Showing 1 words to 3000 words out of 35955 words
_____
*🏚️RANA DAYA 🏚️*
CHAPTER 1
*BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*
**FARKO **
Tana fitowa daga dakin ta soma rera kuka kallon dakin da Mahaifinta ke kwance a cikin. Kafadarta taji an dafa tare da kiran sunanta.
“Ummu Salma, kiyi hakuri Allah zai ba mu
mafita.” Ko bata dago ba ta san Yaya Hadiza ce. Cikin kuka ta ce, “Yaya Hadiza abin nan da bakin ciki, Naira dubu goma tasa za mu koma da Baba gida a haka?”
Yaya Hadiza ta kama hannunta. “Zo muje kafın Yaya ya fito mu ga ya za’ayi.”
A harabar asibitin suka tsaya can in da ba kai kawon mutane, sai motoci da ke aje a gurin. Suka jingina da wata mota ba tare da sun damu da zafin da jikin motar ya yi radau ba.
Yaya Hadiza ta ce, “Salma yanzun ke nawa ne a gurin ki?” Ta ce, “Jarin Awarata gaba daya Naira dubu ne da dari bakwai, kuma kin ga dai kullum in nayi za a samu dari bakwai, dari shidda. Da shi fa muke cin abinci, in kuma an kwashe an ba da ina zamu samu na cin abinci, har ma a kawo asibiti?”Yaya Hadiza ta numfasa, sannan ta girgiza kai. “Taba wannan jarin ba zai yiwu ba, sai dai bari Yaya Auwalun ya fito muji, kin san shi aikin shi na gidan Biredi sai karshen Wata suke ba shi albashi, in dai ba Allah ne Ya kawo mishi dan gyaran wuta ya yi ba.”
Salma ta ce, “To Yaya Hadiza ke babu wani kokari da za ki yi?” Ta ce, “Salma me ya rage min yanzun? Sai fa Gadon da muke kwana a kai.
Shi ma Baban Amira kin san dai ba wani karfi gare shi ba, sai ya fita ya nemo sannan za mu dora.”
Salma ta hango Yaya Auwalu yana ta waige waige alamar yana nemansu. Ta ce, “Ga Yaya can. nasan tabbas mu yake nema.
Yaya Hadiza ta ce, “Yaya Auwal!” Ta kwala
-mishi kira, ya kalli inda suke, sannan ya nufo su
Suka ci gaba da tattauna yanda za su samu kudi. Sa dai kusan minti talatin ba su cimma matsaya ba, zancen dai daya ne na kudi kuma ba su da shi.
Daga cikın motar suka ji ana kwan-kwasa kofar, Salma ta zabura da sauri ta matsa gefe,sannan ta ce Yaya Hadiza matsa, wani mutum ne Ya fito daga cikin motar sanye da shadda mai ruwan kasa, kanshi babu hula. Kyakkyawa ne wankan Tarwada, fuskarshi babu annuri sam-sam.
Hakan yasa gaban Salma faduwa. Ta ce, “Alhaji don Allah kayi hakuri ba mu san da mutum ba.”
Ya kalli sashen cikin asibitin, sannan ya soma latsa wayar da ke rike a hannunsa, suna dai kallon shi ya karata a kunne ya soma magana.
“Haba abokina! Ka fito mana ko in je in dawo ne tukunna?” Ya dan yi shiru, sai kuma ya ce, “To babu matsala, bari in dawo minti sha biyar.” Sai lokacin ya kalli Salma wadda idanunta suka
kasa daina kallon shi. Ya ce, “Nawa ku ke nema
don ci gaba da kula da Mahaifinku?”Salma ta zaro ido tana in ‘ina.Am… in…kudin da muke so?”
“Samu nutsuwa mana yarinya, kin ga sauke numfashi tukunna.” Ya fada a hankali. Ya kalli Yaya Auwal.
“Nawa ku ke bukata a yanzun?” Har suna hada baki shi da Yaya Hadiza gurin cewa, “Dubu goma ne dai yanzun.”
Ya ce, “To cikinku wa zai bini ya amso? Don in na fita sai na kai minti sha biyar kafin in dawo cikin asibitin nan in dauki abokina.”Yaya Auwal ya ce, “To bari in bika, mun gode sosai Alhaji, Allah Ya saka maka da alkairi.” Hadiza da Salma ma suka yi godiya. Ya ce, “Kar ku damu, ku gode wa Allah.”
Nafisa ta kalli Mahaifiyarta wadda take zaune bakin Gadonta, tana shafa mai. Ta ce, “Mama har yanzun ina shakkar yiwuwar
aurena da Yaya Shatima.” Uwar ta dubi Nafisa, sannan tayi dan murmushi. “Yau ita ce rana ta uku da ki ka tambaye ni, ko in ce da ki ka fada min cewa kina shakkar yiwuwar aurenku, amma kin kasa fada min dalilinki na fadin haka. Nafisa ta dan kalli saman silin din dakin uwar,
kamar wadda take son tuna abin da zata fada.
Uwar ta gama shafa mai, şannan ta mike ta nufi gurin durowa tana duba kayan da zata saka. Nafisa ta ce, “Mama nayi la’akari ne da yanda ya ki ya zo gurina, ko ya kira ni a waya. Tun sakon da ya turo min cewa ina jin zan iya auren shi? Na ba shi amsa da cewa zan iya, shi ke nan fa.”
Uwar ta ajiye kayan da za ta sa a kan Gadon, sannan ta zo ta zauna kusa da ‘yar, ta kai hannu ta dafa yar.”Nafisa zan ba ki shawara, kar ki sake ki saka wannan a zuciyarki, aurenki da Shatima kin san babu abin da zai hana shi faruwa sai in dayanku ya mutu.
Kar ki manta Babanki da Babanshi uwa daya uba daya. Kuma su ne suka yanke su hada ku aure ba tare da neman izininku ba, fatana dai ki zama ‘yar zamani mai kula da abin da zai ja hankalin mijinki.
Abin da za ki lura shi ne, Shatima matashi ne dan zamani, mai ilimi, mai kudi, mai kyau. Mata da yawa irin shi suke nema, sai kin dage kin zama jaruma sannan ne za ki zama ‘yarlele, ki dauke hankalinshi daga kan kowace mace.”Nafisa tayi murmushi, “Ni dama matsalata guda daya ce, ya zo mu fahimci juna.Maman ta ce, “Kin san kowane namiji yana da irin nashi ra’ayin, da kuma irin nashi salon. Kila shi nashi kenan irin wannan salon.”
Nafisa ta ce, “Amma Mama kina ganin ba laifi ba ne in nayi masa sakon gaisuwar Juma’a ban yi laifi ba?” Ta ce, “Babu laifi, amma yana da kyau mace ta zama mai kama ajinta a gurin namiji, ba kowane namiji ba ne ya ke son a dame shi ba.
Haka kuma ba kowane namiji ba ne ya ke son mace mara aji, shima yaja aji bare ke mace. Amma dai ki masa sakon sau daya a Juma’ar nan mai
zuwa mu gani, daga yanda ya dauki abin za mu iya fahimtar wani abu.” Nafisa ta ce “To shi kenan Mama, na gode da samun uwa irin ki. Ina alfahari da samun ki matsayin Mahaifiya. Nasan duk duniya babu wanda ya kai ni dacen uwa tagari mai dora ya’yanta a kan turbar daidai.
Bari in je in ci abinci har naji yunwa, da dazu na kasa cin komai, ko in ce cikin kwanakin nan na kasa cin komai.” Uwar ta ce, “Je ki ci kar ki damu kanki ko kadan.”
Munnir ya kalli wayar da ke jone a jikin chajar motar, sannan ya kalli mai jan motar.
“Abokina wayarka tana ruri fa. Mai wayar ya kai hannu ya dago wayar sannan
ya kalli fuskar wayar, da sauri ya daga wayar.
Ta ce. “Hello! Manyan kasar Nijeriya.” Ya ce, “Amna ba dai kin shigo Nijeriya ba?” Ta ce, “Ba ka kalli number din ba ke nan?” Ya ce, “Shi yasa ai na tambaye ki, saukar
yaushe?” Ta ce, “Saukar kwana hudu da suka gabata.
Ya ce. “Amma shi ne sai yau ki ke kirana?” Ta ce, “haka ma za ka ce? Har ma kana da bakin magana tunda ka baro Dubai sau daya rak! Ka kira ni.
“Kin fi ni gaskiya Amna, amma ina da dalilin haka. Cikin satin da na dawo Nijeriya aka sace min wayoyina da Laptop dita, sai da na rasa lambar kowa sai wanda ya kira ni.Ban da haka ma littafin da ni ke ajiye abubuwana na rasa in da na saka, ke kuma kin ki kirana bare in samu lambárki.”
Ta ce, “To yanzun dai yaushe za ka zo?” Ya ce, “Ban da wannan satin, satin da za mu shiga.” Ta dan yi shiru. Can ta ce, “Ko dai ka canja ni ne a zuciyarka?”Ya ce, “Matsayinki yana nan daram! Me yasa ki ka tambaye ni?” Ta ce, “Yanda naga kamar ba
ka yi dokin ganina ba.” “In da kin san tarin ayyukan da suke gabana da ba ki fadi haka ba. Zan tsallake da dama ne fa in zo in gan ki, kin san sabon ma aikaci, ofishin da na samu cike yake da tarin ayyuka.”
“Na gamsu, don tunda muke tare ba ka taɓa fada min karya ba.” Ta fada cikin kwantar da murya.
“Na gode da lambar yabon da na samu a gurinki. In na samu lokaci zamu yi waya.”Ta ce, “Sai na ji ka.” Ya mika ma Munnir
wayar tare da fadin “Maida min ita a caji.” Daidai ya karya kwana. Munnir ya amsa tare da fadin “Abokina wai me ya ke shirin faruwa ne?”
Ya dago ya kalli Munnir, sannan ya yi murmushi. “Wallahi nima ban sani ba abokina, amma tabbas ina ji a jikina babban al’amari zai faru, kuma zai faru din. Nayi wani mafarki kwanakin baya, kuma naji a jikina mafarkin alkairi ne.”
Munnir ya ce, “Allah Ya tabbatar mana da
dukkan alkairi.” Ya ce, “Ameen.” Kofar gidan su Munnir ya sauke shi, sannan ya nufi gidansu da ke Kwarbai a garin Zaria.
Damfareren gida ne mai girman gaske, wanda daga gani ka san ma su gidan da kunbar susa, kila ma da jibin sarauta.
Ya nufi ɓarayinsu ya aje motar ya kwashi
wayoyin shi ya nufi cikin dirkeken falon. Tana
zaune a kan kujera Badi’a tana shafa mata man zafi a kafa.
Ya zauna kan Dardumar da ke gabanta tare da fadin “Sannu da hutawa Hajiya.
Badi’a ta tashi da sauri tare da fadin “Sannu da zuwa Yaya. Ya ce, “Sannu Badi’a.” Hajiya ta ce, “Sannu Shatima, har ka dawo?”
*Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300 idan kina bukatar cigaba ki turo kudin ta wannan account din👇🏻👇🏻*
```ACT > 3024960720
POLARIS BANK
MOHAMMED UMAR ko ki turo katin Mtn ta wannan number 09068032427```
*Idan baki shirya ba kada kiman mgn ki bari sai kin shirya*_____
*🏚️RANA DAYA 🏚️*
CHAPTER 2
*BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*
*Masu son a tallata masu hajar su ko ayi masu sharing link din group din su na kasuwanci zaku iya yin magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku akan farashi me sauki*
Mun tsaya
Munnir ya ce, “Allah Ya tabbatar mana da
dukkan alkairi.” Ya ce, “Ameen.” Kofar gidan su Munnir ya sauke shi, sannan ya nufi gidansu da ke Kwarbai a garin Zaria.
Damfareren gida ne mai girman gaske, wanda daga gani ka san ma su gidan da kunbar susa, kila ma da jibin sarauta.
Ya nufi ɓarayinsu ya aje motar ya kwashi
wayoyin shi ya nufi cikin dirkeken falon. Tana
zaune a kan kujera Badi’a tana shafa mata man zafi a kafa.
Ya zauna kan Dardumar da ke gabanta tare da fadin “Sannu da hutawa Hajiya.
Badi’a ta tashi da sauri tare da fadin “Sannu da zuwa Yaya. Ya ce, “Sannu Badi’a.” Hajiya ta ce, “Sannu Shatima, har ka dawo?”
Ya ce, “Na dawo Hajiya. Akwai aikin da zan yi “a gida ne.” Ta ce, “To, cikin laptop din taka za ka yi kenan?” Ya ce, “Eh.” Hajiya ta ce, “To bari in sa a kawo maka abinci daki, gashi kuwa abin da ka ke son aka yi.
“Burabusko ke nan?” Ta ce, “Eh, kuma akwai farfesun kafar Sa, su zubo maka ko?”
Ya ce, “To Hajiya bari in shiga ciki.” Ta ce “Badi’a!” da sauri ta iso ta ce, “Gani Hajiya.” Ta ce, “Kira min Uwa a kicin.”
Shatima ya nufi sama in da dakinshi yake. Uwa ta iso falon cikin girmamawa ta ce, “Ga ni Hajiya.” Ta ce, “A shirya ma Shatima abinci.” Ta ce, “To Hajiya, kunun zaki za a zuba mishi ko zobo?”
Ta ce, “Kin san shi fa in bani na hada da kaina ba ba zai sha ba, ku kai masa ruwa mai sanyi da lemon kwali kawai.
Yayi nisa cikin aikin sa, Badi’a ta kwankwasa kofa. Ya ce, “Shigo.” Ta shigo da sallama ya amsa. Ta aje ta fita. Ya kalli abincin, tabbas yana son ci amma
yanzun aikin nan ne a gabanshi. A fili ya ce, “Ina
ma nayi aure da sai a ke bani a baki ina aikina.” Daf da kiran Magariba ya rufe komai ya ci
abinci, sannan ya yi wanka ya fito. Lokacin da yaje Masallaci ana raka’ar karshe, don haka ya jone da su. Abin da ke ranshi shi ne in ya idar ya nufi Tudun Wada don kai gaisuwa ga Kakarshi,
Mahaifiyar Babanshi.
Kusan kullum sai ya samu sakon korafinta daga bakin Mahaifinshi, tunda shi kullum ya ke zuwa kai gaisuwa ga tsohuwar tasa.
Daf da kwanar da zata kai shi gidan Kakar ya daga ido ya kalli gidan su Aliya, duk da yasan tarihi ya shafe babin Aliya, kuma ba zai sake ganinta ba yana da kyau ya kalli gidansu don kauna. A fili ya ce, “Alherin Allah Ya kai miki a duk inda ki ke Aliya.”
A cikin gidan Kaka tana fadin tayi fushi, ace tunda ya dawo ba ta samu arzikin ya zo ya duba ta ba, ko sau daya ta ma gan shi taji dadi.
Sai dai ya kira waya ya ce a bata. Ya ce yau gani na zo Kaka kiyi hakuri, yanayin aiki ne Kaka ina dawowa Gwamnati ta bani aikin nan.
Na samu aiki jingim a cikin wannan office din, so ni ke in karkare da komai, in kuma fahimci komai.” Ta ce, “To shi ke nan ka wanke kanka. Har ina cewa ko har yanzun bakin cikin Aliyar da baka samu ba ne.”Ya ce, “Kaka ni fa na jima da sa ma zuciyata hakuri, ba kin zuga su Baba sun ce in auri Nafisa ba?”
Ta ce, “In ji wa ke nan? Ni ban ma san lokacin da suka shiryo abin su ba, ni dai sun fada min kuma nasa albarka.
Nafisa tana da hankali, kuma tana da ilimi.” Ya ce, “Kaka sai dai fa ina zaton zan auri mata biyu ne rana daya, ya ki ke ganin yiwuwar hakan? Ban taba yin shawara da kowa ba sai ke yanzun. יי
Ta ce, “Shatima in kana bukatar sama da haka addini ya baka dama, ni ko iyayenka ba mu da ikon da zamu ja da haka. To da Aliyar za ka kara kenan?” Ya ce, “Wace Aliya kuma, na sani yanzun tayi ‘ya’ya sun kai guda biyu.
Kaka ta ce, “To ai bata yi auran ba.. Tsaye Shatima ya mike tare da maimaita kalmar “Bata yi auren ba?” Kaka ta ce, “Ni kar ka fado min, tana nan gidan da suka ce ba za ta jiraka ba.” Ya ce, “Kaka cire batun wasa!”
Ta ce, “Shi ke nan kowane lokaci ne ake yin wasa? Zancen gaskiya kenan. Amma zauna ka nusu sai Maryama taje gidan ta kira maka ita.
Ya ce, “Ni fa in kin bar ni tuni Aliya tayi aure.”
Ta ce, “Tana nan takan zo gaishe ni a kwanakin
baya.” Ta daga murya.”Maryama zo nan.” Ta zo ta tsugunna ta gaida Shatima. Kaka ta ce, “Je ki kawo masa abinci da ruwa.” Ta kalli Shatima wanda ya yi nisa cikin tunani, ta ce, “Sai dai fa tuwo muka yi.” Ya ce, “Iye! Me ki ka ce?” Ta ce, “Abinci na ce.” Ya ce, “Ba zan ci ba Kaka, ban dade da cin abinci ba, ki aike ta ta kira min ita don in shaida Kaka.
Ta ce, “To goga na Aliya, duk ka birkice, Maryama je gidan Alhaji Garba ki ce ina kiran Aliya.” Ta ce, “Wannan me aikin asibitin?” Kaka ta ce, “Ita.”
Ya bi Maryama da kallo kamar ita ce Aliyar, sannan ya maido da kallonshi kan Kaka. “Naji kuma kin ce mai aikin asibiti.”
Ta ce, “Eh, ai bayan tafiyarka Makarantar koyon aikin jinya ta shiga ta gama yanzun tana aikinta.” Ya mike ya nufi window yana leke tare da fadin “Naji kamar motsi ne.” kaka ta ce, “Ikon Allah sai kallo. To kuma fa in ka faye zumudi Nafisa jikata ce sai in saka takalmin karfe in murza kasa in ce ita kadai za ka aura.”
Ya ce, “Kaka ai in har ta tabbata Aliya ta ce, “To akwai yiwuwar zan yi mata uku rana daya.” Kaka tasa dariya sannan ta ce, “Ashe zaka kafa tarihi a Zaria ” Sallamar Maryama suka ji, bai amsa sallamar ba amma ya ce “Ina take?” Ta ce, “Tana sallah, Mamansu ta ce in ta idar zata zo.
Ya sake kallon Kaka ya ce, “In ko Aliya ce, ban san ma wane irin albishir zan yi miki ba a duniya da na ba ki kujerar Makka, sai dai babu kafar zuwa.
Ta ce, “In ka yi niyya ai ko zuwana na karshe kan kujerar turi nayi aikina, Babanka ya biya askarawa suka yi ta dawainiya dani. Shatima ya yi murmushi, ni dai ki bar batun Makka, zan siyo mimiki kaji ayi miki farfesu mai laushi ki sha kayanki.
Ta ce, “Aikin banza, don kaji kullum Babanka sai ya kawo min.” Ya ce, “To kan Shanu fa..?” Sallamar da suka jiyo ce ta hana Kaka maganar Www.bankinhausanovels.com.ng
sai amsa sallama tayi. Shi ko kasa magana ya yi,
ya lumshe ido yana tunanin yanda zai ga Aliyarshi. Tayi sallama a kofar falon, nan kaka ta amsa. Kanshi yana kasa, ta isa can gefen wata kujera ta zauna, sannan ta gaida Kaka tare da cewa.
“An ce kina nemana, Allah Yasa lafiya?” Kaka tayi yar dariya. “Ga me nemanki nan.”Sai lokacin ta kalli gurin da mutumin yake, don da ta shigo hakika taga mutum amma ba ta tsaya dalle
kallonshi ba. Ya dago ido suka kalli juna. Zumbur! Suka mike tsaye suka zubama juna ido.
Shatima ya yi ta maza ya ce, “Aliya dama kina nan ba kiyi aure ba?” Ta sauke ajiyar zusiya, sannan ta sunkuyar da kai
“Ina yini?” Ta gaida shi. “Lafiya lau.” Ya amsa.
Kaka ta ce. “A tsaye za ku gaisa?” Ya kalli Kaka, sannan ya kalli Aliya. “Zo mu zauna can kujerar kada Kaka taji abin
da zamu fada.” Aliya taja mayafinta ta rufe gefen
fuskarta alamun kunya, zuciyarta kuwa fal murna.
Gani take yi ma kamar ba gaske ba ne, wai
Shatimanta ne a gabanta. Sai da suka zauna ta sake gaida shi. Ya ce, “Ya ya ki ka ji da ki ka ganni?” Ta ce, “Har yanzun bangama yarda cewa ba mafarki nake yi ba.”
Yayi murmushi, “Ni mamakina ashe ba kiyi auran ba?” Ta ce, “Duk wanda suke son in aura ni kuma bana sonsu, sai wan Babanmu