Showing 9001 words to 12000 words out of 18753 words

Chapter 4 - Amani Book Four Complete Hausa Novel

Takori   

31 Oct 2025

65

*****

Fitar sa ba jimawa ta sha maganin da ya aje mata ta cigaba da kwanciya har ta ji kwarin jikin ta, sai ta ta shi ta shiga wanka, a gurguje ta shirya cikin sassaukar shiga ta wuce sassan Ummami.



Tun a hanyar isar ta bangaren Ummami take shirya kalaman da zata doshi Ummami da su.

Ummami na kitchen tana hada Karin kumallon Mai ta shigo kitchen din ta same ta, rabon ta da ita har ta manta tun daga zancen sadaka da aka gaya mata, amma Baba Sahura ta tabbatar mata lafiyar ta kalau ittikafin zuciya ta shiga a kan sadaka, kamar an jefo ta Ummami ta gan ta a bayan ta duk ta rame, amma tayi kyau sosai kamar ramar ta kara mata kyau ne.

Tausayi mai tsanani ya kama Ummami, ta dube ta ta ce ke kam lafiya kika fito haka da sassafen nan? Ke da aka ce ba lafiya ce ta ishe ki ba? Yanzu nake shirin shiga in dubo ki, ina jiran abincin ki ya karasa ne.

Ta samu kujerar zaman cin abinci a kitchen din ta zauna, cikin jin kunya sosai kamar ba Amani Faskari ba mai ido a tsakar ka, ta gaida Ummami, amma bata amsa maganar da Ummami ke yi ba, saboda yau surukuta sosai take ji da ita ba Uwa ba. Tunda itada Mukhy yau babu hijabi. Ummami da rawar jikin ta taje ta juyo farfesun Zabuwa data ke yi mata da hannun ta, ya ji kayan kamshi na gargajiya sai tiriri yake da tashin kamshi, ta zubo shi a wani tangaran mai fadi haka kamar bowl na sarauta ta kawo mata, tana cewa cikin kulawa ki ci maza yanzu, ki shanye romon duka, ko kya ji dadin jikin ki.

Ta karba ta soma ci a yangace, cikin yaukin ta na halitta. Ummami ta lura cikin damuwa ta ke, ba nutsuwa a tare da ita, ga ba walwala, ga hawaye sun ciko a idon ta.

Ummami ta ce cikin tausasawa ki yi hakuri kin ji? Wannan ita ce rayuwar kowacce diya mace a gidan aure, a hankali zaki saba, har ya daina zame miki takura sai armashi da nishadi, kuma ba zan bar ki haka ba In sha Allah, zan baki abubuwan da zaki dinga amfani da su, ki ci ki sha don karin niima da kuzari da koshin lafiya.

Kowacce mace da kika gani da yayan ta gwanin shaawa an ce miki ta sauki ta same su? Soyayyar aure na da dadi, amma wani lokacin sai an jure, rayuwar da Allah ya tsara mana kenan mu mata, wadda muke fatan samun aljannah ta hanyar ta.

Amani da ke neman rushewa da kuka ta ce to Ummami amma da wahala ai, gashi Ya Mukhy bai daina zancen sadaka ba har yanzu, da me zan ji? Da wannan matsawar tasa ko da damuwar maganar Sadaka da naji ana yi?

Tun ranar ban yi barci ba Ummami, ido na bai runtsa ba ko na sakan, ko gyangyadi na yi in na tuno zancen sadakoki sai na farka, na yi duk kokarin da yake so amma duk da haka ya ce bai fasa karba ba.

Ummami na so ta yi dariya, amma ta maze, Me zai karba ne ban gane ba?

Ta ce Ummami mun daidaita kan mu ni da Ya Mukhy jiya, ba kallon juna muke da ido ba, don Allah a yi hakuri a fasa bashi sadaka.

Ummami ta ji dariya na son bada ita, ta ce to ai baki sani ba, a halittar da Allah yayi musu ne mace daya bata isar su, da a kara masa mata uku na aure ba gara miki sadakokin ba? Tunda su ba matsayin ku daya ba dole suna kasan ki ne? Amani tasa hannu ta rufe ido ta runtse shi ta kauda kunya, ta ce.

Ummami, da yardar Allah ni Amani na yi alkawari ni zan ma Ya Mukhy hidimar da mata hudu zasu yi masa, in sha Allahu. Yanzu kam Ummami ta kasa rike dariyar ta sai da ta sake ta kadan, ta ce Magana tana hannun Mai, ba ni na roka masa ba, an kawo masa kyautar su ne daga Sultanate of Damagaram (Zinder) sabida girmama wannnan masarauta da yi masa barka da dawowa gida, duk a cikin shirye-shiryen bashi sarauta ne.

Amani ta daure ta hadiyi miyau da kyar, sannan ta ce Ummami kin ce ni da ke ba surukuta tsakanin mu ko? Uwa ce da yar ta ko? Kin ce in miki alkawarin kula da Mukhy zaki zame min garkuwa a kan sa, to nayi miki wannan alkawarin na kara yi, ina rokon ki, ki taimake ni! Ki yi min garkuwa da wadannan sadakoki.

Zuwa yanzu Ummami ta gama fahimtar Amani irin masu zafin kishin nan ne na balaI, duk irin bayanin da zaka yi musu akan kishiya agidan sarauta bazasu fahimta ba, kuma akan kishi kusan rasa tunanin su da hankalin su suke yi, sai ta ce to shikenan Amani, zan gayawa Mai sakon ki, na zaki iya ma mijin ki abinda mata hudu zasu iya, kin yarda?

Kunya ta kama Amani, ta rufe ido ta ce haba Ummami, ta yaya zaki gaya masa hakan? Ai rokon sa kawai zaki yi yayi min alfarma ya bar su, ki ce ya duba ya gani ban dade tare da Ya Mukhy cikin kwanciyar hankali ba sai yau, kuma shikenan sai a bashi yammata zabga-zabga har biyu, ni to meye amfani na? Sai ta saka kuka tana cewa, wallahi Ummami duk abinda nayi masa a baya na tuba, sharrin shaidan ne da rashin tarbiyyar UWA, ban taba sanin dan uwa na bane, ban taba sanin mutum na da darajar da babu halittar da ke da darajar sa ba sai a kan Ya Mukhy, ji nake in aka bashi sadakokin nan zan mutu Ummami!

Ummami ta ga abun na Amani azimun ne, babu Sarki sai Allah, sai ta ce Amani! Amani saurare ni.

Kullum ki tuna Moukhtar da kike aure Sarki ne, dan Sarki kuma jikan sarki mai jiran sarautar garin su, don haka in kina son zaman lafiya da zuciyar ki ki cire maganar son rayuwa da shi ke kadai daga ran ki, haka suke, haka Allah ya halicce su, haka kuma suka gada daga iyaye da kakannin su (polygamy).

Makami daya zaki rike ya fishsheki a kan su; ke dai kiyi kokarin zama ta kwarai ga mijin ki wadda sauran mata bazasu iya shan gaban ta ba wajen kyawun hali da nagarta da iya tafiyar da shi a shimfida. Kin ganni nan ni Aisata kishiyoyi sun fi 20 na gani a gidan nan, wannan ta shigo wannan ta fita amma ni din dai kin ganni har yau zama daram!

Maina uban shi ba zai kyale shi cikin kewar mace ba, alhalin ya san dan sa ne mai irin halittar sa.

Kunya kuma ta zo ta lullube ta, ta ce Ummami ke mace ce yar uwa ta zaki fahimce ni, ban iyawa, wallahi ban iyawa. Ta mike tana kuka wurjanjan.

Ummami ta janyo hannun ta ta maida ta zaune, tace shanye romon nan ki cinye zabuwar nan Im not in the mood of eating ta bata amsa a haka zaki daure ki ci, don lafiyar jikin ki ko ba kya so. Haka ta sa ta a gaba da lallashi sai da ta cinye, ta hado mata shayi mai zafi sannan ta ce to ki cire damuwar hakan a ran ki, zan yi magana da Mai, shima kuma har yanzu ba wai ya bayar da amsa bane, na san so yake ya tabbatar da daidaitawar ku da canzawar ki don yana korafin kina masa rashin kunya Amani.

Ta kara zama abun tausayi ta ce da Ummami Wallahi Ummami daga yau na tuba! Na tuba na bi Allah na bishi, mun daidaita na bashi hakuri ta sake share hawaye ta ce ai yanzu na yi hankali, ko makaho ya shafa ya san wannan ba Tafisu ba ce, Bata-kai su ba ce.

Ummami couldnt control her laughter, ta yi dariya ta ce shikenan zauna in baki abubuwan da ba sai kin tsaya kina masa wannan zubar da ajin ba, a kan kada ya karbi sadakoki, ki ci ki shanye kawai, ki zama kullum a jiraye da karbar bukatun sa duk yawan su, babu jimawa zaki saba, kada ki kara zubar da kimar ki akan zancen sadaka.

Da haka Ummami ta samu ta lallashe ta ta kuma daddaka mata tsumin Damagaram, da kayan gyara nasu na hakika, sannan ta ce ta koma gidan ta ta kwanta ta samu barci, kada ta haukata kan ta a kan namiji.

Da kyar ta iya komawa sassan ta. ta hana su Tahira zuwa inda take. Ta kwanta a main bedroom nata bayan dawowar ta daga sassan Ummami, amma barcin da Ummami ta ce ta yi don samun nutsuwa ya gagare ta har yanzu, hakika babu tashin hankalin da yafi kishiya a gurin diya mace, gata ita nata bama daya ba biyu a lokaci guda, Mukhtar gari banza ma cike yake da kasaita da izza balle ya mallaki wasu matan bayan ita, ai ita tata ta kare kenan.

Tana ta wannan kukan Baba Sahura ta shigo, Ummami ce ta ce ta je ta zauna da ita har sai Maina ya dawo, tunda bata jin dadi, Baba Sahura na shigowa ta hau tattare dakin da aka hargitsa, ta shiga toilet don ta wanke mata bayin, tayi kamar bata san me take ciki ba, don Ummami ta hana bayi shiga dakin barcin su.

Nan Sahura ta ga zanin gadon a dukunkune cikin kwandon kayan wanki, ta dauka tace bari ta wanke, gulma irin ta Baba Sahura ta ce bari dai ta bude ta samu abun tsokanar Tafisu. Ai kuwa nan ta ci karo da aikin Mukhy. Ta mayar ta dukunkune zanin gadon a hannun ta fito ta tsaya a kan Amani da ke kuka, ta ce.

Uwa, Uwa ashe yau an kashe Boss? Haka da wurwuri?

Daga kwance ta karyo ido ta dube ta don bata fahimci me take nufi ba, ta san dai in Baba Sahura ta gane me take ciki yau ta shiga uku!

Wato shine Ran shi ya dade ya bani a kudundune? Yo ai ni na dauka ciwon tafiyar Alhaji kike yi da ya ce wai ba kya jin dadi, ashe-ashe! To ni kam wace jinya zan yi banda in tambaye ki ya aka yi haka? Kika bada kai daga shigowa daki?

Ai ni na dauka gudun aure zaki dinga yi kullum dare zuwa gun Mowa, irin yadda ake yi a zamanin mu in baa son mijin, irin dai yadda ba kya son Maina, na dauka har sai ya gaji ya daure ki jikin karfen gado Kawai kuma sai in ga kwana daya da zuwa an kar Boss? Kuma da Mukhtar din da ba so ake ba, ake wulakantawa?

Amani kamar ta rusa ihu da wannan habaici na Babar ta Sahura, amma bata yi ihun ba. Tsaki tayi, tayi banza da Sahura, ta juya kai ta cigaba da kwanciya.

Sahura ta hau latsa wayar ta tana cewa ai dole Yaya ya bani goron albishir, har Jalan ba zaa bari a baya ba.

Nan kuwa ta kira Mamma Jalan ta ce Jalan, kunnen ki nawa? Kunne na biyu kara biyu ki sha labari Mamma na dariya ta ce na kara takwas ma sun zama goma Yawwa to yau dai su Uwa an kai munzali, yanzu zan wanke zanin gadon nan, ke baki gan ta ba abun tausayi duk bakin rashin kunya ya mutu!

Mamma ta kashe wayar ta tana cewa Sahura-Sahura ban san yaushe zaki girma ba.

A lokacin Haj Jalan ta fadi ta yi wa Ubangiji sujjadar godiya, ta yarda sa idon iyaye yana taimakawa tarbiyar yara ne kawai, amma kiyayewa tana wajen Ubangiji, a yadda Amani ta taso, wa zai mata wannan kyakkyawan zaton? Har digirin zamani ta yi.

Surutun Sahura ciwon kai yake kara mata, sai ta ce don Allah don Annabi Baba Sahura na yafe jinyar taki ki je, ni lafiya ta kalau ba abinda ya same ni. Sahura ta kara babbakaro dariya sannan ta ce oho dai, mun ga karshen rashin kunyar Tafisu, da karshen rashin So, kwana daya da zuwa an mannewa bawan Allah an tsotse shi tas!.

Sai kuka ya kwacewa Amani, ga damuwar dake ran ta ga bakin cikin da Baba Sahura ke kumsa mata.

Ba wata jinya data wuni yi mata sai shakiyanci, da yamma Ummami ta zo ta gan ta a zaune tana shan madarar rakumi data bata, ta daina kukan amma bata yi wata kwalliya ba don haushin Mukhtar take ji sosai.

Ummami ta dan zauna suka yi hira da Baba Sahura sannan ta koma sassan ta.

Da Mukhy ya dawo daga Dosso gun Ummami ya fara zuwa, yace yana son zai sha tea, ta ce ka je wajen matar ka ta baka mana? Yace Ummami pls, ai na san da ita na ce ki bani din, kada in soma ce mata ina son wani abu, ta ji dadin yi min zancen Sadaka Ummami ta ce to bazan bayar ba, sadaka kuma zan roki Mai kada a baka yanzu, yar mutane na neman zarewa.

Yar dariya Mukhy ya yi, ya tashi zai fita, a ran sa ya ce Umh, Ummami bata san Amani ba ne shiyasa take tausaya mata, ai shi kam wannan Sadaka ko baa bashi ba, ya gode da tayin su da aka yi masa, ko babu komai sun sa jiya ya more iya morewa. Yanzu ma da barazanar su zai ci gaba da samun kan Amani ya cigaba da yin yadda yake so, lokacin sa ne.

Itama sanda take gaban iyayen ta tana kan tsinin ta na Tafisu wane rashin mutunci ne bata tata masa ba? Ai shi nashi nafila ne, tunda bai hadawa da cin zarafi kuma bai taba alaqanta ta da kama da shegu ba wai don tana da kyau, wannan magana ta dade tana haunting din sa duk da cewa in kyau ne ai sai dai su yi kunnen doki shi da ita. Haske kawai ya fi ta.

Ya isa sassan su yana wannan tunanin, ya isa har falon sa yana waya da Kamilu, wanda ya gaya masa su Alhaji sun sauka gida lafiya, yau ga Alhaji a kujerar ofishin sa ta FASKARI INVESTMET (Executive Director) wato Alhaji ya koma office yana dan dogara sanda amma, farin ciki mai tsanani ya kama Mukhy, ya ce da Kamilu duk da haka kada ya dinga barin sa yana ayyuka masu yawa, ya san halin Alhaji sarai, wajen neman kobo. Jin shigowar sa yasa Sahura yi mata sallama, ta ce to Uwa zan je na kwanta, maigida ya dawo ko kula ta bata yi ba don akaifa take ragewa da nail-cut a lokacin.

Har dakin ya shigo bayan sun gaisa da`Baba Sahura da ke fita, sannan ya kashe wayar sa ya saka a aljihun sa.

Ta daga kai a hankali ta dube shi, sai annuri, cikar zati da kwarjinin mulki ke fita daga fuskar sa maabociyar zati da kamala, ya ji dadin labarin da Kamilu ya bashi na samun lafiyar Alhaji da komawar sa office, Mukhy ya sha rawanin sa fari kal, ya fito a cikakken Diffa-Arab din sa, ya tsaya daga kan ta yana warware rawanin, ya ce,

Sweetheart, na dawo me zan samu Maam Amani? Bata yi magana ba, ta cigaba da cutting farcen ta kwarjinin sa da kamshin turaren sa duk sun cika ido da hancin ta, sai ta tuna ta yi alkawarin zama macen kwarai, macen kwarai kuwa tana yi wa miji sannu da zuwa da adawo lafiya. A hankali ta daga sexy eyes din ta ta zube su a kan shi, ta ce,

sannu da zuwa Ya Mukhy.

Ta mike tana cewa bari in taya ka cire rawanin nan, na ga alama tsayi gare shi, ta shiga taya shi warware rawanin, sai ya ruko kwibin ta, ya rike ta cikin hannayen sa ya dube ta da idanun Rahma har cikin ido. Duk kin rame, a abinda bai fi sati guda ba kacal, me yake damun ki haka Tafisu?

Mai neman kuka an jefe shi da kashin awaki sai ta saki kukan dake cin ran ta a hankali, a sukwane ta fada jikin sa. Mukhy ya samu yadda yake so domin ta rike shi gam tana rawar jiki, tana fadin yau a gaban ka zan tube, ka kalle ni da kyau ka gani ba abinda bani da shi da sauran mata ke da shi, watakila nawa ma ya fi nasu cika, idan nayi hakan zaka fasa karbar sadaka?



Mukhy me zai yi banda fashewa da dariya, ya ce By Allah you will be the death of me Amani..





Ya soma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login