Showing 18001 words to 18753 words out of 18753 words
daya ta ce to jeka zan kwanta, yau bana son yawan tashi daga zaunen nan da nake, na dauka tea kake so dama.
Haushi da takaici ya kama Mukhy, ya ce Yau Amani ni kike kora ko? Ko fa turare na ban shafa ba duk sabida ke? Na yi rantsuwa da Allah yau ko ki sallama ko gobe a kawo Sa-dakokin nan, ina dalili? A kan ki a ka fara ciki? Wannan izaya fa ta ishe ni.
Yadda Mukhy ya fitittike yana fadan, ta san da gaske ta kawo shi bango, ta kuma san ya kwatanta mata adalci yadda bata zato, duka daga samun cikin ta zuwa yanzu sau nawa ta kasance dashi bai fi a kirga ba, ita ma kuma shakiyanci ne ta fara kewar sa sosai a kwanakin nan, duk wadancan abubuwan sun sake ta, don cikin har ya shiga watanni na biyar yanzu, duk abubuwan da take ji sun lafa tuntuni, don haka yana mika mata hannu ta kama ba musu, sai ya sa karfi ya ciccibe ta ya daga ta a kan hannayen sa zuwa main turakar sa. Amani ta amincewa ran ta in sha Allahu yau zata faranta ma Mukhy irin yadda bata taba yi masa ba a rayuwar auren su.
You add weight, more weight, Oh! Koda yake ba dole ki kara nauyi ba, bayan girman Baby ina jin daga samun cikin nan zuwa yanzu kin ci buhun Dawa da bokitin daddawa, Zabbi hamsin, Dawisu hamsin, ni kuma na ci ukubar da bana yiwa kai na fatan sake afkuwar ta.
The whole night for Mukhy!!!
**** **** ****
C
ikin Amani na da watanni takwas yanzu, ba abinda Ummami take sai shirin tarbar haihuwar ta, duk abinda ya dace a tanada hatta feeder din jariri sun tanade shi, wasu kayan baby da yawa daga Guinea Saadiyya ta aikowa Ummami don tana shiri da Mukhy sosai. Sau biyu yana zuwa kasar Guinea duba ta da bata da lafiya.
Haka Yayar shi Sayluba ma ya je Tahoa sabida sada zumunci da ita.
A wannan hutun ne aka kawo mata Fajur, hutu, zata zauna har sai ta haihu, a bakin Fajur ta ji wani labari da ya gigitata, wai Mamma Jalan ma cikin ta ya tsufa.
A gigice Amani ta kira Mamma tana son tabbbatar da abinda ta ji daga kanwar tata, Haj. Jalan ta rasa inda zata tsoma ran ta don kunya sai ta hau Amani da fada tana cewa ni abokiyar wasanki ce ko Amani? Don kin ga tsayin mu daya girman mu daya ko? Shikyasa kika maida ni saar ki. A shekaru na ai na wuce haihuwa yanzu, ki zauna Fajur tana gaya miki abinda bazai yiwu ba.
Ita kuwa Fajur tayi rantsuwa ta maya cewa cikin Mamma yanzu yafi nata girma, kuma kusan kullum sai ta je asibiti awo.
Amani sai ta kira Alhaji da kan sa.
Daddy da gaske ne? mamma zata baima su Fajur kanne?
Hawayen farin ciki suka tsirgowa Alhaji Usman Faskari na godiya ga Allah. Ya ce da gaske ne Tafisu, da gaske ne!
Uwa sai ta saka kuka don dadi.
A halin farin ciki dana bakin ciki duka, Uwar su Alhaji ta fi gane ta yi kuka.
Amani har katon Sa da rago tasa aka kayar, ta rabar da shi sadaqa ga bayin gidan ta, tana mai taya Daddyn ta godiya ga Allah, da adduar ita da Mamma Jalan duka, Allah ya sauke su lafiya cikin koshin lafiya.
**** **** ****
EPILOGUE