Showing 3001 words to 6000 words out of 19522 words

Chapter 2 - Binta Yar Jagaliya Book 2 Hausa Novel Complete

muciya ta buga mata a gadon baya tace


"In tazo ta ga saƙona kafin ni in dawo ,


Wayyo Allah maƙota ku temaka min ku temaka min


Wata uwar dariya Binta ta saki tace


"Karo dani ba dadi yasin idona idon rufaida sai na mata abin da har ta mutu baza manta dani ba,


Tana durƙushe tace


"Ai kida ganin rufaida sai a lahira domin yanzu nasan ta isa inda takai ,


Ganin kamar bata ji a jikin taba yasa ta ƙara dauƙar taɓarya ta dai daici ƙafafunta ta maka mata


Ƙara taƙwallah nan maƙotanta suka shigo cikin makirci Binta tace


"Mama lafiya me ya sameki?,


Jikin moƙotanta ne ya yayi sanyi Domin su ba susan abin da take nufi ba sunde ganta a kwance maga shiyan wata daga ciki ce tace babar rufaida lafiya


ƙarar huya ta saki tace


"Wannan can wallahi ita ta naɗan duka ,


Zaro ido Binta tayi ta share hawaye tace


"Na shiga ukku rashin lafiyar take har ta kai haka yanzun nan rufaida ta kirani tace jikin mamanta ba lafiya ciwon hauka ke damunta inzo ita tayi tafiya,


Salati suka saki tuni wajan aka fara jimami


Wallahi ƙarya take lafiya ta qalau



Matsawa Binta tayi irin tana tsoron Hadiza tace


"A kira mazan waje su ɗaure ta tun kafin ta fara duka ,


A guje ta yo Kan binta ai kuwa ta fita nan mutane suka yarda da maganar Binta gudu take da ƙƴar a ka sami wanda zai ɗaure ta ajikin bishiyar lahinsu


Hadiza kuka take tana cewa


"Wallahi ina da hankali Binta kin cika me maƙirci ,


Ba wanda ya kula ta


Wannan kenan


Hajiyan taura Alhaji mansur sai mabiyin sa mahaifin Ramlah Alhaji Nura sai Hajiya kubura mahaifiyar haseena tuni ƴa'ƴa da jikoki suka hallah a taron muzabfar Alhaji mu'azzam da azzam da sauran yan family ɗin Alhaji mu'azzam ya fara buɗe taro da addu'a yace


"Ina me bawa Kowa haƙuri wani dan gajeren al'amari da ya faru a yau juma'a na ɗaurawa mu'azzam Bilal mu'azzam kura aure kuyi haƙuri sakama ƙon rashin sanar da ku muma ya zomana ɓakatatan ne ba zato sai dai ku mai addu'a Allah ya basu zaman lafiya bana son wani gutsiri tsoma a yau amaryarsa zata tare ,


Nan ran Alhaji Nura ya ɓaci kowa yasan Ramlah na mutuwar son azzam Amma saboda wariyar launin fata an zagaye an mai aure tuni mahaifiyar haseena ta ɓata fuska dan anga mahaifiyar su ta mutu shi yasa baffa ke yin abinda ya ga dama ai bata sunƙe da lamarin nasa ba sai taji yace


"Duk wani jika da yake gidan nan to dole ne nan da wata biyu bayan anyi zaɓe kowa hankalin sa ya kwanta su fitar da miji su aure barin Ramlah da haseena na gaji da yawon su kai Muhsin Ramadan wallahi ku kiyaye ni na baku wasu watan Ni inga kun fito da matar aure,


Ran Hajiya kairiyyah ne ya ɓaci tace


"Tun da anyiwa ɗan gold aure ai dole ka tarkata kan ƴa'ƴa da jikoki ka ce su fitar da miji ,


Wani banzan kallo yayi mata yace


"Hajiya kairiyyah ki iya kalaman ki in ba haka ba zaki dana sani,


Murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo ta fita daga ɗakin taro yace


Kowa zai iya tafiya nan kowa ya fita jiki a sanyaye jidda kuwa tana zuwa ɗakin ta ta saka kuka yau wanda take so zai tare da wata matar ba ita ba


Wannan kenan


Azzam wa zai ɗauko wacce yarinyar naso insa a ɗauko ta saidai yanzu ance ta dena zuwa club kaga da abin yayi mana sauƙi ko ba idon mutane a lokacin


Gaban sa ya waɗi domin shi ya manta da zancan binta yace


"Malam Musa zai tsaya abayan gidan su inta fito shi da su Joseph sai su rutsata ta shiga Mota sai a shaƙa mata Powder a Kai ta gidana dake laimon kafin musan yarda za ai bayan an gama zaɓe ,


A jiyar zuciya yayi yace


"To Allah ya temake mu,


Ameen yace ya tashi ya nufi shashin muzabfar a bakin gate ya haɗu da shi yace


"Dan halak yanzu gunka zani fa ,


Ai gani nan na zo ko


Hakane ango

Harara ya watsai mai yace


Wallahi ka kiyaye Ni kasan ko a makaranta ni ke naɗa maka duka yanzu ƙuruciya zata tashi fa


Dariya yayi yace


"Ai mun girma tunda kai aure Ni ina da baby mushi ga ciki,


Banza yayi mai suka shi ga aguje mufeeda ta tawo gun sa tace


"Uncle azzam congratulations 🎉 ,


Daga yarinyar sama yayi sosai ta shiga dariya tace


Uncle yaushe zaka kaini gun antyna

Cikin sauri ya dubi Mubaraka


Ƙasa tayi da idonta tace


"Sannu da zuwa Allah ya sanya alkhairi,


Ameen ya ce


Ya sami gu ya zauna ya ɗora mufeeda a cinyar sa zance yarinyar ta shiga yi mai yayin da Mubaraka ta ɗauko lemo da ruwa ta ƙawo mai da gashashshan nama ta ɗora a kan Center table ta bar gun

Muzabfar yace


"Babyn jike gun momin ki ki zauna ki ƙƴale uncle ɗinki ya ci abinci,


"To daddy ta bar gun ,
Wanna kenan

*CI GABAN BINTA YAR JAGALIYA*

Jifan gafiyar ɓedu

*Ba tsuntsu ba tsarki*


By


Oum Yasmeen


Na kammalah book 2 ki ɗaure ki mallaki naki opay bank

8141785374

AMINA ALHASAN MUHAMMAD ki toro shidarki ta wannan number 09061890481


Ban hanaki karanta littafi na ba amma kinsan Allah baya yafe hakkin wani a kan wani typing a kwai huya ki daure ki mallaki naki ba kuɗi mai yawa 300 kacal


Ki yiwa Allah da Manzonsa ƙarki karantan littafina in kinsa baki siya ba sai kujera sai an gama littafi ku dinga ƙaramar murya a temaka a baku

Ki karanta halalinki








Dan Allah duk wacce ta siya ta ruƙe amana ƙarta fitarmin da book ɗina

https://chat.whatsapp.com/Fu2P8PebrYYAXRI3z0vvXh




Ƙafafuwan ta fututu ta dawo hanyar gida domin har gidan gwamnati taje ga wata irin yar gajiya da ta kwaso ta dawo da alƙawari kala kala da gwamna yayi mata indai har ya sami shugaban kasa kaso cas'sa'in na cikin damuwar kuɗin ta ya rago domin tasan zata sami ninƙinsu unguwar tayi shiru baka jin motsin komai kowa ya tafi ya kwanta ga wani irin duhu da garin yayi alamace da ke nuna damuna ta shigo daman yau anyi zafi ga rana bishiyoyi sai lumshi suke suna bada wata iriyar iska tsiƙar jikin ta har tashi take saboda irin sanyin da take ji hasƙen farin wata sai kaɗan sauri ta ƙara dan ta lura ruwa yana gab da kecewa wata baƙar mota ce ta sha gaban ta ƙaucewa tayi ta ci gaba da tafiya ta ruƙe jaƙarta da kyau ji tayi yinwar da take ji babu ita ta ɗaga ƙafafuwanta ta fara sauri ji tayi an saka mata ƙarfe a bayan ta tana kyautata zaton bindiga ce aikuwa ilai ita ce ɗaga ƙafafuwan ta tayi zata zuba gudu nan yace


"Ƙina ƙara motsi sai na fasa ƙwaƙwalwar ki da alburushi ,


Jikin tane ya hau mazari ta ɗaga hannu wanta sama ashe bashi kaɗai bane zaratan sojojine majiya ƙarfi su shidda sun zaga yeta ɗayan yace


"In kina son ki da lafiya shiga cikin mota ,


Ba yarda ta iya bakinta ya mutu bata da wani sauran zaɓi da ya huce ta bishisu gidan baya suka buɗe mata ta shiga inda mutum biyu suka sata atsakiya ga wasu irin shigun bindugu a hannun su sauran suka shiga gaba sai wani tsoho driver ba damar ihu domin duk ihun da za tayi ba me jinta wasu zafafan hawaye ne suka shiga zubo mata yawa ansaki fanfo wani abu ɗayan ya ɗauko ya fesa mata bata ƙara sanin inda kanta yake ba baƙin hanya suka tsaya wata mota ci ta tsaya fara ƙal da ita wani matashine me jini a jika yana sanye da farar t-shirt da jeans baƙi ga hula p-cap yasa ya sa face mark ba zaka iya gane ko wane ba ga baki ɗayan su suka fito suna sara mai amsar key ɗin motar yayi ya basu nasa ya buɗe ya shiga a guje driver ya ja ya bar gun su kuma suka shiga cikin farar motar suka bar dajin

Ƙarfe 7:38 na safiya


Idon ta wani irin nauyi yayi da ƙƴar take ɓuɗe shi za bura tayi ta yaye lallausan bargon da aka lunluɓeta kallon ɗakin ta shiga yi anya kuwa duk abin da ya faru ba mafarki take ba murza idonta tayi ƙara ta ƙwallah ta tashi da sauri ta sauka daga luxury bed ɗin komai na ɗakin farine harta laburayan fararene iska sai ƙada su take ga ɗan hasƙen da ya shigo ta taga cikin sauri ta nufi ƙofa jinta tayi gam a rufe nufar taga tayi ta leƙa



Ware manyan idanuwanta tayi wasu irin gine gine ta gani masu kyau da tsari ga jami'an tsaro sai zurga zurga suke a gidan saƙin labulan tayi ta shiga raira kuka me ban tausayi tambas tasan Ubangiji ne ya kamata domin baya barin hakkin wani a jikin wani ko da gine ginan da ta gani ta shaida ba a ƙasar nan take ba ko tana babban birnin kura wato laimon tashi tayi ta shiga bugu ƙofar ba kakƙautawa bata san an buɗe kofar ba ta cigaba da bugu bata ankara ba ta jita kane kane a jikin mutum a razane ta ja da baya manyan idanuwanta ta buɗe gabanta ya yanke ya waɗi ganin wake gabanta yana sanye da wando three quarter ba riga ga wani irin yalwatatcan gashi a kwance a faffaɗan kirjinsa jikin sa duk a mulɗe yawa dan danbe fatar sa har ɗaukan ido take saboda hasƙenta ga ƙananun gargasa lub lub ra ƙuɓewa tayi jikin ta ya saɓi rawa wani irin shock ta shiga bata taɓa ganin namiji a haka ba kuma irin wannan maji ƙarfi iya dana sani yau ta shege ta ƙara haɗa fuska yayi sexy eyes ɗin sa ya ware su tar a kanta kafuwanta ya duba wanda sukai fututu ya dubi zanin gadon sa duk yayi ɗauɗa yace


"Ke wacce irin wawuya ce wacce bata san ciwon ƙanta ba ina ƙwanci ina damuna jibi ƙafafun ki to wallahi sai kin wanke min zani kuma da hannu ba da washing machine ba,



Kuka ta saki ta ɗurƙusa ta haɗa hannu biyu tace


"Dan girman Allah ka mai dani gida kai haƙuri wallahi ni ba yar iska bace ƙar ka cuce rayuwa ta wallahi nayi nadamar a bin da nayi maka tun ba yau ba wallahi bazan iya wanke wannan blanket ɗin ba,


Dariya ya saki har sherarrun haƙuransa farare tas suka bayyana

Shagala tayi tana kallon sa saboda wani irin kyau da yayi

Lura da irin kallon da take mai ya haɗe rai yace


"Keee mayyar maza ya zaki sa duda abin da keke so shi zan baki a sanga batare da kin biyani ba ko kin sha wahalar zuwa club kuma wallahi tun huri ki ɗauki wannan bargon ki wanke min ƙaaaazaaama ya ja ƙarshan ,


Dan Allah kai haƙuri ka mai dani inda ka dauko ni



wata loca ya buɗe ya ciro wasu miƙakƙun kudi yan dubu dubu ya watsa mata yace


"Ga sadaƙin ki auran ki nayi ,


Ihu ta zunduma ta zube a ƙasa tana kuka tace


"Wallahi ƙarya kake ,



Ta kuwa ya fara har inda take ganin ya kusan cin mata idanuwansa sunyi wani irin ja haka fusƙarsa


A gi gice ta tashi ta fara ja da baya yana bin ta har ta kai bango bata da hanya guduwa saboda ƙawanyar da yayi mata da hannayansa ko wannan su yana iya jiyo numfashin ɗan uwansa yace .........✍🏻

"Ki iya kalaman ki ƙar kisani inyi abin da ban niya ba ki tattara kuɗin nan tun kafin ranki ya ɓaci wankin da nace kiyi ƙar kiyi ki bari indawo in same ki baki yi ba ,


Wani marayan kuka ta saki tace


"Ina jaka ta ɗan Allah ka sakeni in tafiya ta?,

Har yaje bakin ƙofa ya tsaya cak yace


"Zo ki murɗeni ki kwata ki saranki kin shigo gidan nan kenan zama daram,


zaman da ɓaro tayi a bakin gado ta gumi tayi ta rasa ta ƙameme tunanin da zatayi duniyar ta yi mata zafi jin alamu ƙarar kofa da sauri ta tashi mulɗewa tayi taji abuɗe yawa ba wayayyiba sosai ta shagala da kallon floor an kashe dukiya wajan tsara shi floor biyu ne a haɗe sai aka raba shi da water bubble partition sai kawo huta yake kala kala ga tamkeƙen pic ɗinsa yawa zai magana a kusa da dining room shida mahaifinsa sun rugume juna suna murmushi jin taku tayi da sauri ta juyo ya sha yadi fari sosai yayi kyau ya fito a babban mutum da kamalal sa ta fito kwar jinin sa ya cika mata ido niya tayi ta cimai mutunci ta zage shi ko zai sake ta amma ina ta kasa yawa yayi mata asiri tayi ƙasa da kai ta baza ta ma iya kallon sa ba ta ja baya ƙwallah ta tarar mata a ido tace


"Dan Allah da Manzon sa ka fitar


hannunsa ya zuba a aljihu cikin deep voice ɗinsa yace


"Ga abinci nan a dining ki ci daga yau na canza wa me min abinci ke zaki ɗin ga yi ba abin da babu a store ƙar kiyi gigin fita daga gidan nan in kuma ƙinƙi gaki ga hanya nan hmmmm ya saki murmushi na gefen baki ya wuce,


Turuss kalaman sa na ƙarshe sun ɗaga mata hankali dafa wata luxury s sofa tayi jiri na ɗi banta tuni numfashin ta yake kai wa da komowa ta tsinemai yafi cikin kwando ganin ba sarki sai Allah yasa ta meke ta nufi dining wasu hadaddun luxury warmers ne yan gidan stainless steel vacuum sai ɗaukar ido suke yawa an haɗa da sirkin gold na farko dambum cuscus yaci kayan lambu da hantar rago ɗanyan ta buɗe farfesun kazane yaci kayan kamshi kadan ta zuba ta buɗe na alemo da lemon kwakwa ne sai na mango juice tissue zara ta goge bakinta ta koma ɗakin da tafito zanin gadon ta ƙalla fasa wankewa tayi ta shiga toilet shagala tayi da kallon sa ta yarda da komai na azzam me kyaune mayukan gyaran jiki ta gani kala kala yawa mace ga wani dugun glass anzube towel set farare tas da su ko wanne da amfaninsa cire duguwar rigar ta tayi cikin bathtub shiga da yake ta gama haɗa komai ruwan sai kamshin turaran wanka yake gamawa tayi ta ɗauki towel me dan girma ta daura iya gwiwa abar busar da kai ta dauko ta busar da kanta ɗaukan rigar ta tayi ta sa a washing machine bayan ya gama wanke wa bata jira ya busar da ita ba ta ɗauka ta shanya zanin gadon ta yaye ta ɗauko wani a cabinet ɗin toilet ta canza tasa wannan a Landry basket curtain ɗin ta ja ta rafe ko ina saboda wata iska da ta taso tuni aka ɗauke huta solama basu kunnata ba wata irin iska ake mehaɗe da walkiya hawa kan gado tayi ta ta kure



Wanna kenan


"Mu'azzam ka kai ta gwajin da nace ka kai ta ?,


Aa yau nayiwa Dr nazeer magana zai zo


Kofin hannuta ta ajjiye tace


"Okay ,


Hajiya ni bara in tafi


Allah ya tare


Ameen ya ce ya fita a main floor ya tarar da su Ramlah yawa an musu mutuwa sunyi jigum jigum suna jin takunsa ko wacce ta zuba mai ido yawa me shirin gano wani abun suna ganin ya ƙaraso kusa da su ko wacce ta ɗauke idonta suka gaisheshi cikin kissa haseena tace


"Yaya zan bika inga anty zarah ,



Ɗagowa yayi ya kalli ta domin shi wallahi ya manta da zancan ta ya manta da yabar mutum a gidan nan yawa ne ciwon baki yace


"Ba yanzu ba ya wuce warsa cikin sauri domin ruwa ya kece yawa da baƙin ƙwarya cikin sauri ya shiga mota malam musa ya jashi suka tafi dake nan kusa da sune nan da nan suka isa sojojin da suke mai gadi suna jin horn ɗinsa suka buɗe da yake duk ruwan da za ai ko iska basa matsawa har gaban bangaren sa aka kaisa ya shiga floor ƙasa ba kowa kai tsaye bene ya hau ya shiga ɗakinsa ya shirya ya fito





floor ƙasa ba kowa kai tsaye bene ya hau ya shiga ɗakinsa ya shirya ya fito



Cikin ƙanan kaya iya kyau yayi kyau yawa wani balarabin Turkiyya wandon jikin sa dark ash t-shirt ɗin baƙa anyi rubutu a jikin ta ansa gallery depth da fari kitchen ya nufa haɗa coffee yayi wanda ya ji kayan ƙamashi sai da ya matsa lemon tsami shidda yafito ko sugar besa ba a kitchen ɗin ya zauna yaja kujera ya fara sha a hankali yawa me koyar cin abinci tashi yayi ya dauko system ɗinsa ya fara duba aikin da akai yau kacokan ya maida hankalinsa kan system ɗin jin ihu yayi da sauri ya tashi ya fito ya nufi ɗakinta murɗawa yayi ya shiga ya ƙunna filar wayar sa yace


"Lafiya ?,


taso wa tayi tamanta da yanayin da take ciki ta rungume shi ta saki kuka so yake ya hanata amma ina ya kasa yawa anruƙeshi nunamai ƙasan ɗakinta take tana kuka wani kumurcin mucijine yana fasa kai yayi ƙasu da sauri ya ɗauketa cak yawa wata yar baby suka fito waya yayi an danan sojojin suka zo suka shiga ɗakin kunyace ta kama shi gani duk ta maƙalƙaleshi Allah yasa ya ƙauce da ita basu ganta ba ganin irin kayan da yake jikinta fita sukai da shi ya dawo floor yace


"Ki sauka tunda kinga sun fita da shi ko ,


Yawa wata yarinya ta shagwaɓe baby face ɗin ta tace


"Uhmm dan Allah ka fitar dani daga nani gidan,


Kafe tayi da sexy eyes ɗinsa shi kansa besan cewa abin da tayi zai mai saurin illah irin haka ba kallon fatar ta yake tana wani sheƙi gata ba fara ba amma tana da wani sirƙin kala me ɗaukar hankali ko dan shi a tsarinsa ba yason farar mace ne owo uwa uba shagwaɓar da tayi ta tafi dashi daƙƴar ya iya buɗar baki yace

"To sauka ƙarki ƙarya ni,

Ƙunya ce ta kamata ta gyara ɗaurin towel ɗin jikin ta tace


"Kayana na wanke ko zaka shiga ka ɗauko min ?,



Girgiza mata kai yayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login