Showing 18001 words to 21000 words out of 27017 words
sa ranar gaya min wata magana
kana dagawa tunda dai kasan dole ne zan ji ta to
gaya min kawai zan fi jin sauki in na ji ta a
bakinka maimakon a ce wani ne zai gaya min.
A hankali ya dago ido ya kalle ni cikin natsuwa
ya ce min aure zan yi miki Yaacuwuna, na daga
91
ido na kalle shi, damuwa ce karara a fuskarshi ko
ni da ya ce zai aurar ba tare da nasan mijin da yake
nufin banin ba babu irin wannan damuwar a tare
dani, tunda dai nasan a tsakanin biyu ne za a yi
daya, ko a baiwa Mubarak ni ko Mansur, wanda
duk aka yi da shi zan zauna tunda su dukansu ina
da dalilan da za su sa ni zama da su.
Na kawar da wannan tunanin daga zuciyata na
daga ido na kalli Babana cikin natsuwa na ce
mishi Baba wa ka ke nufin baiwa ni? Na dan
sunkuyar da kaina kasa don kunya da girmamawa.
Auren ai na zumunci ne, cikin hanzari na dago
na kalle shi a zuciyata kuwa dadi ne ya kama ni,
wato dama Baba yana sa ne da zumuncinshi da
kullum ake yi mishi gori a kai, wato dama yayi
niyya a kaina ne zai gyara zumuncin nashi ta
hanyar bada aurena gare su?
Ai kuwa dai duk wanda ya baiwa ni zan zauna
da shi da zuciya daya in kuma yi mishi ladabi da
biyayya irin na aure. Amma don in kara samun
natsuwa cikin zuciyar tawa sai na tambaye shi
cikin 'ya' yan wanka ne ko na kannenka za ka
baiwa ni Baba?
Sai da yayi gyaran murya saboda yanda ta
make take nema kuma tayi rawa kafin ya iya ce
min a'a wannan dan uwan uwar taki Lantana ma
92
zuwa gidan nan Mahammadu Nalami shi zan
baiwa ke, don kara karfafa musu zumnuncinsu ai
kin san abokin wasanta ne?
Kadan ya rage in suma a tsugune saboda
tsananin kaduwar da nayi. Nalami fa kace Baba?
Ya gyada kai tare da cewa eh shi nace, ban san
yanda a ka yi ba sai tsintar kaina nayi ina yiwa
Babana tambayoyi.
Zumuncin Babah Lantana yasa ka baiwa
wannan mutumin ni naka zumuncin fa Baba?
Shiru yayi yana kallona bakina ya sake yin subuta
ya ce mishi, ba zan auri Nalami ba Baba, domin
babu abinda ya hada ni da Babah Lantana balle
zumuncinsu da har zan je ina auren danginta.
Tuni na soma kuka ina fadin me nayi maka
Baba? Me nayi maka da ka ke taimakon masu son
ganin nayi bakin ciki a kaina? A gabana kayiwa
Innata alkawarin ba za ka bada rikona ba ne
saboda ba za ka iya rabuwa da ni ba to me yasa za
ka bada aurena a inda kasan zan yi bakin ciki.
Nan da nan kawai sai naji zuciyata tana raya
min babu abinda yasa a ke yi min irin wannan
musgunawar illa don uwata ta rasu, Yaya Dijah da
aka yi aurenta Innarmu tana raye ai bata irin
wannan tozartawar ba nan take na soma kuka da
iyakacin karfina.
93
Kan ka ce meye wannan sai ga makwabta suna
shigowa tambayar me ya faru? Babah Lantana ta
tsaya tana yi musu bayani ai ba komai a ka yi mata
ba tunda ga uban nata nan a zaune wai daga yace
zai bada aurenta ga wani dan uwana shi ne take
wannan borin kar ku dada kar ku rage.
Maimakon a gamsu da bayariin nata sai kuma a
hau salati dan uwanki? In ta ce eh sai a gyada kai
a'a tayi ihu, to wane dadinki taji balle aje ana
baiwa wani dan uwanki ita? Wannan ya gayawa
wannan mutane sai shigowa suke yi yayinda ni
kuma nake kwance a kasa ina ta faman kurma ihu.
Gaba daya a wannan lokacin fatana bai wuce
dayan biyu ya faru da ni ba, in ma dai Babana ya
tausayawa kukan da nake yi ya fasa bada ni ga
Nalami ko kuma azabar kukan yayi dalilin da nima
zan bi bayan Innata in huta da bakin cikin zama da
Babah Lantana.
Ban san yanda aka yi ba har Umma taji tazo ba
sai jinta nayi ta katse Babah Lantana tana mnai
cewa, In ban da 'ya'yan yau ba su san biyayyar
yaye ba yaushe za a ce ka tarawa ubanka irin
wannan Jama'ar mu da yaushe? Umma tayi maza
ta ce mata ke dai kam Lantana ba ki san biyayyar
yaye ba da kin santa kuwa da ba haka ba, da ba ki
a1kata ma irin abubuwan da ki ka aikata ba.
94
Ke wannan sharrin ma da ba ki kulla shi ba, me
yasa baki ba shi tsohuwar yarki da ki ke tashe da
ita shekara da shekaru ta rasa mijin aure ba?
Wannan ai ba huruminki ba ne ki ka shiga don
kuwa ba ki yi mata rikon da za ki zartar mata da
irin wannan hukuncin ba.
Da sauri Babah Lantana ta shiga fadin ai ni ce
ma ni ce na hada? In ke ce in ma ba ke ce ba ce dai
duk daya, yi kokari kiyi hakan a kan "yarki da ki
ka bari tana tanbada kina kallo in ba nema ki ke
sai taja miki irin abinda kema ki ka jawa iyayenki
ba.
Mero kam ai tayi sa'a tana da uban da za a sa
shi yayi mata aure da mijin da aka san ba nata ba
ne don a cutar da rayuwarta, sai dai ba tanan take
wai an danne buduri a ka yace ai ba nan take ba.
In kin yi ne don kin ga duk abinda ki ka yi
mata a zaman da ki ka yi da ita bai ishe ki ba
ruwanki kema kina da 'ya'ya abinda ka shuka
kuma shi ka ke girba, mai rabon ganin badi kumna
ko ana dakawa a turmi sai ya gani, haka ana
muzuru ana shaho zakaran da Ubangiji ya nufa da
cara sai yayi.
Don haka tashi mu tafi Mero, ta sunkuyá ta
kama hannuna na mike na tashi tsaye tana fadin ke
ai kin yi arziki da Ubangiji ya ce yayi miki miji
95
wasu ba gasu nan ba sun tsufa a titi da suna da
iyayen na gaske ai da ba su zuba musu ido ba.
Ki tafi da ita ina za ki kaita? Ko za kije ne ki
kara bijirar da ita? Umma ta waiwayo ta kalleta
cikin nutsuwa tace mata ai mu ba mu bijirewa
iyayenmu ba balle mu haifi masu bajirewa, ba zan
bar miki ita ba ne balle kiji dadin cusa mata wani
bakin cikin tunda ke ba Imani ne da ke ba.
Babu wata za dai ki kai mishi ita ne yayi
abinda ya saba, ta ce eh zan kai mishi ita biyo ni
ke kuma ki hana ni ko ki kwace ta.
A kofar gida muka samu Mubarak yana tsaye,
ganina tare da Umma ya sa shi wucewa gaba ya
fara tafiya muna shiga gidan yaja ya tsaya, wacce
irin musiba ce wannan Umma? Ta ce, Eh ai
rayuwa ta gaji ganin al'amura da dama sai addu'a
kawai don haka ba' yana nufin komai ya kare ba
ne.
To me ya saura Umma? Tayi murmushi tare da
fadin da yawa. Ni kam in ban da kuka babu abinda
nake yi, duk bayanan da Umma ke yi na zai wuce
watarana kuma sai labari jinta kawai nake yi
kullum abinda a ke gaya min ke nan wata rana sai
labari, har yanzu kuma ban ga alamar abubuwan
za su wuce ba tunda kullumn wasu muna nan
abubuwan sai kara samuna suke yi, duk wata fitina
96
ko tashin hankali da na gani a rayuwata ban taba
ganin abinda ya kai cewan da Babana yayi wai zai
ba da aurena ga Nalami ba, in dai ba tashin
hankalin rasa uwata da nayi ba ne.
Ana cikin haka sai ga Baban Mubarak Albaji
Muhammadu ya shigo, menene ne haka a ke ta
kuka ke kuma kin tasa ta a gaba kina kallonta?
Umma ta shiga rattaba mishi bayanin abinda ya
faru.
Hankalinshi a kwance ya ce to ba shi kenan ba
ina ce yarshi ce? Kowa yayi shiru har da ni din
saboda ba zan iya ci gaba da yin kukan a gabanshi
ba, jimawa kadan sai kuma yayi tsaki kafin ya
sake cewa amma bai kyautawa kanshi ba da ya
bari a ka maida shi abinda a ke cewa an maida shi
din, bari in je wurin Mallam Sule mu tafi wurin
nashi tare muji yanda za a yi.
Umma ta ce, To Ubangiji yasa muji alheri, ya
ce amin. Nayi kukan bakin ciki a wannan lokacin
har sai da na rasa hawayen a idona, na rinka jin
tanfar ni din komai nawa ya kare ciki kuwa har da
farin cikin rayuwata.
A duk lokacin da Mubarak ya zaunar da ni da
Dufin rarrashina ko ba ni hakuri kan balin da nake
Ciki bana sauraronshi, saboda ni kam can cikin
Zuciyata bana jin haushin Babana da mutane ke ta
97
fadin maganganu marasa dadi a kanshi, nafi iin
Ciwon Mubarak gani nake tanfar inda yayi wani
abu mai karfi da wuri tun lokacin da nayi ta fata da
burin yayin watakila da wannan abinda ya farun
bai faru ba.
To wai sai a yanzu da Babana ya riga ya furta
wannan maganar shi ne suke ta faman zirga-zirga
aje wurin wannan aje wurin wancan ana kamun
kafa wanda bana zaton zai yi wani tasiri don
magana daya kawai Babah Lantana zata yi ta
birkita komai shi ne kai din ba Dattijo ba ne tunda
ga shi kayi alkawari za ka canza.
Daga ranar da Alhaji iuhammadu yace bari ya
kira Mallam Sule suje wurir Babana zuwa cikar
kwana bakwai ya tura wa Bapaia mutane daban
daban har sau biyar daga ciki akwai tawagar da
Liman ya jagoranta ta Malamai wadanda suka yi
mishi nasihohi a kan muhimmancin bayar da aire
a inda ya dace wato bin kufu'i don a samu zimatu
lafiya fahimtar juna da girmamawar da a ke bukata
tsakanin miji da matarshi.
Haka nan mai unguwa ya jagoranci mayan
unguwa bayanshi Alhaji Muhammadu abokanshi
Sun je har sau biyu.
Yanda na samu kaina cikin kunci da bak ciki
haka Mubarak ba zan ce ya fini ba ne, kawai don
98
ni kadai nasan abinda zuciyata ke ciki, amma ko
daga jin irin aiken da Babanshi ke yi daya bayan
daya an san lura da halin da dan shi ke ciki yasa
shi yin hakan duk wanda yaje ya dawo kuma
maganar guda daya ce ita ce ta ya riga yayi
alkawari don haka ba zai saba ba.
Daga gidansu Mansur ma an turo suma ba su yi
nasara ba. Yaya Dijah da mijinta ma sun zo suma
duk a banza, haka Yakumbo Halima wacce ita
kam kaca-kaca suka sake yi da Babah Lantana, a
wannan lokacin bana iya zaman gida ko da na
mintuna ne, Babah Lantana da Asabe ba su da
wata hira sai ta bukin nawa suna lissafin irin
kwalliyar da za su yi.
Don haka ina idar da sallar Asuba in na mike
gidan Yaya Dijah nake tafiya a hanya nake gama
lazimin da nake yi da addu'o'ina a gidan Yaya
Dijah ba ma komai sai kuka ko kuma muyi shiru
amma duk da halin da muke ciki na bacin rai taja
ta tsaya kan bata yarda in tafi ko ina ba.
To ki tafi ina Maryam? Kuma ki tafi ki bar ni
da wa? Ki bar ni ni kadai? Tambayoyin da ta jero
min kenan lokacin da na gaya mata niyyata ta
barin gida in yi tafiyata in shiga duniya ya fiye
min auren Nalami sauki.
99
Tana maganar tana kallona, yanzu nan za ki iya
tafiya ki bar ni ni kadai? To ni kuma in zauna in yi
me? Ba a karbarwa mutum ne Maryam da na
karbar miki wadannan fitintinun da ki ke rayuwa a
cikinsu, tana fadan hakan ta kama kuka, kuka
Auwa mai tsanani.
Hakan yasa shi kawar da wannan tunanin
saboda sanin da nayi gaskiyar magana ta gaya min
da ana karbarwa dan uwa wani al'amarin na
kaddarar rayuwarshi na yarda da Yaya Dijah zata
iya karbar min don ban taba shiga wata fitina ta
bar ni na shigeta ni kadai ba.
Gaba daya na bijirewa Mubarak na daina
sauraronshi na daina shiga gidansu gani nake
tanfar har da sakacinshi ya kara jawo min abinda
Babah Lantana tayi min na hada ni da Nalami.
Kina nufin ke kin fini shiga fitina ne yasa ki ke
nema ki hada min da wulakancinki Kan halin da
nake ciki? Tambayar da yayi min kenan a ranar da
ya biyo ni gidan Yaya Dijah na ki fita ia ba shi
umarnin shigowa har cikin falonta in da nake
kwance tunda har falon mijinta da ya fara shiga na
ce ba za ni ba.
Niyyata yayi maganarshi ya gama ban ce mishi
uffan ba amma ban san yanda aka yi ba hakan ya
100
gagare ni, na' samu kaina da tambayar menene
fitinarka ba abinda kake so aka yi ba?
Zuba min ido yayi yana kallona cikin
matsananciyar kaduwa me yasa ki ka gaya min
wannan maganar? Na kawar da kaina gefe don kar
in ga kallon da yake yi min. A hankali na ce ai ba
yau ka ke ganina ba.
Yayi maza ya ce kuyo Maryam kwadayi ne da
ni a kan karatunki ganin badi kamar yanzu kina
shirin fita ne yasa yin hakuri na danne zuciyata.
Dago ido nayi na kalle shi cikin natsuwa na ce
mishi 'Boko?; ya ce eh, na ce to na daina yin shi
daga yau har abada kuma ba zan yi ba tunda dai
saboda shi ne kayi sakacin da kaja min wannan
musibar.
Don haka kara kina kawai ka daina wahalar da
kake yi a kaina tunda bokon da zai sa ka aure ni
ban yi shi ba, ba kuma zaih yi shi ba. Cire ni kawai
cikin matan da za ka aura, koda yake ma ni ban
taba sanin kana son aurena ba in ban da wannan
karon ban taba jin ka ce kana sona ba na soma
kuka.
Ka kyale ni kawai ka fita hanyata bana sonka
bana kuma son komai naka, daga yau kuma kar ka
sake yi min wani aike ba na so ka daina jin
tausayina.
101
Mikewa yayi ya fita daga falon ya tafi ba tare
da ya tsaya yiwa Yaya Dijah sallama ba.
Yaya Dijah ta shigo bayan tafiyar tashi, da kin
daina yiwa Mubarak irin wannan abinda ki ke yi
mishi da wanne zai ji ne? ni dai ban taba jin
Lausayinshi irin na yau ba kinga irin zubewan da
yayi?
Bakin ciki ai baida kyau, ni kuma ban tabbatar
ma za ayi aurenki da Nalami ba don jikina da
Zuciyata ba su yarda da hakan ba nafi zaton wata
hanya zata bullo da zata zame mana wata mafita ta
warwarewar al'amuran kałamanta suka sanya ni na
samu natsuwa har na yarda nayi wanka na shafa
min na sanya daya daga cikin kayanta.
Muje kicin muyi girki ka utanen gida su ji
yunwa ba mu ba su abinci ba, na kalli agogo na ce
ga su Inna ma sun kusa dawowa daga Makaranta,
muna cikin girkin Isiyaku ya sake shigowa ya
gaida Yaya Dijah kafin ya gaishe ni ya kuma
shaida min tare da Mubarak suke.
Yaya Dijah tayi maza ta kalle ni ya dawo, to
kar ki yarda ki sake 6ata mishi rai na ce to na tashi
na fita na same shi gaba daya idanuwanshi sun
kada sun yi jazur.
Ki ka ce ba ki tab6a sanin ina sonki ba saboda
ban taba gaya miki ba? Shiru nayi ban ce mishi
102
komai ba, ya sake yi min wata tambayar shi yasa
ki ka nemi wulakanta ni saboda. wasu suna gaya
miki su suna sonki?
Wani shirun na sake yi ban tanka mishi ba, to
tunda ban taba cewa ina sonki ba, yanzu a wane
matsayi ki ka ajiye ni ke nan? Ban kalle shi ba na
ce mishi kayi hakuri, ina gaya mishi hakan fushin
da yazo da shi ya gushe.
Rannan ina kwance a dakina cikin dare idona
biyu bacci ne ya gagare ni, in ban da sakar zuci
babu abinda nake yi, in saka wannan in kwance, in
saka wancan. Aurena da Nalami da kullum Yaya
Dijah ke cewa bata tabbatar za'ayi shi ba saboda
jikinta da zuciyarta ba su ji kamar za'ayi shi ba.
Kullum kara matsowa yake yi, Babah Lantana
da kawayenta tare da 'yarta sai shirye-shirycnshi
suke tayi ko a ina take samun kudin a take ta
kashewa oho.
Ni kam cikin zuciyata ban tabbatar da maganar
ta Yaya Dijah ba tunda ban hango wani juyi da zai
zo ya hana aukuwar auren ba, in dai ba wata
kaddara ta Ubangiji ba ne tunda dai komai na
auren Babah Lantana ta sayo irin wanda taga yayi
mata daidai.
To haka zan zauna in yi ta zuba ido ina kallo
har ranar auren yazo a daura a kai mishi ni? In har
103
aka yi haka kuma to me zai faru? Me zai biyo
bayan hakan? Wanne hali zan shiga? Wacce irin
rayuwa zan yi a gidan Alhaji Nalami?
Rayuwar aure da Alhaji Nalami to a ya ya zata
kasance ke nan? Wadannan sune jerin tambayoyin
da suka addabi zuciyata, da na zurfafa cikin tunani
mai tsanani sai naga aurena da Nalami kamar baya
cikin jerin biyayyar da ya kamata in yi wa Babana,
domin shima sa shi aka yi ba ra'ayin kanshi ba ne
yin shi.
Ita kuma wacce ta hada din da ta hango wani
alheri a ciki komai kankantarshi to da bani ta tura
ba tunda ni kam ai bata nufina da wani alheri, to
haka zan zauna in yi ta yarda kullum Babah
Lantana sai ta cuce ni ta cuci Babana?
Ina kawowa nan na mike na sauko daga kan
gadon na tsallake shimfidar Asabe da ke kwance a
kasa na bude kofa nayi waje ko ban tafi na bar
gida ba a yau ina son ganin yanda duhun dare yake
in da hali ma kuwa ina ganin tafiyata kawai zan yi
in yaso bayan wucewar ranar auren na dawo.
Sannu a hankali cikin sanda na nufi kofar
gidanmu, zare sakatar na sake jawo kofar a hankali
na rufe don kar in bar musu kofa a buda bayan
kuma dare ne kasancewar dama kudina a kulle
suke a bakin zanina yasa ban tsaya tunanin komai
104
ba na kama hanya, hanyar baya na yi nufin bi don
kar wani tsautsayi yasa in gamu da wani don in yi
nisa da gida kafin gari ya waye in san in da na
nufa.
Ban yi wata tafiya mai yawa ba naja na tsaya
cak saboda muryar da na jiwo a bayana tana
tambayata ina za ki cikin daren nan?
Kadan ya rago in karta da gudu saboda
tsananin kaduwar da nayi in ban da kawai a
kowane hali na kasance ko na samu kaina muryar
da na jin ba za ta taba bace min ba, in dai ba
Mubarak ba ne wannan to Aljani ne abinda naji
uciyata tana gaya min ke nan, to shi kuma me zai
fito da shi waje a cikin duhun daren nan a kuma
daidai wannan lokacin na karfe biyu da rabin dare,
in ban manta ba abinda na gani ke nan a dakinmu
kafin fitowàta.
Ina kike nufin zuwa a wannan lokacin? Kina
nufin tana da asara in ki ka aikata wani abu
makamancin wannan da kike shirin aikatawa? Ai
bata da asara, watakila ma abinda tafi son gani ke
nan.
Kalaman nashi suka sanya zuciyata ta
sakankance cewa lalle shi ne ba wani aljani ba,
don haka na juyo muka fuskanci juna, hasken farin
105
wata yayi dalilin haduwar idanuwanmu nan take
na soma kuka.
Kawo hannunki kiji, kawo hannunki kiji irin
abinda kirjina ke gaya min, kawo hannunki ki taba
nan din nan ban ba shi hannun nawa ba sai dai na
dcga idona na kalli nan din da ya ke nuna min,
mazaunin zuciyarshi ne.
Kwana nake yi ina zaune Maryam ban samu
mutsuwar da na iya dora kafadata a kan shimfidata
ba shi yasa nake barin dakin in fito waje