Showing 21001 words to 24000 words out of 34829 words
miki addu’ar sakaiya ta gari, ban da haka ma tun kafin kiyi min hakan ke xin uwa ce don haka ne ma a yau bani da wata uwar da ta fiki, to in har hakanne me yasa nake cewa ka sake ta kana qi? Sai ya ce ai shi aure ajali ne dashi in wa’adinshi ya cika sai kaga kamar a mafarki.
A wannan lokacin tausayin Ado nake ji, don na tabbatar da daxin komai yake ji ba don gaba xaya al’amuranshi sun sauya, yin su kawai yake yi amma can cikin zuciyarshi ina ganin kamar akwai wani abin da yayi matuqar takura mishi gashi kuma yana dawowa gida
daga kasuwa zan ganshi yana wasu abubuwa waxanda shi kaxai yasan me yake yi.
A wannan lokacin al’amuranshi da yawa sun sauya, mafi yawancin lokaci a yanzu ya koma shigowa gida ne wajen sha xaya da rabi ko sha biyu duk da ba wata jituwa mai yawa ba ne tsakanina dashi, wannan sabuwar xabi’ar tashi ba daxi take yi min ba, amma nayi kamar ban san me yake yi ba, don kar ya xauka na wani damu dashi.
Rannan tun bayan Sallar Magriba ruwan sama ya kece kamar da bakin qwarya, amma Ado bai shigo gida ba da ya idar da Sallar Isha’i, har wajen sha biyu saura kwata na dare, kamar in kulle mishi qofa don in hana shi shigowa xakin in ya dawo, sai naga to na menene yin hakan? Ai kulawama yabawa ne.
Da safe ma haka daga sallar Asuba bai sake shigowa ba sai da ya shigo don yin shiri ya fita kasuwa ban ce mishi komai ba, zai kawo cefane in yi girki amma ba zai tambayi nashi abincin ba, in na ajiye ma ba zai tava ba, a zuciyata na ce shima dai zaman namu ya ishe shi hanyoyin rabuwa yake bi wataqila jira yake yi Mama ta sake bashi wani umarni mai qarfi kafin yayi sakin don tasan dai saboda ita yayi.
Muna cikin wannan zaman da Ado na kowa ta kanshi yake yi, duk rashin mutuncin da yake tatawa kuma kallonshi kawai nake yi, iyaka dai ina yi ina lissafin kwanakin da suka saura casa’in xin su cika
.
I
na zaune
a tsakar gida bayan fitarshi kasuwa sai ga wayar Inna ta shigo, ina vare-vare cikin yanayin rawar jiki na xauki wayar a dalilin na kirata yafi sau talatin bata amsa ba, Hello Inna salamu alaikum.” Duka gaba xaya na haxa mata saboda zumuxi, bata tsaya amsa gaisuwata ba sai ta soma tambayata ni wane irin zama ku ke yi ne ke da wannan yaron?
Da sauri na tambaye ta, wane yaron Inna? Ta ce, mijinki mana, cikin zuciyata nace to itama Inna mijina take kiran Adon? Kafin in soma yi mata bayani kan munanan xabi’unshi da nake shirin gaya mata don in roqe ta ta qara tsaya min da addu’a akan rabuwarmu don ta zo cikin sauqi ba tare da ya cutar dani ba, sai na ji ta soma cewa “kin ga ki shiga hankalinki da ni fa.” Cikin hanzari na tambaye ta me nayi Inna?”
Maimakon ta bani amsa faxa ta soma yi mu ma fa da ki ke ganinmu ba ma wulaqanta
aure mutuntashi muke yi in miji ya zalince mu, kuma mu zuba mishi ido saboda mun san watarana ba zai yi ba, mu wulaqanci ne kawai ba ma yarda da shi ba kuma mayi wa wani, to amma ke na menene yana iyakar qoqarinshi a kanki kullum sai kin wulaqanta shi, kin ci mutuncinshi, da sauri na tambaye ta, me nayi mishi Inna? Tun bayan wannan abinda ya faru na sake yin wani abu ne? ko shi ya kawo karata wurinki don ya haxa ni dake, kiyi ta fushi da ni? Tunda ai dama can
Inna kin sani ba, son mu yake yi ba babu kuma abinda bai yi ba wajen ganin ya taimaka an quntata mana sai kawai nayi ta soma faxin kinci gidan ku na ce miki kinci gidanku da wannan bayanin da kika tsaya kina yi min Inna sake ji an ce min anga mijinki a waje bayan qarfe tara na dare yana zaune to ni dake ne sakarya kawai mara hankali zaku hankatashi ne?
Tuni na soma yiwa Inna kuka sosai ita kuwa bata kula da kukan nawa ba faxa kawai take yi, nan da gobe kamar yanzu in ban ji kin xauki matakin gyara al’amari a tsakaninku ba to zaki yi mamakin abinda zan yi akanki ta ajiye wayarta.
Kuka sosai na zauna nayi saboda na gane itama Inna a yanzu so take in miqawa Ado kaina bata damu da abinda zai biyo bayan hakan ba bata tsaya nayi mata bayanin da zai fahimtar da ita gane shima adon bai da wani kwaxayi mai qarfi a kaina ba tunda ai nayi mishi tayi na saki shi ne bai kula ba, to sai kuma yanzu da zaman namu yayi matuqar yin xaci bama tsami ba sai ta ce ta bani daga nan zuwa gobe da safe to me take so in yi mishi?
Na zauna nan wurin zuciyata sai kake sake take yi ta saqa wannan ta kwance
ta saqa wancan ko abincin rana rannan ban yi ba saboda zuciyata a quntace take.
Wajen qarfe shida na yamma ya dawo gida, alamar dai daga kasuwa yake don dama lokacin dawowarsu kenan. Ban iya xaga ido na kalle shi ba, saboda raina yayi matuqar vaci da abinda yayi min na haxa ni da Mahaifiyata da yayi, ban tava sanin Inna tana iya fushi dani ba in ban da a ‘yan kwanakin nan a kuma sanadin aurenshi, auren da a farkonshi daga ni har ita qin shi muke yi muna neman tsari dashi har ma ni ce mai danne zuciyata in bata haquri akai, to ko kuma menene yayi mata daxi da auren a yanzu oho?
Har bayan Sallar Isha’i ni da Ado babu wanda ya ce wa wani ci kanka, kowa sha’anin gabanshi kawai yake yi, ya fito daga wanka ya sanya kayanshi ya fesa turare kamar dai yanda ya saba yi kullum shirin fita yake yi kamar dai kar in ce mishi komai in bar shi yayi tafiyarshi sai kuma na tuna Inna da kalaman kashedin da tayi min na in ta sake jin an ganshi a waje bayan taran dare zan gamu da ita
.
A
zuciyata na ce uhun in ban da Inna mutumin da ya riga ya mallaki haqoranshi talatin da biyu wanda ba wani ganin juna da mutunci dama can muke yi ba xan gara ma a xan zaman wuri xaya da muka yi shi ne ma aka xan yi wa juna xan alheri a ciki shi ne wai zata yi fushi da ni saboda shi na sani nima wani
lokaci nakan xan ji tausayin shi, saboda matsin lambar da yake fuskanta a wurin Mama a kaina.
Wacce ita xin kuma da gaske madadin uwa take a wurinshi suna kuma son juna yana girmamata babu wanda yayi zaton zai iya bijirewa umarninta a kaina, to amma duk da haka ina ganin ni an takwaran ace dole ni ce zan nemi shiri dashi ba a daidai kuma lokacin da yake fito min da halaye iri-iri.
Qirjina sia harbawa yake yi val-val-val saboda tsananin qin yi mishi maganar da nake shirin yi, sakai yayi ya fita ya miqo hannu zai ja qofar ya rufe a daidai lokacin da na buxe baki na ce mishi ina magana, yaja ya tsaya nuna alamar wai ni yake sauraro.
Sai da ya ji ban sake cewa komai ba lokacinne ya sake dawo da kanshi cikin xakin, kin ce kina magana? Ban iya cewa komai ba in ban da hawayen da suka soma zubowa daga idona, shar-shar-shar tanfar dai ba kukan na wuni ina yi ba.
Maida qofar yayi a hankali ya rufe sannan ya juyo gare ni, me ya faru Humaira? Baki da lafiya ne? ban iya ce mishi komai ba, babu abin da yake cin zuciyata irin tilasta nin da Inna tayi sai na nemi shiri dashi bayan kuma tasan me hakan yake nufi, ta kuma xiban min qanqanin lokaci na na yin hakan, ganin da na yi ya nufe ni da shirin tava ni ya sani kai
gwiwoyina qasa na durqusa ban daina kukan da nake yi ba.
Hannu biyu ya saka ya jawo ni jikinshi nayi maza na zame, me nayi miki Humaira? In wani laifi nayi miki yasa ki wannan kukan na roqe ki kiyi haquri, ki kuma gaya min shi don gobe kar in sake yi miki shi. Rarrashin da yayi min ne yasa ni gaya mishi cewar yana haxa ni da Mahaifiyata.
Da sauri ya ce min ban tava yin hakan ba Humaira, ai nasan tana sonki ba zan vata ki a wurinta ba, ban da haka ma yaushe ne na soma mu’amalla da ita da har zan je ina kai sukarki wajenta? Me ya faru wanda yasa ki ka ce ina haxa ki da ita? Ban kalle shi ba na ce mishi ta ce ni nake saka yawon da ka ke zuwa, ya xan yi murmushi kaxan ya ce bana fita yawo Humaira, hira nake zuwa shagon Sani mai shayi, wurin taruwar samari ne mu xan yi hira in xan ji xan sauqin zuciyata, kema in bar ki ki xan sake.
Ba zan iya zama dake shiru ba in yi ta zuba miki ido ban kula ki ba, gashi kuma a yanzu ina cikin wani hali na canka-cakare, ban san abinda nake ciki ba a yau, ban kuma san abinda zan fuskanta ba, iyaka dai kawai nasan ina cikin wani irin ruxani da ban tava shiga ba, wanda kuma na shige shi ne a sanadin aurenki da nayi.
Hausawa suna faxin wai tsalle xaya mai jefa mutum rijiya, ya kuma yi dubu bai
fito ba. Wani lokaci naka yin tunani in ce da dai ace na sani to da naji kashedin da kika yi min na cewar kar in karvi aurenki in nayi wannan tunanin sai in ce da nayi hakan wataqila da ban samu kaina cikin halin da nake ciki ba, wataqila da rayuwata bata canza ba daga yanda take wataqila da yanzu ina nan ina zamana lafiya ina tafiyar da harkokina cikin kwanciyar hankali da gamsuwa.
A duk lokacin da tunani ya tsananta gare ni na rasa yanda zanyi in warware wa kaina matsalolin da na samu kaina a ciki, sai in ce wa kaina to in sauwaqe miki auren mana in zauna lafiya tunda dama ba da wata kyakkyawar manufa aka karvi auren ba, to in kuma nayi wannan tunanin sai kuma in samu kaina da tambayar kaina, in na yi hakan zan koma kamar yanda da xin nake? Zan iya fidda ke cikin raina, in koma walwala da nishaxi kamar da?
In zan yaudari kowa ba zan yaudari kaina ba, ina son zama dake sai dai kuma abubuwan da nake ciki da barazanar da nake fuskanta za su bar mu mu zauna tare? To in ina cikin wannan barazanar me ya kamata in yi? Shine haquri, haqurin kuma yana nufin dole sia na rinqa yin nesa dake saboda kar in aikata miki abinda zai zamo rashin adalci in tilasta ki yin abinda
bakya so duk da nayi qoqarin yi miki hakan a baya dalilai biyu ne ko uku suka ingiza ni yin hakan.
Na farko dai tsananin matsuwar da nayi a ikanki na biyu jin hirar ku da nayi da Ramla sia na gane har da ita ke zuga ki na uku kuma shine ban hango abinda na hango ba a yanzu, ban ce mishi komai ba, ban kuma tsaya tambayar shi abinda ya han go ba, iyaka dai kawai na miqe na shiga banxaki nayi wanka na fito xaure da farin tawul a qirjina, har lokacin yana zaune a inda na bar shi can cikin xaki na wuce na zauna a bakin katifa bayan na ajiye kayan shafana kusa da ni.
Ko ba ka ce kana sona ba ma ya riga ya zama min dole in baka kyautar kaina tunda abinda Inna take so kenan, zuciyata ce tayi min waxannan kalaman.
Ina magana ne na xan xaga murya kaxan na gaya mishi bai vata lokaci ba ya shigo, kallo xaya yayi min ya kawar da kanshi gefe me ki ke so in yi miki Humaira? Ban kalle shi ba na ce mishi mai zaka shafa min, ya sake kallona da xan guntun tawul xin da ke jikina ya durqusa a gabana yana faxin ba shafa man ba ne matsalar Humaira, abinda nake tunani shine kanwa ko
andre lever sold
ba za su yi min wani amfani ba, na ce to shi kenan nasa hannu na lakato man zan shafawa kaina, sai kawai naga ya karve man ya xaga
hannayen naw aya sagala akan kafaxar shi wai don ya ji daxin shafa min man sosai.
Har Asuba tayi ban iya daina kukan da nake yi ba, saboda dalilai guda biyu, na farko dai in ma Mama taci galaba a kan Ado ta tilasta shi sakina in zama qaramar bazawara kamar yanda dama can tayi buri tunda nasan tana da qarfi akan al’amarinshi, ko kuma aurena dashi ya ci gaba kamar yanda ya kwana yana yi min alqawarin in kwantar da hankalina in saki zuciyata muyi zamanmu lafiya babu abinda zai samu aurenmu.
Babu mai sa shi ya rabu dani ya kuma godewa Inna da ta sanya ni nayi mishi alherin da nayi mishi, to in auren namu ya ci gaba da akan son ran Mama ba tunda nasan ba za ta tava son zamana da xan uwanta tunda tun asali ma ba don a zaunan ta sa shi yin auren ba, zan samu zaman lafiya da kwanciyar hankalin da nake buqatar samu a rayuwar aure na ko kuwa na rinqa zama cikin fitinar Mama kenan tayi min ta yi wa mahaifiyata?
Shi kuwa Ado wanda ya kwana cikin matsanancin farin ciki gani yake yi tanfar matsananciyar wahalar da na gamu da ita a wurin shi ne ta sanya ni kukan da nima na kwana ina yi, don haka ya kwana yana rarrashi da ban baki da faxin kalamai masu nauyi tare da alqawarin zai tabbatar min da cewar shi xin namiji ne.
Na idar da Sallah kenan sai ga Hajiyar Giyaxe ta shigo, na tabbatar Ado ne ya turo ta, kai lalle Ado namiji ne ko ya ya aka yi yaje gaban Hajiya yayi mata wannan bayanin? Oho. Cikin zuciyata ne kawai nayi wannan tunanin, oh’oh sannu Humaira sannu kin ji? Sannu Aishatu sannu da haquri kin ji? Allah dai yayi miki albarka, ya kuma qara rufa wa uwarku asiri ku dukanku ukun, haka aka yi haka nan aka same ku lafiya lafiya sai alheri.”
Sunkuyar da kaina qasa nayi ban iya ce mata komai ba, saboda tsananin kunya ai ma kin yi qoqari kin taimaki kanki kin yi abin da ya dace ayi miki, to amma duk da haka sake shiga ki qara wani wankan don ki qara gasa jikinki sosai, ban yi musu da ita ba.
Ado ya shiga kai-kawo da hidimomi iri-iri ko kunyar su Hajiyar Giyaxe da Hajiya ‘Yar dubu da suka zo gidan baya yi, wai har hira yake yi da su Hajiya ‘Yardubu ta kalle ni ina makure wuri xaya saboda zuciyata ta qi yi min daxi, ta qi yarda da cewar in sake ta tayi walwala taji daxin al’amuranta, musamman da yake na jiwo maganganun da Mama ta gayawa Ado sanda ya shiga wurinta da safe bayan Hajiyar Giyaxe tazo wurina saboda akwai haxakar bango tsakanin cikin xakina da nata.
Amma wai sai Hajiya ‘yardubu ta kalle ni ta ce min oh’oh mahaqurci dai mawadaci, wannan fa shine wai komai wayon amarya
a sha manta, to yau dai Adamu ya zama miji qarya kuma ta qare.
Kuka sosai na kama yi ita kuwa Hajiyar Giyaxe ta soma yi mata magana Hajiya ke dai munin nan naki bai da wani daxi, zo ki tafi gidanki kije wurin naki mijin ki bar min Aishana ta huta, qaryarta bata wani qare ba me akai kuma da maza, da za ki ce mata wani qarya ya qare?”
To haka al’amarin ya zama, shiryawata da Ado sai ta haifar da al’amura masu yawa a ta vangarena dashi dai sai nake ganin tanfar ba a tava son wata ‘ya mace kwatankwacin irin son da Ado ke nuna yana yi min ba, ko kuma don ban tava sanin yanda son yake ba ne, ban kuma tava yin dacen ganin wacce ake son ba ne? oho.
A tsakaninshi da Mama kuma abin ya qara cavewa har ya shiga zullumin shiga cikin gida da dai ace yasan in bai shiga ba ita ba zata zo ba to da ya rinqa daxewa bai shiga don maganganun ba su da daxi, to qa’ida ne kullum sai ta shigo da safe da daddare sannan a gabana ma gaya mishi take yi ba fa a kanta muka soma ganin yarinya takai budurcinta ba, duk ‘ya’yan xakina da kake gani ‘yanmata aka same su yauwa ba sabon ba ka tava mace ka haukace.
To wannan ma har wata mata ce da za’a ruxe
akanta? Yayin da itama Mama take wannan tashin hankali itama Inna nata sha’anin
take yi, aike biyu tayi tana tambayar Ado ya bada lokacin da ya ga ya dace azo ayi min jere a sanya min kayana don mu ma mu ji daxin zama a inda muke, shi kuwa sai yayi murmushi ya ce a gayawa Inna tayi haquri kawai ta huta ai shi xin mace ya nema ya kuma samu an bashi, don haka ya gode da alherin da aka yi mishi maganar kaya kuwa a bar su ba shi da buqatarsu waxanda aka kawo mishi sanda aka kawo mishi matar shi sun ishe shi.
Kusan sati biyu ne da faruwar abin da ya faru a tsakanina da Ado tun lokacin nan kuwa ban sake yarda ya tava ni ba, tun yana haqurin har dai na qure