Showing 27001 words to 30000 words out of 34829 words

Chapter 10 - Mijin Ta Ce Book Two Complete Hausa Novel

Sodangi   

18 Oct 2025

188

yi mishi, tunda ko jiya yazo da wani sai na ji ya ce min za ki yi miyar ne ta soyu da kyau ta yanda zata daxe bata yi komai ba, ta Haiyar Giyaxe ce gobe zata tafi.

Da sauri na xago kai na kalle shi, tafiya zata yi?ya ce ina laifi goben ta ce watanninta uku kenan a gidan, na ce sai tayi ai kwanci tashi babu wuya, amma kuma har na soma kewarta tun kafin ta tafin. Ya ce, to ko zan je ne in gaya mata ta haqura ta bar tafiyar sia kin haihu an yi suna tukunna? Shiru nayi ban amsa mishi ba saboda ina jin kunyar irin wannan

zolayar da yake yi min.

Da wuri sosai na gama aikina na kawo mishi ya gani, ya ce min to sai ki shirya in anyi Sallah sai muje tare kiyi mata sallama, na ce to. Cikin zuciyata ina murna zan shiga gidanmu har inga Innata, bayan kwanaki tamanin ban ganta ba, duk da ga ni gata saboda bata shigo ba nima bai bar ni na shiga ba. A wani gefen kuma ina fargabar ganin Mama saboda mun yi kwanaki ba mu sa juna a ido ba.

Wanka nayi sosai na xau kwalliya mai kyau sai sheqi nake yi ina xaukar ido, doguwar riga ce a jikina ta shadda gwan shep xinta yayi matuqar fitar da surata da kyau ga xinkinta yayi matuqar kwanciya. Ado ne ya saya min shaddojin guda biyu ya bayar aka xinka min su, na sanya qananan ‘yan kunne da abin wuyansu waxanda

suma shi ya saya min su a dalilin sha’awar da suka bashi sai dai a hannuna ne na sanya wara-waran daham da zobunansu na kuma xaura wani xan siririn agogo da zoben G.L, suma kyautar Adon ne.

Ya kalle ni cikin wani yanayi da na tabbatar nayi matuqar burge shi, ya ce “Ba za ki fesa turare ba ne? ai gida kawia zamu shiga.’ Na ce ‘uh’uhn bana son turaren na jikinka ya ishe mu, bai ce min komai ba in ban da kallona da ya sake yi.

“Xan kawo min turame biyu cikin ka

yan aurenki aro.” Nayi murmushi na ce, zan fa xunka su, ya ce eh na ji kawo min dai, naje na kawo mishi akwatin ya zubawa zannuwan ido yana kallonsu, babu wata atamfa a ciki da ta wuce dubu xaya da xari biyar, ni nafi zaton ma zannuwan da dangin uban Ado suka zo dasu daga qauye ne na gudummuwa Mama ta zuba a cikin akwatin ta xora sabulai da man shafawa ta bayar.

Zavo min guda biyu masu kyau a ciki, nasa hannu na zavo mishi su ya kuma gamsu da zaven da nayi mishin ya sake maida kallonshi kan abinda ya saura a ciki, dama zannuwan shida ne? na ce a’a takwas dai kwanaki baka ari guda biyu ba?

Ya ce, af, haka aka yi to zuba min waxannan sabulan da man in haxa mata, na ce to ai ka kwashewa Hajiyar Giyaxe kayan auren nawa. Ya ce eh ai ba kya son su, da kina son su da tuni kin xinka su kin saka, na ce to ai yanzu ina son su zan kuma xinka su in xaura don ma dai bani da keke ne da da kaina zan xinka abina.

Bai amsa ba iyaka dai ya tasa ni a gaba muka fito, bayan yasa makulli ya kulle qofar xakinmu ya kuma sake kulle qofar gida. Na sake xaga ido na kalle shi daidai sanda yake kulle qofar gidan, idanuwanmu suka haxu na xan kawar da kaina gefe ya ce, uh sai dai ki

faki ido ki kallan mun kwalliyata amma ba ki san ki ce tayi miki ba, ban tanka mishi ba iyaka dai nasan yayi kyau ba kaxan ba.

A tsakar gida Hajiyar Giyaxe tana alwala ta amsa sallamar da muka yi tare da yi mana oyoyo mai yawa, na ce hala Hajiya Sallar Isha’i zata yi? Ta ce uh’uh me zan zauna yi har yanzu ban yi Sallah ba? Alwalar kwanciya nayi, na ce to kwanciyar ma har da alwalarta? Ta ce eh, muka bi bayanta zuwa xakinta wanda dama shi ya fi kusa da qofar zauren gidanmu har muka shiga bata gama yi mana bayani kan muhimmacin wannan alwalar ba, muna zama kan shimfixar da tayi mana ta koma bakin gadonta ta zauna tana kallonmu.

Ni in ce ko dama iya shege ne kawai ya saki yin abinda ki ka yi ba qin auren kike yi ba? Na yamutsa fuska naqi yin magana, yayin da Ado ya ke dariyar maganar tata da tambayar ta me ki ka gani Hajiya? Ta ce eh to abin ne nake kallon shi wani iri, ashe dama ana so ake kaiwa kasuwa, an je don iya shege har ana qwale miji da guduma, yanzu kuma sai naga ana ina aka saka dashi ba aso ko quda ya sauka akan shi.

Ado ya kama dariya yayin da ni kuma na shiga shure-shure cikin yanayin shagwava da jin kunya ina cewa

bana so Hajiya, bana so.

Kin gani Hajiya za ki sa ta tayi shure-shure duk ta shuire kwalliyarta ta lalace, yana maganar yana kallona cikin murmushi ga alama daxi ya kama shi an ce ina wai ina aka saka dashi, ai ni da cewa nayi Hajiya tafiya tun yanzu ba za iki bari sai wata daga cikin amaren ta sauka anyi suna kafin ki tafi ba?

Hajiyar Giyaxe ta qyalqyale da dariya ta ce, kai dai gaya min kawai in sani cewar taka amaryar tana kan hanya.’ Xaure fuska sosai nayi naqi kulawa da zancen nasu, iyaka dai na jawo kayan da muka zo mata da su na ajiye mata a gabanta na kuma ciro kuxin da ya bani ya ce in bata na haxa tayi ta godiya tana sa mana albarka, tayi man addu’ar samunzaman lafiya, kwanciyar hankali da kuma zuriya mai albarka. Ado ya ce amin.

Ta miqe ta xebo wasu kayan tana nuna mana daga gidan Atika aka kawo su, nayi murna nayi musu addu’a na tashi na bar Ado yana sa hannu a aljihu alamar zai mata wata kyautar ta daban.

Ina barin xakin Hajiyar Giyaxe can wurin Mama na shiga, samun Babana da nayi a xakin baisa ta sake min fuska ta amsa gaisuwar da nake yi mata ba, shima Babana amsa gai

suwar

tawa a yanaayin kadaran-kadahan na dai san sau biyu na ganshi yana fakon idon Mama yana kallona.

Ga dukkan alamu kuma nasan canzawar da nayi ne yafi komai bashi mamaki, gashi kuma nayi kwalliya ta xaukar hankali, ban wani ja zance yayi nisa ba, saboda ganin irin karvar da suka yi min na miqe na fita. Ban tambayi su Habiba ba don kuwa nasan dukkansu suna jin shigowata suka yi kamar basu ji ni ba.

A kusa da qofar xakin Inna na ci karo da wani lafiyayyen injin xin wanki mai matuqar kyau sai da na qare mishi kallo sannan na shigo cikin xakin nata tana zaune kan kujera, gaskiya ne da Hajiyar Giyaxe ta ce min ta fara murmurewa. Ina murmushi na miqa hannu na xauki Adam karo na farko da na ji ina son shi tare da sunan da aka sanya mishin.

Na sake kallonta cikin murmushi na ce “Inna rowar yaron nan take yi sai in yi ta aiken a kawo shi kina hanawa, bata kula zancen ba, ta miqe taje ta kawo min

yugurt

mai sanyi mara sugar ta ajiye min, nayi murmushin farin ciki saboda ganin canjin da ta samu, na ce Inna ashe injin xin wanki kika samu shi ne nake ta aiken ki ba da kayan wanki in yi miki kina cewa babu, ba ki gaya min ba. Wa ya saya miki?

Ahmad ne ko Salisusu? Ta waiwayo a hankali ta kalle ni cikin natsuwa ta ce min shi mijinki fa? Ba kiyi tunanin shi ya saya min ba, sai ki ce Ahmad ko Salisusu? Shiru nayi ban ce mata komai ba, itama ta xan yi shiru sai jimawa kaxan ta kalle ni ta ce min to, wanda ba kya zaton ne ai na xauka ya gaya miki ne shi yasa ban ce Sa’adatu taje ta gaya miki ba.

Amarya ce yau a gidan tayi maganar cikin murmushi nima na xan yi mata murmushin kaxan ta shigo har cikin falon Inna ta zauna muka gaisa, ta miqe zata fita tana faxin kai amma xinkin nan naki yayi min kyau a ina aka yi miki? Na ce a’a ban sani ba, haka naga an kawo su a xinke ta sake cewa kai ai auren wayayyen miji mai son matarshi daxi ne dashi.

Shiru nayi ban tanka mata ba, ta fita na kalli Inna cikin mamaki na ce har cikin xakin nan yanzu Zubaida take shigowa? Bata tanka ba ta ce min sha nonon mana, na ce uh’uh Inna ina dashi a gida ta ce haka ne ai daga wurin naku aka kawo to me za ki ci? Na ce ban son komai Inna sai dai ina so kiyi min qullin kunu tayi maza ta kalle ni tana tambayata yau kuma qullin kunu kike so? Naga kuma aike ba mai san

kunu ba ne shiru nayi ban ce mata komai ba, itama sai kallona take yi na kuma san kyau taga nayi.

A’ah auren naku fa ya xan kwana biyu kai tafiyar lokaci bai da wuya, na ce me ki ka gani Inna? Ta ce, to ko wannan canzawa da kika yi ai ya isa a san ba shekaranjiya bane ban ce mata komai ba, ta xan sake yin murmushi ta ce ai dama tunda naga maigidan yana maida jikinshi na ce to an zauna lafiya kenan.

Shi dai aure ai kin san ba komai ba ne illa yi nayi bari na bari in zaka zauna da mutane kuma to ka zauna da su akan gaskiya nace to Inna.

Ado yayi sallama ya shigo Inna tana yi mishi sannu da zuwa ga dukkan alamu dai ya zama xa sosai wurinta cikin zuciyata nace kai Ado ma dai da qoqari yake ko da dai shi da bakinshi ya sha kiran kanshi da ‘namiji’.

Inna su sa’a basu taso ba ne? ta ce mishi eh in ma sun tashin ba su riga sun iso ba ya zauna suna hira da jin hirar tasu kasan sun riga sun zama abokan hirar juna sosai, a hirar da suke yi na fahimci Ado ne ya sanya Sa’adatu da Baba qarami a Makarantar Islamiyar unguwarmu ban dai tsoma musu baki cikin maganganun su ba.

Suka yi hirar su suka gama da ya ce mata zamu tafi sai ta ce mishi da jira nake yi Sa’adatu ta shigo don ta raka ku da kai da kafin nan ko sai da safe a kawo muku? Ya ajiye xan makullen da ya

kulle qofar gidan ya ce mata gasi in ta dawo ta kai mana ta rufe gidan ta kawo makullin nan sai mun dawo zan zo in karva ta ce mishi to muka fito.

Ba mu dawo ba sai wajen goma da rabi na dare saboda unguwannin masu yawa muka je har gidan mai babban allo da gidan Alhaji mai kuxi da gidan Musa abokin Ado wanda shima bai daxe da zama ango ba, a hanya muna dawowa tun daga nesa Ado ya hangi Mama a tsaye a qofar

gida cikin damuwa yake ta nanata faxin me kuma ya fito da Mama waje tare da waxannan sakarkarun yaran?

Dama dai ayi sa’a ba wata fitina suka xauko mana ba na ce to amin muna isowa yayi maza ya fito daga cikin

taxin

in ban da ma na tsaya na xauko mana ledar sayayyar da yayi mana da mai

taxi

ya tafi dashi.

Lafiya kike tsaye a waje a cikin sanyin nan Mama? Ina fa lafiya tana faxi tana qara tafa hannu tare da salati, me ya faru Mama? Ya qara tambaya don ya san abinda ya farun, uhun xaukan wa kaina abinda yafi qarfina nayi na xauko fitina na saka cikin al’amarina yana nema kuma ya buwaye ni ya buwayi duk wani nawa.

Cikin natsuwa Ado ya tambaye ta fitinar sai kawai ta nuna mishi ni, yayi kasake yana sauraronta tana gaya mishi nema take sai ta raba ka da zumuncinka ba kuma zai yiwu ba, ba zan barta tayi nasara ba, don babu inda na ji an ce don mutum bai yi aure ba ba zai shiga aljanna ba.

Buqata dai kawai mutum ya kama kanshi ne ba a qi aure kuma a rinqa leqe-leqe ba, to amma zumunci fa? Sau nawa ka ji ana cewa wanda bai yi shi ba ko yaje

zai wuce saboda a yakanshi sun kai sai makaran zumuncin ya kamo shi ya hana shi wucewa? Tana rufe baki don hutawa Ado yayi maza ya tambaye ta me aka yi ne

Mama?

Ta ce, ai dama nasan ba za ta yi akan sanin ka ba, to dubi qofar gidan yanda ta kama shi ta kulle ta bar su suna tsaye a waje don su ce kaina ku samu matsala a tsakaninku.

Ado yayi mata rantsuwa ya ce mata ba ita ce ta rufe gidan ba, ni ne Mama, ya kuma gaya mata yanda aka yi duk har ya bar

key

xin a cikin gida nan da nan kuma ya tura ni na shiga na karvo na samu tana cewa haba Ado, yau ku ke tare da su in ba ita ta saka ba yaya za’ayi ayi haka? Ni kam cikin zuciyata na ce Mama kenan, wanda take so ya more baya laifi a wurinta, komai yayi sai ta ce ba shi ba ne in ma shi da kanshi ya ce shi ne taga zai xorawa kanshi laifin da bata so ya xauka sai ta ce to sa shi akayi. Ado yayi ta bata haquri har dai ya samu ya lallavata ta shiga gida.

Muna shiga xakinmu ya kalle ni cikin natsuwa ya tambaye ni “Humaira za ki iya zaman qauye kuwa? Da sauri na bugi qirjina na ce qauye? Ya amsa eh, na ce hu’un su qauye manya, to ni me ma zai kai ni wani qauye? To ko Giyaxe abinda yasa take yi min daxi ai saboda Hajiya tana can ne.

Bai sake yin maganar ba, iyaka dai rannan nasan Ado bai wani yi bacci sosai ba duk

da ya saba yin bacci mai nauyi dake baiyanar da alamar gajiyarshi a duk lokacin da al’amura suka afru a tsakaninmu, amma a yau har cikin dare da na farka idon shi biyu na ganshi. “Lafiya baka yi bacci ba?” Ya ce, min lafiya, tunaninki ne ya hana ni yin bacci, ya kamata in samar mana wani wuri da zamu zauna cikin ‘yanci da kwanciyar hankali Humaira, bai kamata ace kowane lokaci kina cikin fitina da fargaba ba, musamman a wannan lokacin da kike da juna biyu.” Juyawa nayi naci gaba

da baccina na qi kula zancen nashi saboda bana son kirana mai juna biyu da yake yi.

Tun washegarin ranar dai na lura Ado yana yin wasu abubuwa da suka fi kama da lissafe-lissafe da kuma kintse-kintse sai dai da yake gaba xaya al’amarin ya tafi ne kan takardu sai ban maida hankalina wajen neman sanin abin da yake ciki ba tunda dai bai ce min ba sai nima ban tambaya ba.

Kwana biyu da tafiyar Hajiyar Giyaxe ina zaune a falonmu ni da Ado in har da wata rana da na soma tunanin lalle juna biyu yana nufin wani abu mai girma da muhimmanci da wahalarwa kamar yanda kullum Ado ke gaya min, to ranar ne don kuwa wuni nayi a galabaice saboda amai, ko abincin rana ban iya girkawa ba balle na dare. Ado ya dawo daga kasuwa da yamma ya same ni a kwance nayi mishi bayanin abinda ake ciki ya ce to abin da nake faxin zai tabbata kenan?

Ya sake kallona ya ce min to sannu kin ji Humaira? Na ce mishi to ya sake kallona ya ce min amma in na roqe ki ai zaki iya yi min wani alheri guda xaya ko? Na ce mishi eh, ya ce to wanka nake so kiyi ki sanya min wannan rigar a jikinki in ganta, xazu naje na karvo ta daga wurin xinki in kin iya yi min haka shi kenan don ta rashin girki babu komai, sai in fita in je in nemo mana abinda zamu ci na ce mishi to.

Muna zaune da Ado bayan nasha kwalliya cikin sabuwar rigar da ya karvo min daga wurin tela ta xinkin kanfala ‘yar asali, sai kallona yake yi yana murmushi ke kin gan ki kuwa? Ban ce mishi komai ba iyaka dai kawai nima nasan nayi kyau, to me dame kike so in je in kawo miki?na xan rage fara’a kaxan na ce mishi ni dama ka bar ni haka kawai tunda lalurar ciki take ai ba a biye mata…zai ci gaba da yi min magana sai ga Suwaiba ta shigo da gudu, murna take yi farin ciki mai yawa ne ya bayyana a fuskarta wai in ji Baba wai ku zo yanzu-yanzun nan kai da ita

.

T

ana

faxin hakan ta juya da gudu ta tafi tanfar dai wata yarinya ‘yar qarama, Ado ya waiwayo ya kalle ni, nima kallon nashi nayi ko lafiya? Na ce ba zan iya sani ba sai mun je mun ji. Nasa hannu na xauki gyalena, ya kalle ni cikin sanyin jiki ya ce ko dai za ki bari ne in je in ji tukuna? Na ce to ai cewa tayi muje tare kar ka je kai kaxai xin kuma ya zama maka laifi, ya ce haka ne to muje.

Muna shigowa gida Babana muka fara gani a tsakar gida sai Mama da kuma Innata da ke can wajen bakin qofarta ga dukkan alama kuma kiranta aka yi ta fito. Muna shiga gidan muka tafi qasa don gaida Baba, amma maimakon ya amsa gaisuwar da Ado ke yi mishi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login