Showing 15001 words to 18000 words out of 18753 words

Chapter 6 - Amani Book Four Complete Hausa Novel

Takori   

31 Oct 2025

64

in dawo da filo na nan, mu kwana tare a gadon nata.



Ta dauka wasa yake yi, amma ba jimawa sai gashi ya dawo cikin fararen kayan barci riga da wando masu kauri a jikin sa samfurin Blooming Dales, yayi wanka ya kara yin fresh da shi, har da turaren sa da ya san yana jan hankalin ta da shi wato Azzaro Visit ya fesa, ya taje sumar kan sa tayi lub gwanin shaawa duk dan ya ja hankalin Hajiyar tasa ta ta yarda ta bi shi, yana shigowa ya jefa filon a gadon Ummami, ya haye yayi kwanciyar sa yana danne-danne a wayar hannun sa.



Amma sabanin baya da hakan ke tasiri a tare da ita, ta isa gare shi da kan ta, ta ce Ya Mukhy me kake so? Shi kuma yace message ko Amani. Don a irin wannan yanayin ko Mukhy bai yi magana ba ta san yana gayyatar ta ne, daga messaging bata sanin sanda yake zarcewa.

Amma sabanin sauran renakun na baya, yau matukar haushi Mukhy ya bata. Ta zaro idanun ta waje tana fadin.

Ya Mukhy! Ka rufa min asiri ka tashi, gadon Ummami ne fa ya ce ko na Mamma Jalan ne, in baki tashi mun tafi ba nima a kai zan kwana, ta yaya karfi da yaji kin hana min karbar kwarkwara yanzu zaki bullo da wannan yaren da ban gane masa ba?

Kunya da tsoron kada Ummami ta zo ta gan shi kwance a gadon ta duk ya addabe ta, ta shiga rokon sa Allah Annabi ya tashi, kada Ummami ta ce basu da sauran kwalli a idanun su.

To ki tashi mu tafi, tunda ke kina da sauran kwallin a idon, sarkin masu kunyar suruka, ba kuma rokon ki nake ba umarni ne ki tashi mu tafi.



Kamar ta fashe da kuka ta ce wallahi na gaji, Allah ya gani yanzu bana so, kai abinka babu hutu sam? Ko inji wani zubin ai yana bukatar hutu balle mutum, ni yanzu ba sadakoki biyu ba, in ma su goma da mata uku zaka karo, bisimillah, ga fili mai doki, don kaga bana so ne kake amfani da hakan kana uzzura min, to na baka dama yanzu Ya Mukhy ka karbi Sadakoki as much as you like.

Mukhy yayi sakale! Daga kwance yana jin ta, yana mamakin ta, yarinya kamar mai hawainiya, rana daya daga yin amai duk tabi ta birkice tana masa tutsu, in ya ce gaban sa bai fadi ba da wadannan kalaman nata ba ya yi karya, don kamar ta daina son nasa kenan.

Kenan ta daina damuwa da shi ko watanni biyar basu rufa suna amarcin ba.

Shi kuma yanzu ne ma ya fara so da dokin Amani ta kasance tare da shi, sakamakon niima irin ta mace mai yaron ciki da ta fara saukar mata.

Murya na dan rawa, Mukhy ya ce ki yarda mu tafi, I will not force you kin sani, I will never force a woman to sleep with me, ni ba wasu Sadakoki da nake so yanzu, ONLY AMANI- I LOVE!

Ki tambayi Ummami ki ji tuntuni na ce ta gayawa Mai bana so, bana bukata, matata AMINA ta ishe ni rayuwar duniya, domin ta fi min goman su.

Hawaye take yi sosai, amma kalaman sa na tasiri sosai a ran ta, sun sa ta jin kan ta ya kumbura, ta ji ta a Tafiun ta, kamar tana yawo a kan gajimare.

Ni bana so ne kana zuwa inda nake yanzu, Kiss din ma dana ke cewa ina so, kana min yanga a kai to yanzu bana so, barci kawai nake so in yi ta yi, kada a tashe ni!

Ta fada da iyakacin gaskiyar ta, tana kaucewa kaifin idanun sa. Yau Mukhtar yana ganin ikon Allah, da kyar ya ce Ni Mukhtar dan Issouffou Massaoudou, na yi alkawarin bazan kasance da mata ta Amani a daren yau ba, sai bisa yarda da amincewar ta.

Amma ai ina gani kana toshe hanci da ka shigo, wato doyi nake yi ko? Ta kara fashewa da sabon kuka.

Ni ban ce kina doyi ba, dakin ne ina shigowa naji yana wani wari-wari da ban saba ji ba tuwo na ne fa, kuma ni yanzu shine abinci na, kada in je gidan ka ka ce kuma na kai maka wari gida kuma to yanzu saboda Allah Amani, me kike nufi?

A wane dalili ina da mata ta a cikin gida na zan yi kwanan gwauranci? Ai ko ban ce ban yafe ba, Allah zai saka mini sau sabain, tun da na lallashe ki na kuma yi miki duk alkawarin da zan iya kin ki ji.

Ya mike yana cewa. Since you insist, do as you wish.

Ya dauka ganin bacin da ran sa ya yi muraran, zai saka ta biyo shi, amma har dare ya tsala bata ba alamar taita a lokacin ma ta kai Zaria a barcin ta har da minshari na kwanciyar hankali da hutu.

Kwanan kadaici da damuwa yayi, sai yanzu ya san yayi mugun sabo da Amani yadda baya zato, kuma ta shiga ran sa yadda baya tsammani. Bai san yana son Amani har haka ba, bai san soyayyar da yake mata ta yi wannan zurfin ba, sai yau da duk inda ya mirgina babu ita sai filin ta a gadon barcin su, ya rasa kulawar ta a gefen sa, da nacin ta na son yayi kissing din ta, ko saukar numfashin ta a kunnen sa yau bai samu ba, wanda hakan yasa Mukhy yayi kwanan wahala ba yar kadan ba.

Yayin da Amani tayi barcin ta cikin salama, don koda Ummami ta dawo dakin bata ko tashe ta ba, don ta gane da gaske tana bukatar hutun.

**** **** ****



Washegari da ya zo gaida Ummami, ya maka bakin glass don boye kumburin idanun sa da launi da suka canza irin na rashin barci, yana ta cin magani, kuma har suka gama hirar da zasu yi da Ummami bai yi korafi akan Amani ba, ya barwa ran sa, mai nufin ya yi fushi da ita.

Ita Ummami ce da kanta ta fahimci hakan, don haka sai ita ce da kan ta ta dauko zancen Amani, inda ta ce masa cikin lallashi.

Maina sai ka yi hakuri da Amani yanzu, a lokacin da mace ke da yaron ciki ta kan samu sauye-sauye a jikin ta, wani zubin har da na halaye da dabiu, sakamakon halittar da ubangiji ke yi a mahaifar ta.

Wata kuma tsanar mijin take gabadaya, ta ji bata so ya zo inda take, wata kuma kamshin jikin sa ma bata so sam.

Abun daban-daban ne (from one woman to another), ka yi fatan Allah ya raba su lafiya kawai, kai kuma ka jure na dan lokaci ne, in kuma a kawo sadakokin toh? Sai in yi wa Mai Diffa din magana.



Mukhy ya rasa a yanayin da kwakwalwar sa ta karbi zancen Ummami, idan ya fahimta daidai, to Amani juna biyu gare ta kenan shiyasa take masa tutsu? Allah da girma yake. Wannan wane irin rantsatstsen rabo ne na gaggawa haka daga Allah! Burin Alhaji Usman zai cika, cikin dan lokaci kalilan na hada zuria tare da shi, Ummami da Mai zasu samu jikoki daga gare shi tun suna raye da sauran karfin su. Tsakanin Hon. Usman da Mai Diffa, bai san wa zai fi farin ciki da wannan kyakkyawan albishir din ba. allah abin godiya.

A lokacin Maina ji ya yi son Amani na ninkuwa a ran sa, kamar yau ne ma ya fara koyon son nata. Bacin ran ta da ya kwana da shi yana tafiya daga makogaron sa yana narkewa.

Mukhy, ya lumshe idanun sa a hankali, ya samu kan sa yana tambayar Ummami ko sai zuwa yaushe ne Amani zata iya koma masa daidai ta daina sababbin dabiun ta da ke ci masa rai haka?

Dariya Ummami ta yi, ta ce ya danganta, mai yiyuwuwa in cikin ya cika watanni hudu ko biyar. Mukhy ya mike tsaye cikin daburcewa ya na cewa.

Ummami, ko dai wata kasar zamu tafi ta ga kwararren likita? Ummami ta ce babu inda zaka dauke ta da karamin ciki jirgi ya jijjige shi, don babu wani likita da zai mata maganin wadannan abubuwan sai lokacin tafiyar su ya yi, babu inda zaku, har sai Allah ya sauketa lafiya don ga dukkan alamu, cikin Amani mai tsirfa ne, in ka dauke ta kuka tafi wani wurin ina zaka nemo mata ire-iren abubuwan da take son ci din nan?

Suka saki wannan hirar suka cigaba da wata hirar daban, amma dai Mukhy ya saki fuska ba kamar sanda ya shigo ba. Daga bisani Amani ta fito falon, ya bita da kallo tana zama daga kasan kafafun Ummami, Mukhy ji yayi kamar ya ciro cikin daga jikin ta ya ajiye a nasa ko Amani ta samu lafiya su cigaba da rayuwar su mai nagarta yadda suka saba.

Ummami sai ta tashi ta fita cikin gida ta bar su a falon. A sanyaye ta ce, Ya Mukhy ina kwana? An tashi lafiya?

Ga dukkan mamakin sa sai ya ji baya jin haushin ta yanzu, sai tausayi, ya tausasa murya ya mika mata hannu, yana mata kallon rahma da kulawa, yace ta shi mu tafi kawai, duk abinda baki so na daina, in ma ya kama mu raba daki sai mu raba, amma (for now) ban iya zama a gidan nan ni kadai.

Sakamakon yadda ya sa idanun sa cikin nata, ya kuma tausasa harshe sannan ya bata hannu, sai ta kasa tankwabe tasirin wannan soyayyar da sadaukarwar, tunda har ya yarda in ma daki zaa raba a raba, shi dai kawai ta kasance cikin gidan sa, don gani tayi ya fi ta zama maraya a kwana daya kacal, duk da gashi a dakin mahaifiyar sa.

Sai kawai ta juya ta soma hado kayan ta da ta kwaso, ta fito da su rie da jakar tana kiran Tahirah, Tahira da dam aba wani nisa suka yi ba suna falon da suke zama su jira ta ta zo da sauri ta amsa ta yi gaba da su, Mukhy ya saka ta a gaba suka kama hanyar komawa gidan su.

Baba Sahura ma yau sai komawa tayi sassan Ummami da zama, da ta zo ta tarar sun rufe sassan su da safiyar Allah. Su Sugrah ma duk sai wajen Ummami suka koma gabadayan su, wai Maina da kan sa ya ce musu su tafi sai ta neme su.

**** ***** *****



Umami ta ce Allah ya taimaki Mai Diffa, na zo da kyakkyawan albishir. Sarki ya tattaro hankalin sa ya baiwa Mowa, ya ce ai ke fara ce mai farar aniya da farin albishir kullum, kullum alkhairi ake ji a bakin ki, fadi ina sauraron ki”. Ummami ta yi murmushi ta ce cikin ikon Allah ina kyautata zaton Maina ya samu rabo. Maana maidakin sa na da juna biyu. Sai Mai Diffa ya dan tsura mata ido, kafin kawai ta ga Sarkin Diffa Maimartaba Issouffou Massaoudou, ya kai goshin sa kasa ya yi sujjadah, dama a zaune yake a kan darduma.

Sarki ya yi wa Allah godiya, ya ce zai sa a fara sadaqa da addua ta musamman a kan Allah ya sauke ta lafiya.

Tun daga wannan ranar nan ake ririta Amani a gidan sarautar Diffa, aka kara mata hadimai a sassan ta, aka hana ta aikin komai sai dai ayi ta tuka mata tuwon dawa tana ci da naman zabuwa ko na dawisu a ciki, tayi wani irin bulbul tayi kumatu sumul irin na matan sarakai, Amani an samu mulkar mutane yadda ake so, amma ita da miji ko oho don ko daki sun daina hadawa.

Iyakaci da safe ya zo ya duba ta sannan ya dan sumbace ta ya fita fada, yana fadawa ran sa duk in the process na zama Uba ne, har ramewa Mukhy yayi a kwanakin nan, don ta ce yana matsowa kusa da ita nausea din yake zuwa mata.

In ka ga Maina wannan lokacin har duhu yayi, amma kwarai yana son ganin an haife jikan Ummami da Hon. Usman lafiya, shi yasa yake daurewa da tsirfar Amani, yake biye mata don dai ta zauna a sassan ta kusa da shi, amma me? Yau dai ta kawo shi makura, ta kawo shi bango, don ya lura abin nata har da mugunta kuma amma cike take da koshin lafiya da kuzari.

Misalin karfe bakwai na safiyar ranar da ya fito daga wanka ya ganta a dakin sa yau, ta gyagije kamar ba itaba ta ci kwalliya da wani yadin karen miski na kasar Senegal da aka yi wa dinki Senegalese, rabon ta da shigowa turakar sa har ya manta, wai ta zo su gaisa kafin ya fita, ya fito wanka ya tadda ta zaune gefen gadon sa tana waya da Alhaji ne ko Maman ta bai gane ba, tana ta smiling, kai ga dukkan alamu dai da Mamma Jalan take wayar, saboda rashin kunya irin na Amani ji yayi tana gaya mata wai har ta fara jin motsi da mutsu-mutsu a cikin ta, bai ji me Mamma ta ce ba dai ya ga ta hau murna tana cewa don Allah a kawo ta da wuri.

Tana ajiye wayar ta daga kai, sai ta ga Mukhy yana mata kallon nan nasa da ita kadai ta san fassarar sa, ya mika mata hannu daga tsayen da yake, Amani ta sunkuyar da kai ta rufe ido, Mukhtar ya janyo ta a hankali ya rungume ta ya cire wayar daga hannun ta, yana rada mata cikin kunnen ta isnt this punishment enough? Ki ji tausayi na Amani, na daina barazana da sadaka, nayi hakuri for quite this time amma Its a promise it will not be hurting, I will treat everything in a soothing and romantic manner, and I will make sure ban jigata baby na ba, Ive tried for you Amani, for your happiness I truly tried kin sani, wata daya ba kwana daya bane, kada abun ya koma da daukar hakki na kuma.

Da wannan Mukhy ya samu ya kalallame Amani har y karbi duk abinda yake so. Ta ce a ran ta ashe dama can ya iya lallashi girman kan sa ne ke hana shi sai yanzu da ya aga kwal uwar daka. Duk ya bata tausayi ya. Ta yarda yayi hakurin kamar yadda bata zata ba for her own well-being. Amani ta daure yau ta amshi Mukhy din ta a safiyar yau da dukkan jaruntakar ta, suka jima suna farantawa juna rai, kuma yayi kokari ya cika alkawarin da ya daukar mata, ya biyar da ita cikin sassaukan yanayi na soyayya mai shiga rai.

Yau gashi har cikin yayi watanni hudu amma Amani bata bar feleke na masu yaron ciki ba, tun bayan wancan encounter din nasu bata sake yarda da shi ba, kullum jiya I yau, cewa take kamshin jikin sa nausea yake saka mata. Yau ma dai Mukhtar tura ta kai bango, a daren yayi shirin barci ya shigo dakin ta ya tarar tana ta cin gyada dafaffiya, ga cikin ya fara bayyana sosai ta cikin rigar barcin ta ya mata kyau kuma, abin ki da doguwar mace, kan ta babu kallabi ta sha kananan kitson da Sugrah ta yi mata gwanin shaawa.

Yayi sallama ta amsa, ya zauna gefen gadon ta ita kuma tana daga zaune a kan tumtum a kasa, ya ce ina Baba Sahura ko har ta kwanta? Yanzu ta wuce, bayan ta kawo min gyada to amma Amani cin komai hayau- hayau haka, ba kya tunanin zai lalata miki ciki? Komai kika samu sai kin ci, sai kace Kura, ni kam wannan Baby ya ya kake so in yi ne? Baka tausayi na sam. Gabadaya ka canza min my real Amani, daga yar gayun Tafisun ta zuwa typical, local, Amani.

Anyway Alhamdullah alaa kulli haal, with your arrival to the esteemed royal family. You My dear. the incoming PRINCE of DIFFA!.

Ta saki wani lallausar murmushi wanda ya taho from ear to ear, kafin ta ce cikin zolaya don tsaf ta gama gano shi, kana son wani abu ne Ya Mukhy? Ya Harare ta wata irin harara mai cike da soyayya sannan ya ce cikin gatse shima,

Aah, sabon kitson nazo gani, zuciyar ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login