'amalla da kayanshi.
Duk da hakan sai na ce to tunda yanzu hidimar
sallah a ke yi bari in bari bayan sallah na dauki
wannan matakin amma yanzu bari in yi adon
sallah kawai.
Bakin yadin na sanya wanda jikinshi yafi kama
da voil ko silk tasha ado irin na barnina a gaban
rigar dan madaidaicin ado da yayi matukar kawata
rigar ta zamo gwanin sha'awa, na sanya takalmi da
gyale tare da Jaka da suka dace da kayan.
Sannan na dauko 'yar sarkar da 'yan kunnena
tana sanya ga kuma warwarai da agogo, in tsaya
cewa nayi kyau ma bata baki ne kawai, na tsaya
79
gaban dogon yaron Innata da Babah Lantana ta
fitar a dalilin hanata saida gadon da nayi na dauko
shi na kawo dakin.
Kallon kaina nake yi a cikin shi cikin zuciyata
na tabbatar ban taba yin kyau irin na yau din ba,
ko ba a gaya min ba kuwa dama nasan ni din mai
kyau ce, don kuwa kowa ya ce da Innata nake
kama Innata kuwa mata ce da ta rayu mutanen da
suka santa suna ba da labarinta.
Yau kam duk mishikilancin shi da taurin kanshi
in ya ganni ba zai iya kame bakinshi yayi shiru ba,
sai ya yabi kyan kwalliyata sai ya furta wata kalma
da zata zamo mai karfi a tsakanina da shi.
Ina tsaye a wurin ina kara feshe jikina da turare
tare da kara kallon kaina a madubin Asabe ta shigo
dakin tana zage-zage nayi kamar in tanka mata
tunda nasan da ni take yi sai nayi maza na baiwa
kaina shawarar kame bakina tare da hanzarta barın
gidan don ba zai zamo mata komai ba ta rufe ni da
dukan da zai yi dalilin da zata tumurmusa ni ta
lalata min kwallioyar sallar tawa ba.
Don haka nayi maza na yafa gyalena na kuma
shuri takalmana nayi waje, gidan Umma na nufa
zanje in yi mata barka da sallah daga nan taga
kwalliyata.
80
Nayi maza na yamutsa fuska na ce, a'a Umma
ni fa ba don kowa nake yi ba, tayi murmushi, au
haka ne Maryamu kai wannan kayan sallah naki da
kyau suke kai ji wata sarka kai kai kai, wa ya saya
miki wannan sarka Mero?
Na shiga dibi-dibi cikin sa'a ta sake tambayata,
Dijah ce ko? Nayi maza na ce mata ch, lokacin ne
na kara sanin darajar sarkar.
Nabi umarnin Umma na shiga nayi wa Baba
barka da sallah a falonshi na fito daidai Mubarak
yana shigowa gidan ban daga ido na kalle shi ba
balle in gane irin kwalliyar da yayi na dai san
kawai na shaki kamshin turarenshi.
Baba ya bani goron sallah, nayi maganar ina
nuna mata kudin da ya banin, tayi godiya. Kai
wannan kwalliya taki tayi kyau, bani plate guda
biyu Umma zan ba wasu, zuciyata ta soma yin
nauyi da na soma tunanin har uwarshi ta gane don
shi nake yin abubuwa masu yawa amma shi bai
gane ba, ko kuma ya gane ya ki nunawa saboda
bai da bukatata.
Babu wanda ya ganni bai yabi kwalliyata ba sai
shi sai kokarin karbar waina yake yi wai wasu
bakin sun kara zuwa mishi.
82
Iko sai Ubangiji, girman 'ya mace babu wuya
ai duk in da budurwa takai kin kai Maryamu, kin
kuma yi kyau irin wanda ba a zaton miki ba.
Nayi murmushi na ce Umma kenan, na juya
tare da cewa na tafi, da sauri ya biyo ni wata kila
yayi zaton zan tsaya mishi ganin ban nuna alamar
hakan ba ya sa shi fara yin magana ina za ki ne
haka?
Ban tanka mishi ba, da ke fa nake magana, na
sake yin kamar ban ji shi ba, tafiyata kawai nake yi
to tsaya mana ki ji maganar da zan gaya miki, cak
naja na tsaya saboda abinda zuciyata ke raya min,
ya biyo ki ne ya gaya miki wata muhimmiyar
magana, zai yabi kwalliyarki ne wata kila ma yayi
abin da zai fi hakan dadi a gare ki.
Naja na tsaya ya iso ya same ni, maimakon in ji
ya kama hanyar gaya min wata magana mai dadi
sai naji ya fara jero min tambayoyi ina za ki ne
haka? A hankali na ce mishi gida, to me za ki je
kiyi a gidan da ki ke irin wannan saurin? Nayi
shiru saboda ban ga kamar zan iya amsa irin
wadannan tambayoyin ba.
Muje in kai ki kiyi hoto, ban kalle shi ba na ce
na daina yin hoto a daidai lokacin kuma na kama
tafiyata cikin zuciyata ina tunanin bai iya komai ba
sai sayayyan kaya mai kyau amma bai san yaga
83
kayan jikin wanda ya sayawa ya yaba kwalliyar da
aka yi da su din ba, to ko meye amfanin sanya
kayan nashi?
Ina dosar kofar gidanmu na hango Mansur shi
kuma yana fitowa daga zauren gidan namu ga
alama nemana yaje yi daga in da ya hango ni ya
saita kyamararshi ya soma daukana a hoto, kan mu
gamu yayi min hotuna da dama.
Muna gamuwa da shi ya soma furta min
dadadan kalamanshi masu sanyaya zuciya da
sanyata cikin wani hali na natsuwa da farin ciki.
Alfarmarki nazo nema, ta me fa? Ya sake
kallona cikin wani yanayi tanfar dai tsoro yake kar
ya nemi alfarmar bai samu ba. Cikin natsuwa ya ce
min gaishe-gaishen yan uwa da abokan arziki
nake so in roke ki muje tare.
Ba wani tsaya yin wani tunani ba na ce mishi
muje, dadi ya kama shi don in kara mishi jin dadin
kumá na sake ce mishi, jira ni ina zuwa, na wuce
na nufi gidanmu da nufin in canza kayan jikina in
sanya wanda yayi min.
Cak! Naja na tsaya a cikin zaure ina sauraron
maganar da nake ji tana fitowa daga bakin
mutumin da zuwanshi gidan namu ya zama ka'ida
in bai zo ba wannan satin to sati mai zuwa za ka
84
ganshi ya zo, a yanzu kuma har da tsaraba ya ke
zuwa mata da shi
Ba dai kin ce kin ba shi wadannan kajin yaci
ba, ta ce eh, to ki gaya mishi kawai ba zai yi
jayaiya da ke ba, cikin zuciyata na ce oh'oh shi
kam Babana ko me a ke nema a wurinshi kumna
yanzu oho? Sanin da nayi Mansur yana jirana shi
ne abinda ya hana ni tsayawa in ji zancen nasu
sOsai, na shiga gida kawai na wuce su na shiga
dakina na canza kwalliyata cikin kayan da Mansur
yayi min wanda suma suka yi matukar karbata.
Na fito na same shi yana tsaye ni yake jira yana
ganina ya saki wani lallausan murmushi, kin san
kuwa al'amarinki yana bani mamaki, da sauri na
tambaye shi mamakin, sai ya kalle ni ya ce min, to
komai ki ka yi kyau ki ke yi Maryamu, komai ki
ka sa yayi miki kyau ko kin taba sanin ke din
daban ce da duk wata budurwa da ki ke gani?
Ai ni a wurina da za ki bar ni da na yi wa kaina
alfarma na daina kiranki da suna Maryamu in
koma kiranki da sunan (Ta fi su) saboda ke din
daban ce a cikin 'yanmata duka.
Murmushi kawai nayi naje na shiga bayan
motar da Mansur ya tanada don zuwa gaishe-
gaishen yayin da shi da Isiyaku suke gaba.
85
Babu inda ba mu je ba har gidan Yaya Dijah da
Jumare da Yakumbo Halima, shima ta bangarenshi
mun je mun gaida tsohuwar Kakarshi ba mu dawo
ba sai bayan La'asar.
Ina fitowa daga cikin motar na hangi Mubarak
a kofar gidansu ta wajen gidanmu yake
fuskantowa abinda na tabbatar shi ne dawowana
yake son gani.
Yana hango nin kuwa na ganshi ya dunfaro
gidanmu yana tahowa nayi maza na shige cikin
zaure don kar ya same ni a waje. Ina shiga sai
gashi ya shigo, sannu da zuwa nayi mishi gaisuwar
duk da ba dabi'ata ba ce yinta bai 6ata lokacinshi
wajen amsata ba.
Me ke tsakaninki da Mansur? Abinda kawai ya
bukaci sani kenan, na dan yi shiru saboda
nauyinshi da nake ji, sai naji ya ce min kiyi
magana mana, gaya min kawai ai gara in sani, me
ke tsakaninki da shi?
Cikin karfin hali da jarumtaka na bude bakina
a hankali cikin natsuwa na ce mishi, saurayina ne,
to da kyau! Abinda kawai ya fadi kenan ya juya ya
fita. Ya bar ni tsaye a cikin zauren sai dai
maimakon in wuce in shiga gida nima kasa
motsawa nayi a wurin ban san dalili ba har kusan
minti uku da fitan shi ina tsaye a inda ya bar ni.
86
Sunkuyar da kaina kasa nayi ina kallon faratun
yatsuna can cikin zuciyata dai ba zan iya cewa ga
takamaiman abinda nake tunani ba.
Motsin da naji ne ya sani dagowa cikin sauri,
Mubarak ne ya sake dawowa gabana yayi
mummunan faduwa saboda yanayin da na gani a
tare da shi, tsoro ya kama ni nan take naji jikina ya
dauki rawa, dukana zai yi ko me?
Bacin rai da ke fuskarshi ba mai tsanani ba ne,
sai dai da ganin yanayin da ke tare da shi ka san ya
shanye wani abu saboda yanda idanuwanshi suka
canza launi.
Me ki ka ce min yana tsakaninki da Mansur?
Shiru nayi ban iya ce mishi komai ba, kiyi magana
magana ki sake gaya min irin maganar da ki ka
gaya min dazu. Wani shirun na sake yi ban tanka
mishi ba.
Ai ban san kin iya rashin kunya ba sai yau, kina
nufin don kin koyi rashin kunya sai ya zama za ki
ya cin fuskata kici mutuncina ki bata min, to ai
ban san saurayinki ba ne shi yasa na bar ki kina
hidimominki, to anma tunda ke da bakinki ki ka
gaya min to ina so in sake ganinki da shi ki ga
abinda zai faru.
Ina so in sake ganinki da Mansur ko in ji
labarin an ganku tare ki ga yanda zamu kare ni da
87
ke, mara kunya kawai, wacce ko wayo bata da shi,
yana fadin hakan yayi shiru sai dai bai juya ya fita
ba.
Sake tsare ni yayi yana kallona wani irin kallo
da ba zan iya tantance irinshi ba, saboda kainaa a
sunkuye yake hawaye suna ta zubo min, yana
kuma kallonsu amma bai sa shi tafiya ya kyale ni
ba.
Tun kwanaki ki ke nema kiyi min wulakanci
me nayi miki? Me nayi miki da ki ke so sai kin
bata min rai? Ki gaya min in laifi ne in baki hakuri
in kuskure ne in gyara, amma ba zan lamunci,
rainin hankali ba daga wurinki.
Ya juya ya fita nima na lallaba na shiga gida
na hau gadona na kwanta, kuka sosai na kama yi.
Asabe tana kallona tun tana shiru har ta soma
magana ita kadai, in dai namiji ne matsalarki ai
kuwa ba ki yi kukan ba tukuna musamman ma
wannan dan iskan da ki ka likewa mai kwashe-
kwashen tsiya, ban dai tanka mata bá.
Ban sani ba ko kashedin da Mubarak ya yi min
ne ya tsorata ni na kasa sake fita tare da Mansur,
ban iya sake zuwa ko ina ba sai dai kawai in yi
kwalliyata in zauna a gida.
A 'yan kwanakin da na zauna a gidan nan ne na
gane Babana da Babah Lantana ba karamin
88
dasawa suke yi ba, ji da shi Babah Lantana take yi
ba kadan ba, ko abinci zai ci sai ta zauna ta tasa
shi a gaba yana ci tana kara mishi tana yi mishi
wata hira mai dadi da zata sa shi ya ji natsuwa
cikin zuciyarshi.
A zuciyata na ce wato itama dai matar nan ta
iya komai na kyautatawa raini ne kawai da
wulakanci yasa bata yi, ko wanene ta samu yayi
mata wa'azin da ta gyara halinta? Oho, tunda ko
nima dai wannan sallar sau biyu tana zuba abinci a
kwano tana bani, ban karba ba ta sake kawo min
soyayyun kaji nan ma naki saboda zuciyata bata
kwanta min kan in ci ba, amma duk da haka hakan
da tayi yasa al'amura sun dan yi sanyi fiye da da.
Kwana bakwai a ka yi Babana ya fara fita,
Babah Lantanan ce kuwa ta ce babu in da za shi
sai an kwana bakwai, ya zauna shima ya huta a
cikin iyalinshi.
Rannan ya fita ya dawo naji shi yana ce mata
yau dai kasuwar ta dan yi nauyi ga abinda a ka
samu, na kasa kunne in ji abinda zata ce mishi
tunda kullum ya dawo ya ce mata babu kasuwa
fada take kamawa tayi ta sababi tana fadin ya dai
6oye kudinne kawai amma wane irin rashin
kasuwa bayan dazu ta wuce ta wurin taga yara sun
kewaye shi suna sayen abubuwa?
89
Abin mamaki sai naji yau ta ce inishi to ai yau
da gobe kenan, Mallam a ka ce wai kayan
Ubangiji in babu kasuwa ai sai ka dawo gidanka
ka hau sabon gadonka kayi kwanciyarka ka
wataya.
Ta soma zuba mishi abinci yana ci yayinda ni
kuma can cikin zuciyata nake fadin to da haka ki
ke yi mishi wa zai damu da rashin kirkinki balle
har aje ana yi miki rashin kunya.
Suna cikin hirarsu nima ina sha'anina a daki
sai na jiwota tana tambayarshi, to in kirata ne ka
gaya mata? Yayi shiru bai amsa ba, in ban da
uh'uh din da na ji ya fada, don haka na kara kasa
kunne wajen sauraron magana tasa sosai don na
gane da ni a cikin zancen nata.
To amma ai yau ne kayi alkawarin gaya mata,
da safe ka ce a'a yanzu da yamma ka sake cewa
uh'uh to me ka ke nufi? Ko za ka saba alkawari
ne? Dattijo da saba alkawari? Ya sake yin shiru.
Ai fa aikinka ke nan in ana magana da kai kayi
gum da baki kamar wani mai cin najasa, taja wani
mummunan tsaki alamar dai ranta ya soma 6aci,
ko ma ya riga ya bacin, ai dama nasan karya ka ke
yi ba za ka iya gaya mata ba ka ce za ka iya, abin
bakin ciki wai uba yana tsoron 'yarshi.
90
To in ba za ka iya gaya mata ba ni in gaya mata
tunda ni kam ai ba tsoronta nake ji ba yayi maza
ya ce mata uh'uh to in kira maka ita? Yayi shiru ba
ga ta can a daki ba? Kai Mallam kai kam ba ka da
dattaku, kai tir!.
Kalaman nata suka sanya ni naji wani iri, ga
bakaken maganganun da take ta gayawa Babana
ina ji, ban da haka kuma na tabbata ko wace irin
magana Babah Lantana take son ya gaya min to ba
mai sauki ba ce, kan haka sai naji maganganun
nata sun sanya tsigar jikina yana tashi.
Ban iya ci gaba da zaman da nake yi ba,
mikewa nayi na fito nazo na durkusa a gabanshi
cikin natsuwa da girmamawa na ce mish1 gaya min
maganar da ta matsu in ji Baba, ko menene gaya
min kawai zan iya dauka.
Ai kai Mahaifina ne, kai ka rene ni ka kuma yi
min duk alherin da uba ke yiwa da, na kuma
godewa Ubangiji kana sona ba ka yarda ka bayar
da rikona ga kowa ba, don haka babu wani dalili
da zai sa ka rinka