Showing 12001 words to 15000 words out of 18753 words
sumbatar ta ta koina, don ya samu ya mantar da ita zancen sadaka.
Amma bata yi shiru ba, cigaba ta yi da fadin.
Wallahi Ya Mukhy da gaske nake na tuba, na tuba na bi Allah na bi ka ba zan sake ba, to ni nace kin min laifine a bani sadaka a kan hakan? Ko shi Mai (Sarki), bai san ma me kika yi min ba, balle ya bani sadaka don ya rama min.
Alada ce kawai kyakkyawa ta gidannan yake son ya cikasawa, alada ba addini bace Ya Mukhy, besides yanzu addini ya daina supporting concubinage, irin wannan auren wasu malaman ma yanzu suna fadin bai halatta ba a wannan zamanin, tun da baa yaki balle a samo ganimar bayi.
Mukhtar ya kasa hadiye dariyar sa yace Ya Shaikh! Amani kenan, su bayin basu da yaya? Kuma yayan su ba bayi bane? Baki san ana gadar su ba daga iyayen su? Kuma in ban karbi Sadaka ba aure kike so in kara da kuruciya ta mata su cika min kwanya?
Ai adalci ne aka yi miki, ta hanyar girmamaki, a baki su a matsayin ababen ikon kisai kin so zasu zo inda nake haka sai kin nemi hutawa zan bukace su. Mukhy ya cigaba sumbatar ta a dokance, yana cigaba cewa,
In kina son mu zauna lafiya kada ki sake yi min zancen Sadaka, wallahi na gaji da jin zacen nan, na gaji Amani, ki bar ni in huta.
Amani kawai nake so yanzu, amma kina neman haukata min ita, duk kin birkita min Amani ta koma kamar zararriya.
Daga haka ya juya akalar hirar tasu zuwa wadda yafi so a yi, wadda ya dawo cikin dokin ta, Amani bata da zabi ban da bin umarnin sa, na barin zancen sadaka da baya so, ba don ta gamsu cewa Mukhtar ya fasa karba ba, tunda kuwa bai furta fasawar da yawun bakin sa ba har yanzu.
Sai taji duk kokarin sa na faranta mata rai, ta hanyar nauikan soyayyar sa da sumbar sa mai shiga har kololuwar ran ta yanzu sun daina sanyata nishadi ko irin yanayin da yake saka ta a baya. Ta dai yi hakuri ne ta kyale shi amma yau bata yi kowacce hobbasa ta taya shi.
Mukhtar a ran sa ya ce in haka mata ke kin kishiya da dukkan zuciyar su, willing to do everything ga mazajen su don su kada a yi musu ita, da ya baiwa duka maza shawara su kara aure, ko don mata fitinannu irin Amani su shiga taitayin su.
Shi kam yau dan gata ne sai yadda ya juya abar sa.. madalla da iyaye masu son cikar farin cikin yayan su irin nasa iyayen. ko babu komai sun samo masa kan Amani yadda baya zato, daga jiya zuwa yau ya mori auren sa har fiye da kima, daga jin zancen sadaka.
***** ***** ****
Ummami a bar maganar sadakokin nan, don Allah ni dai Mukhtar na yafe, ban san ba ko can gaba, amma (for now), a bar su, ina tsoron ta kamu da depression.
Jiya ni kadai na ga abinda na gani, har cikin barcin ta sambatu take tana zancen sadaka, I was terriby scared a daren jiya, sannan ma dai Ummami ni (shes okay for me), kada ku tara min mata su tsofar da ni da tension din su tun da sauran kuruciya ta, kai Ummami jiya na ga boni!
Umami ta yi ta dariya ta ce ka tabbata ta isa? Har tayi yawa Ummami, amma kada ki gaya mata na ce a bar su, bar ni in ta cin albarkacin su.
Mukhtar zai kashe ta da dariya, don haka ta wuce toilet ta bar shi a wurin ta san ba komi bane gyaran da ta yi wa Amani ne jiya yake dawainiya da shi.
Don haka a wadannan sati hudun, Maina Mukhtar, ya rakashe son ran sa, ya more kuruciyar sa iya morewa, yayin da yar Daddy duk ta zama kamar kazar mayu don rama da rashin nutsuwa, don har zuwa lokacin da bakin sa bai ce mata ya fasa ba.
Abin ya zame mata kamar masifa, sabida yadda kullum son Mukhtar karuwa yake a ran ta, haka kishin sa na neman karar da numfashin ta. Duk bayin da aka bata ta kore su ta kawo tsofaffi. Tahirah da Sugrah kawai ta bari. Ta kasa nutsuwa duk da nasihun da Ummami ta ke yi mata kullum, a kan ta fitar da batun kishiyoyi ko sadakoki daga ran ta in tana so ta zauna lafiya da zuciyar ta, ta kuma tsira da lafiyar jiki da kwakwalwar ta.
Kusan watan su uku kenan da tarewa a sassan su. Amani ta soma zazzabin dare. Ga wani tashin zuciya na babu gaira babu dalilli da ke uzzura mata. Sai kuma wani babban tashin hankalin da ya same ta yanzu, ba ta son Mukhtar ya kusance ta ko kusa ko alama, kai har kiss dinsa da take mararin ma, wani zubin har take rokon sa yanzu bata so kwata-kwata don dacin da take ji a cikin bakin ta. Komai daci yake yi mata, ta rasa appetite din ta gabadaya.
Komai taci bata jin ainahin dandanon sa sai dai ta tura don kada yunwa ta yi mata illa.
Allah sarki Amani, ga dai mulki, da jin dadi fiye da wanda ta baro a gida Katsina, ga soyayyar Mukhy ta gama samu yanzu, ga kulawar uwar miji data mahaifin sa, tana kwance ake mata komai sai dai ta wanke goma ta tsoma biyar, ta zama wanke hannu ka taba ko da can ma hakan take gareta, amma duka wannan bai hana a wannan dan tsukin kewar Daddy da Mamma ya dame ta ba, ta daina jin dadin komai, komai ya daina burge ta, amma haka ta yi shiru bata gayawa kowa abunda ke damun ta ba, tana ganin kamar nausea din yana zuwa ne kawai sabida Mukhtar ya uzzura mata.
Ba ya bari ta huta yadda ya kamata ko ya bari har sai ta ji marmarin abun kafin ya bukata, duk sanda ya bushi iska kawai sabida yadda Uwar sa ta dage da yi masa gyara na manya ya gama haukata shi, gashi ya sa yanzu har abun ya fita kan ta, bata ko son ya zo kusa da ita.
Tun tana jurewa don tana ganin zazzabin ta ne idan ta daina zazzabin zata koma daidai, amma ina! Abu ya ki barin ta, har a daren yau da komai ya fara kankama ta bangaren sa kawai sai ya ji Amani ta ture shi, ta mike ta dirgo kasa, ta hau kwarara amai, kamar zata amayar da yan hanjin ta, duk kyankyamin Mukhy da vomiting amma bai ji kyankyamin na Amani ba, ya dafa bayan ta yana mata sannu, ta koma gefe tana maida numfashi bayan ta gama kakarin aman bakidaya, ya rasa inda zai sa kan sa da damuwa, dama dai yana ta noticing canjin da take samu a kwanakin nan, daga na mood har na behavior, ya ce da safe zaa kira likita ya duba ta, ta ce atafau kada ya fara, ita bata son allura. Ita ta san matsalar ta daya kawai ya daina kusantar ta, in ta samu hakan zata koma daidai.
Don haka ta kulla abinda take ganin zai fishshe ta cikin ran ta, don ko bayan ta huta da aman data gama, dan anacan nata bai bar ta ba a daren sai da ya samu yadda yake so.
Garin Allah na wayewa Mukhtar na tafiya fada ta sa Sugra ta hau hada mata kayan ta da duk abubuwan da zata bukata, ta ce ta ai mata su dakin Ummamitana zuwa yanzu. Tahirah da wasu kuyangin suka tasa a gaba kaamr wasu body guards din ta sai dakin Ummami. Bazata zauna haka kawai Mukhy ya kashe ta kwanan ta bai kare ba.
Ummami na cikin magana da kuyangin ta tana basu umarnin abinda zasu yi yau, don ita ce da girki, Amani ta shige su da sauri, cikin takun ta mai kama da na macen Dawisu, ta shige can kuryar dakin Ummami ta haye gadon ta ta kudunduna don sanyi take ji sosai yana shigar ta, ta cigaba da barcin ta cikin kwanciyar hankali, tana fadi a ran ta (at last she is safe).
Ummami bata tashe ta ba har hantsi ya dubi ludayi, ta gaji da barcin ta tashi don kan ta, ta kuma tashi ne da wata azababbiyar yunwa kamar ta ci babu, aka yi saa Ummami na dakin lokacin da ta tashin, tana ta zabga hamma irin ta yashewar ciki, Ummami ta sa ta a gaba ta zuba mata ido tana mamakin kamannin su da Jalan, ita Ummami din da Jalan ba wani kama suke yi ba, sai na dirin jiki, amma Amani da Jalan kamar an tsaga kara, musamman in ta tuna kuruciyar Jalan din da yammatancin ta.
Tuwo, Ummami Tuwo zan ci!.
Ta fada tana hamma tana ture bargon jikin ta, sakamakon zufa da ke karyo mata. Alamar zazzabi-zazzabin data tashi da shi yau ya sauka.
Dama kina cin Tuwo? Kika ce min ke sam ba kya son Tuwo Ummami ta tambaya cikin mamaki wallahi shi nake so yanzu, kuma na Dawa, miyar kuka, irin wanda Ya Mukhy ya saya min a Lagos da zamu wuce Saliyo Ummami ta yi dan jim, kafin ta ce to bari in sa a tuka yanzu, ai bazaa rasa Dawar a kitchen ba, ina yawan tukawa Mai ita. Pls Ummami, a saka daddawa da yawa tayi doyi sosai miyar.
Ummami ta juyo tana kallon ta, kallo na kurullah sanan ta yimurmushi ta ce to bari a yi sauri, Allah ya sa akwai daddawar.
Amma maimakon tasa kuyangin ta su yi mata da kan ta ta shiga kitchen ta yi mata kyakkyawan tukin tuwon dawa, miyar kuka ta zabga mata daddawa da naman Dawisu, tana yi tana adduar Allah yasa abinda take zargi ne, Allah yasa ita zata fara yi wa Mai Diffa wannan albishir din.
Har yamma lis, tana kwance kamar ruwa a gadon Ummami, tayi dai-dai da kafafu an ware mata AC, sallah ce kawai ke tada ita.
Ga aladar sa kullum sai ya fara zuwa gun Ummami kafin ya wuce part din su, in ya dawo daga fada, haka in zai shiga fada ma sai ya fara zuwa wajen ta sun gaisa da safe, sun yi hira ta da da mahaifi, sannan ya wuce fada.
Yau ma da ya dawo sai ya zarce sassan Ummami, domin yayi mata sai da safe, sai ya tarar da ita tare da Hajiya Tarha watau kishiyar ta, suna magana, Saadiyya Yayar sa ce ta haihu, wato yar wajen Haj. Tarha, ana so a je Guinea da yawa don a yi mata barka, shine ta zo tambayar iznin Ummami ko zaa tafi har da matar Maina?
A bisa rokon ita Saadiyya din, don Gimbiya Sayluba ma wato babbar Yayar su zata je.
Ummami ta ce Eh toh, bana ce ba, amma bana jin Maina zai bar ta, don bata jin dadi kwana biyun nan.
Sai da gaban Haj. Tarha yayi mugun faduwa, don dama abinda take son tabbatarwa kenan, don an kai mata gulmar matar Maina har ta samu rabo. Ta yi amai a kan hanyar ta ta wucewa sassanta kuyangin Tarha sun gani. In banda haka ina amaryar da ko shekara bata rufa ba a dakin ta ba ina tafiya wani barkar haihuwa har kasar Guinea?
Ta dan sukurkuce tana fadin ai toh, abinda na ji gaskiya ne kenan? Har ta yi tuntube daga zuwa?
Ummami sai da gaban ta ya fadi, wato baka taba raba gidan sarauta da gulma da daukar zance, ko ita da ke tare da su dare da rana zargi take, bata tabbatar ba, zargin ma yau ta fara shi, amma ashe har zance ya cika gida har je kunnen kishiyoyin ta?
Tsoron ta Allah tsoron ta kada Sarki ya sa abinda Maina zai haifa yayi irin rayuwar da yasa Maina yayi, wato tashi ba tare da kulawar iyaye ba, wai don nema masa tsari daga magauta.
Sai ta shiga adduar ita kam gara in ma cikin ne da Amani, to Allah yasa ta haife diya mace, da dai ta haifi namiji yayi irin rayuwar da mahaifin sa yayi.
Menene tuntube kuma ni ya su? In ji Ummami, har addua take kada Amani ta fito ko tayi motsi daga kuryar daki don bata so ma Tarha ta gan ta.
Sai ga Mukhtar ya shigo dakin da sallama, daidai Ummami ta rako Tarha zata tafi, tana gaya mata tuntube yana nufin an samo rabo.
Sai Ummami ta kira kariyar Allah a zuciyar ta, ta hanyar cewa;
UIzu bikalimatullahi tammah, nimal shaitanin wa hammah, wa min kulli ainin lammah.
Sannan ta ce wa Tarha ni dai kin ganni ban sani ba!.
Ya gaida Haj. Tarha dake fita, sannan ta wuce. Ya zauna a kujerar da Tarha ta tashi yana cewa,
Ummami ki yi hankali da ita fa, ni bana son kirkin Haj. Tarha sam, duk kudin goro nake musu ita da Haj. Ummu Aymana, ban yarda da ita ba, na bi kirki da gudu na tattake ba takalmi a kafa ta.
Ummami ta yi dariya ta ce lallai Maina ka ji Hausa a Katsina, kada ka damu, Tarha ba irin Ummu Aymana bace, akwai dai kishi wanda dole ne a tsakanin mataye da ke auren miji guda, amma bata da mugun nufi a kai na, sannan tsakani na da kowa a gidannan hasbunallahu waniimal wakeel.
Bana tsoron kowa sai Allah, kai dai ka rike Allah, sannan ka rike sallah, ka kuma rike addinin ka da imanin ka, wallahi kai da kowa sai gani sai hange.
Mukhtar ya gamsu da bayanin mahaifiyar sa, ya zauna dab da ita kamar zai shige cikin ta, yana fadin na gaji da yawa Ummami, mulkin alumma ba abu ne mai sauki ba, ina matukar ganin kokarin Mai, bawan Allah!
Ni kuma yanzu ga matar gidan can kuma ba lafiya na kasa gane kan ta.
Ummami ta sakar masa harara ta ce fita ka bani wuri kada surutun ka ya tashe ta, da kyar ta samu barci Mukhy ya ce wa kenan? Tace ita wadda kake zance barci take yi? Kuma a cikin dakin ki? Mukhy ya tambaya da mamaki. Ta ce eh mana, me ye da dakin nawa da bazaayi barci a cikin sa ba? Ba haka nake nufi ba Ummami? Ita bata da daki ko me?
Ummami ta mike tsaye ganin ya fara fusata, ta kwantar da murya ta ce Ka kyaleta don Allah Maina, har kayan ta ta hado ta dawo nan, na lura bed rest take so ta yi, duk da dai batace min komai ba.
Mukhtar sai ya mike tsaye yana cewa yau nake jin abinda ba zai yiwu ba Ummami ta ce ya yiwu ya gama, baka ganin bata da lafiya ne? Na tabbata matsanta mata kake Ummami ko suma take tana farfadowa bazan iya kwana ni kadai ba.
Umami ta ga ran sa ya soma baci, sai ta ce to Tarha da take so a tafi Guinea da ita wajen Saadiya ashe bazaka bari ba?
Ya ce what! irin yadda ya tsorata abun saida ya baiwa Ummami dariya.
Kai tsaye ya wuce dakin Ummami ita kuma sai ta dauki mayafin ta ta bar musu dakin kada a yi abun kunya a gaban ta.
Tana jin duk abinda suke fada domin lomomin tuwo take kaiwa bakin ta a lokacin, wani na bin wani, Mukhy ya bi abinda ta ke ci da kallo ya ga tuwon dawa ne da yaji kanwa da wata bakar miya, duk dakin ya cika da warin daddawa, yana toshe hanci ya ce.
Halan AMANIE baki da lafiya? Halan something is fishy with you? Whats this annoying smell for?
Amani ta ajiye kwanon tuwon, ta hau side hannu, sannan ta daga robar ruwa ta kai bakin ta ta shanye tas, kamar Giwa, ta daddage ta saki gyatsa mai ban haushi, Mukhy ya rasa inda zai sa kan sa da wannan sabuwar Amanin mai matukar ban haushi da takaici, yaushe rabon yayi magana ta yi masa banza!
Tashi kiyi brush mu tafi muyi wanka mu kwanta haka don Allah, na debo gajiya tausa nake so kimin yanzun nan, kin ji Amani-Amani na?
Ta russunar da idonta kasa ta ce ka yi hakuri Ya mukhy, ba inda zani gaskiya, na dawo nan kenan. Mukhtar ya soma shaqa, sai ya juya kawai yana cewa to babu laifi, bari in je in yi changing, sai