Showing 21001 words to 24000 words out of 27017 words

Chapter 8 - Halin Rayuwa Book 2 Hausa Novel Complete

Sodangi   

28 Jan 2025

188

in yi ta
zirga-zirga tsakanin gidanmu da naku, tsoro nake
kar su fake ni su sace min ke suyi sanadin shigata
cikin halin da yafi wanda nake ciki.
Tunda na gane abin da suke son ganinn nayi
kenan to amma yanzu da ki ka fito din nan za ki
tafi ban sani ba yar uwarki bata sani ba, me ki ke
nufi da yin hakan'? Kina nufin za ki iya bada kanki
ga wani ne?
Kin san abinda barin gida ke nufi kuwa
musamman wurin 'ya mace? Kina nufin za ki iya
tafiya inda za ki rayu ba tare da ni ba yar uwarki
ba? Kina nufin in akwai alheri a cikin tafiyar taki
ni ba zan baki wannan shawarar ba?
Don me ki ka shirya tafiya ba tare da kin nemi
mu tafi ni da ke ba? Ke ce ba kya sona ki k: cewa
ni ne saboda kawai ban ta6a buda baki na gaya

106
miki ba, ban taba zaton sai na furta miki da fatar
baki ba, baki ai yana furta karya Maryamu, zuciya
kuwa takan tilasta gabobi suyi bayanin abinda ke
cikinta.
Ban iya cewa Mubarak komai ba saboda kukan
da nake tayi. Yi min alkawari a yau a in da muke
tsayen nan a cikin sararin nan na Ubangiji cewar
ba za ki taba fita ki tafi wani wuri ba tare da kin
gaya min ko kin gayawa 'yar uwarki ba.
Ki kuma yi min alkawarin ba za ki ta6a auren
wannan mutumin ba ke ba shi kadai ba Maryamu
yi min alkawari na wani ba zai taba taba min ke
ba.
Nayi maza na gyada kaina tare da furta kalmar
nayi da bakina, duk kuwa da ban san yanda zan yi
in cika alkawarin da yake tasa ni ina yi mishin ba,
to muje in maida ke gida ki kwanta.
Nayi maza na girgiza kai nuna alamar a'a, cikin
nutsuwa ya dago idonshi sama na tsawon lokaci
kafin ya dawo da kallon nashi gare ni, kina ganin
zai yiwu muyi ta tsayuwa a nan har gari ya waye?
Da sauri na ce mishi eh, ya girgiza kai a
hankali nuna alamar a'a mutane za su yi mana
mummunan fahinmta marasa tunani daga cikinsu su
zarge mu da abinda bai kamata zargin zai fi
tsanani a kanki ba zan so ayi hakan ba, don zai iya

107

zamowa bata suna zai iya zamowa dalilin da Baba
zai yi fushi da ke, ba zan ji dadin hakan ba, ina so
ki rabu da shi ne lafiya kin gane? Na gyada kaina
nuna alamar na yarda.
Muje in kai ki gida, ban sake yin musu da shi
ba ya tasa ni a gaba sai da yaga shigana cikin
gidanmu har sai da na maida kofar na kulle sannan
ya juya ya tafi.
Na sake yin wata sandar a hankali zan shiga
dakinmu, sai kawai naji kofar dakin a kulle,
abinda ya tabbatar min da cewar Asabe tana kallon
fitana daga dakin bata dai yi min magana ba ne,
kawai sai da taji na fita na bar gidan ta mike ta
rufe kofa ta koma tayi kwanciyarta.
Yaya zan yi? Abinda na tambayi kaina lokacin
da na taba naji kofar dakin a kulle, fita zan yi in
koma inda na baro Mubarak ko kuwa zama zan yi
a nan in jira gari ya waye ta tashi ta bude in shiga?
Ko kuwa sa hannu zan yi in buga kofar don taji na
dawo ta tashi ta bude min in shiga? In yaso kowa
ma yasan na fita da daddaren.
Har na matsa jikin kofar da nufin fara bugawa
sai kuma naga kai to in Babana ya fito ya tambaye
ni ina naje a cikin tsohon daren nan in ce mishi
me? In yi sanadin da zai yi bakin ciki? Kai ba zan
iya ba da in yi haka gara kawai in kwana a tsakar

108

gidan in jira gari ya waye a bude in shiga in yaso
ko don in kaucewa 6ata mishi sai in ce fita fitsari
nayi Asaben ta kulle kofar.
Don haka na shiga kicin na hau kujera na zauna
ina kallon irin berayen da ke zirga-zirga daga kicin
din zuwa tsakar gida da wurin wanke-wanke
wanda yawan ta'adin abinci ya kara haddasawa.
Wajen Asuba naga fitowar Babana zai wuce
ban dakin gidan, nayi maza na kauce daga inda
nake zaune na koma lungu sosai ya gamå abinda
zai yi ya fita ya tafi Masallaci, sai ga Babah
Lantana ta fito daga ita sai zani a kirji tana ganin
kicin dinta a bude ta leko cikinshi tana haskawa.
Satar min naman miya za ki yi? Kamar in
tambayeta ko ta taba ganin inda da ya zamaa
6arawo a gidan ubanshi? Sai kawai naga to a na
me zan tsaya ina irin wannan cacar bakin da ita,
bayan ta riga ta buge ni tayi nasara a kaina tasa
Babana ya dauke ni ya baiwa mutumin da babu
wanda yasan me ke tsakaninsu sai su biyun suka
san abinsu.
Ba fa satan miki naman miya taje yi ba,
iskancinta ta tafi shi ne ni kuma na maida kofar na
kulle ta dawo ta same ta a kulle shi ne ta shiga
kicin din ta zauna don kar ta buga kofar a ji ta a

109

tambayeta daga ina take? Iskanci kamar ya ya? Ta
bukaci sani.
Asabe ta tsaya tana yi mata bayani, ai dama
rana dai-dai ne bata bude kofa cikin dare ta tafi
can wajenshi sai sunyi abinda za su yi sannan ta
dawo ta shigo ta kwanta gajiya nayi jiyan na rufe
mata kofar.
Babah Lantana ta tabe baki ta ce, ki ka sani ma
da ba ki rufe mata ba kin barta ta shiga tayi
kwanciyarta ta huta ni kam yanzu ai bani da sauran
matsala da ita balle har in je ina kai kararta
wajenshi a kan tana zuwa kwanan gida, to a na
me?
Kwanaki tara ne fa kacal suka ragewa zaman
nata a cikin gidan nan, gidan da kullum sai ta yi
wa mutane gorinshi sai kuma ta koma gidan
Nalami, Nalami kuwa wannan matar tashi in dai
tana nan a yanda nasan ta tooo ta dan yi
murmushin iya shege ta wuce ta shiga bayan gidan
tana fadin, dama in mutum ya ce ba zai yi sharar
Masallaci ba ai zai yi na kasuwa.
Duk abinda suke fada ina jin su shiru kawai
nayi saboda ba ni da wani abinda zance musu
huce bakin cikin da suka sanya ni a ciki.
A haka muka kasance a çikin gidan nan har a
ka wayi gari ana cewa saura kwana biyu ne daurin

110
auren nawa abinda yayi dalilin da na zama tanfar
mara hankali saboda tsananin kidima da gigicewa,
babu abinda bai zo ya roki Babana ba amma yayi
shiru bai ce komai ba.
Babah Lantana sai hidimarta take yi, babu
abinda yafi komai. daga min hankali irin tsananin
farin cikin da take ciki, wuni take yi tana dariya
bata gaji ba, kan abinda bai taka kara ya karya ba
ma sai ta kyalkyale da dariya ta bugi cinya tare da
shewa kafin ta ce sai ni Lantana 'yar Babanta,
mata a gidan Mallam Habu mai timatir, kowa yaci
tuwo tare da ni miya yasha.
In rasa in da zan tsoma raina in dan ji dadi nayi
kuka a wannan lokacin har na fige na fita cikin
hayyacina, ga shi bana ci ba na sha nayi
mummunar ramar da na zama tanfar majinyaciya,
wai a irin wannan halin da nake cikin kuma sai
manya su rinka zaunar da ni suna cewa wai in yi
hakuri wata rana sai labari.
Ba don dai kar in yi wata magana na ce na fadi
ba daidai ba ga shi ni kuma a' yanzu nema nake in
rabu da kowa lafiya don gani nake tanfar ba zan
wuce wannan lokacin ba, bakin cikin da ke
addabar zuciyuata zai kashe ni kowa ya huta, da na
tambaye su ni yaushe ne wata ranar nan da kullum
a ke gaya min amma ban taba ganin tazo kan

111
al'amarina ta mayar min da shi abin bada labarin
ba?
A wannan lokacin ko gidan Yaya Dijah bana
iya zuwa saboda rashin kuzari na wuni nake yi a
kwance kamar yanda nake kwana a kwance don
haka ban san abinda take ciki ba amma dai itama
na gaya mata na gaji da jin zancenta na bata
tabbatar za'ayi aurena da Nalami ba saboda wai
jikinta da zuciyarta ba su yardan mata za'ayi
hakan ba.
Na ce to sai yaushe za su yarda? Sai sun ganni
a dakinshi? Daina gaya min haka Yaya Dijah, bar
ni kawai in fuskanci abinda yake gabana, ina fadin
hakan ta kama kuka nima ban tsaya bata hakuri ba
nasa kai na fita na bar gidan, ban sake komawa ba.
Mubarak kuwa sai yazo kofar gidanmu sau
biyu sau uku ban iya tashi na fita ba saboda bani
da jarumtakar yin irin wadannan abubuwan kuma
a wannan lokacin sai nafi sha'awar a ce kowa ya
fita harkata a bar ni kawai ni kadai in yi ta
kwanciyata ina tunanin Innata da sauran abubuwan
da sukai saura.
Bikin nawa ba wani biki ne da Babah Lantana
tayi wa wani sayayya na abin arziki ba, amma ta
shirya kawatashi ta hanyar tara tsofaffin
kawayenta da suka yi gwagwarmayar rayuwarsu

112

tare har ma da Dafau Mai kalangu naji tana cewa
zata kira.
A al'ada ranar sakun lalle rana ce da Amarya
tare da kawaycnta kan tafi yawon ban kwana, sai
cikin dare take dawowa in an je an kamo ta a kawo
ta gida a sa mata lalle, a irin wannan ranar ni na
wayi gari ne a kan gadona ina kwance babu wata
kawa a tare da ni ba a kira min ita ba nima kuma
ban nemarwa kaina ita ba.
Ina daki a kwance ina kallo Asabe ta sha
kwalliya ta fita itama Babah Lantanar hidima sosai
take yi tare da 'yan bukin da suka fara zuwa mata.
Ina daki ni kadai in saka wannan in warware in
saka wancan wai Nalami Babana ya yarda zai bada
aurena gare shi in zama mallakinshi?
To zai yi hakan a dalilin ya daina sona ne ko
kuwa dai da gaske abin yafi karfin nashi ne?
wannan shi ne abinda yake ta kai kawo a cikin
Zuciyata.
Da daddare kawar Babah Lantana ta sani a lalle
saboda babu wanda ya tako cikin gidan, cikin
dangin Innata da Yaya Dijah don sun ce babu
ruwansu da bikin.
Ni da mai sakun lallen kallon juna muke yi da
ido zuru-zuru ta juya tana fadin oh'oh amaren

113
yanzu suna da abin mamaki babu ruwansu da duka
don an saka musu lalle.
Babah Lantana ta taso daga inda take tana
fadin ai bata yi kukan sakun lallen ba, ita wannan
ai tata rashin kunyar ta daban ce, ni kuma ba a
wannan abinda ni bari ka gani, in na zo na sharara
mata mari ai zata yi mai dalili.
Ta zabura ta taho cikin saurinta da nufin
shararan min marin, wasu cikin kawayenta masu
dan hankali suka tare ta tare da fadin a'a haba mai
shararawa Amaryar tana cikin lalle ki sharara mata
mari me yayi zafi haka?
Ina ruwana ni da lalleta tunda dai bata da
mutunci a sa mata lalle ta ki yin kuka saboda ta
matsu a kaita gidan mijin ko me? A haka dai ana
wasa ana dariya a ka cimma burinta na dukana a
cikin taron kawayenta da ta tara a gidanmu.
Wata daga cikin kawayen nata da naji suna kira
da sunan Lari baby duk da kokkodewarta wai baby
take amsawa, ta matso kusa da ni cikin natsuwa ta
ce min kin gani ko Amarya " yanmata ke yarinya ce
don haka zan gaya miki lamarin duniyar nan sai a
hankali, kar ki yarda kiyi abinda za ki cuci kanki.
Zauna wuri daya kawai ki nutsu kar kiyi abinda
zai je yazo ya dame ki shi lallen nan da ki ke gani
ba karamin al'amari ba ne, wasa da hakkokinshi

114

wurin amarya al'amari ne babba. Shi ke sawa ki
ga wasu amaren sun zama wasu, kar ki yarda ki ce
za ki fita daga dakin nan ki fita waje kin ji ko?
Amarya mai fita da lalle haukacewa take yi kin
ji ko? Na ce mata to, saboda tsoratar da nayi da
irin bayanin da tayi min din.
To ina ruwanki ne da ki ke rattabo mata
wannan bayanin? Tayi tambayar tare da galla mata
harara kai ke daima da dogon baki ki ke, taja tsaki
ta juya ta fita.
Uh'uh Anti Lantana gara in gaya mata ta sani
shi da ai na kowa ne, ai sai kiyi ta fita ta fita. Duk
da bayanin da matar nan tayi min zuciyata bata
hakura ta bar ni na zauna lafiya ba, kai-kawon da
take yi yayi tsanani ko mikewa a gadona gagarata
yayi ina zaune ne kawai ina sauraron abubuwan da
take gaya min.
Daren nan na yau shi kadai ne yai saura min
gari na wayewa za a daura min aure tunda daurin
auren ma na safe a ka ce za'ayi kenan daga nan
zuwa wayewar gari ne yai saura min, to haka zan
zauna shi ke nan magana ta kare ko kuwa ya ya
zan yi?
Shi ke nan sai in zauna a daura min aure da
mutumin da Babah Lantana ta kawo min? da
Babana ne don ra'ayin kanshi yaga zai bada ni

115

gare shi da ba zan yi jayayya da auren ba tunda ni
din mallakinshi ne, to amma Babah Lantana, in
zauna in karasa waycwan gari a Cikin gidan nan
yana nufin na yarda da auren da za'a daura min.
In sa kai in fita kuma ina tsoro saboda bayanin
dakawar Babah Lantana tayi min, ina cikin
wannan kai-kaWon sai kawai na tsoro matsayar da ta
sanya ni mikewa tsaye ita ce ta da in zauna a daura
min aure a kaiwa Alhaji Nalami ni gara kawai in
fita in bar gidan in yaso duk abinda zai faru da ni
ya faru dani a can gaba.
Da wannan tunanin cikin zuciyata nasa kai na
fita daga gidanmu sai dai ban san yanda aka yi ba
ganina kawai nayi na kama hanyar zuwa gidan su
Mubarak.
Ina dosar gidan na hango shi zaune a kan
dakalin kofar gidansu yayi zaman dirshan a kasa
kanshi a sunkuye, har na isa kanshi bai ji motsi ba
saboda ya riga ya shagala kan abinda yake yi.
Na kasa ce mishi komai don ban san me zan ce
mishi ba, kusan mintoci biyu zuwa uku kafin ya
dago kai daga sunkuyon nashi yana ganina ya dan
kadu bai ji isowar tawa ba da sauri ya shiga
goggoge fuskarshi da tafukan hannayenshi duka
biyu.

116

Me ya fito da ke a cikin daren nan? Tambaya
yayi min cikin wani irin yanayi na nuna karfin hali
da jarumtaka ban tsaya ba shi amsa ba sai kawai
nasa kai na nufi cikin gidansu, maimakon in wuce
can ciki kamar yanda na saba kofar wurinshi na
tura na shiga nasa kai na wuce falon na shiga har
can cikin dakin nashi abinda bai taba faruwa ba a
rayuwata hasalima yau ne shigana wurin Mubarak
na biyu.
Can cikin dakin nashi a kayace yake matuka ga
Ramshinshi da na saba ji a tare da shi katuwar
katifa a yashe a kasa tasha shimfida mai daraja ga
tarkacen takardu tare da laptop a gefe sai wardrope
wacce na tabbatar kayanshi a ciki. Gabana sai
faduwa yake yi yana harbawa da sauri da sauri, me
ke shirin faruwa ne? me ya shigo da ni nan wurin?
Abinda ke ta kai-kawo cikin raina ke nan.
Mubarak ya biyo ni har can cikin dakin yaja ya
tsaya a bayana cikin wani irin yanayi na sanyin jiki
da tsorata da abinda yaga nayin me ki ke so a
kawo miki Maryam? Ban tanka ba ban kuma
waiwaya na kalle shi ba, na kai guiwowina duka
biyu kasa na durkusa a kansu, ya sake biyo ni
kasan yayi yanda yaga nayi muka fuskanci Juna.
A hankali cikin nutsuwa cikin wata irin murya
mai laushi da taushi a dalilin karaya da tsoratar da

117
tayi na soma yi mishi magana, zuwa nayi a yau
don in yi maka godiya bisa dawainiyoyinka da
alhairorinka a garce ni.
A sanina ban taba sanin wani mutumin da ya
kai ka yawan alhairi ba ka taimaki maraicina ta
hanyoyi daban-daban da ba zai yiwu in fade su ba.
To me ya kawo wadannan maganganun
Maryam? Yayi min tambayar a sanyaye
idanuwanshi kuma suna kafe a kaina. Na kawar
da kaina daga kallon da yake yi min kafin na soma
ce mishi Babana yayi nufin aurar da ni ga wanda
yayi niyyar bada ni gare shi bana zaton akwai
wani dalili da zai hana shi yin abinda ya shiryan
in dai ba wata kudura ba ce ta Ubangiji.
Ban ki auren don raina maganarshi ko bijirewa
umarninshi ba, naki auren ne a dalilin sanin dalilin
kulla shi da aka yi a yanzu ina cikin wani hali da
ba zai fadu ba, don haka nazo wurinka in roke ka
kayi min wani alheri tunda kai mai alherin ne
kullum a gare ni.
Da sauri ya tambaye ni me ki ke so in yi miki
Maryam? Gaya min shi ko menene shi zan yi miki.
Na sake sunkuyar da kaina kasa sosai kafin na
soma ce mishi, ni din budurwa ce nafi zaton daren
yau shi ne dare na bankwana a tsakanina da kai,

118
don haka nazo wurinka ne in yi maka kyauta daa
abinda nake ganin tanfar naka ne.
Muryata ta soma rawa jikina ya soma kaduwa,
hawaye suka soma gudu daga idona suna zuba
shar! Shar!! Shar!!!! Gaba daya hankalin Mubarak
ya sake tashi, ya tsunduma cikin wani hali da ya fi
kama da kidima.
To menene na wannan kukan? Me ki ke so in
yi da ki ke wannan kukan yanzu a gabana? Na ce
ki gaya min kawai ko menene zan yi miki shi, kiyi
shiru. Nace kiyi shiru.
Kwan! Kwan!! Kwan!!! Muka jiwo
kwankwasa kofar falon nashi, lokacinne na san bai
shigo ba sai da ya kulleta da sauri ya mike wajen
kofar ya bude.
Me ke faruwa ne Ahmad Mubarak? A hankali
naji Umma tana yi mishi tambayar, me ki ka gani
Umma? Ta dan yi shiru kafin ta ce mishi ji nake
kamar ba kai kadai ba ne. Ya sake cewa me yasa
ki ka fadi haka Umma?
Ta canza tambayar da tambayarshi to me ka ke
yi har yanzu idonka biyu? Bakin ciki ne ya dame
m Umma, ina bakin cikin raba ni da Maryam da a
ke son a yi.
Rabuwa kam ai an raba ka tunda gari na
wayewa za a daura aurenta, kai dai kayi hakuri

119
Kamar yau ne za ka ga ya wuce wata rana kuma ai
sai labari, ko ma ka kwanta kar in sake Jin ka a
waje, ya ce mata to.
Ta juya wurinta shima ya maida kofar ya kulle
ya dawo har lokacin ina durkushe a inda ya bar ni
ya sake kai guiwowin nashi kasa ya sake
durkusawa kamar yanda dama yayi muka fuskanci
juna.
Da gaske ne Babana zai raba mu don haka nake
so in yi maka kyauta ta alfarma don ta zamo
girmamawa ga al'amarinka da ke cikin zuciyata.
Yayi ajiyar zuciya mai karfi kafin ya tambaye
ni mecece kyautar taki Maryamu? Ban kalle shi ba
na ce mishi 'BUDURCINA' yayi matukar kaduwa
da jin kalmar da na furta, don kuwa sai da hakan
ya bayyana a fuskarshi, ban yarda mun hada ido
ba na ce mishi karbi budurcin kawai a wurina bani
da sauran bukatarshi bada shi zan je gidan nashi ba
shi yasa nazo' yanzu don in kawo maka shi.
Mubarak ya zama tanfar wani mutum-mutumi
sai faman bari yake yi tanfar wanda yayi wanka da
ruwan sanyi a cikin sanyin hunturu, da kyar ya
buda baki ya soma yin magana, a'a kar muyi haka,
ba sai kin yi min haka ne zan san ina da matsayi
mai girma a wurinki ba.

120
in kin bar shi a nan ma nawa ne, ai nawa i
Maryam zan kuma karbe shi ai ke tawa ce naa
kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login