Showing 3001 words to 6000 words out of 33177 words

Chapter 2 - Yan Biyu Ne Book 1 Complete Hausa Novel

Mrs Kd   

03 Feb 2025

256

ce tafaka can gefen titi baka wuluk, su hadiza ne suka fara sauri suna fadin, yar baba ki sauri muwuce kafun su futo su sace mu, wani kallon banza tamusu tace" kukam anyi matsorata aikam kunsa sena tsaya naga su waye zasu fito" nikam inajin tsoro" fatima tafada tana zare ido, "dallah gafaracan matsoraciyar banza " nidai kam tafiya zanyi" hadiza tafada tana kallon A'isha, aikam ba wanda ya isa yatafi sekun tsaya " jin haka yasasu shuru bawacce takara magana acikinsu saboda sunsan hali, wasu manya-manyan mutane ne suka fara fitowa suna dan gudu- gudu, kofa suka bude , kafarsa yafara futowa da ita wacce take fara kal, kana yafuto gabadayansa, dogo ne fari tas dashi yana da dogon hanci, idanunsa sanye da glass baki, sumar kanshi baka kirin se sheki take, sanye yake da kananun kaya ajikinshi, kallon hadiza da fatima tayi tace kowa ya goya jakarsa yashirya gudu, basu mata musuba suka goye jakan kunansu a baya, alamar su tafi tamusu , aikam sukai cigaba da tafiya, seda suka zo kusa da motar ta sheke da dariya harada rike ciki, tana fadin kuga wani me kama da mata tana fada tana dariya takara cewa wannan ai dan daudu ne, su kansu bodyguard din tsayawa sukai suna kallonta, shikam ranshi yabaci sosai, glass din idonsa yacire ya kalle ta sosai, ya tabbatar dashi dai take, gashi shi ba abun yasa adaukomai ita ba mutane agurin afara video, ganin bayadda zeyi yasa shi komawa Mota afusace, ganin ya shiga Mota suma suka shige, seda suka wuce , sannan tadena dariya , kallon su hadiza tayi tace " ku nifa dagaske mutumin nan yabani dariya Allah yana kama da mata" sudai shiru sukai basu ce komai ba, umarnin su tafi tabasu, hanyar gida suka nufa gaba dayansu, baffa ne yafuto daga daki yana fadin" wai ina ja irrar yarinyar nan ta tsaya be"? malam kasan halinta sarai seta gama tsokanarta sannan tadawo gida" aikam idan tayo tsokana aka kawomun kara cazanyi suka mata sumata duka" yafada dai-dai shigowarta, aikam jaraf a kunenta tace " dama nasan ai kaime farin gemu baka sona" ke dan gudanku ina kika tsaya"! makarantar ce fa da nisa nifa nama kusa nadena zuwa" soki keyi ki zauna a gida ki dinga janyo fada ko" inna hafsatu tafada, kallonta yar baba tayi tace" nifa wlh dama nasan bakwa sona , aunty zainab ce da inna babba kawai suke sona" tafada tana shugewa dakin inna nemuna, baffa ne yace , kunjini da ja irrar yarinya to kifuto kiyi wanka yau juma'a mutafi masallaci" labulen dakin tabude tana fadin, " amma zaka bani kudin juma,a ko"? " ni bani da kudi kinasan dai iyayen naki basuzo sun baniba" to ai ko nidai bazanjeba haka kawai naga kawayena sunata siye-siye ni ina kallon su" aikuwa sekinje" baffa yafada , dama sun saba duk ranar juma'a se ya dage setaje masallaci ita kuma tace se yabata kudin juma'a shi kuma yace baze bataba, karshe dai se yabada kudinnan zataje, inna memuna ce tafuto daga daki tana fadin" ah ah yau kuma wacce wainar kuke soyawa kaida jikar taka" kin gansunan tundazu suke yi wai bazata je masallaci ba seya bata kudi" au to ai sun saba ze bata ne" aikuwa yau bazan bata sisi ba" inna memuna ce ta dafa kafadar ta tana cewa" haba yar baba A'isha ta kije kyi wanka kizo nabaki sababbun kayan da aunty zainab ta dinka miki kisaka kutafi masallaci keda baffa ko" wani tsalle ta daka ta dane inna memuna tana cewa" kai shiyasa nake sanki sosai yau zanyi kwalliyar da ban taSa yiba" to shikenan jeki kiyi wanka" tom" bahon wanka tadauka da ruwa aciki tashige bayi, inna hafsatu ce tace" bazaki kashe sanyin ruwan ba ruwanfa yanada sanyi karki mura" ,daga bayin tace " ai inna karama nariga ma nafara wankan" to shikenan ai ganinai keda bakya wanka da ruwan sanyi " , shi dai baffa be kara bi takansuba yashige dakinshi dan ya shirya,
gaba daya ranshi abace yake zuciyarsa kam kamar tafashe, sunayin parking be jira sun bude mai kofa ba yabude yafuce, security din gidan sunata mai sannu da zuwa ko takansu be bi ba, part dinshi yawuce , yana shige yacillar da wayarsa akan bed gaban mirror ya tsaya yana karewa kanshi kallo, magannunta ne sukemai yawo a kunnuwansa, afili ya furta" wai nina ke kama da mata" ya karasa maganar yana yazubo da kwalaben turaren dake kan mirror suka zubo ?asa, gaba daya ya hargitsa bedroom din masu aikin da ke aiki a bangaren ne suka jiyo, daya daga ciki ce tafuta da gudu tanufi part din Momy sa , a garden tasameta tana hutawa cikin hanzari takarasa, "ma ba lafiya a bangaren irfan" cikin harshen turanci take maganar, dasauri matar da aka kira da Ma tamike , "muje " abunda tafada kenan suka nufi part din, suna shiga bedroom dinsa tawuce, tana shiga taga dakin a hargitse shikuma yana zaune bakin gado rike da hannunsa ga jini na zuba, tuni hankalinta ya tashi , matsawa kysa da shi tayi tana fadin"meke damunka haka my son mekayiwa kanka" Momy ki barni kawai" haba my son kalli fa jini a hannunka tashi muje nama treatment" rike shi tayi ya mike suka futa, umarni tabada da a gyara mai bedroom din, zaunar dashi tayi a falour tamai treatment din ciwon, kai kace wani ciwo ne na kuzo mu gani, kanshi ta dafa tace "my son meke damunka"? kallonta yayi yace, " Momy ina kama da mata"? kallonshi tai tace, "meya hadaka da mata kaida kake namiji" Momy tambayarki nayi kibani amsa" no my son baka kama da mata" to amma waye yace maka kana kama da mata"? Momy wata yarinyace tace mun wai ni ina kama da mata wai ni dan daudu ne" kowa ce ita karya take kawai dai kyanka tagani tace kana kama da mata" Momy ban taba jin Sacin rai irin na yauba" sorry my son kadena bata ranka akan wata banza kasanfa banason naganku cikin bacin rai ina shiga danuwa" amma Momy wlh se na dau mataki akan ta" shikenan idan hakan zesa ka huce kadau matakin" yanzu dai kadena fushin nan karkasa nashiga damuwa" ok Momy "


=؞?=؞? YAN BIYU NE =؞?=؞?

Story and writing by Hadizatu
'?
'?

Mrs (KD)

Romantic love story

Yar amanar jajirtattu=ت?=ت?

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
=ت? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*=ت?
'?
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i_.'?
Marubuciyar littafin
SOYAYYA DA IZZA
Ayanzuma nakara kawomuku wani sabon book
dina me suna (YAN BIYU NE)
ku biyoni domin kuji ya labarin ze kasance
karki bari abaki labari my sister

page 5

________________ "Wai bazaki futo mutafi ba "? "kai baffa ganinan kwalliya zan karasa fa" wato kice kinan kina kwalliyar aljanun nan ko"? futowa tayi tana fadin muje nagama inna babba ki kwashemun kayan kwalliyata" kallonta baffa yayi , tasha hoda kamar ne zuwa tashe tayi zizare da bakin kwalli a lebenta tasa jan janbaki, anja kwalli asaman ido, dinkin doguwar rigace ajikinta ta atamfa da mayafinta kalar baki, baffa ne yakalle ta yace " wannan kwalliyar fa ta aljanu " kai baffa kwalliyar tawa ce ta aljanu"? yo ta aljanu ce mana wannan aida dare ne seki tsorotani" baffa ai irin wannan kwalliyar ake yayi , dandai kai tsoho ne shiyasa baka saniba" Inna hafsatu ce tafuto daga dakin girki tana fadin, " wai ku haryanzu baku tafiba kunanan kunata cecekuce" " kemadai kyafada sesun makara tukun sa dawo gida suyi" Inna memuna tafada tana ajiye butar dake hannunta, " aini kwalliyar tace taban tsoro shi yasa natsaya" inzaku dawo kutayomana da salak mu dora kan abincin rana" to semun dawo, ke kuma zamu wuce" tisata gaba yayi suka fuce, "kai jama'a basa gajiya da fada kullum" wlh kuwa ai yarce bataji ,bara nashe na doramana abincu" suna tafe suna fada , wai a lallai baze ri?e mata hannu ba, shikuma yadage sedai ya rike mata hannu karta shige cikin jama'a ta bata, seda suka karasa Masallacin , dardumarsa ya shimfida musu suka zauna, laziminsa yakeyi , itakuma tanata wasa da gashin jikin dardumar, hangoshi tayi acan gaba yana shimfida tashi abun sallar, " lah ga me kama da dandaudu can" afili tayi maganar hakan yasa baffa yajita, " ke waye yake kama da dandaun" kallonshi tayi tace " nifa magana nayiba kaine dai kake ji uwa nayi magana kuma tsufa ne yasa kake jin haka" oho ai na dauka magana kikai" am baffa inje gurin kawayena" kallonta yayi yace"ba inda zaki kijanyomun rigima" shirutai bata kara maganaba, seda akai Sallah aka idar suka kama hanyar gida, tunda suka tafi take ta zubure zumburen baki tana hade rai, baffa natamata hira tayi banza dashi " wai ke mene kike ta fushi" bata kulashiba takara hade rai " haba yar baba yar baffanta mekikeso nasai miki" me kifin dake can nesa dasu ta nuna "to tsaya inbaki ki siyo ko" hannu yasa alajihunsa yafuto da dari uku yabata yace taje ta siyo shi kuma ze sai salak anan, karba tayi ta tafi , tana zuwa tace abata kifi na du tamikamai kudin, seda yasamat a takarda yadamata a bakar leda ta amsa, me gurasa ta hango yana tafiya, " ungo kifinka nafasa siya dama ni gurasa nayi niyyar siya" kallonta yayi yace "aikam baki isaba bazan baki kudiba tunda kin riga kinsiya" nidai banson kifin ungo abunka" mikami tayi ya amsa kudinta ta fuzge daga hannunta dama be ida ajiyesuba ta kwasa dagudu, baffa ne yaganta tanata tika gudu yace, " ke tsaya mana meye kike wa gudu haka"? baffa bakomai me gurasa nagano zan siya" kinfasa siyan kifin"? eh baffa na fasa kwantai ne" yo muje zamu tadda me gurasan a gaba" seda sukai gaba dukaga ne gurasar tsaida shi tayi tasai na dari biyu tarike darin, shikam baffa be masan me takeyiba, seda tagama siya suka wuce gida,
zaune yake a sit din baya wayace kare akunnenshi yanayi, da alama abu me mahimmanci yake tattaunawa, a hankali yake maganar cikin natsuwa, seda yagama wayar yakalli driver din yace, "malam Aminu mu wuce gida saboda lokacin lunch yayi , su Momy kar sui tajirana" "to yallabai angama" daga haka dukai hanyar gida, seda duka shiga cikin gida sukai parking, security dinne suka taso dansu budemai kofa, kofar yabude yana futowa , alamar su koma yamusu, "malam Aminu futo mun da sallaya ta ko" ok yallabai" futonai da sallayar yayi yamikamai amsa yayi yana fadin " malam bara nabaka kudin sadakar almajirannan na ranar juma'a sekaje can cikin gari kayi sadaka ko" "to yallabai Allah yakara arziki Allah yabiya bukatu" ameen ya rabbi" kudin yaciro yabashi rafas fin yan dubu-dubu ne har guda biyu, karba yayi yana kara kwararo addu'a, tafiya yake a nitse bangaren Momyn su yanufa, sallama yayi a falour bakowa , sama yanufa yana isa falour yatarar dasu , Momynsa ce da Irfan azaune afalourn, karasawa, yayi falourn , daya daga cikin kujerun yanema yazauna, "Momy barka da gida" yawwa my son sannu kadawo" eh Momy nadawo" ganin Irfan bemai maganaba yace "yau kuma waya kar zomun naga rai ahade" uhmm wai wata yarinya ce tace mai me kama da mata" dariya yayi har fararen hakoransa suka bayyana, shikam Irfan kara tamke fuska yayi " kai amma fa gaskiya yarinyarnan bata kyautaba to me tagani tace kana kama da mata" haba bro mekwa nake dashi namata dazata ganni tacemun me kama da mata hardafa cewa wai dan daudu" wata dariyar Sawban yayi " au dariyama kakeyimin ko zaka sanine" haba dai nina isa nayi dariya aisedai natayaka bakin ciki tunda nima abun yashafeni, tunda ai kamarmu daya, nima kaga idan taganni zata cemun me kama da mata" ai ka kyaleta kawai zannunamata mace da namiji ba'a taba hadadu koda abakine" to Momy kinjifa bazaki maganaba" to me zance my son nariga nabashi hakuri yaki seya je ya rama" to yanzu dai Momy angama lunch"? bandaniba bara na tambaye su"? wayar dake ajiye kan dining tadauka da alama dan haka aka ajiyeta, kirati ta tambayesu suka ce sun kammla, ajiye wayar tayi takalli Sawban tace "my son sun kammla" ok taso muje muyi lunch kaji my blood" nifa yau banama Sha'war komai" aikam sekaci in ba hakaba mu maka dura" dariya yayi yana mikewa, dining din suka zauna su duka , abinci kam kala kala bawanda babu, kaikace su walima suka hada, abincin sukeci suna raha suna dariya,
suna shiga gida tajiyo muryar babanta aikam dagudu tashiga taje tafada jikinshi tana dariya, baffa ne yace seta karya ka wannan yar" banbareta yayi daga jikinshi yana cewa zauna mana yar baba karki karasani" zama tayi tana bude ledar dake gefen baban nata, takalma ne kafa biyu se hijabi da mayafi baba wannan nawane "? "eh nakine yar baba sunmiki kyau'? "eh baba yayai kyau sosai" "baffa kaga kayana baba yasiyomun" kai yayi kyau" gurisu Inna kunga kyana "kai sunyi kayau maza kije ki ajiye su ko" "baffa ina yini"lafiya lau ya hanya" lafiya lau baffa ya muka sameku" muna lafiya" baffa ai na dauka du Salisu da Zainab sun karaso" ah ah basu karasoba watakila suna hanya dai" to Allah yakawosu lafiya" ameen

=؞?=؞? YAN BIYU NE =؞?=؞?

Story and writing by Hadizatu
'?
'?

Mrs (KD)

Romantic love story

Yar amanar jajirtattu=ت?=ت?

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
=ت? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*=ت?
'?
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i_.'?
Marubuciyar littafin
SOYAYYA DA IZZA
Ayanzuma nakara kawomuku wani sabon book
dina me suna (YAN BIYU NE)
??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ku biyoni domin kuji ya labarin ze kasance
karki bari abaki labari my sister

page 6

__________________ Duk ranar juma'a sukanzo gida gaba dayansu har yar autarsu Zainab itama a garin kano tayi auren, shikam mahaifin A'isha yanzu tafiyar da yakeyi harta kwana , tunda bashida aure yanzu garuruwa daban-daban yake zuwa irinsu , ilori, patogurt, nasarawa lafiya, akure enugu, da dai sauransu, dan haka baya zama sedai idan Friday tayi yakan zo gida aci abinci tare, yauma hakanne tafaru dukaninsu duk sunzo , anata hira ana raha, baffa ne yakalli baban A'isha yace " Umaru yakamata fa kadawo mutum" baffa mutum kuma"? kwarai kuwa mutum" ina nufin yakamata kayi aure kaga bazakayi tazama haka ba duk mutumin da bashi da aure ai ba mutum bane" kwarai kuwa yaya nima inaso nama maganar amma, yakamata yaya kayi aure wlh" to nidai baffa yanzu ni ko sha'awar aure banayi , bazan iya zama da kowacce mace ba yanzu , saboda bazan taba samun kamar A'isha ba" muma munsan bazaka taba samun mace kamar aisha ba" amma yaya ga yar gidan gwaggo dije nan yar kanwar inna baba" hakane kam Zainab nima na yaba da hankalinta" nidai abba inde kun tabbata bata da matsala to na yarda" bata da wata matsala kawai kaje kanemeta" acewar inna hafsatu Mahaifiyarsa" nikam ina da wata magana" inna memuna ce tafada, kowa kallonta yayi , baffa ne yace "to munajinki" yawwa ni ina ganin lokaci yayi da za'a nemi yan uwan marigayiya" kwarai kuwa dole anemi yan uwanta kodan A'isha datake kara girma kullum kada azo lokacin da zata fara tambaya kuma ba amsa" wannan gaskiya ne yakamata a nemo danginta, insha allah baffa koda acikin harkan tafiya- tafiye nane zan bincika" yawwa to hakanma yayi Allah yabamu sa'a" bara nakawo abinci" inna karama tafada tana mikewa, abinci takawo musu gabadaya tahada musu da Umar da Salisu harda Zainab tahadamusu su uku, itama tazuba musu itada inna baba, shi kuma baffa shikadai, A'isha kam ita kadai aka zuba mata tanaci tana musu Surutu sunata dariya, Salisu ne yakalle ta yace "yar baba amma dai kina zuwa makarantar ko" eh kawu ina zuwa" yawwa kinga idan kina zuwa makaranta kullum zanmiki kyauta me kyau" tom kawu insha Allah zan dinga tafiya kullum inna karama kidinga tashina da asuba" inna karama ce tace "sekace tashi zakiyi" Allah zantashi" to nikuma indai kika dena tsokana nima zankawo miki kyauta" tom baba Allah nadena" to nima baza'a barni abayaba nima zan miki kyauta idan kika dena tsayawa wasa idan aka taso makaranta boko da islamiyya kidena tsayawa ko ina , kifara dawowa gida su baffa susan kin dawo seki futa wasan" tom aikwam duka nadena" to Allah yasa kidena" baffa yafada. baffa Allah zandena" to ai shikenan" yau kwata-kwata yar baba bata futa wasaba saboda yau tana jikin iyayenta. se karfe 7:00 dukansu suka watse, kowa yatafi, aisha ce taje gurin baffa tana cewa "baffa nifa zan futa dandali" a wannan tsohon daren babu inda zaki" baffa dare fa beyiba kofa isha ba aiba" babu inda zaki nace" kuka ta tafi tanayi, dakin Inna babba tashige, tana kuka, "ah ah yar baba meke damunki kike kuka" baffa ne yace bazanje dandali ba" to ai kinga dare ki hakura kuma kinmanta abunda iyayenki suka cemiki" karkuma kiyi rashin ji suce sun fasa" to shikenan Inna babba nafasa zuwa" amma Allah yasa kar baffa yafadamusu" ai baze fadamusuba amma kuwa idan kika sake ze fadamusu" bazan ma sakeba " to shikenan kwanta ki bacci" tom" kwanciyar tayi daga haka bacci yadauketa,
maza da mata ne a cakude, kowacce acikin matan dakalar shigar datai, amma sedai gaba dayansu ba shigar daza'a ace kwara ita, Irfan na hango a kan kujera ga kwalaben giya kan teburin gabansa, mata da maza ne suka zagayeshi, shikam ya harde yana kallon kowa dai-dai , yana shan giyar dake cup din hannunsa, kida kam se tashi yakeyi masu rawa nayi masu kallo nayi, a takaice dai club ne, alamar kira yayima wani dake kusa dashi da hannu,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login