Showing 18001 words to 21000 words out of 34829 words
Mama kawai Mama kawai za ku kashe mata qaninta don kun ga yana ji da ita dama auren haxin baki ne, ni kam na takura wuri xaya in ban da kuka babu abin da nake yi.
Suna barin xakin na faxi jikin Ado ina ta faman kuka ina roqonshi gafarar abinda nayi mishi, tsorona kar ya rasa rayuwarshi a sanadin abinda nayi mishi ne ba tsoron abinda Mama zata zo tayi min ba.
Ina cikin haka naji kamar an yi min magana, a firgice na ce iye, na’am? A hankali ya buxe baki ya ce min yi maza ki kulle qofa kar Mama ta shigo ta same ki, da gudu naje na kulle qofar na dawo na durqusa a gaban Ado, kuka sosai nake yi yayin da shi kuma yake kwance bai motsa ba lokacin ne na gane tsoratar da nayi ne ya hanani gane ya farfaxo, tun sanda na ji atishawa da hamdala sai nayi zaton ko daga wani wuri ne.
Muna cikin haka na ji isowar Mama tana faxin “Lallai yau
za’ayi wacce za’ayi, buxe min qofar in ga abin da yake ciki in bai tashi ba ai sai dai in haxa su za’ayi a haxa su gaba xaya in kuma nayi sa’a ya tashi to uwata zata ci gari na wayewa kuma zan tattara ta koma xakin uwarta.” Gwam-gwan-gwan, duka suke yi da iyakacin qarfin su nayi matuqar tsorata don ji nake yi tamfar zasu
valla qofar su shigo, don haka na tsallaka can bayan katifar na maqure.
Ado ya tashi zaune nayi matuqar qara tsorata saboda ganin da nayi tanfar zai buxe qofar ne saboda yawan kiran da Mama ke mishi “Adamu! Adamu!! In kana nan amsa mana in ji ka.” Cikin qarfin hali ya ce, “Lafiyata qalau Mama, je ki gida kawai sai da safe.” Da kyar ta haqura ta tafi saboda ganin da tayi ya qi yarda da buxe qofar.
Har gari ya waye ban tashi daga inda nake takuren ba, yayin da shi kuma Ado ya koma falo ya zauna ban san me yake yi ba sai da na ji an yi kiran Sallar farko ban ga shigowarshi don yin alwala ba, lokacin ne na miqe da kyar na tashi saboda ciwon da jikina nima ke yi min na leqa shi yana zaune ne kan kujera ya kuma kwantar da kanshi akan masagalin kujerar ya kuma xora hannayenshi duka biyu a kan nashi alamar dai ya addabe shi da ciwo.
Durqusawa nayi da gwiwoyina duka biyu na ce mishi
“kayi haqurin abin da nayi maka.” Da iyakacin gaskiyata haqurin kawai nake bashi ba tare da wani tunani ba, don na riga na tsorata na kuma yi nadamar xaukan wannan mummunan shawara da nayi, na yi amfani da ita da Ado bai farfaxo ba to da wanne hali zan shiga? Ba abinda Mama zata yi ne matsala ta ba, girman laifin ne na tsorata dashi.
“Kayi haquri.” Bai amsa ba, bai kuma motsa ba daga yanayin kwanciyar tashi, shiga Masallaci da ya ji anyi shi ne abinda yayi dalilin miqewar shi ya nufi banxaki sai da yayi wanka sannan yayi alwala ya fito yayi raka’atil fijr, sannan yayi sallar Asuba ya idar yana jan carbi nima na idar na shafa fatiha sannan na kalle shi na sake ce mishi “kayi haquri ka ji?” bai kula ni ba.
Aka soma buga qofa da qarfi kamar na jiya da daddare, gwan-gwam-gwan. Ya miqe ya buxe, Mama ta shigo da xamarar gyale a qugunta riqe kuma da sharveviyar dorina a hannunta, nayi maza naja can baya na maqure a jikin bango sai faman kaxuwa nake yi, don in ta soma dukana yau ban san wanda zai qwace ni ba, tunda shima Adon bai huce ba daga mummunan abinda nayi mishi.
Yau za ki gamu da ni, yau za ki san vakko miya ce in ma uwa ki ce ta turo ki
ku kashe min shi to zaku san qarya ku ke yi yau zan yi maganinki ke da iyayenki masu koya miki mugun abu.”
Me ya faru Mama? ya yi maganar cikin natsuwa, ta xago ido ta kalle shi kamar zata yi mishi magana sai kuma ta fasa, wataqila don ganin da tayi tanfar vata lokacinta zata yi, don haka ta zabura ta xago bulalar da niyyar sharva min, ni kuma na takure ina sauraron ta inda zan ji saukarta, sai kawai na ji shiru.
Mama tayi maza ta waiwaya don ganin abinda ya riqe mata bulalarta ta baya, taga Ado a tsaye da bakin bulalar a hannunshi, sake min bulalata, tayi mishi maganar cikin tsawa, nan da nan yayi hakan tare da faxin na sake Mama, amma kiyi haquri kar ki ce za ki tava ta, ai in mun yi faxa ba rama min zaki yi ba, nima da kaina in kin bar ni zan rama ai ba fin qarfina tayi ba.
Ran Mama ya kai matuqa wajen vaci, da ta gane ba zai barta ta buge ni ba, ta shiga zage-zage tana haxawa har da shi a ciki, kiyi haquri Mama, kar ka sake bani haquri, tayi maganar cikin tsawa da fusata, kiyi haquri Mama, ya sake bata haquri. A hankali kuma cikin natsuwa da nuna ladabi har ta xan sassauto tayi kamar zata juya ta fita, muje gida yanzu ina zuwa Mama, kamar ta yarda zata yi hakan sai kawai naga ta juyo da iyakacin qarfinta ta xaga dorina zata sharva min, da sauri
ya sake kama dorinar ya riqe, ta sake juyowa tana kallon shi cikin qarin fusata, zaka riqe min bulalar ne kuma? Cikin natsuwa ya sake ce mata, mace a gidan mijinta Mama ya kamata ace tana da ‘yancin walawa, hukuncinta ya zamo a hannun mijinta ne kawai ba wai duk wani wanda ta yyiwa wani abu sai kawai ya zaro bulala ya ce zai buge ta ba, ba tare da ya sanar da mijin ta ba.
To ai nan ba gidan ka bane, balle ka ce na mijinta ne, cikin hanzari ya ce haka ne. Mama ta ci gaba da maganganu gidan mijina ne ni naga dama kai da ita ku ke zaune a gidan ita xin kuma ni naga dama ne na ce a baka ita ko nawa ka kashe a cikin hidimar auren?
Ya ce, babu, ta ce to babu inda zani yau sai ka rubuta takarda ka sake ta tukunna tunda dama komai akan alqawari muka yi shi da kai, ya ce haka ne to kije gida ina zuwa. Ta sake faxin babu inda za ni ai gidan mijina ne in naga dama na ce a nan xakin zan kwana kana da yanda zaka yi dani ne? A hankali cikin natsuwa ya ce mata babu, ya waiwayo ya kalle ni a inda nake takure ya ce min shiga ciki.
Nayi maza na tashi na shige cikin na bar shi a nan don yin hakan ya fiye min sauqi akan zaman da nake yi a cikinsu, ina ganin abinda ke faruwa. Ina so tabar min gidan a yanzu tunda na mijina ne, ya ce ai na ji Mama
, amma na roqi arzikin ki xan yi haquri kaxan ki xan saurare ni ba wani lokaci mai tsawo zata xauka a cikin gidan ba.
Mama tasa kai ta fita, shima Ado ya koma ya zauna akan kujera, ni kuma ina can cikin xaki maqure wuri xaya, qirjina sai faman bugawa yake yi val-val-val saboda ban tava ganin abinda ya firgita ni irin na jiya da yau ba, Ado da Mama suna kace-nace bayan kowa yasan kullum Ado akan bin umarnin Mama yake.
Wajen qarfe takwas da rabi na ganshi yana shiri kamar in tambaye shi ina za shi? Sai kuma na fasa, saboda yanda fuskarshi take xaure gashi kuma dama ban saba yi mishi irin waxannan tambayoyin ba. Yana fita daga gidan na koma can cikin xaki na zauna ina tunanin in yanzu Mama ta shigo ko ya ya zan yi da ita? Oho.
Sai kawai naji sallamar Hajiyar Giyaxe da sauri na fita naje na tare ta, tana riqe da
food flask
xin da aka kai mata abinci a hannunta, nasa hannu na karvi
food flask
xin tare da faxin, gani ga ki amma ba ki tava shigowa ba sai yau, don na kai miki tuwo kin ji miyar amayar mai zaqi shi ne ki ka kawo min
food flasks
? To bari yau ma zan sake aiko miki da wani tuwon don gobe ma ki sake shigowa ki kawo min kwanon.
Tayi murmushi ta ce, oh’oh-oh’oh, ni ba don kwanonki na shigo ba, zuwa
nayi don maigidan ya ce min in zo in zauna mishi a gidan kafin ya dawo.” Cikin zuciyata na gane abinda yasa Ado yin hakan, shima tsoro yake kar bayan shi Mama ta shigo ta same ni ni kaxai.
Muna zaune da Hajiyar Giyaxe mu biyu hira muke yi bayan nayi mata abin karyawa ta karya ta qoshi, sai sakucen haqoranta take yi da tsinken sakace a dalilin farfesun kaza da tasha, sanin da nayi cewar tun asalin dama can Hajiyar Giyaxe tana son Innata tana kuma matuqar sona ya sani sakin jiki da ita sosai, har na kwashe bayanin duk abin da ke tsakanina da Ado, da abin da ya faru daren jiya da abinda yasa ya turo ta taya ni hira duk na gaya mata, don kuwa neman abokin magana nake yi saboda damuwa tayi min yawa.
Hajiyar Giyaxe tayi min wani lalataccen kallo ta ce, to abinda ya rinqa yi wa uwarki ba sa shi aka yi ba? Yanzu ma kuma za’a sa shi yayi ne? ba gashi nan ba a yanzu kullum yana kai-kawo a tsakani kuma da ban sani ba ai nasan ba da gangan yake yin abinda yake yin ba, to kuma in ban da shirmenki da kayi cuta ka cuci abokin zamanka ai gara shi ya cuce ka, tunda babu wani abin da ba ayin sakayya akanshi musamman ma ace shi wannan abin kan lamarin aure ne. yanzu ace Innarku bata
soma ganin sakayya ba? Innarku fa surukaye uku tayi rana xaya, wane arziki ne ya wuce wannan? Kuma kana ganinta ma a cikin gidan ai kasan walwalarta ma ta xan sauya jinin jikinta ma ya soma dawo mata saboda wahalarta ta soma raguwa, gashi yanzu kullum zaka ganta a wadace cikin harka ni a zatona ma na ce ko mijinki ne oho, na ce anya shi ne kuwa surukayen nata waxancan xin ai dukansu ‘ya’yanta ne, ta gyaxa kai ta ce oho ban sani ba, amma ina ganin mijinki ma yana cikin aini ba yarinya ba ce nace haka ne Hajiya.
Hajiyar Giyaxe ta gyara zama ta ce, to ko wannan tijara da ja’irar yarinyar nan mara kunya tayi wa Babanki da wannan mata shekaran jiya in ban da alhakin Innarku da ya kama su me ya kawo hakan? Nayi maza na vallo varin goro na miqa wa Hajiyar Giyaxe ta shiga goga shi a magogin goronta tana watsa shi a bakinta, ni kuma na qara mannewa
da jikinta kafin na qara tambayarta ni me ya haxa su ne Hajiya?
Ta ce, uhun in ban da iya shege menene wai kama su tayi suna yin wani abu ranar girkinta bayan kuma dama da nata girkin da natan duk ita kaxai aka haxawa, na sunkuyar da kaina qasa cikin yanayin jin kunya, cikin zuciyata dai cewa nake yi lalle yarinyar nan da kafirin iya shege take, yanzunnan
Babana ta yiwa irin wannan iya shegen? Ita kuwa Hajiyar Giyaxe babu ruwanta, sai bayanin ta take yi amma da maganar tazo wurina na gaya musu dukansu ita mijin nata na gaya musu dama gulma da munafurci ne ya saku yin hakan, don ku cutar da Binta, to gashi nan abin ya koma kanku.
Ni kam ban yarda na tofa cikin wannan zancen ba, illa iyaka dai na amsa sallamar Hajiya ‘Yar dubu, itama riqe take da
food flask
xina a hannunta na kalle ta nayi dariya nace, kema kwanona ki ka kawo min? ta ce, oh’oh, wane kwano ne zai fiddo ni a ruwan nan? Uwarki ce tayi wa Mallam waya ta ce mishi wai mijinki babu lafiya, gabana ya yanke ya faxi me Inna ke nufi da wannan wayar da tayi kar dai itama zafina take ji?
Ina yake yanzu, ko yana ciki ne a kwance? Tayi tambayar bayan sun gama gaisawa da Hajiyar Giyaxe, sun yiwa juna ban gajiyar biki har tana faxin ai ban san kina nan ba Hajiya da na zo miki hira, Hajiyar Giyaxe ta ji daxin hakan da ta gaya mata ta kwashe zance duka ta yi wa Hajiya ‘Yar dubu, har da yiwa bayanin kwaskwarima na ce ah Hajiya…kan in faxi abinda zan faxa Hajiya ‘Yar dubu ta daka min tsawa ke tafi can ki baiwa mutane wuri akan zai tava ki ne ki ka kwantara mishi qarfe kina
neman kashe shi?
To zauna ya bar ki ba shi kenan ba sai ki rinqa jiqawa kina sha ko ki kai inda za ki kai. Hajiyar Giyaxe ta ji takaicin maganar, ta ce a’a Hajiya wannan ai ba zancen da za ki yiwa yarinya ba ne, sai kiyi mata faxa kawai irin wanda ya dace da ita.
Rannan cikin dare na yi wa Inna waya don in gaisheta, bata xauka ba kamar yanda dama kullum nake mata washegari ma da sassafe na kira ta bata amsa ba, gashi kuma ina ji ta bugo waya ta gaida Ado da jikinshi, a zuciyata na ce ha’a to me na yi wa Inna? Me babban allo yazo gaida Ado wai da jiki, ya gaya mishi gani nan zuwa zai turo ni don in gaishe shi amma naje zauren shima ban same shi ba ya tafi.
Na dawo xaki na zauna zuciyata takai matuqa wajen vaci, me nayi musu? Me nayi kowa yake fushi da ni? Ban san yanda aka yi ba kawai naji hawaye suna zuba a idona, kuka na soma yi sosai.
Ado ya juyo ya kalle ni, me ya same ki Humaira? Me ya saki kuka kuma yanzu? Ko kuma kin tuna da irin takurawar da nake yi miki ne? rarrashin da yake yi min ya sanya ni buxe baki na ce mishi ban san dalili ba ne kowa sai jin haushina yake yi. A hankali ya ce min haba Humaira, kowa fa kika ce, kenan har da ni cikin masu jin haushin naki? Na
gyaxa kaina nuna alamar eh har dashi.
Ya ce, uh’uh ni bana jin haushin ki,ina dai so ne kawai in xan rinqa danne zuciyata ina yin haquri kar in rinqa yawan sakin jikina ta yanda zan yi tasa rai a kanki ina matsa miki tunda na gane da gaske kike yi ba kya son haka xin.
Ban tankawa zancen nashi ba, iyaka dai na riga na sawa zuciyata wani al’amari tunda na gane har da Inna cikin masu fushi da ni akan Ado, bata lura da irin tasa Ado a gaba da Mama tayi ba kan sai lalle Adon ya sake ni.
Kwana wajen huxu a jere daga wurin Inna ake kawowa Ado abincin dare na kuwa gane hakanne a dalilin Sa’adatu da ke kawowa da ganin irin kwanukan da ake zubo mishin kuma kasan ba qaramin girma Adon yake dashi ba a wurinshi, yana gama cin abincin in ya gama abin da zai yi zai duqunqune kan ‘yar kujerar da ke falon yayi kwanciyarshi iyaka dai bai cika yin wani barci ba, bini-bini kuma zan gan shi yana jiqa jar kanwa ko
andre lever sold
yana sha.
Rannan cikin dare ruwan sama mai qarfi ne yake sauka kamar da bakin qwarya, ina kwance can cikin xaki akan katifata bayan na shafe jikina da mayuka masu qamshi da qara laushin jiki sai da na feshe jikina sosai da turare mai sansanyar qanshi
, sannan na shige cikin bargona na ruhu.
Ina jin yanda ruwa ke sauka da kuma sauraron tsawar da aka yi ina mai karanto addu’o’in da ake yi lokacin saukan ruwa, ko kuma tsawa. Ni kin kawar min da kofin da kanwar nan ke ciki ne? a hankali na ce mishi eh, ai ban san kana so ba ne ya ce ina so mana Humarai, ai kema kin san ina da buqatarta, gashi yanzu ruwan sama yayi qarfi yaya zanyi in je kicin in samo wata? Na ce to ko in zo in kawo maka wata, ya ce bar ta kawai zan yi haquri tunda ga ruwa yayi qarfi.
Kwanaki kusan tara a jere babu abinda ban yi ba, wanda zan sa Ado ya tanka min na jan hankali da hila don dai in samu in sallama mishi kaina tunda na gane abinda nayi mishin ne ya sanya Inna har yanzu bata xaukan wayata, amma ya qi. Yana ganina a kusa dashi da lalatacciyar shiga sai yayi maza ya kawar da kanshi ko ya haye kan doguwar kujerarshi ya ja abin ruhuwa ya lulluva ya ce, wai bacci yake ji. Da rana kuma yana Azumi.
Cikin zuciyata na ce to ko dai ya tsorata da abinda nayi mishi ne yake ganin kamar a yanzu ma in ya matso kusa dani zan sake maimaita mishi? Gashi Mama ta tasa shi a gaba kullum sai ta shigo gida ta tasa shi a gaba kan sai lalle ya sallame ni, ita auren
nawa ya riga ya ishe ta gara kawai a yanzu don in ance sai an kai kwana casa’in to bata san me zamu sake yi mishi ba cikin waxannan kwanakin.
Yana faxin kiyi haquri Mama, ba yau ba sai ka ji ta soma rattabo mishi maganganu tana tuna mishi sanda ta xauko shi daga qauye da irin wahalar da yake ciki a wancan lokacin da kawo shi gidanmu da tayi ta maida shi abin da ya zama a yau amma yake nema ya butulce mata saboda aurena.
Shi kuwa sai ya ce mata ai ban manta ba, Mama na gode miki da wannan taimako da ki ka yi min ina kuma yi