Showing 24001 words to 27000 words out of 34829 words

Chapter 9 - Mijin Ta Ce Book Two Complete Hausa Novel

Sodangi   

18 Oct 2025

185

haqurin nashi, don haka akan dole jiya da daddare na haqura na qyale shi yayi yanda yaso, wanda ba ni da na ji a jikina ba shima yasan ba qaramin takura nayi ba.

Amma duk da haka da gari ya waye na fito na kama ayyukana na gida, don dai in samar mishi da kwanciyar hankalin cewar bai qware ni ba, duk da ni kam nasan ya qware nin, ina sunkuye ina qarasa wanke wurin da nayi wanke-wanke ban san hawa ba ban san sauka ba kamar daga sama sai kawai naji saukar bulala a jikina da iyakacin qarfina na qurma ihu.

Ina xaga ido naga Mama ne mai dukan, kuma na yanka da gudu na nufi xakina saboda neman mafaka

, da saurinta ta biyo ni tana faxin “Ja’ira mai gadon raba zumunci, ai ni ba za a kawo min wannan iya shegen ba, a hanya muka gamu da Ado ya fito daga xakin cikin sauri daga shi sai gajeran wando

Boxers

fari sol, hannu ya saka ya tare ni ya hana ni shiga xakin ya maida ni bayan shi na tsaya, me ya faru Mama?” yayi tambayar cikin natsuwa duk da dai fuskarshi ta riga ta baiyanar da motsuwar zuciyarshi.

“Kaga ja’iri mara kunya, a gabana ka ke tava ta?” tayi maza ta sake xaga hannu zata sharvo min bulalar ya tare da hannunshi, “Matata ce ai Mama don na tava ta ba wani laifi nayi ba, sannan na fara gajiya Mama, zuciyata ba za ta iya ci gaba da xaukar irin wannan abin ba, kin yi sammakon zuwa dukan yarinyar nan alhalin ba ki san yanayin da ta kwana a ciki ba, ko tana da lafiya ko bata da ita.”

“A’a qarya kake yi gaya min dai abin da kake son gaya min xin, ja’iri mara kunya mara mutunci akan wannan ja’irar yarinyar? Ai in ba hanzarin raba ku nayi ba to in ba sa’a nayi ba ina zaune ne kawai zanga ka rufe ni da duka.”

Ta sake sharvo bulalar ban san yanda aka yi ba sai kawai na ganta a hannun shi, “Haba Mama, wannan fa bulalar doki ce kike duikanta da ita.” Ban ita nan.” Tayi mishi irin tsawar da bata tava yi mishi ba, a’a Mama

ba zan baki wannan bulalar ki buge ta ba.

Bayan bata yi miki komai ba, in kuma tayi miki ma ai ni ya kamata ki gaya wa in yi mata nasiha sai in bata ji ba ne zan sake dubawa in ga wani matakin da zan xauka amma ba duka kan wannan ba, ai ba zai yiwu a buge ta tana budurwa sannan yanzu ma tana matar aure tana hidimar mijinta da xaukar xawainiyar shi ace za a buge ta, ko nima da nake matsayin mijinta in tayi min laifi a yanzu haquri zan yi tunda nima akwai abubuwan da nasan haquri zata yi dani a kansu.

Ni ban tava ganin ana bin matar aure gidan mijinta a buge ta ba sai ita, gaskiya ni kar a sake yi min haka Mama, na roqe ki don bana so.

Kasaqe Maman tayi tana kallon Ado, cikin kaxuwa da mamaki. Ai in bar maka ita ta sangarce ta lalace kenan, tafi qarfinka taje tana rabaka da ‘yan uwanka tunda su abinda suka fi iyawa kenan?

Ya ce, a’a ni ban san abinda suka fi iyawa ba, Mama na dai san haqququwana da ke kanta tana qoqarin tsare min su, maganar zumunci kuma ba ita ce ta haxa ni da su Ibrahim ba mata suka kawo Baba kuma ya ce bai yarda a rinqa shigo mishi da matan banza cikin gidan shi ba.”

Kasaqe Mama tayi tana sauraron Ado cikin kaxuwa da mamakin kalaman bakinshi, uh yanzu nasan kasan mace

, tasa kai ta fita kamar ace tayi fushi zance ya qare amma ina?

Da daddare nayi wanka ina zaune gabanshi yana shafa min wani mai a tabon shatan dukan Maman da ke jikina, yana yi yana faxin nan da shekara guda in muna raye ba za ki ga tabo a jikinki ba Humaira, tunda ni me za ki yi min in buge ki?

Ai in ma kin yi min laifin dukan to bai wuce in yi kamar zan kaxe miki qura da bakin rigata ba, tunda nasan ba za a xauki wani lokaci mai tsawo ba zan dawo miki da lalurata.

Muna cikin haka sai ga Mama ta shigo har can cikin xakin, tana ganinmu ta soma faxin uhun, ni fa nasan ba haka kawai kake yin abinda kake yin nan ba, don haka na yafe maka duk laifuffukan da kayi a sanadin zuwanta gidannan in ma haxin baki suka yi na su vata tsakanina da kai to ba su isa ba, ba za su raba mu ba.

Rubuta mata takardarta kawai in tasa ta a gaba in kai wa uwarta ita don in gaya mata gata nan na kashe wannan wutar aniyar kowa kuma ta bishi, kamar dai in ce amin sai na fasa saboda Ado da kuma ita Mamar kanta don haka sai na faxi kawai a zuciyata.

Shiru Ado yayi yana

jinta bai tanka ba tayi rarrashi da ban baki iri-iri bai motsa ba, da ta tunzura da shirun nashi sai ta ce mishi, amma dai ka san dagewa kan zama da itan ya

na nufin ne kayi zavi tsakanina da ita. Yin wannan zavin kuma ba qaramin fitina zai zama maka ba, don zaka fita daga gidan nan zaka fita daga cikin harkokina, za kuma ka fita daga cikin dukiyar mijina da ka yi wa kane-kane, sannan ko kayi hakan zan kuma iya bi ta wata hanyar da zan rabaka da ita da qarfi tunda in kai ban gaya maka ka ji ba shi uban ta ai zan gaya mishi ya ji. Ya ce mata haka ne.”

Muna cikin haka ne sai kawai ga Suwaiba ta shigo da gudu, “Mama wai ki zo da sauri ga Anti Habiba tazo.”

Suna barin xakin, Ado ya kalle ni cikin wani yanayi da yafi kama da na tausayin kai, cikin qarfin hali ya tambaye ni in na ce miki ina sonki za ki gamsu? Da sauri don in kwantar mishi da hankali na ce mishi me zai hana? Ya sake kallona cikin natsuwa ya ce, “Duk abubuwan jin daxin da nake ganin kamar yau ma za ki daure kiyi haquri dani in same su sun rushe ko?

Nayi murmushi na ce, sai dai in kai ne baka so.” Ya saki wani lallausan murmushi ya ce, “Humaira in tambaye ki mana?” na ce to, dama dai kayi sa’a in san amsar tambayar, kin tava sanin wani abin da yafi aure daxi? Nayi dariya na ce in dai auren na namiji ne kamar ka to ina ganin kamar babu. Daxi ya kama shi, ya jawo ni

jikinsa.

Rannan kwana muka yi ni da Ado tanfar dai dama mu xin ba baqin juna ba ne, tanfar kuma ya mance da kasadin da Mama ke yawan yi mishi na cewar tari mai qarfi in kayi a wannan xakin ina jin shi, don haka babu wani abin da ku ke ciki wanda ban sani ba.

Harkar gabanshi ya yi, nima kuma ban takura mishi ba, saboda a yanzu nima ba zai yiwu in ce ba na sonshi ba, ban da haka kuma na riga na gane Inna tana son auren namu a yanzu in kuwa haka ne to zan yi komai wajen ganin Mama bata qwacewa Inna mijinta ta kuma sake hana ta jin daxin surukinta ba.

Washegari da safe Ado ne ya shiga gida don gaida iyayenmu, ya dawo yake gaya min cewar, kin ji ashe wai zuwan nan da Habiba tayi jiya uwar mijinta ce ta kora ta bayan mijin ya naxa mata dukan tsiya, kuma don wulaqanci baki ga doguwar wasiqar da suka haxo ta da ita ba, wai ta zauna a gida daga nan zuwa watanni uku don ta koyi tarbiyya.

Na kalli Ado kawai cikin zuciyata kamar in faxi wata magana sai kuma na tuna ba zai yarda in gayawa Mama wata magana ba, don haka naja bakina nayi shiru na vuge da cewa kai abin bai yi daxi ba, yaushe aka yi auren da har za’ace a dawo gida ayi zaman wata uku?

Ya ce, to ai kin san bakinta itama kuma ba kunya ne da su ba, na dia ja bakina nayi shiru. Kiyi abin karyawa da ita

na ce to. Tun daga lokacin ya zama min qa’ida inna yi girki bayan abincin da nake zubawa na cikin gidanmu zan kuma zuba na Habiba daban. Ado ne yasa ni yin hakan ga kuma kwanukan su Ibrahim safe, rana da dare, amma duk da haka ban fita ba a wurin Mama, wai ban sa mata nata kwanon daban ba, na sata a haxaka sai kace ni tawa uwar ba a haxakan na sakata ba.

Saboda gudun fitina, bayan kuma ni nasan zai yi wuya Inna taje tana wani xiban abincin da na aika dashi a kunya da kara irin nata ma ba za ta je tana yin hakan ba.

Tuni dama Mama ta riga ta yaxa rashin jituwar dake tsakaninta da Ado, bata bar shi ya zama sirri ba a tsakaninsu, don haka kowa yasan da maganar, ta xauka hakan zai zamo tozartawa ga shi Adon ko kuma Innata ace ta mallake mata qani ta rabata dashi, ta sani ba kanta ta jawa magana ba, don kuwa mutanen da suka santa suka san komai na sirrin zaman gidanmu da dalilin da ya sata tasa Ado aurena sai albarka suke sawa Adon suna faxin mun gode mishi kaga min jarumin yaro ai gara da yayi mata haka.

Wannan magana da ta riga ta bayyana kowa ya san da ita yasa dawowar Habiba gida ya zamo abin gulma abin tattaunawa a tsakanin mutane wasu ma faxi suke yi to ai gashi nan tana qoqarin fidda wata ga tata nan an korota.

Baba Yahya da kanshi ya nemi wani abokinshi ya xauki Habiba a motarshi suka je har gidan don maida ita xakinta, daga nan su baiwa uwar mijin haquri, tunda dai an yi sa’a hutu suka bayar basu furta kalmar saki ba.

Amma uwar mijin Habiba tayi qememe ta qeqasa qasa ta ce ai tunda da bata hutun nan sai tayi shi in dai ba sun gwammace auren ya mutu ba ne, tunda dai ai sun san ‘yarsu zata gidan wasu, amma basu tsaya suka yi mata tarbiya ba.

Shi kuwa uban mijin da suka koma ta wurinshi ko zai yi halin maza ya ce a’a tunda an riga an kawo ta to shi kenan iyaka dai a kwave ta don gaba kar ta qara

sai yace tunda hukuncin da Hajiya ta zartar kenan sai dai ayi haquri aje kawai in lokacin yayi a dawo da ita.

Wurin Ado naji labarin saboda abinda aka yin yayi matuqar vata mishi rai, ni kam murmushi na xan yi can cikin zuciyata dai cewa nayi ashe dai ba Babana kaxai aka yi wa irin wannan kamun kazar kukun ba.

Duk da irin hidima da xawainiyar da nake yi da Habiba saboda tausayinta da nake ji gashi kuma na gane xan qaramin ciki ne da ita koma bata nake yi ko ba ta zo ba in aike mata dashi don nasan tana buqatar kulawa ta musamman amma bata gamsu ba haka Mama gaba xaya jin haushina suke yi tanfar dai ni naje na fito da ita daga

gidan mijin nata.

Kullum dai ta shigo xakina sai ta zagi xakin sannan shigarshi babu qa’idar sallama a wurinta, sau biyu tana samuna kan shimfixa tare da mijina amma hakan bai hanata shigan mana xaki babu sallama ba. In kuma abu ta gani ko na xiban mata sai tasa hannu ta kwashe sauran.

Rannan dai abin nata ya ishe ni ta shigo falo babu sallama bata ganni ba ta biyo ni can cikin xaki bayan kuma tasan Ado yana gida muna tare a ciki, don haka na kalle ta na ce mata “Habiba kar ki sake shigo min xaki babu sallama, bana so kuma in kin yi sallamar ma ban yarda dan baki ganni ba ki biyo ni cikin xakina, don kuwa wurin sirrina ne ni da mijina.”

Sai da tayi wa xakin kallon banza sannan ta tambaye ni, meye a cikin wannan sukurkutaccen xakin naki da babu komai a ciki sai ‘yan tarkacen kujerun da?” na ce ai ba kayan xaki ne aure ba, Habiba da sune to da tuni anyi nasarar korata daga gidan da kuma ba a koro wasu daga nasu gidajen ba, don haka aure daban kaya daban in ana maganar aure kuwa to miji shi ne maganar in aka yi dacen samun shi to shi kenan zance ya qare.

A fusace tace mijin da kike gadara da shi xin dai ai kawunmu ne kuma kema dolenki sai kin fito, na ce oho kin dai riga ni fitowar sannan ko Kawunki ne ba mijin ba ne tunda ba za ki yi abinda nake yi dashi ba, don haka kar in sake ganin kin zo kin xaukar mun wani abu ba ki sanar da ni ba.

Kin kuwa san duk yanda ki ka kai da gadara da abinshi saboda kusancin da ke tsakaninku, baki kaini ba, tunda kin sha faxo mana xaki babu sallama, kina ganin mu a shimfixa guda xaya, ko ba haka ba? Gidan Kawu ai ba abin gadara ba ne gidan miji shi ne abin gadara ba ki ga ni daga shigowana sai nayi kane-kane na kankane komai ba? Na wuce zan kai abinda na qwace a hannun nata kicin in ajiye.

Ado ya leqo daga xaki “Ke Humaira menene haka? Maida mata dasu, na ce to na kawo na bata ta karva ta fita ta tafi sai kuma gata ta dawo ta dangwarar mun da su ta juya ta tafi tana maganganu kici ki qara kece baquwar daxi na ce eh ni ce baquwar su na kuma gode da na yi sa’a na samu a gidan mijina.”

Nayi ta zuba ido ko zan ga Mama ta shigo da bulala ko kuma ta turo a kira mata Ado don ya amsa tambayoyi kan abinda ya faru tsakanina da Habiban, ban ji ba, a zuciyata na ce ta haqura kenan, sai da na gama abincin dare na aike musu da shi naga an dawo min da abincin gaba xayan shi wai in ji Mama ace min bata so in haxa duka in cinye ita tun kafin asan

za’a haifi uwata ta same ta ne a duniya tana cin abinci, abincin ma kuma mai daxi tunda ita tuni tun da daxewa a cikin rufin asirinta take raye.

Na kalli Suwaiba da ta rattaba min bayanin nayi murmushi da gangan na kalle ta na ce mata Kawu mijina ne ina kuma son shi kamar kamar in yi ya ya? Ni kaxai nasan yanda nake jin shi a cikin raina, don haka babu wani abin da wani nashi zai yi min in ji takaici, balle Mama wacce uwata ce sannan da umarninta ne aka yi min wannan aure mai daxi ki bata haquri kafin in zo da kaina in bata.

Ta juya ta tafi ga alama kuma ta gane gatsen da nayi mata, na sake zuba idon ganin Mama ta shigo bata shigo ba. Cikin zuciyata nace in ma dai savanin Mama da Ado yayi tsananin da ta fita harkarshi ko kuma tana nan tana shirya abinda take shiryawa. Ko da yake dai a yanzu itama tana da matsalolin da suke kewaye da ita, ga Suwaiba da aka qi karvar aurenta daga dalilin xaguwa ga Habiba an ce ta dawo gida ta qara koyon hankalin zama da manya, ga Zubaida da yanzu ta watse musu kusan kullum sai ka ji ta tana zuba rashin kunya a cikin gida wai da Mama take yi daga baya kuma ka ji faxan ya rikixa

ya koma tsakaninta da su Habiban.

Ga al’amarin su Yaya Ibrahim da ya riga ya baiyana har duk mutanen unguwa sun gane kusan kullum sai wani dattijo mai mutunci cikin mutanen dake ganin bari su bada haqqin maqwabtaka yayi sallama da Babana akan su yana tambayar shi anya Alhaji haka za’ayi ta zubawa yaran nan ido ba za a xauki matakin da ya dace ba?

Ga Anti Sha’awa daga zuwan Amarya kuma wai komai ya susuce mata, bini-bini sai ka ganta a gida ita da ‘ya’yanta wai tayi yaji saboda wai mijin yana nuna bambanci a zahiri, sai Maman ta kwaveta ta ce mata ta koma xakinta kawai taje ta duba taga irin matakin da ya dace ta xauka saboda a yanzu ba zai yiwu tazo ta zauna a gida ba, tunda ga Hajiyar Giyaxe ga kuma maganar Suwaiba da Habiba.

A duk lokacin da na tuna Mama da irin iko da gadaran da ta gwada na ganawa wanda bata so azabar yunwa da ta wulaqanci da duka sai in ji kamar zan ji daxin abubuwan da suke faruwa da ita, wanda nasan mafi yawancin mutane dariya suke yi mata sai dai kuma in na tuna ‘yan uwana ne sannan Babana ba jin daxin hakan yake yi ba sia in ji tausayi ya kama ni, in ce ina ma dai

a kanta abin yake faruwa ba akan ‘ya’yanta ba.

Rannan Ado ya dawo gida bayan Azahar, cefane ya sake kawowa mai yawa sosai da sauri na fito daga xaki na karve shi guda xaya, xayan kuwa qin bani yayi yace muje in kai miki wannan. Muna tafiya yana tambayata sau nawa ki ka yi aman bayan fitana?

Na ce, a’a ban ma sake ba ina jin fa dama tin nan ne ya xaga min hankali don nafi son da safe insha kunun gyaxa da alala, ya ce to ki jiqa gero mana, na ce to ko kuma in ce Inna tayi min qullin, ya ce a’a ina dalili baki taimake ta kin yi mata ba sai ki sa ta aiki? Ban yi magana ba na soma fiddo cefanen don in san irin adanar da zan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login