Showing 3001 words to 6000 words out of 45298 words

Chapter 2 - Kulsum Book 1 Complete Hausa Novel

23 Sep 2025

609

sane yasa tagane yashigo dakin, yaxo ya xauna kusa da ita ya jawo hannuta ya sumbata yana kare mata kallo, yarinyar so innocent..........
Sakonnin soyayya ya aika mata a darenan da kyau,masu rikitarwa, har ya samu biyan bukatan shi, saida yaji kukanta na yawa sanan ya dan saurara mata......

Koda ta farka da safe baya cikin dakin, dakyar ta tashi ta shiga toilet ta tsarkake kanta tayi wanka ta fito tayi sallah harta koma bacci, sai wajen 10am ta tashi, tayi mamanki still baya na,ta tashi ta leka ko ina a gidan amma bayanan kuma babu alamunsa......

Ta koma daki dan duba kayan sa, nan ma wayam tagani sai wata wasika daya ajiye mata kamar haka
Matata mai sona, Allah yayi miki albarka kin biyani ni arayuwa.......amma dan Allah ina naiman gafararki da ki yafemin dan bawai na aureki dan ina sonki bane face sha'awarki danayi, kuma ni bazan iya zina ba shiyasa na aureki, amma kiyi hakuri sumy, na sakeki saki biyu sannan ga kudade masu yawa nabar miki ki kula da kanki, karma kice xaki naime ni dan kuwa baxa ki taba ganina ba. Sannan kina iya zama acikin gidan na wata daya kafin kudin hayan ya kare..............ina miki fatan alheri.

Bissalam
Innalillahi wa inna'ilaihi rajun kawai take fadi, ta fadi kasa tana rusa uban kuka shi kenan taga ta kanta

kursum ce ta shigo gidan da abincin karin su, ba karamin girgiza tayi ba da taga kawarta cikin yanayin nan tace miya faru? Kukan mai kike yi? baki da lafiya ne, a gigice take jero mata tambayo yi......... sumy kam kasa cewa komai tayi, ta mika mata wasikar daya ajiye mata, kursum ta girgiza matuka data karanta kasa cewa komai tayi, itama ta zauna sai kukan suke babu mai rarrashin wani. =?-?=?-? kaico

Daga bisani suka tashi suka dau kayan sumy da makudan kudin daya bari suka bar gidan.....

Yazid kuwa tunda ya tashi yawuce Airport yana sauri baya son missing flight dinshi na 7am, Allah yasa yana xuwa dama shi kawai ake jira, jirgi ya daka sai kanon dabo.......

Umma ce da kanta taje dauko shi a airport, dan kawai yasan ta damu dashi, suna cikin mota umma tace, son wato ka gujemu ko, wajan wata daya kenan bansa ka a ido ba idan nakira wayan ka saika ga daman dauka......
Yace to umma ya kikeso inyi, keda kika fi bawa aikin ki (fashion designer ce) mahimmanci, ko a gida baki da lokacin kowa saina aikin ki, ki wuni kina aiki a office kuma ki dawo gida kinayi, har Abba ma yafiki samun lokaci na, "tace my son kamin uzuri dan Allah, aikin nawa ne dole saida attention sosai in ba haka ba komai bazai yi daidai ba, ni kaina inason kasance wa da family dina shiyasa ma nakeson daukan hutu kona wata biyu ne......yace toh shikenan umma duk yadda kikai yayi daidai, shidai arayuwan shi yanason ummansa bai hadata da komai.

Koda gimbiya hafsatu ta karanta wasikar sumy, sai cewa tayi karta damu dama maza basu da tabbas, itama tayi mamaki yadda yayi ta zubar da kudi kaman bai san ciwon suba, indai aure takeso zata iya naima mata wani ta aura kodan ta huce haushi.
Kursum tace haba gimbiya kamata ace kin naimo mijin nata ayi magana,tunda da hadin bakinki akayi auren nan kuma ai kinsan kawunsa, gimbiya tace tab aini yanxu ko nayi trying number kawun bai shiga kashe wayar take
kuma yarinyan ita da kanta ta nuna shi take so kuma xata aure shi, toh miye laifina aciki.......ki fice min yanxu nan marar kunya, wato kece da bakin magana ita da aka saka bata zoba sai ke, wawiyar banza.
Kursum ta fice ranta abace,bata taba ganin zalamar miyar mata irin gimbiya ba, ita dai kanta kawai tasani......

Ta koma dakinsu, har lokacin sumy kuka take duk ta rame ta fita hayyacinta lokaci daya, kursum tace mata dan Allah ki bar kukan nan haka, indai ina raye a duniya toh saina naimo shi na daukar miki fansar abunda ya miki, koda kuwa zaiyi causing life dina, dat is a promise, sau daya nataba ganinshi amma bazan taba mantawa da face dinshi ba......
Tana taba sumy baki hardai ta hakura ta barwa Allah komai..

*Bayan wata biyu*

Sumy sai rashin lafiya take ga zazzabi da weakness da take ji ga yawan amai , shiyasa gimbiya ta kaita asibiti, doctor ya mata gwaje gwaje ya gano tana dauke da cikin wata biyu.......aka sallamo su suka dawo.
Gimbiya ta kirawo kursum ta gayamata sumy na dauke da cikin wata biyu, sai data girgiza da jin wannan xancen, yanxu ya sumy zatayi idan tasan tana dauke da cikin wanda yama manta da zamanta, gimbiya tace ga test result din saiki bata ki kara kwantar mata da hankali, kinsan mai karamin ciki batason tashin hankali gudun kar ciki ya zube.
Ta karba sum - sum ta fice, tasamu sumy na karatun al-qur'ani, sai da tajira ta idar sannan ta mika mata test result din, sumy ta karba ta duba saida gabanta ya fadi tace wake dauke da ciki ? Kece kowa?
Kursum tace kinsan dan Adam ajizine, duk yadda ubangiji ya tsara aka ke faruwa babu wanda ya isa yaja da ikon Allah, komai na duniyan nan jarabawa ce, Dan Allah kiyi hakuri ki yarda da kaddaran da Allah ya daura miki, sumy tace meke faruwa ne ? kinsani a duhu fah.

Ciki gareki na wata biyu sumy, kece keda cikin ba kowa ba, hawaye kawai sumy take tana addu'an Allah yasa hakan yafi alheri agareta, kursum tace amin.

Daddy ne ke tuki hankali kwance, yana murnan yau zai ga diyar shi tilo a duniya, wajen shekara guda rabon daya ganta..

Ya iso makaranta, har visitors lodge (inda iyaye ke zama idan sunzo ganin ya'yan su) aka kaishi, aka tura kiran sumy tazo dad dinta yaxo.....ita da kursum suka je wajen daddy suka gaishe shi, gaban dad sai da yafadi ganin yadda sumy ta rame sai haske data kara sosai, yace kursum, sumy bata da lafiya ne? Kursum tayi shiru ita dai tarasa dalilin daya sa idan tana gaban baban sumy take jin wani iri, kaman akwai wani connection tsakanin ta dashi.........kukan sumy ne yadawo da ita daga tunanin da take, tana kuka tana ba daddy labarin abunda ya faru tun daga auran ta har izuwa yanxu da take dauke da ciki, daddy kasa magana yayi sai hawaye kawai, gaskia ya tausayawa sumy ba kadan ba, duk laifin hajiya hadiza ne, da yanxu sumy na gida agabanshi hankalinta kwance.
Yana taba sumy hakuri akan karta damu jarabawa ce ta ubangiji, komin wuya akwai dadi, ya ajiye masu shopping din daya masu sa'annan ya masu sallama zai koma kano, karshen shekara zai dawo ya dauketa, ya dauko makudan kudi yabasu suna ta godiya..

Daddy kam yayi niyyan kwana biyu, amma bazai iya jure ganin sumy halin da take ciki ba, shi kanshi daurewa kawai yake amma ranshi a bace yake, aka ya tattara ya koma kano,

Hajiya hadiza na hakimce a parlour a zaune tana jiran shigowan daddy gidan, dan ta kwarara mai buhun bala'in data saba akan yaje ganin yar tsintuwo bada izinin taba....
Yana shigowa ta gane muryanshi da sallaman da yayi bata ma damu da yanayin shi ba, ta hau zaginshi damai rashin kunya ta ko ina, daddy kam kasa magana yayi ma saboda bakin ciki ta riga tamai yawa, nan take shikam ya yanki jiki ya fadi sai jin faduwan mutum tayi tim akasa.....=?3?=?3?

Ta kwallawa samira (yar aiki) kira maza ta fito Alhaji ba lafiya, samira ta fito da gudunta tana hajiya, alhaji ne ya fadi da alama ma rai yayi halinsa.
Hajiya a rude tace "samira kiramin wayar shehu nasan baiyi nisa ba,kirashi mukai alhaji asibiti.....

Baba shehu da sauri ya iso gida,suka sa alhaji a mota sai asibiti
likitoci sun yi iya kokarinsu, amma rai yayi halinsa (kulli nafsin za'ikatul mauti), abun tausayi hajiya da baba shehu sai kuka suke yau sunyi babban rashi.
Doctor yasamu baba shehu da hajiya ya tambaya su ya akayi suka bari har zuciyan alhaji ya buga alhalin sunsan yana da ciwon zuciya, hajiya tayi tsuru tsuru bata ce komai ba illa kukan da take tayi dan tasan tabbas itace silan ciwon zuciyan alhaji, yanxu gashi ya tafi ya barta, kuka kawai take tana nadaman abunbuwa data shuka mai........

Nima kasa rubutu nayi saboda mutuwan daddy ba karamin girgizani yayi ba...... Rip=?-?=?-?=?-?



[10/14, 8:11 PM] Badee Social:



Page 2? 6? ~ 3? 0? ('



*Kano*

Mutuwa daddy ba karamin girgiza jama'a tayi ba, mutane da dama sun sanshi da halin kwarai da taimakawa talakawa, Sam ba ha'inci ko xalinci a lamarin sa......mutane sai shigowa ta'aziya suke, baba shehu na daga waje yana amsan gaisuwa...
Hajiya kuka kawai take dakyar take ma iya amsa gaisuwan da ake mata, hajiya mario ce tadawo gefen ta tana kara bata baki akan tayi hakuri addu'a ya kamata tamai bawai kuka ba.
Zainab ma tayi rashin daddy ba kadan, dan daddy ne kadai yake kwabarta da mata nasiha sosai game da yanda tadau rayuwa da zafi, yau gashi tayi babban rashi. Tana kaunar shi tamkar shiya haife ta..
Har gida yazid yaje yama xee ta'aziya, ya tausaya mata sosai dan yasan yadda suka shaku da daddy ba kadan ba, wani irin sonta ya karaji a zuciyan shi....har dakin hajiya yaje ya mata gaisuwa, ta amsa ba yabo ba fallasa dan yanxu tadan rage kukan nata, dazai wuce ta bashi sako ya kaiwa mairo tare da shi mai Albarka. ........yazid kam yana jin haushin yadda hajiya ke cewa umman sa mairo sai kace a kauye Ina laifin maryam ma......=? ?=? ?=? ?


Bauchi
Yan makaranta kam sai shirye shiryen xana jarabawa shiga ajin karshe ake babu wasa kowa ya dukufa da karatu, sumy kam ciki ya shiga wata tara, haihuwa ko yau ko gobe, "Sam bata da labarin mahaifinta ya rasu wata bakwai da suka wuce.
Kursum da gimbiya kadai suka San da rasu war shi, sunki sanar matane akan lalular da take tare shi. Sun fiso saita haihu sannan su gaya mata.....

Bayan kwana biyu, sumy ta tashi da nakuda mai tsanani, da gudu kursum ta kira gimbiya sukai rushing dinta zuwa hospital , Allah yasa haihuwan taxo mata da sauki ta haife kakkyawan baby gal wanda babu bambamci da ubanta kaman an tsaga kara an karya...washe gari likita ya sallamo su suka dawo...
Ranan suna ba wani bidiri akai ba, duk da gimbiya ta gayyato mutanan ta, yarinya kam taci suna hanifa son kowa kin wanda ya rasa.
Sumy kam sai murna take, ba karamin son hanifa take ba, dan yanxu tama daina jin haushi mijinta asalima ta yafe mai duk abunda ya mata...tana fatan Allah ya hada hanifa da ubanta wata ran.
Kursum ce ta shigo daki ta kwantar da hanifa da tayi bacci, tace akwai abunda nakeson gayamaki sumy amma kiyi hakuri bamu gayamaki ba tun lokacin saboda cikin ki, Allah ya yayiwa daddy rasuwa tun wata takwas da suka wuce....
Innalillahi wai inna'ilaihi raji'un kawai sumy take furtawa, kuka take na tashin hankali shikenan daddy ya tafi ya barta yanxu bata da wani gata, yanxu ya zata koma gida da zama, dan bata manta da azabar da tsanar da hajiya ke mata ba tun tana karama, hawaye kawai take tana Allah yaji kanka da rahma daddy......Kursum kam tashi tayi tabar dakin dan bazata iya ganin kawarta cikin yanayin da takeba.......itama tasan tayi rashin daddy ba kadan ba, dan shine ya mamaye mata gurbin uban da bata dashi.


*kano*

Gaba daya family din daddy sun hallara a parlour din gidan tare da lawyer (alkali) sa dan karanto will (wasiha) da alhaji ya bari kafin ya rasu......
Baba shehu kam sai murna yake dan yasan dole yasamu abu mai tsoka, dan tun rasuwar daddy ya maida kanshi managing director din oil company dinsa.
Mommy da xee suma suna zaune suna jiran barrister yafara bayani..
Barrister shu'aibu ya fara da addu'an sannan ya fara bayani yace tun lokacin da alhaji yakamu da ciwon zuciyan yasan bazai dade ba, shiyasa yazo ya sameni ya bani takardar nan, acewarsa duk ranar da baya duniya yanaso acika masa burinsa dake rubuce anan......barrister ya Bude yafara bayani kaman haka
Ni Alhaji Tanimu Bawa na damkawa ya'ta sumayya dukiyata kashi hamsin acikin kashi Dari, sannan na bata matsayin managing director na oil company dina da kuma gidan da muke ciki duk na mallaka mata su.
Acikin kashi hamsin daya rage na bawa hajiya hadiza kashi ashiri, kashi goma na bawa Zainab, kashi goma na bawa shehu sai sauran kashi goma akai masallaci da gidan marayu.
Ina fatan iyalaina zasu cikamin burina , sannan banyi haka danna matawa wani ko wata rai ba.....bissalam

Barrister ya gama karantawa sannan ya mikawa mommy takardar, yace alhaji yamai xancen nan da shekera daya atura driver yaje ya yaje ya dauko sumy daga makaranta, mommy tace to insha Allahu xaai haka, barrister yamasu sallama yatashi ya tafi.

Baba shehu kam fuskan nan babu annuri ko kadan, wato haka alhaji zai sakamai duk irin kokarin dayama company dinsa shine zai bashi 10% kawai acikin uban dukiya daya tare, kuma harda ba yar'sa director din company din, yarinya karama da komai bata sani ba, "Yayi murmushin mugunta da tunanin halaka yarinya kafin ma ta shigo gidan nan..
Hajiya kam bata damu da abunda tasamu ba asalima abun duniya bai dameta ba, takai cinta daya shine yadda alhaji ya bawa sumy komai daya mallaka alhalin bama yar'sa bace ta jini, zata bar sumy ta zauna a gidan amma tayi alkawarin making life dinta miserable.

Zee sai murna take, dan batama yi expecting samun wani abu ba, tunanin ta daya shine Wacece sumy ya take, itadai tasan sumy diyar alhaji da mommy ce amma bata taba ganinta ba.


*Bayan shekara daya*

Sun gama exams sai shirye shiryen tafiya suke, kursum dake wasa da hanifa tace sis yanxu kina ganin idan nabi ki gidanku ba matsala , nidai ina tsoro kar hajiya tamin wulakanci ta kore ni, dan yanda kike ban labarin halinta na rashin kirki nasan tana iya wa.
Sumy tace karki damu nasan yanxu ta canza tunda shekaru sun ja, kuma makauniya ce ba lailai bane tasan kina gidan ba......

An turo driver daga gida daukan su, sai sallama suke da kawayen su da sauran malaman makaranta , suka shiga har office din gimbiya hafsatu sukai mata sallama ta dauko wani dan karamin box ta bude taciro wani hadadden pink diamond da take ajiye dashi wajen shekaru goma sha takwas da suka wuce ta damka wa kursum a hannu, tace yaudai na cika alkawarin, kursum tace wanna na miye kuma, gimbiya tace matar data kowa kine tun kina jiririya tace in baki idan kin tashi tafiya kya iya siyarwa ki samu na rike kanki,
Kursum tai mata godiya sosai suka fice, sun iske driver na jiran su, suka shiga mota...
koda suka shigo cikin gari sun tsaya suka shiga gidan Inna sadiya (mai kitson su) suka gaishe ta sosai ta amsa da fara'arta dama tasan da zuwan su, sumy ta mika mata hanifa, Inna ta amshe ta sai wasa take mata tace karku damu zan rike muku ita har kudawo daukan ta dama nagaji da xaman kadaice. .....
Kursum tace Inna mungode sosai, da munyi settling zamu zo mu dauke ta yanxu ki rubuta mana number wayan ki yadda idan mun isa gida zamu kira, dan yanxu ba waya ahannun mu, "Suka bata kudi masu yawa wanda zai ishe su kafin su dawo, suka kama hanya sai kanon dabo...
amota sumy sai kukan rabuwa take da hanifa, tabbas tasan barin hanifa wajan Inna shine daidai dan tasan hajiya bazata taba yadda da cewan tayi aure harta haihuwa ba, shiyasa ma tabar ta hannun Inna kafin tasamu yi mata bayani. ......
Sun shigo kano kenan, sumy tace gaskia yaka mata kindan gyara fuskan ki kodan kwalli ne kisa a ido, kursum tace kinsan ni bana kwalliya asalima ko kayan kwalliya ban dashi, sumy ta mika mata handbag dinta tace bude kidau powder ki sha fa,
Daidai lokacin da kursum ta amshi jakar sumy wata katuwar motar petur ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????dake tafe ta bangaje motar su, kofan side din da kursum ke zauna ya Bude ta fado kan titi rike da jakar sumy, sai birgema take harta buge da wani katon dutse, sumy da driver kam suna cikin mota dake kamawa da wuta sai gangarawa motar take cikin daji harta bugu da wani katon bishiya tayi exploding baammm kawai kake ji. ...

=?3?=?3?=?3?=?3?

*Xarah B??*

*Dedicated to Bady social*

~Luv u all~=??=??=??


*Xarah B??*

*Dedicated to Bady social*

~Luv u all~=??=??=??
[10/14, 8:11 PM] Badee Social:


Page 3? 1? ~ 3? 5? ('



Kursum ta farka taganta a gadon asibiti, duk jikinta ya kurje ga farin bandage da aka daura mata a kai dan tsayar da jinin dake zuba, sai kuka da ihu take tana Kiran sunan sumy.
Da gudu wanda ya tsince ta a hanya ya kawota asibiti yaje ya kira doctor malik yana gayamai patient din ta tashi amma kaman bata hayyacinta...
Doctor ya shiga yana mata magana, amma ita kam ihu kawai take tana Kiran sumy, ya tsira mata allurar bacci ya fito.
Yace Bala daka tsince ta babu waya ahannunta ko wani abu dazai sa musan family dinta ko inda take zama, Bala yace gaskia babu sai dai ko jakarta xaa duba, dan koda na ganta akwai karamar jaka tare da ita, ya mikawa doctor malik jakar, suka zazzage jakar daga kayan kwalliya sai wani wallet mai kyau suka bude, pictures din daddy kuda biyu Dana kursum ne aciki sai wani karamin littafi an rubuta sumayya tanimu bawa.
Doctor malik yace ai wanan hoton alhaji ne, kuma ba shakka wanna yarinyar yar'sa ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login