Showing 6001 words to 9000 words out of 18753 words
har ta ce ta samu tear, a yadda take jin radadi a tare da ita. Abun na Mukhy duk da cewa (is not by force, is so gentle, so soothing and so romantic), domin yana yi ne yana hadawa da lallashin ta a kowanne dakika, ta hanyar kwantar da gashin kan ta da hannun daman sa, kuma baya rushing, yana yin komai a sannu, sannan yana bari ta huta na wasu awanni yana bata labarin rayuwar sa a Paris da irin wahalhalun da ya sha wajen neman na kai da neman ilmi, to amma fa ita a wurin ta akwai mugunta da son ladabtar da ita duk da haka.
A wurin Maina Mukhtar yadda ka tafiyar da matar ka a daren farko a haka zata mike, don haka Mukhtar bai yi da sauki ba, sosai ya baiwa Amani irin darussan soyayyar da yake so ta tashi dasu. Ta mika da su har karshen rayuwar su. In fact, sai da ya fanshe duka kwanakin auren nan nasu da aka kwange masa a daren jiya da wunin jiya kadai, ko yace ya sauke wahalar duka samartaka data tuzurancin sa within 24 hours only.
Da asubahin ranar Amani ta kafa sabon kuka, musamman data ga bazata samu yadda ta ke so daga gare shi ba, wato so take Mukhtar ya lalace yayi ta lallashi da tarairayar ta, kamar Romeo kada ya je ko’ina, amma tuni shi ya tashi ma yayi wankan sa ya zuba farar shaddah Wagambari, kyale ta yayi tana ta yi riii-riiii-riii, wai don ya ce ta taka da kanta zuwa toilet, bazai iya barin lokacin sallah ya shige shi ba, shi baya son rakin nan nata, ya hau shirin tafiya masallaci, ta tabbatar fita zai yi, sai ta kara rushewa da kuka.
Da ya rasa yadda zai yi da kukan nata don baya son jin sa ko kadan, zuciyar sa tabuwa take, tsinkewa take, sai ya yi wa Baba Sahura waya, yana tsoron kada yau ma Amani ta sa yayi missing jamI kamar yadda ta sa shi sallah a daki jiya, da wannan kukan nata mai bukatar ya lalace a lallashin ta.
Sahura na shan barcin bayan asubahi wayar Maina ta tashe ta, da sauri ta tashi zaune ta amsa, sai ta ji gyaran muryar Mukhy yana cewa, yi hakuri Baba Safoorah, na tashe ki daga barci, Im so sorry.
Nan da nan Sahura ta wartsake ta ce Babu komai Maina, Allah ya sa dai lafiya kuke, ran ka ya dade? Gabana ya fadi.
Sai da ya kai zuciya nesa sannan ya iya cewa Yar ki ce bata ji dadi ba, ni kuma ban san taimakon da ya dace in bata ba, sannan inaso in samu sallah. Ya fada cikin dakewa, don ya gwammace ya kira ta akan dai ya kira Ummami, duk da itama Baba Sahuran yana jin kunyar ta, amma ya san gara wata kunyar a kan wata. Baba Sahura nan da nan ta je gano, ta soma murmushi ta ce ranka ya dade ai ba abun damuwa bane, ba sai na zo ba, hada mata ruwan zafi cikin abin wankannan ka saka ta a ciki kamar minti talatin, ka bata panadal ta sha tayi barci mai kyau shikenan zata samu karfin jikin ta in sha Allahu.
Har ya je ya yi sallah ya dawo tana nan yadda ya bar ta amma barci na fizgar ta.
Bayan sun aje wayar itada Mukhy Baba Sahura kasa rike wannan labarin ita kadai ta yi a ran ta, bakinta har kaikayi yake, ta kira Ummami ta sheka mata labari, Ummami ta ji kunya amma sai ta hau ta da fada tana fadin ita fa Uwa ce ta dinga kama kan ta, ta daina shiga shaanin su, ta kuma hau murmushi ita kadai, a lokacin tana tare da Mai a turakar sa, amma ya fita sallah bai dawo ba, tana ta murmushin ta na farin cikin yau Mukhy ya zama magidanci, sai ga Mai ya shigo, tana rike da wayar a hannun ta.
Me ya faru ne Mowar Sarki? Irin wannan murmushi da sassafe ban yarda kalau ba. ke da wa kike waya da asubahin Allah?. Ta yi yar dariya ta ce labari Sahura ke bani wai yau Maina ya zama magidanci, shine nake mata fada na ce ta daina shiga shaanin su. Farin cikin Mai Diffa ya kasa boyuwa, Ummami ta kara da cewa kuma ta ce diya ta ta kawo mutunci fal, kamar yadda dai aka san gidan mu. Alhamdulillah.
Mai Diffa ya daga hannu ya yi wa Allah godiya, yace ki shirya kyauta ta musamman ki bata in ji ni, amma kada ki gaya mata dalili, ko ta san mun sani, to ya maganar sadakokin da Sultan ya bashi? Tunda sai yanzu ya angwance ma?
Anya basu yi wuri ba Ummami?
Ummami ta ce gaskiya dai, a dan dakata kadan, a tsahirta ko zuwa ta yi haihuwar fari ne, su fahimci juna sosai tukunna, da koyon rayuwa tare a gidan sarauta, wanda basu tashi sun girma cikin sa ba. Don na lura akwai kuruciya har yanzu a tare da su su duka musamman ita.
Mai Diffa ya yarda da shawarar Ummami.
**** **** ****
Ka ce wai nauyi, nauyi ne da ni, don haka bazaka iya daga ni ka kai ni toilet da kan ka ba Ya Mukhy?
Amani ta fada cikin marairaicewa, kafin ya amsa ta sake cewa “to shin wa ya dauko ni ya kawo ni dakin nan? In ji dai na san ba da kafafuna na shigo ba?
Amani ta bashi dariya sosai da wannan maganar, amma da yake ba gwanin yin ta bane murmushi yayi, haka ta cigaba da nacin sai ya dauketa ya kaita toilet yadda Romeo yake yi wa Juliet, dariyar ta subuce masa wannan karon, sannan ya ciccibeta ya dauka duk da nauyin nata da yake korafi ya nufi toilet da ita.
Ke dai ki rufe min bakin tsiwar nan, kafin ki zaburo ni na kara dinke shi. An ce na hada ruwan zafi a Jacuzzi in saka ki a ciki na rabin awa, kada ki tashi. Amani ta fiddo ido Wane irin ruwan zafi kuma Ya Mukhy? Haihuwa nayi? Mukhtar ya ce To me marabar ki da mai haihuwar tunda na bude hanyar haihuwar? Mace sai tambayar tsaya tana fama da kan ta, amma ba ta tsayawa ta ci ribar zance.
Mukhtar ya dire ta a toilet ya hada ruwan yasa hannu yaji shi da zafi cau, kamar na wankan jego, sai ya dauka haka Baba Sahura ke nufi, ya dauki Amani ya tsumbula ta a ciki, da ta yi wani zillo sai ga ta ta koma jikin sa ta shako shi, sai gashi shima tsudum ya biyo ta sun fada cikin ruwan tare, shima ya ji zafin yace, wash! Muguwa!
Ta ce ai gara mu sha zafin tare Mukhy ya ce of course, tunda tare muka sha dadin ma! Amani ta rufe ido tana jin kunya, in wani ya gaya mata wannan Mukhyn Alhaji ne mai wannan daure fuskar da rashin walwala kamar malaikan daukar rai zata musa, tabbas (mace mai canza namiji a aure komai zafin sa).
Amani ta boye kan ta a kirjin Mukhy cikin murya mai ban tausayi ta ce ni kam ban gane komai ba sai azabar da ka bani Ya Mukhy, muryar ta abin tausayi ta saka Mukhtar ya rungume ta sosai a cikin ruwan, ya sumbaci lips din ta affectionately sannan ya ce, kada ki damu kin ji ko Sweetheart, don na farko ne shi yasa, you will soon come begging for more!
Amani ta rasa inda zata sa kan ta don kunyar da Mukhy ke bata yau, amma ta lura Mukhy ko a jikin sa. Yau cikin nishadin sa yake komai.
Don haka tare aka yi wankan jinyar, Mukhtar da Amani.
Aka zo maganar wankin zanin gado, yace ni kam bazaki saka ni aikin wahala ba bayan wanda na kwana yi, ki dauki abin ki ki wanke. Amani ta yi narai-narai da ido, ta ce ai ka san ko a gida ban taba yin wanki ba, balle na zanin gado, ni fa ko bras dina Rakiya ke wanke mun da azama ya bada amsa nan kuma ba gida bane wajen neman lahira ne, wallahi in bazaki wanke ba, Baba Sahura zan kaiwa ta wanke. Amani ta bare baki zata yi kukan nata na gado, Mukhy ya ce cikin kwafa,
kina farawa ina karawa.
Sai ta maida bakin ta ta rufe har da toshe shi da hannun ta, shi kuma ya yaye zanin gadon ya aje shi gefe ya ce ta shimfida sabo.
Bata kula da sanda ya dauka ya jefa shi a kwandon kayan wankin su ba, ta shimfida sabon bedsheet ta lallaba ta koma ta kwanta, sai Mukhy ya baro magani ya kawo mata da kofin ruwa.
Amani ta ce narka min shi a kan cokali, ban iya hadiyar kwayar magani ba Mukhtar ya ce Amani kina wahalar da ni ina wahalar da kai ko ka wahalar da ni? Ko dai mun wahalar da juna? Kema fa yarinyar nan na lura a matse kike, Allah ne yayi cewa ni din nine da kin hana sadakoki na masu shigowa samun sauran komai a tare da ni.
Tun da ya fadi haka Amani bata sake kula shi ba, ta juya ta kwanta ba tare da ta karbi maganin ba. Mukhy ya ce.
Gara ma ki karba ki sha, don ki warke kafin dare, this is your daily duty as a house wife, tunda ke kadai ce for now, gara ma ki sani tun yanzu ban fasa karbar sadakoki na ba, sai ranar dana karbi ta goma! Zan rufe kofa. Amma har a Aljannah ina fatan ki zamo shugabar mataye na.
Amani ta tashi zaune, idon ta fal hawaye, duk da cewa ya karramata cikin maganar sa ta karshe amma ko kadan bata son zancen sadaka kamar yadda bata son mutuwar ta, ta ce a sanyaye.
Yaya Mukhy, wanda ya sake cutar da wani tsakanin mu daga yau, koda da zazzafar magana ne, ko maganar da dayan mu ya nuna baya so, bayan mutual understanding din da muka samu yau, and forgiveness to each other, ina rokon Allah ya bi masa hakkin sa a kan dan uwan sa!. Sai kuka.
Juyawa yayi bayan ya ajiye mata maganin akan bed-side din, jikin sa ya dan yi sanyi da jin kalaman ta, ya yarda da gaske Amani bata son maganar sadaka. Ai kuwa shi maganar yanzu ma ya fara domin ya samu makamin yakin sanya Amani ta yi masa abinda yake so a duk lokacin da ya ga dama da barazanar Sadaka, ba don wai ya yanke a ran sa zai karba ko ba zai karba ba.
Ganin kukan da take bilhaqqi take yin sa, sai ya koma lallashi To shikenan, ki yi hakuri Sweetheart, idan na daina maganar Sa-daka, kullum sau nawa zaa yi mun alfarmar?
Kafin in fita fada, da bayan na dawo? Kin ga ke din Sweetheart dina ce bana gajiya da rabar niimar da Allah ya yi miki, ga ki Sweet 16 Amanin Mukhy, Allah da ya halicce ki ba da kyawun sura kadai ya bar ki ba, daga sama har kasa har ciki Amani Tafisu ce, Tafisu ba dai abunnan ba. Ya karasa da rungumeta sosai yana kissing idon ta da suka yi narai narai da hawaye, ta ce ko sau nawa kake so Ya Mukhy, ko zan mutu zan amince, in dai zaka bar maganar sadaka.
Sai Mukhtar yaji wani dadi a ran sa, ya riko hannayen Amani cikin tafukan sa, ya kai su ga fuskarsa suka tallafi lallausar sajen dake kwance a kowanne gefe na fuskar sa.
Balle ma bazaki mutu ba, sai dai hakan ya kara min son ki, sannan ki yi ta suburbudo min yaya ina kara son ki da kaunar ki, ina kara kula da ke Tafisu.
Ke din wata mutum ce mai daraja a waje na saboda ALHAJI! Wadda komai tsayin lokaci da canjin da zamani zai kawo, ko tsufa, ko canzawar halitta saboda shekaru ko girma da ya same mu, ko wani abu makamancin hakan, bazan taba iya wulakantawa ba.
Daddyn ki mutum ne da bazan taba manta alkahirin sa a rayuwa ta ba. Don haka zan kula masa da tilon Tafisun sa, in adana masa ita a daki na ni kadai, in mayar da ita TAFISU TA GASKIYA, amma ba da komai tawa Tafisun zata fi sauran mata ba sai da nagarta, kyawun hali da rikon addini, kula da miji da iya soyayya ga mijin auren ta, da kuma iya kula da yayan ta da iyayen ta.
Kalaman sa sun kashe Amani don dadin su a ran ta, Mukhy ya daina ce mata shashasha, ya yarda ita din, ba ballagaza bace. Idon ta fal hawaye ta dube shi da dukkan kauna da soyayya a kasan idanun nata, ta soma magana cikin rauni murya.
Na san bazan ce ina son ka ka yarda ba yanzu Ya Mukhy, na san na makara, bazan ce maka tuntuni ba kin ka nake ba, kishin yadda Alhaji ya fifita son ka a kaina ne ya sa nake kyarar ka ka yarda ba, bazan ce maka a kasan raina ina yawan yaba surar ka da a fili nake kushewa ka yarda ba, don na bar baya da kura mai yawa, bani da say a yanzu da zai yi tasiri a zuciyar ka a kan SO, tunda baki shi ke yanka wuya, kuma maganganu zarar bunu ne.
Na fadi maganganu cikin jahilci da yawa, wadanda da inada dama a yanzu, da na mayar da su na hadiye su a ciki na.
Mukhtar ban fara son ka don na ga kai waye bane, ko don nasabar ka, ni dai kawai gani nan ne, zan iya cewa tun a Saliyo! Ranar nan. Na fara samun sauyi a zuciya ta a kan ka.
Ka yi min rai Ya Mukhy kada ka karba Sadakoki, ba don ni ba!
Ta cigaba da matsar kwallah tana cewa duk abinda kake so zan maka daga yau, ko da ya fi karfi na, zan aro karfin a duk inda yake, wani irin kishi ne da ni a kan ka, mai barazanar haukata ni, idan suka shigo.
Mukhtar yama rasa me zai ce don dadi yau. Ya shirya tsaf cikin irin kayan gidan su, amma bai nada rawani a kan sa ba.
Your actions will prove your words Hajjaju, babu bukatar rantsuwa anan Hajiya Amani, abun nufi, in gani a kasa kawai, Mukhy sama Mukhy kasa ana kula da ni, wato ki cigaba da yadda kika fara yau, saboda ke dinnan tsoro kike bani, sakamakon halin ki na hawainiya yau fari gobe baki, na rantse tuban ki na muzuru ne a yawancin lokuta, ba kya taba tuba don Allah! Sai kin ji wuya.
Maganar sa ta so ta bata dariya don tasakanin sa da Allah ya fada. Iya karantar da yayi mata kenan sama da shekaru goma. Halin ta mai wuyar canzuwa ne don an ce hali zanen dutse ne, sai dai ma iya cewa zata rage wasu in aka cigaba da ankarar da ita a hankali cikin kauna da soyayya.
Zani gun Mai, daga nan zamu je Dosso nadin sarautar dan sarkin Dosso, probably sai Maghriba zan dawo.
Ya juya zai fita, Amani daga kwance ta kira sunan sa, muryar ta abun tausayi ta ce.
Ya Mukhy!
Ya dakata ba tare da ya juyo ba. Sai ji yayi Amani ta ce. Baka yi min goodbye kiss ba, you know I love your kisses!
Mukhtar dai yau duk abubuwan da ke faruwa a mafarkai yake kallon su, amma gara ya zarce a cikin mafarkin nan da dai ya farka daga niimomin dake cikin sa.
Murmushi yayi ya daga mata gira da kafada a tare, ya ce cikin dariya.
Na ki din! Maana wato ba zai yi goodbye kiss din ba, har da make kafada alamar ya ki, sannan ya fita yana mata murmushin dake neman narka zuciyar ta.
Idan wadannan canje-canjen da yake gani a tare da Amani cikin dan lokaci na gaskiya ne kuma zasu dore, baya jin zai yi maraba da wasu kwarori, kowacce mace kazama kuma dukun-dukun zai gan ta a kan Amanin sa. Sai dai ita din Zuma ce sai da wuta, amma hakika Amani ta sanya shi cikin madaukakin farin ciki yau, da yake fatan su dawwama a cikin sa har karshen rayuwar su.
***** ****