Showing 9001 words to 12000 words out of 27017 words

Chapter 4 - Halin Rayuwa Book 2 Hausa Novel Complete

Sodangi   

28 Jan 2025

185

na tozartawa da take yi
mishi, koda a bayan idonshi ne balle kuma abin ya
kawo kan idonshi.
Raina ya kai matuka wajen 6aci jikina har
yana rawa na gaji da irin wulakancin da a ke yi wa
Mahaifina a kan idonshi, a kan idona saboda raini
da tozartawa. Ban san yanda aka yi ba sai kawai ji
na nayi na bude baki ina cewa Babah Lantana,
Babana ko ya baro garinshi da danginshi ai kuma
bai yi kama da wanda ya aikata abin kunya ba.
Don kuwa bai da wata alama ta rashin mutunci a
tare da shi.
Tana jin haka ta zabura ta mike da ke nake ko
kuwa rashin kunyar taki ta kai ma za ki zage ni nc?
ko ba da ni ki ke ba ai cin mutuncin mahaisina kia
ke yi a gabana da kuma 'ya'yan da ke da su ya
rufa muku asiri.

46

Ta shiga zage-zage tana dura min ashar, ni
kuma ina daki ina fadin a'a haka kawai kullum sai
kin wulakanta shi yana kallonki don kawai kin ga
baya yi miki magana? Ana cin arzikinshi ana
kushe shi? Babana in mutumin banza ne zai rike
miki 'ya'yanki ne?
Asabe tasa kafa ta taka min shimfidata kamar
yanda ta saba yi kullum, maimakon .in karkadeta
kamar yanda na saba sai na kalleta na ce mata
gaskiya wannan wulakancin ya ishe ni haka ke ki
taka min shimfida sannan a zagar min ubana ina ji,
ya isa haka.
Da sauri ta mike ta zauna a tsakiyar gadon, ke
yarinya ina ganin fa wani abu yana yi miki yawo a
kai, ni sai in sauke miki shi bari kiji in gaya miki
na harareta na ce kai haba yarinya ai tana bayan
uwarta.
Ta zuba min ido, to ba zan daina ba yi abinda
za ki yi ta sake tattakawa, na fita naje na tsaya a
kofar dakin Babah Lantana don rabon da in shiga
dakin har na mance da lissafin tun dai ranar da ta
mare ni a kan na taka mata sabuwar ledarta.
Naja na tsaya daga waje na ce Baba ya amsa na
gaishe shi kafin nayi mishi bayanin abinda ke
faruwa na taka min shimfida da Asabe ke yi
kullum.

47
Kan ya ce komai sai kawai naji Babah Lantana
ta karbe maganar, ai nan karar Asabe ki ka vi
wurin ubanki ke nan ga mai uba ko? Aiya sannu
mai uba yiwa wacce bata da uba wulakanci. Dadin
abin shi kadai gare ki na juya zan koma dakin
saboda jin shi Baban nawa bai ce komai ba.
Sai naji tana cewa kai ku kam da kuna da wani
asali ba a san irin iya shegen da ki ka yi wa
mutane ba. Na ce uba ai shi ne asali Babah, ai ni
da asalina a ka ganni tunda a gidan ubana aka
ganni wanda ya rasa uba ai shi ya rasa asalirishi.
Gari na wayewa nayi duk abinda na saba yi na
yau da kullum dina, ia jira Babana ya fita sai
kawai na leka na kira Isiyaku tare da yan
Almajiran nan dama na gaya musu kar suyi nisa.
Gaba daya kayan dakina na fitar da nawa da
wanda ba nawan ba na share dakin tas na cire
cinyayyar ledar da ke ciki na wurgar da ita ina
aikin Babah Lantana tana jaddada min in dai
hankali da kayan Asabe don ita duk kayanta masu
tsada ne.
Ban tanka mata ba na dauke yar shimfidata
daga kasa na baje ta karkashin katifar da ke kan
gadona sannan na maida katifar akai na jawo wani
tsohon zanina na shimfida na gyara komai na
maida kayan na ajiye kofar dakin ma na sanya

48

mishi sabon labulen da Yaya Dijah ta bani sanda ta
gaya.min abinda zan yi ban iya ba, sai yau na
kunna turaren tsinke.
Nayi wanka nayi kwalliya suma su Isiyaku na
ce sujeisuyi wanka su dawo na ba su kudi na ce su
sayi sosa da sabulu na mika masu kwalbar
Vaseline din da, dama yake boye cikin kayana
bana amfani da shi.
Daidaddare ina idar da sallar Isha'i na dare kan
gadon nayi kwanciyata gabana sai harbawa yake
yi, Asabe ta shigo ta ganni kan uba' abinda ta fara
fadi ke nan kafin taci gaba da cewa, ai kema kin
san ba zai taba yiwuwa ba k ce za ki dawo da
kwana a gado. Za ma ki fito da shimfidarki duk
inda ki ka kaita ko kuma ki san nayi saboda ba za
ki hau gadona ki matse ni ba.
A lalace na kalleta na ce mata kuna da gado ne
a gidan nan? Ai duk wani gado da yake cikin
gidannan in ba ki sani.ba in gaya miki na Innata
ne, na sake kallonta na ce ina ce wannan ne ki ke
cewa naki? Kan ta bani amsa na ce mata ba ki da
kyau ba, don kuwa wannan gadona ne da na gada a
wurin mahaifiyata, kin kuma san kayanta ba zai
zamo na baitilmal ba, tunda tana da magada.
Kace-nacen da muka fara yasa Babah Lantana
fitowa tana tambayar Asabe menene? Ta tsaya

49

tana yi mata bayani, nima ina daga kwance ina
mita tare da kunkunin da ake iya jiwowa.
Haka kawai ni da gidan ubana an zo an takura
min, in gaskiya ne abinda ake fadan kowa yaje
gidan ubanshi ya zauna mana, wannan gadona ne
da uwata ta mutu ta bar min a ka zalunce ni aka
kwace min shi a ka maida ni kwanciyar kasa ba
kuma zan sake yarda da hakan ba, sai dai duk
abinda za ayi ayi amma ba zan sauka a kai ba."
To ai sai ki gyara ku kwanta tare ko? Na ce a'a
ba mai sake hawa min kai ai bata da gadonta balle
ta ce ana ta kason take hawa,
Hankalin Babah Lantana yayi matukar tashi,
bata saba ganin ina yi mata rashin mutunci irin
wannan ba, wata kila kuma bata taba zaton irin
wannan ranar zai zo ba.
Ni ki ke gayawa wadannan maganganun? Na
ce oho, ni dai na gode ina da uba kowa ya san shi
dangin uban ne kawai bani da su, yana kuma sona
tunda ko unguwa bai barina in je balle yaje ga
bada rikona wurin wadan su in je ina zama agola,
sai dai a kai mishi karata ya yi min duka amma ba
ya tura ni gidan wasu da sunan riko ba.
Da sauri Babah Lantana ta juya wurin Babana
da ta bari a daki tana yi mishi magana irin wacce
ta saba, wato kana jin rashin kunyar da 'yar iskar

50

yar nan taka take yi wa mutane: amma kaja
bakinka kayi shiru, kayi wani shememe a kwance
kamar gawar sababi ko? To tashi ka bani wuri don
a kan ka abin'zai kare tunda kai ne ka rasa abinda
zaka haifa a duniya sai tyar iska.
Tashi ka gani in sauke katifar inibáiwa Asabe
ita kai ka san nayi, don ba zai yiwu,ita tana gado
Asabe tana kasa'ba.
Ina jin haka nayi maza na yiwo waje don nasan
abu ne mai sauki Babana ya sauka a gadou Babah
Lantana ta dauki katifar ta baiwa Asabe ita.
Dakin na shiga na kara kallon katifar da Baban
nawa ke kwance a kai sai da na fito tsakar gida sai
na ce mata, Babah in dai wannan katifar ce to ba
taki ba ce ta Innata ce, don haka ko kin fito da ita
zan karbeta.
Shiru tayi bata tanka min ba, ina shiga dakina
na gane hikimar da Babah Lantana tayi min
saboda ganin Asabe da nayi kan gadon a kwance
ta babbake ko'ina.
Ki bani gadona na fadi hakan tare da kokarin
janye katifar da ke kan gadon ban san yanda a ka
yi ba sai ganina kawai nayi muna wani irin dambe
ni da Asabe, danbe mai tsanani irin nà kwatar kai.

51
"Dake ta Asabe, bugi ja'ira kar kiyi mata da
wasa. Abinda Babah Lantana ke gaya mata ke
nan.
Sallau ya dogara sandarshi da yake
dindingisawa ya fito daga dakinshi kwanaki tara
da yin abin har lokacin bai gama warkewa ba.
Babah kenan, za ki kara ba Mama? Iyaye suna
yiwa ya'ya tattalin abin arziki suna gudarwa
ya'yansu fitina amma ke kullum cikinta ki ke jefa
su.
Babah Lantana tayi maza ta juya gare shi ta
kafa mishi wani gigitaccen mari kau! Tanfar ba shi
ta gaurawa irin wannan marin ba, bai motsa ba
daga yanayin da yake, ni kam ko sau nawa za ki
maren ai zan gaya miki gaskiya tunda dai an ce
min uwa ta kwarai tana yarda da shawarar
ya'yanta matukar su din sun kai munzali na
mallakar hankali.
Ke Asabe in kin yarda ki bar fadan nan, fada
ne fa na rashin gaskiya yarinya tana zaune a gidan
ubanta mun zo mun kankane komai ai da gaske ne
kowa a nuna mishi gidan ubanshi mu tafi mana.
Sallau ne yasa sandarshi ya raba tsakanina da
Asabe muka rabu da yake daga ni har ita babu
wanda yaji alama na dukanmu muna son rabon da
a ka yin sai dai hakan bai sa na yarda da mu kwana

52
mu biyu a kan gadona ba, bałe aje ana fito da
katifar Babana a bata shi a bar shi a kan wayar
gado.
Duk abinda ke.faruwa Babana yana daki yana
jin komai amma bai ce uffan ba, har a' ka yi aka
gama ina jin ko shi. ne abinda yafi 6atawa Babah
Lantana rai ta shiga-daki ta figo gýalenta ta fito
tana fadin zo Asabe. fito nan yau, kam in kai ki
gidan uban nan naki da kullum:a ke yi min
gorinshi.
Ta tasa ta a gaba suka fita suka bar gidan, naje
na kulle kofar gida nazo na ihau gadon.na/kwanta,
tausayin Babana yayi matukar kama ni, babu
abinda yafi komai tsayawa a raina irin kifin nan da
Babah Lantana ta jefawa laya abaki ta daure: da
zaren ilo tasa a ka je aka jefa a rafi, awai yan
uwanshi su cinye shi a haka.
Zuciyata ta raya min acewar wata kila yi tayi
don ta daure bakin Babana komai tayi kar ya ce
mata komai, tunda ga skir a yariza ko ne, za'ayi a
gabanshi ba zai bude bakinshi ya ce don me ba?
To amma yayi ta zama a haka ke nana? Wannan
shi ne abinda yafi komai damuna.
A haka har gari ya.waye na tashi nayi sallah
naje na gaida Babana, na kama hidimomin gida na
Byara gidan tsaf lungu-lungu duk inda ya dade ba

53

a gyara ba ma na gyara shi komai yayi tsaf
Babana ya fito daga daki yasa hannu ya dauki
kwandonshi, kasuwa yake nufin tafiya, nayi maza
na' 'ce mishi "Lah, Baba har za ka tafi kasuwar ba
ka karya ba?"
Cikin' natsuwa ya kalle ni ya ce min da wani
abu ne a gidan? Na ce mishi eh Baba, ya ce min to
ya nemi wuri ya zauna a kan shimfidar tabarmar
shi na kawo mishi lafiyayyan abin karyawa ya
karya abinda ya dade bai samu hakan ba don tuni
Babah Lantana ta daina ba shi abin karyawa yaron
nan ba yana nana a ciki ba?
Na ce eh Baba, ya ce to ba shi mana ko babu ne
in rage mishi a nan? Na ce akwai na diba naje na
kaiwa Sallau na dawo na zauna a gefenshi, gabana
ya fadi, ganin yadda wuyan rigarshi tayi dikin-
dikin.
Baba wannan rigar taka ai tayi datti ka canza
wata mana, ya sunkuyar da kanshi ga rigar alamar
yana kara dubata, ai duk rigunan nawa masu datti
ne, na ce to bani in wake maka su. Ya ce To kafin
.ya sake cewa ko ki bari sai gobe saboda sabulu.
Na ce bani kawai Baba akwai sabulu, ya ce to.
Isiyaku ne ya wanke min kayan ya goge su inaa
kallon yanda suka tsufa suka zama 'yan fake-fake
saboda jin jiki yayinda zuciyata ke tuna min da

54

dadewan da nayi ban ga Babana da sabon dinki ba
ko da kuwa da sallah ne.
Komai nashi a hanmun Babah Lantana yake, ita
kuma bata da adaloin cewa shima ya yi wa kanshi
don a gha mijinta fes ta kanta da 'ya'yanta kawai
take yi ko ni ma da zaninshi nake jira in daura to
da yanzu ta kai ma ba ni da na daurawa don tun
sallar farko da Babah Lastana tayia gidanmu bata
sake sawa an yi min sabon dinki ba
Rannan a kicin nayi girkina ban je zaure ba,
muka zauna tsakar gida muka yi hidimominmu na
zuba a kwano na baiwa Ísiyaku ya kai wa Mansur,
ni kuma na dauka da sauri naje na kaiwa Babana,
na zauna na tsare mishi tumatirinshi ina yi mishi
cinikin, yayinda shi kama ya koma dan lungu yaci
abincinshi saboda Babana mutum ne mai kunya.
A hanya ina rike da kwanon abincin da na kai
mishin ina tunanin daga yau in dai zan yi girki to
kuwa zan zuba in kai mishi sannan ba zan sake
barin Babah Lantana da wankin shi ba, balle yaje
yana yawo dikin-dikin.
Yana dawowa da yamma naje na wanke
bayangida na kai mishi ruwan wanka yayi ya fito
na kawo mishi wankakkun kayan shi ya saka yana
tayi min addu'a, naji dadi cikin raina har ina

55

tunanin ashe dai in ban da Babah Lantana da
Babana bai canza min ba.
Kwana uku da tafiyar Babah Lantana sai ga ta
ta dawo, tsofaffin kawayenta suka dawo da ita, su
Delu da sauran su. Suna kallona ina kallonsu ban
ce musu kala ba sai gyada kai suke yi nuna alamar
mamaki, in gumu ta gumu kuma su juya suyi kus-
kus din su.
Wata kila don a kaina suke maganar yasa suke
yin kus-kus din don daga baya naji su suna cewa
ai dan halal bai manta mafari, to ita Lantana da ta
samu fili ta mike kafa sai ta ce babu shegiya sai ni,
Ummm in banda dai hannunka bai rubewa
yanke shi ka yar kuma Hausawa suka coe wai naka
sai naka yaushe zan sake shiga wannan maganar?
Ko ni cikin zuciyata na yarda da maganar Delu
cewar da sa hannunta Babah Lantana ta samu yin
abubuwan da ta yi wa Babana, don haka na
kudurawa raina wannan karon ba zan taba yarda in
ga za a sake yi mishi wani abin in zuba musu ido
ba, sai dai ko suyi a boye amma ba kiri-kiri ba irin
na da.
Suka fito suka wuce ni a tsakar gida ina jin
Delu tana fadin lalle wannan yarinya ta rike, ita
kuwa Babah Lantana fadi take yi, ai ta wuce duk
yanda ku ke zato, ni kuwa na bisu da kallo a

56

zuciyata na ce duk sun kode sun yamutse babu
wata mai kyan gani a cikinsu in banda Babah
Lantana saboda ba su sake samun wani mai
tsautsayin a ka ba da zai kwashe su a matsayin
aure ba.
Washegari da safe na shiga kicin na koma can
lungu ina aikina na bar wa Babah Lantana nata
wurin da na tabbatar zał isheta, tana isowa sai taja
ta tsaya daga waje, to fito ki bani wuri ko? Don ba
zai yiwu in zauna ni da ke a ciki ba ga kuguna ga
naki. Mai wuri yazo sai mai tabarma ya nade, nayi
kamar ban ji ta ba, ina ci gaba da aikin da nake yi
Ko ba ki ji ni ba ne? na ce ki dauki kayanki ki
koma zaure ina ce dama a can ki ke aikinki? Na ce
gaskiya ba zan rinka girki a zaure ba, bayan ga
kicin a gidanmu, iye?
Nayi shiru ko kallon in da take ban sake ba, to
ba ri yazo ya raba wannan fitinar don na gaji da
rashin kunyar da kike yi min ta ju ya ta tafi ni
kuwa nayi girkina na zuba na zuba yanda na saba,
naje na kaiwa Babana wurinshi na dawo da
kwanukan sannan na zauna naci nawa yara ma
suka ci nasu suka watse.
Kwana biyu a jere Babah Lantana bata girki .
bata baiwa Babana komai sai in ya fita tasan
abinda taci ta baiwa Sallau, wai ba za ta sake yin

57

girkin ba sai ya raba rigimar da ya hada ya hana ni
shiga kicin don yin komai tunda ai kicin na matar
gida ne.
Ni kuwa komai nayi in zuba da yawa in kai
mishi ko mai fura da nono mai kyau na gani sai na
saya na kai mishi ko ta lura ta gane bai samu
matsalar da take so ya samu ba ne, tunda in dai
don yayi magana tayi hakan ai tasan ba zai yi ba
saboda ita tayi mishi wannan sanadin.
A karin banza ga koma shiga kicin din tana yin
girkin ga kuturin nawa ga natan.
Gaba daya al'amura suka cakudewa Babah
Lantana saboda ta gane kwata-kwata na daina
tsoronta, ya' yanta da take sawa su azabtar da ni
kuma ta gane ba zai yiwu ba saboda su dukansu
sun tsorata da abinda ya samu Sallau.
Rannan ina zaune a dakina sai ga Asabe ta
dawo har da Jakarta da dah ta tafi da ita a kan za a
kaita gidan ubanta ita ma. Ina ganin ta na daga
hannayena duka biyu sama na ce Ubangiji na gode
maka da kasa uwata ta haife ni tare da ubana da ka
jarrabe ni da maraici ma ba ka jarrabe ni da na
uban ba sai ka rufa mion asiri ka zaunar da ni tare
dashi.
Ka kuma sa shi ya so ni bai ta6a yarda da
shawarar mugaye na ya bada rikona ga wasu ba,

58
na shafa a fuskata. na gyara zamana a bakin
gadona.
Da wa ki ke wadannan maganganun? Tayi
tambayar a fusace na ce da wanda ya tsargu tunda
ni dai ban ambaci sunan kowa ba, ina zaune a
gidan ubana kuma to ai babu wanda ya isa ya hana
ni 'yancin yin magana, haka kawai in mutum yaga
abinda nake yi ban yi mishi ba to kowa yaje gidan
ubanshi mana.
In da gaskiya cikin lamazin ai cewa aka yi kije
a kai ki wurin naki. don ki huta gorin da ake yi
miki to sai kuma ki dawo mana yau?
An dawo din sai kiyi abinda za ki yi na ce babu
abinda zan yi sai gori babu kuma mai hana ni.
Muna cikin haka sai ga Isiyaku ya shigo da
saurinshi, murmushi yake tayi alamar yana cikin
farin ciki, na kalle shi na taya shi murmushin dona
in zolaye shi, na ce mishi yaya na gan ka da
jallabiya har da bagaruwa da dabino, ko
makwabcinku Alhaji Madugu ya dawo ne?
Yaja wani mummunan tsaki kafin ya ce na
rantse Anti Mero da gangan kike yi, Alhaji
Madugu da ko katangar gidanshi bai yarda
taba ba shi ne zai dawo Umra ya bimu da tsaraba
irin wannan? Yaya Mubarak ne wajen mu goma ya
Daiwa ya shiga lissafa min yaran na gidaje daban-

59

daban, na ce Ubangiji ya karba musu badar da
suka yiwo, addu'o'in da suka yi mana ya karba
mana ya ce amin.
Dadi mai yawa ne ya kama ni don kuwa ba
karamin kewar Mubarak nayi ba, dan sauki-saukin
abin ma shi ne Mansur ya rage min kewar tashi da
ba karamar waiala nasha ba.
Za ka share zauren nan ne? Isiyaku yayi
murmushi cikin yanayin nokewa, gaskiya kiyi
hakuri Anti Mero gida zani inyi wanka, in sa
kayana zan je in raka Yaya Mubarak sallar Juma'a,
na ce to babu laifi sai kun dawo.
Na koma daki na zaro tsintsiyar zaburi na nufi
zaure don in kara kalelece zauren saboda in yazo
ya samu wurin cikin tsabta tunda nasan
saukowa daga Masallaci nan zai zo.
Ina sharar zauren ina lissafin rabon Mubarak da
gida a zuciya, na ce kwana ashirin da uku daidai,
kwanakin sun tafi da yawa al'amura masu dama
sun faru a bayanshi ga shi dama mun dade babu
wata mu'amallah a tsakaninmu tun kafin tafiyarshi
hidimar kasa, ko da dai shi ba mai hira ba ne balle
in ce zamu baiwa juna labarai masu yawa.
Ni kam zan yi kokari in koyi ba shi labarin
abubuwan da aka yi baya nan, ina cikin haka sai
kawai naga wata gabjejiyar kafa ta tako cikin

60
zauren, in daga ido don ganin mai kafar bakon
Babah Lantana na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login