Showing 12001 words to 15000 words out of 33177 words

Chapter 5 - Yan Biyu Ne Book 1 Complete Hausa Novel

Mrs Kd   

03 Feb 2025

258

dakai muna rokon alfarma idan nayi labarai yanzu zansa cikiyarta," numfasawa yayi kana yace "kasaka ai taimako ne" "yawwa mungode Allah yakara girma, se alfarma ta biyu," "inajinka" "yallabai dan Allah inasan a sanar da duk wanda zeyi wani program daya sa cikiyarta" "ok ai ba matsala, yasunanta"? "A'isha" gabansane yafadi, wanda shikansa be san dalili ba "ok kaje kafara kuma ka sanar da sauran ma aikatan dasu sa cikiyar yarinyar "tom yallabai" daga haka yatashi yafuce, haka kawai yaji lamarin yabashi tausayi, haryana tunanin, koya family din yarinyar suke yanzu, ko ya idan bega Irfan ba bayajin dadi duk da rashin jituwa tsakaninsu seya daga waya yakirashi' jiyayi gaba daya jikinsa yamutu hakanne yasa yazauna a gidan rediyon bejena talabijin ba,
yana zaune a falour shida Momy, dan yace yau bazeje ko inaba se yamma, wayarsa yadauka yadanna kiran Joseph, umarni yabashi daya kaiwa yarinyar nan lunch, kuma yafada mai daga yau base ya kara fadamai ba yadinga kaimata abincinci akan lokaci, bayan yagama yakashe wayar, kallonshi Momy tayi tace "my son waza a kaiwa abinci kuma" "Momy wata yarinyace " to meye hadinka da ita"Momy kanwar abokina ce" baki tabude zata kara jefomai wata tambayar yace "Momy Please tambayar ta isa haka" daga haka tai shiru tacigaba da danna wayarta.
su Inna ne zaune a tsakar gida sun tisa rediyo a gaba, suna jiran suji anyi cikiya, aikam ana idar da shirin da akeyi aka sako cikiyar, Inna babba ce tace, "ya Allah kasa mudace Allah ka bayyana mana ita" ammeen " Inna karama ta amsa, su Umaru ne da baffa da Salisu suka shigo, tambayarsu suka fara ya ake ciki, Umaru ne yace "yatafi munkaisa guraren datake zuwa harda makarnatarsu, kuma yayi tambayoyi sosai, amma sedai babu abun zargin" inlillahi wa ina ilaihi rajiun ya Allah kai ka jarabemu dawannan hali damuke ciki ya Allah kafutar damu ka bayyana ta" ammeen suka amsa su duka.
karfe 6:30 yayi wanka yashirya cikin kananun kaya, bakaramin kyau yayi ba, futowa yayi yatarar da Momy a falour a zaune anamata tausar yan yatsun kafarta, "Momy nafuta" to seka dawo" daga haka yafuce, mota aka bude mai yashiga "club zamu wuce" angama yallabai" daga haka suka dauki hanya, yana isa gurin, kowa hankalinsa ya dawo kanshi, abokansa duk suka nufosa, gurin zama suka kaishi yazauna, kana suma suka zauna, kwalaben giya aka ajiye musu kan table, Sabeer ne yadau daya yabude ya tsiyaya a cup glass, yamikama Irfan, hannu yadagamai alamar baya bukata "kai mutumina yaukuma bazakasha ba" no yau bansan shan giya " wata budurwa ce tazo tazauna gefensa, "beb Irfan dan Allah yau kayarda mukasance tare" tayi maganar tana shafa kirjinshi ,hannunta yadauke yana fadin "ok esha ya isa naji" mikewa yayi yacewa abokansa "guys nifa zan wuce gida" ok to shikenan semun hade" daga haka yafuce itakuma tabishi abaya se bodyguard dake gefen hannayansa, mota suka bude musu suka shiga, suka ja mota suka fuce daga gurin, "gidana zamu wuce"angama yallabai" juya sitiyarin motar yayi suka nufi inda yafada, kwanciya esha tayi kan kirjinsa tana shafa libs dinsa wadanda suka kasance pink colour, ganin haka yasashi daukan remote ya danna, take ya raba tsakinsu dasu Joseph yazamana basa ganinsu, hade bakinsu yayi yana tsotsarta itama tana kama harshensa tana tsotsa, hannunsa yasa cikin rigarta yana shafa brest dinta yana matsa su, ahaka sukaji anyi parking, sakinta yayi yana kara danna remote din, take suka bayyana, zagayowa sukai suka bude musu motar, futowa sukai, suka wuce ciki, lambobi yadanna kana kofar tabude, shiga sukai, falour suka shiga, "zauna ina zuwa" abunda yafada kenan yashige ciki, kofar dakin yatura a hankali, duhu dakin baka ganin komai, light din wayarsa yakunna kana yakunna fitulun dakin tuni haske ya gauraye dakin, zabura tayi tamike, kallonta yayi yaga alamar tayi kuka gashinan idonta harya kubura "meyasa biki kunna hasken dakinba "? "ban iya ba" tafada a hankali" "kinci abinci" ah ah "to meyasa biki ciba" shiru tayi tai kasa dakanta "tashi kije kiyi brush kizo kici" tashi tayi tanufi bandaki "ke tsaya" yafada, tsayawa tayi tana kallonshi, kallon rigarta yayi tabaya yaga duk ta baci da jini "biki amfani da pat din dana sa akawomiki ba"? "bangantaba" abunda tafada kenan tana juyar dakanta, gurin kayan yanufa yana dubawa yaduko ta yace "baga taba zoki karba kije kisaka" ban iya ba" goshinsa yadafe yace "wai ke biki iya komai ba" zumbura baki gaba tayi, tunanin yadda ze samata yake dan shima besan yadda suke sawa ba, tunawa yayi da esha tana falour yasa yadauki panties din da pat din yafuta, yana zuwa ya tarar da ita a falour, mika mata yayi yace "taimaka kisamun wannan ajikin panties dinan" karba tayi tana kare mai kallo tace "Irfan meya hadaka da wannan kuma kai ba mace ba kuma ba kanwaba" "kinga in zaki sakamun ksa idan kuma bazaki saba kibani" gudun kada yabata rai yasa ta fara sawa, seda tasa kamar guda biyar tamikamai, karba yayi yana shigewa, binshi tayi da kallon mamaki, yana zuwa yamikamata yace "gashinan ki dau guda daya kiyi wanka kisa" karba tayi tana shigewa toilet, shi kuma yafuce, falour yakoma, yakamo hannun esha suka shige bedroom dinsa, bayan tayi wankan tadauka tasa kamar yadda yace, kana tadawo tadau abinci taci, tazauna a gurin tayi tagumi tana tunani, 'ita kenan haka rayuwarta zata kasance anan gurin'


=؞?=؞? YAN BIYU NE =؞?=؞?

Story and writing by Hadizatu
'?
'?

Mrs (KD)

Romantic love story

Yar amanar jajirtattu=ت?=ت?

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
=ت? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*=ت?
'?
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i_.'?


Marubuciyar littafin
SOYAYYA DA IZZA
Ayanzuma nakara kawomuku wani sabon book
dina me suna (YAN BIYU NE)
ku biyoni domin kuji ya labarin ze kasance
karki bari abaki labari my sister

paid book 300
account number 9045749823
bank name Opay bank
shedar biya ta wannan number =?G?=?G?=?G?
09030849138 WhatsApp only
ko kuma katin waya ta wannan number
09045749823 Airtel

page 12

______________Kwata-kwata yau jin kanshi kamar mara lafiya, dan haka yana dawowa ya wuce bangarensa, kayan jikinsa ya rage kana yafada toilet danya watsa ruwa, bayan yafuto yadau kayan bacci yasa kana yafeshe jikinsa da turare, yahau kan bed yaja blanket, yau ko dinner beyi ba, haka yayi bacci,
"baffa kada ku damu munyi cikiyarta sosai, saboda afanmu ma yabada umarnin duk wanda zeyi labarai ko wani shiri ya tabbata yasa cikiyarta, " "Allah ya sa dai mudace" "insha Allah za'a dace" "to Allah yasa" ameen suka amsa dashia gaba dayan su, mukewa Abubakar yayi yana fadin "ni zan tafi gida , da safe innaje gurin aiki zanji ya ake ciki" "to shike nan Abubakar se da safe" daga haka su Umaru da Salisu suka rakashi, seda suka dawo , Salisu yace ze wuce gida da safe ze dawo yaji ya ake ciki, sallama sukayi ya wuce, ita dama Zainab dama su Inna sun korata gida,
cikin dare taji wani zazzaSi me zafi ya rufeta, harta blanket din data rufa seda yadau dumi, hawaye ne kawai ke bin kuncinta, ga rawar sanyin datakeyi, ahaka dai har asuba tayi, dakyar tamike, tanufi toilet, tahada ruwa tayi wanka, kana tafuto takoma kan bed din takwanta, taja blanket.
kiran sallar asuba ne ya farkar dashi, mikewa yayi yashiga toilet, yayi wanka yayo alwala ya zura jallabiyya, yau bayajinma ze futa masallaci, dan haka ya shimfida abun sallah, bayan ya idar yadauko qur'ani yashiga karantawa, seda yayi izu biyu, kana ya ajiye yadau azkar yayi na safiya, kana yayi addu'a, yashafa, komawa yayi yakwanta yaci gaba da baccinsa, kullum abunda yakeyi kenan daga asuba zuwa lokacin, se kuma yakoma bacci
gari yafara haske, agogon dakin ne yafara ruri, bude idonsa yayi a hankali, yaga gari har fara haske, janye esha yayi daga jikin shi yamike, tawul yadauka yadaura ,inda agogon yake yanufa yakashe, kana yanufi toilet, wanka yayi yafuto, yadau riga yasa, sallaya ya shimfida, ya tada sallah, duk iskancin Irfan indai lokacin sallah yayi baya darawa se yayi, kome yake kuwa, bayan ya idar, yakoma kan kujera doguwa ya kwanta, bayasan yakara komawa kan bed din, anan kan kujera bacci yakara daukeshi,
Inna babba ce ke dama kunu ita kuma Inna karama na jefa kosai, almajirai ne suka cika gidan sunata karbar sadakar koko da kosai, wanda Umaru mahaifin A'isha yasa ayi, sadaka kam sunatayi makarantun almajirai, domin amusu addu'a Allah ya bayyana A'isha, Salisu ne ya shigo gidan bakinsa dauke da sallama, amsawa sukai su duka, durkusawa yayi ya gaida baffa, ya amsa , kana ya gaida su Inna, suma suka amsa, Umaru ya gaisar, ya amsa, yana fadin "Salisu da sassfen nan baka bari rana ta fito ba" "ai ina ganin idan nazauna hankalina baze kwanta ba" to hakan ma yayi" baffa yafada , bara 11:00 tayi nakira DPO naji halin da ake ciki" to Allah yasa dai muji alkhairi" ameen suka amsa su duka,
se karfe 12:00 yafarka yana tashi yaduba agogo, "kai ashe nayi bacci sosai" daga haka yashiga toilet yakara watsa ruwa, yafuto yashirya cikin shadda kalar brown, yadora hularsa, kana yafeshe jikinsa da tura rukansa, futowa yayi yanufi bangaren iyayensu,
"esh kitashi zan wuce gida gurin mom" bude ido tayi ta kallesa, yashirya tsaf se kanshin turare yake, "zaka dawo ne" "eh anjima zan dawo inzaki jirani to" "eh zanjiraka" "ok zanturamiki 1.5 million a account dinki" "ok thank you so much" batai mamaki ba domin yana bata fiye da haka in yaso, shiyasa tana san ya gayyaceta, "amma kitashi kiyi sallah mana" "tom abunda tafada kenan" "zansa sukawo breakfasta" "ok" daga haka yafuce, baya iya cin abinci a ko ina sedai gida tare dasu mom da Sawban da Daddy, to hakama Sawban duk inda yaje seya dawo yaci abinci, mom tasaba musu dahaka, bayan yafuta yabada umarnin akaiwa esha abinci, amsawa sukai, kana suka bude mai mota, yashiga,
tana kwance taji anturo kofar batai motsi ba, taga wani wanda bashi ke kawo mata abinci ba yashigo, ya ajiye ledojin hannusa, kana yafuce, itakam a yanzu bazata iya cin komai ba, saboda yadda takejin jikinta, knocking akaiwa esha tabude kofar, yamikamata ledojin hannunsa takarba, tamaida kofar ta rufe, "kai gaskiya oga na bidirinsa" meya faru "? dayan yatambayesa "mata biyu ya ajiye fa " "mutumina kudi fa aka ce, kai ma in kanada kudi goma ma zaka iya hadawa" "gaskiya kam kudi yayi" dariya sukai , duk cikin harshen turanci suke maganar,
bayan ya isa gida, yagansu duk sun hallara a dining, harma sun fara breakfast, "lah momy baku jirani ba ko"? "to baka futo dawuri ba shiyasa" karasawa yayi yana zama, gaida iyayen nasu yayi suka amsa, kafadar Sawban yadafa yana fadin, "yadai najika shiru, koda yake kai dama baka magana" be kula shiba yaci gaba da cin abincin sa, "wai momy anya kuwa lokacin da kika haifi Sawban yayi kuka kuwa" "da beyi ba kaima ai bazakayi ba" Daddy yafada yana dariya, "ai Daddy naga bayasan magana" "to kai kuma maganau " "eh naji ni maganau ne dama na yadda" "wai dan Allah Sawban yaushe zakai aure"? "bansaniba kaga ka kiyaye ni" "wlh Sawban kafiye san girma kumafa shekarun mu daya, wai momy da minti nawa ya girme ni ne"? "ai kam da rabin awa ya girmeka seda yafara shakar iskar duniya sannan kai ka shaka" "to ai idanma auren ne gaba daya zan hadaku namuku " "ai Daddy nabarwa Irfan girman" "wato saboda anyi maganar aure ko"? "nima banaso rike kayanka" "na lura yarannan bakwa san aure" momy tafada tana kallonsu "rabu dasu karshen shekarar nan zan musu aure" "nifa senan da 3 years zan yi" Sawban yafada "ni abarni ma nanda 2 years zanyi" aikam baku isa ba nima inasan naga jikoki na" momy tafada tana hade rai alamun gaskiya take" mikewa Sawban yayi yana fadin "ni zan wuce office" to seka dawo bakaji anyi zancen aure ba" momy tafada, "to seka dawo" Daddy yafada "adawo lafiya ango" harara Sawban ya galla masa, kana yafuce, abincinsu suka cigaba da ci suna fira,
bayan ya isa office , kujera ya zauna yadauko takardun dake kan table din yana dubawa, wayar dake office din yadauka, yayi kira yace yana bukatar aturo mai Abubakar yanzu, bayan yagama yamaida wayar mazauninta, ba daewa aka turo kofar, Abubakar ne yashigo, bakinshi dauke da sallama, amsawa yayi yana nunamai gurin zama, bayan yazauna ne, yakalleshi yace, "Abubakar ya batun yarinyar nan data bata kuwa ansamu wani labari akanta"? "wlh yallabai shiru har yanzu bawani labari" "to ina ganin idan mun tashi aiki inasan karaka ni gidan su yarinyar naga iyayenta" "tom yallabai" "ok jeka lokacin labarai yayi" daga haka yafuce, tunani yafara cikin zuciyarsa cewa 'taya za ai yarinya karama haka ta bata, kuma haryanzu ba labarinta wannan abu da daure kai'
zazzaSin yafara sauka jikinta, hakan yasa ta tashi tazauna, amma duk da haka batajin zata iya cin komai, hawaye ne ke bin kuncinta tana tuannin lokacin da bata da lafiya yacca hankalin su baffa ke tashi, idan zata sha magani kowa seya hallara ana lallabata, yanzu kuwa babu ma wanda yasan matsalarta ba wanada yasan meke damunta ballantana yamata magani, hawaye take hartana shashshekar kuka, tashi tayi tashiga toilet dan ta karasa ruwa ajikinta, danta lura kamar wankan datai dazu shiya dan rage mata zafin zazzaSin, kaya tacire tahada ruwa, tayi wanka, pant dinta tadauka tamayar, tunda taga be Saci ba, kuma tun jiya tasaka shi, pat din jiki tadaye, tasa iya part din, dama tayi wankan tsarki, dan taga jini be kara zuwa mataba tun jiya, hakan yasa tayi wanka, dama ta iya, bayan tafuto ne ta zauna kan kujera tana tunanin gida, zuciyarta ce ,tace mata 'ke dena tunani aikin kusa tafiya gida tunda yace kina gama jini kifada mai ze maida ki gida' tu no hakan yasa ta dan murmushi afili tace, "alhamdulillahi nakusa tafiya gida kenan" can kuma ta hade fuska tace, "to meyasa bayasan yakaini gida ina jini " ganin bata amsar tambayar ta yasa tayi shuru, Allah Allah take yashigo tafadamai ta dena gani yamaida data gida, ko abinci taki ci saboda zumudi,
bayan sallar la'sar yatashi daga aiki, Abubakar yakira yace mai su tafi, motarsa suka hau suka tafi, duk inda suka shiga a unguwar kallon motar ake, parking sukai a dai-dai kofar gidan, Abubakar ne yashiga, yafadamusu sunada bako, baffa ne yace ashigo dashi, bayan yafuto yasanarwa Sawban zasu iya shiga, Abubakar ne yayi gaba shikuma yabishi abaya, tabarma aka shimfida musu suka zauna, kallonshi kawai suke suna tunanin ina Abubakar yasamo balarabe, baki yabude yace "ina yininku"? se lokacin suka kara cika da mamaki jin yayi hausa "amsawa sukai su duka suna mai anzo lafiya "lafiya lau" yafada, Abubakar ne yafara magana yana fadin, "wannan shine me gidan rediyon danake aiki kuma yana da gidan talabijin nashi" Masha Allah" "am Abubakar yakawo cikiyar yarinyarku wajenmu, kuma munan muna cikiya, amma sedai haryanzu shiru, amma ina ganin meze hana kusanar da jami an tsaro" "munyi hakan dazunan ma muka kira DPO din yake fadamana haryanzu basu samu abun zargi ba" amma nayi mamaki jin shakarun yarinyar kuma harta bata haka, kuma da kidnapping ne da tuni sunyi waya tunda su kudi suke bukata" "mu kanmu yanzu munkarya gani muke bazata dawo ba" "no inshallah za a ganta, amma bata da aljanu" bata da wani alhanu yarinyar nan" "saurayi fa" bata dashi yarin yace ai" "wannan lamarin akwai daure kai, amma ku kwantar da hankali, yanzu idan akwai hotonta kubawa Abubakar, nikuma zansa yakai gidan television dina a haska, " amma fa mungode sosai" Umaru yafada, "bakomai aikinmu ne ai taimako, to mu zamu wuce" lt ar ao ku gaida gida mun gode sosai" su baffa da su pIppnna suka amsa, sukuma su Salisu da Umaru suka tashi dansu rakasu, bayan yatashi yazaro kudi a aljihunsa, ya ajiye musu, yana fadin gashi ayi wa almajirai sadaka, godiya sukai mai sosai, har gurin motarsa suka rakashi, daga haka sukai sallama yashiga mota ya tafi, sukuma suka koma

=؞?=؞? YAN BIYU NE =؞?=؞?

Story and writing by Hadizatu
'?
'?

Mrs (KD)

Romantic love story

Yar amanar jajirtattu=ت?=ت?

https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
=ت? *JAJIRTATTU

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login