Showing 30001 words to 33000 words out of 34829 words

Chapter 11 - Mijin Ta Ce Book Two Complete Hausa Novel

Sodangi   

18 Oct 2025

183

sai ya kalle ni ya ce min, ke ga xakin uwarki can tafi ki shiga, kaima ga taka uwar nan jeka wurinta shi kenan kowa ya riqe nashi, magana kuma ta qare dama ita ta ce a baka ita na baka yanzu kuma ta ce ta gano munafurci da raba zumunci in raba na raba magana ta qare kar in sake jin wani ya ce wani abu zan sava mishi.

Cikin kaxuwa

mai yawa Ado ya ce ka raba min aure Baba me nayi maka? Baba bai tanka mishi ba ya wuce ya shiga wurin Zubaida, ga alama a wurinta yake. Inna ta biyo bayana zuwa cikin xaki don ni kam ma ban wani tsaya jin komai ba, tuni na haye kan gadonta na kwanta sai Ado da Mama ne a tsakar

gida, “kin sa Baba ya qwace min mata Mama? Ta ce ka kwantar da hankalinka ai dama ni nasa shi ya baka ita yanzu kuma ba ka san wacce zan sa a baka ba nan da kwana tara ma za’ayi komai tunda na riga na gama komai ai ba zan barka ka zauna haka ba, tunda nasan ka riga ka xanxani daxin mace.

Ba ke ki ka bani Humaira ba Mama kaddara ce ta bani ita ba kuma zan rabu da ita ba, ba kuma na son kowace iri za ki sake bani in gidan da ki ke cewa zan bari ne akan zama da ita zan bar shi zan fita daga harkokin da kike cewa zan fitan miki, zan fita daga dukiyar tashi abinda ba a tsammani na zan mayar dashi zan riqe Humaira ne kawai Mama don ita kaxai xin nake buqata a yanzu.

Kai Ado, tayi mishi tsawa mai qarfi zaka zage ni ne? yayi maza ya ce ba zan zage ki ba don ke uwata ce amma kuma ba zan yarda ki raba ni da matata ba, Mama ban ga abinda tayi miki ba ina kuma sonta.

Ni kuwa ina shiga banxakin Inna na kama aman tun daga falonta har bayan gida da sauri Inna ta biyo bayana tana qoqarin taimakona. Ado kuwa ya juya ya fita ya bar gidan ban san inda ya tafi ba sai dai bai xauki lokaci mai tsawo ba sai gashi ya dawo, kayayyakin ciye-ciye

yaje ya sayo min har cikin xakin da nake kwance ya shigo bai saurari maganar da Mama ke yi mishi na kar ya shiga xakin nan ba haquri yake ta bani wai in kwantar da hankalina kar in ce zan xaga hankalina.

Nayi murmushi na ce babu komai ni kam ai dama a nan nake su suka xauke ni suka baka ni in sun ce in sake dawowa ba zan zarge su ba don haka kaima kayi haquri, ya ce min to me kike so in kawo miki yanzu? Na ce babu komai kar ka damu ai ga Inna in ina son wani abu zata yi min, ya ce to sai da safe.

Tunda Ado yasa kai ya bar gida cikin dare a cewar sai da safe bai sake dawowa ba, babu ma wanda ya ce ya ganshi a unguwar don ina jin Mama tana tambayar ‘ya’yanta sun ga Kawunsu kuwa? Su ce mata a’a Inna ma tayi ta neman shi a waya amma

babu layinshi, ya rufe. Ina jin ta tana faxin ni Binta wannan yaro ko ina ya shiga haka oho. Ban dai ce mata komai ba amma ni kaina a cikin damuwar nake don kuwa nasan yana cikin vacin rai mai yawa.

Cikin zuciyata dai addu’a sosai nake yi mishi don kuwa ina matuqar tausayin halin da ya samu kanshi a ciki wanda kuma a dalilin aurena ne ko da dai na sani a farkon al’amarin ni suka yi nufin cutarwa, amma hakan ba zai rage min komai a tausayinshi da nake ji ba tunda nima a yanzu ba zan iya cewa ba na son shi ko kuma ban damu

dashi ba.

Rannan da safe muna karyawa ni da Inna na kalle ta cikin natsuwa na ce mata “Yau kam in Ado bai zo gida ba Inna zan fita in neme shi a irin gidajen abokanshi da muka jejje, ta ce to ya yi kyau kam hakan duk dai ke ma ba lafiya ke gare ki ba, amma abin ai yayi tsanani daga sai da safe abu ya tafi har kwana uku? Muna cikin wannan maganar sai muka jiwo Babana a tsakar gida yana cewa Mama, yaron nan fa Ado ko kasuwa ba ya zuwa, ta ce rabu dashi ja’iri mara kunya da butulci wai shi nan yayi fushi ne a dole ga mai zafin rai ya bar gida, aje a nemo shi in yaso ya samu hanyar cewa sai an mayar mishi da ita sannan zai dawo to yaje duk inda za shi an hana shi itan yafi ruwa tafiya.

Inna ta ce uh’uhun abin tausayi yana zaman zamanshi dai aka tsoma shi cikin wannan fitinar da ba a sa shi wannan auren ba ai da yana nan yana harkokinshi da ya saba cikin kwanciyar hankali, kema da yanzu kina naki xakin, shiru nayi ban ce mata komai ba.

Sa’adatu ce ta shigo gida da gudu rungume da qatuwar Jakar da kayana yake ciki wanda kayana ne na gida da kayan da nayi biki da su

a ciki don tun ina gida nake amfani da Jakar. Hajiya Kubra ce ta bani ita, tana ajiye Jakar a tsakar falon Inna ta sake komawa

da gudu na jawo Jakar kusa da ni nasa hannu na buxe ta ina dubawa duk wani abu nawa da naje gidan da shi da wanda ya saya min da kanshi ya tattara min ya saka a ciki har da akwatin sarqoqina don dama yasan in da nake voye su, na miqa wa Inna akwatin sarqoqin tare da yi mata bayani gaba xaya kayana ne Ado ya tattara ya aiko min da su.

Ta xan yi shiru cikin tunani kafin zuwa can ta ce duk abinda yayi niyyar zartarwa don ya samar wa kanshi kwanciyar hankali da ya rasa muna yi mishi addu’a ta fatan alheri ba kuma zamu ji zafin shi ba. Cikin zuciyata na ce itama Inna ta hango abinda na hango kenan, cewar Ado zai haqura da aurena ne yasa ya tsintsinto kayana ya aiko min dasu.

Muna cikin haka sai ga Sa’adatu tana shigo da kayan kallon shi da ya saya bayan auren mu a dalilin Mama ta ci gadon nashi na samartaka, Inna tayi maza ta ce a’a wannan ai ba nan za ki kawo ba can xakin Mama za ki kai mishi, ta ce a’a nawa ne bani ya ce yayi in sa a xakinmu in rinqa kallo. Da sauri Inna ta ce a’a shi da yake cikin wannan hali yayi kyauta da kaya mai daraja haka?

Na ce, a’a Inna bashi ya bata ba? Ta ce to ina yake yanzu? Ta ce na dai ganshi ya baiwa Yaya Ibrahim makullan gidan ya ce wai yaba Mama shi kuma ya hau mashin ya tafi.

Inna ta sake cewa kai wannan al’amari

yakai inda yakai, yaron nan yana cikin wani hali kuyi mishi addu’a. Sa’adatu ta ce wa Inna shima ya ce in gaya miki kiyi haquri kuma kiyi mishi addu’a ta ce to ni me yayi min ma? Nan da nan kuma ta shiga jero addu’o’in da yace tayi mishin, zuwa can kuma ban san tunanin da tayi ba sai naji ta ce ni in da zai samu ya kama muku haya a wani wuri ai da nasa an gyara muku gidan ba kaxan ba ta shiga bani labarin irin gadaje da kujerun waje da Alhaji Abba yasa ake kawowa Hajiya Kubra wai don itama ta rinqa juya kuxi a hannunta.

Inna tana faxin haka sai zuciyata ta shiga raya min irin qayataccen gidan da zata shirya mana in har Ado ya kama mana haya da zai yi hakan kuwa ko da wane irin daxi zamu ji ni da shi oho?

Washegari da safe ne Ado ya sake zuwa unguwar har ya shigo gida sai da ya fara shiga wajen Babana ya gaishe shi sannan ya shiga ya gaida Mama ya fito zai shigo wurinmu ina jin Mama tana ce mishi ai na xauka ba za ka sake shigowa gidan ba ne saboda an qwace maka Inna Majandi, in kuma baka daina shigowa kana shiga wannan xakin ba to zan sa mai gidan ya hana ka shiga mishi gida, ban ji ya ce mata komai ba.

Inna ta amsa sallamar da yayi ya shigo suna gaisawa naji tana tambayar shi lafiya

dai ko? Ya ce qalau Inna, na xan yi zirga-zirga ne saboda in warware wasu abubuwa wasu kuma in kammala su, na kuma gama shi ne nazo in yi miki bayani, ta ce mishi to, daga ni har ita muka shiga sauraro don mun fi zaton takardar sakin aurena ya kawo min, sai na ji ya ce akwai wasu sharuxxa da kwanaki aka sanya min akan aurena ban sani ba ko rashin cika su ne yasa Baba ya baiwa Humaira umarnin dawowa gidan don haka na tsaya naga na cika su.

Inna tayi shiru alamar shi take sauraro shima kuma da yake yasan hakan sai kawai ya ci gaba da yi mata bayani na farko akwai maganar gida cewar in bar shi na biyu akwai jarin Mama da nake juyawa sai na uku shi ne in fita gaba xaya daga cikin kasuwancin Baba. Inna ta ce tow, ya ce to waxannan xin duka na shirya yin su don haka ne ma

naje nayi wa Baba Yahaya bayanin komai ya kuma ce min in zo yana zuwa in na zo xin kuma kafin ya iso to in shaidawa Liman da Malam Harisu makwabcinmu don su zo su taya shi zama shaida na zan mayar musu da abinda suka nemi in mayar musu don suma su bani matata da suka karva.

Inna ta sake cewa haka ne, ya ce to bayan wannan ma Inna akwai gidajena guda biyu da nake karvar hayarsu da bus da take yi min zirga-zirga ina kuma da shago da ake yin xikin a ciki shi wannan shagon nawa ne da kuxina na gado na saye shi na kuma zuba kekunan, Musa ne yake

lura da komai nashi, don shima gwanin tela ne ban kuma tava samun matsala da shi ba, yasan komai nawa na gaya mishi abinda ya saba bani ya rinqa kawo miki ki rinqa sayen sabulun wankin yara, su kuma gidajen da motar zan mayar wa Baba da abinshi don a cikin dukiyarshi na saya.

Inna tayi maza ta ce a’ah to in kayi haka kai kuma fa? Ba wahala kayi wa dukiyar ba, ka kuma yi tattali?ya ce eh, amma ban same su ta hanyar da ta dace ba, don haka zan mayar mishi zan je in nemi nawa ni dai in suka yarda muka rabu lafiya dasu suka bani matata na tafi da ita to shi kenan komai mai sauqi ne, sai da tayi tayi mishi addu’a da godiya kan alherin da yayi mata sai ta ce mishi to in ka xauki matarka ina za ku koma?

Sai da ya xan yi shiru tanfar dai nauyin abinda zai gaya matan yake ji zuwa can sai naji ya ce mata qauyenmu

zan koma, da gudu na fito daga xakin da nake kwance ina riqe da xankwalina a hannuna durqusawa nayi da gwiwoyina biyu a qasa na ce mishi qauye? Bai kalle ni ba bai tsaya amsa maganar da nayi mishi ba sai kawai ya ci gaba da yiwa Inna bayani, dangin mahaifina mutane ne masu karamci da zumunci, na kuma yi miki alqawarin matuqar ina raye cikin lafiyata to ba zan bar Humaira ta

shiga cikin matsalar da zata dame ta ba, don haka na roqe ki ki qara yin haquri ki kuma yafe min abubuwan da nayi miki.

Cikin wata irin murya mai rauni naji Innan tana ce mishi to amma kai ma na roqe ka kayi haquri ka fara tafiya tukuna in yaso daga baya sai kazo ka xauketa.

Maimakon ya ce wa Inna to sai kawai naji ya ce mata a’a Inna, ai in nayi haka ya zama min kenan tanfar na rasa komai bayan kuma don in same ta ita kaxai xinne yasa na bayar da komai xin da nake da shi saboda haka zan tasa ta a gaba ne mu tafi. Ina jin ya faxi haka ban jira amsar da Inna zata bashi ba sai na ce mishi a’a babu wani qauye da zan bika mu tafi, ban tava zuwa qauye nayi kwanakin da suka wuce guda bakwai ba, bana iyawa. Sai kuma haka kawai in bika can in zauna? Ba a can aka haife ni ba mahaifiyata ma ba a qauye aka haife ta ba.

Ado ya tashi ya fita saboda jin sallamar Baba Yahaya, ya barni a nan ina durqushe ban gama lissafa mishi abinda na fara ba, yana barin xakin Inna ta kalle ni ta ce qauye kuma? Wannan wace irin fitina ce? Maimakon ta saurari amsar da zan bata tunda naga kamar tayi min tambaya ne sai kawai naga ta rushe da kuka, kuka kuwa mai tsanani irin wanda ban saba ganin tana yi ba.

A tsakar gidanmu gaba xaya mutanen da

Ado ya nema sun hallara ana zazzaune har da Babana wanda yasha mur sosai don nuna alamar babu wasa, Mama ma tana gefe tun kafin a kira ta ta fito ta zauna. Liman yayi addu’a ta fatan a dace da duk abin da za’ayi ya zaman ya zamo shi ne mafi alheri kuma ayi komai lafiya a tashi lafiya aka shafa da amin.

Baba Yahya ya kalli Ado ya ce, to me ya faru ne Ado? Ado ya gyara ya soma rattabo bayani tun farko yanda aka yi Mama tasa shi karvar aurena al’amuran da suka yi ta faruwa bayan auren da sharuxxan da ta sanya mishi na cewar za su faru in har ya ce zai ci gaba da zama da ni da kuma yanda Babana ya kira mu muka zo ya ce ni in shiga xakin uwata shima ya shiga na tashi uwar shi kenan ya raba aure, magana ta qare. Kowa yaje ya riqe tashi.

Ya ce, to shi ne nace wataqila rashin cika waxancan sharuxxa da aka gaya min ne yasa aka zartar min da wannan hukunci, don haka na kira ku saboda ku shaida zan cika sharuxxan dan nima a bani matata in tafi da ita, kowa ya yi shiru yana sauraron abin mamakin da Ado ya rattaba yayin da shi kuma Babana ya shiga faxin lalle kai xin nan butulu ne ban sani ba, Mama kuwa kuka ta kama yi tana faxin wai bata tava zaton Ado zai qulla mata sharrin da ya qulla mata ba.

Liman ya katse su ta hanyar cewa, to amma wannan lamari da ban mamaki yake

,

ashe bani da Alhaji Yahaya ba ne muka je ba da haquri don iyayen mijin ‘yar uwarta su barta ta koma xakinta ta zauna suka qi muka dawo muna vacin rai da baqin cikin wulaqancin da aka yi mana na qin yarda ta koma ba?

Baba Yahya ya ce eh, to shi ne kuma kai da kanka kake cewa a dawo maka da wannan ka raba auren Alhaji a ina ne uba ya samu ikon qwace ‘yarshi daga wurin mijinta, alhalin ba mijin ne yace baya yi ba, ai daga faxin ka bayar an ce an karva to baka da sauran iko, kai Ado kana son matarka ka kuma shirya cika sharuxxan duk tsananinsu don a baka ita? Cikin ladabi ya ce eh Mallam, to kawo su.

Ado ya shiga miqa takardu yana bayani har da na gidajen nashi da motar ya ce ita kamma direban ya ce min ya kawo ta suka ce eh mun ganta bayanin kuxi a banki da na hannun mutane da wanda su kuma ake bin su bashi duk ya bayar. Mallam Harisu ya ce amma Alhaji yanda yaron nan yasan komai na kasuwar nan taka da kuma dawo da wannan dukiya da yayi wacce da can baka san da ita ba baka ga kamar ka yafe mishi ka bashi matarshi suci gaba da zamansu kaima kuci gaba da harkokinku bai fiye maka ba? Tunda kowa ya san shi ya san shi ne a tare da kai babu kuma wanda bai san jarumtakar shi ba yana rabuwa da kai fa wasu a kasuwar a kuma kusa da kai za su qwace maka shi ba kuma zaka ji daxin hakan ba, kan Babana ya buxe baki

yayi magana sai Mama tayi caraf ta ce, to ya tafi mana da can da babu shi Alhaji bai nemi kuxinshi ya samu ba?

Wannan neman kuxi da yake yi mishi ma ai neman kuxi ne na kashe mu raba, Baba Yahaya ya ce eh da ki ka sa shi yin hakan ba in ba haka ba a ina ki ka samu wannan dukiya da ya dawo miki da ita? Me ki ke dashi? Ko kina so ne in tuna miki da…da sauri Liman ya ce a’a Alhaji kai kuma me ya kaika yin haka? Baba Yahaya ya ce abin baqin ciki ne da matar nan Mallam, gaba xaya ta hana gidan nan zama lafiya, ka duba yanda aka yi da dalilin da yasa ta qulla wannan aure da kuma abin ya juya ta inda bata zata ba maimakon tayi nadama kan muguntarta tayi ta istigafari sai kuma ta tasa xan uwanta a gaba da masifa, to za ki rasa shi za kuma kiyi kuskure don shi ne komai na hidimar gidanku ke da mijinki.

A wurinka ba, kai kake ganin hakan ai ku ku ka shiga tsakanina dashi, Baba Yahya ya ce to ai shi kenan kai Ado a ina ka samu inda zaka koma xin? Ado ya sunkuyar da kai qasa ya ce can nake so in koma wurin dangin ubana

,

yana faxin haka Mama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login