Showing 18001 words to 21000 words out of 35955 words
gobe zan
zo ko da dare ne. Ta ce, “To Alhaji mun gode.” Ya ce, “Bana ce bana son alhj ba.” Ta ce, “To in ce maka ya ya?”Yanda tayi maganar cikin muryar tausayi duk sai
ya ji tausayinta ya karu a zuciyarshi. Ya ce, “Ki ce min haka to. Kada ki manta na ce, addu’a za ki masa ba kuka ba.” Ta ce, “To.” Ya shiga mota ya wuce.
Salma tabi motar da kallo har ya bace. Sannan ta ce, “Allah Ya biya ka da gidan Aljanna.” Ta shiga gidan ta samu har an soma wanke tukunya za a dora girki. Ta kira Yaya Hadiza ta bata kudin ta kuma fada mata yanda suka yi.
Tunda ya gama al’adun shi da ya saba yi kafin ya kwanta, bacci yake ji sosai. Amma yana kwanciya sai ya ji baccin ya kama gabanshi. Tunanin gidan su yarinyar nan Ummu Salma
ya tuna yanda gidan yake a rube, kowane lokaci
gidan zai iya fadowa a kansu. Yarinyar nan ya
tabbata bata kai sa ar Badi’atu kanwarsa ba, kuma
bai ga alamun tana zuwa Makaranta ba..
Sannan kai gaskıya yana bukatar taimakawa yarinyar nan sosai. Ya rumtse ido a cikin zuciyarshi, ya ce ya dauki alkawari tsakaninshi da Mahaliccinshi zai taimaki Umma Salma
Zai inganta rayuwarta ta hanyar bata ilimi. domin daga ganinta. Ya tabbatar tana bukatar ilimi, tana son karatu. Gaskiya gobe zai mata tambayoyi.
sai dai a rin wannan lokacin da yake tsakiyar hidimar auransa
ba shi da halin yi musu wani gyara domin aiki ne ba karami ba. Haka lamarin yarinyar yayi ta damun sa ya kasa bacci har kusan Asubahi..
Washegari ya dawo aiki ya yi wanka ya saka
farar jallabiya kar!, takalmi ma silifa yasa mai dan
tudu ya kwashi wayoyinshi da makullin mota ya
nufi kasa
Da motar ya nufi Masallaci, da suka idar da Magriba ya nufi gidan su Munnir. Bayan sun gaisa ya ce, ya zo su shiga su ci abinci.
Shatima ya ce, “Bana jin yunwa. Muje ka raka ni muyi gaisuwa.” Munnir ya ce, “Waye ya rasu?” Shatima ya ce, “Baban yarinyar nan da suke kwance a asibiti.” Ya kwatanta mishi.
Munnir ya gane ya ce, “Allah Sarki! To bari in
fada ma Fatima.” Ya shiga ya ce da matarshi sun
fita sannan ya zo suka wuce Sai da suka yi Isha’i
sannan suka karasa gidan.
Da suka yi fakin suka tsallaka gurin ‘yan zaman makoki suka gaisa. Yaya Auwal ya tashi ya zo yana sake fadin “Sannun ku da zuwa Alhaji.
Shatima ya ce, “Na kawo abokina zai yi musu gaisuwa. Shi ne ya yi musu jagora zuwa dakin Innarsu. Daga waje suka tsugunna suka gaisar da ‘yan ciki.
Innar ta leko bakin kofa. Yaya Hadiza ta kwala ma Salma kira. Idar da sallarta kenan a dakin Baito, ta fito ko takalmi babu, ta ce “Yaya Hadiza gani.”
Ta ce, “Dama su Alhaji ne suka zo.” Tayi saurin karasawa kusa da su, ta tsugunna. “Yaya sannun ku da zuwa.” Ya dube ta.
“Salma ya karin hakuri?”
“Da godiya.” Ta gaida Munnir shima yayi mata gaisuwa. Suka mike suka soma tafiya, Inna tana musu godiya. Ya waiwayo yaga Salma a tsaye, dama gidan da duhu, kila ma ba a taba saka wutar lantarki a gidan ba.
Da wayar Munnir suka haska don su ga hanya. Shatima ya ce “Zo mana Salma.
Munnir ya bude motar ya shiga, Shatima ya jingina da motar. Tazo ta tsugunna a gabanshi cikin ladabi. Ta ce. “Gani Yaya.” Ya ce, “Tashi Salma.” Ta mike.
Ya ce, “Dama zan tambaye ki ne kina zuwa Makaranta? Ta ce. “Eh, ina zuwa Islamiyya.” Ya ce. “Boko fa?” Ta ce, “Tun da na gama J.S.3 ban samu damar wucewa ba.”
“Saboda me?” Ya tambaye ta.”Saboda lokacin Babanmu ya soma rashin lafiya, ba ya fita neman abinci, ni ce ni ke nemo mana abin da zamu ci. In yi talla ko in soya awara a waje.”
Ya ce, “Ba ku da wani Yayan? Wancan ba wanku ba ne?” Ta ce, “Yaya Auwal shi ne ke aikin gidan biredi ana biyanshi dubu tara a wata. Lokacin kudin maganin Baba yake biya, ba sa isa ma.”
Shatima ya ce, “Yanzun ke ce ki ke ciyar da ku? Shekarunki nawa ne ma?” Ta ce, “Shekaruna goma sha shida, idan wannan Azumin yazo.”
Ya ce, “Sha biyar da watanni.” Ta ce, “Eh.” Ya lumshe ido cikin tsananin tausayin ta. Can ya ce, “Salma!” Ta ce, “Na’am!” Ya ce, “Fada min taimakon da ki ke son in yi miki?” Ta ce, “Kamar ya ya? Ai kayi mana duk wani taimako, abinci muka fi bukata kuma ka ba mu.”
Ya ce, “Ban da wancan, ke kanki ni ke son in taimake ki, taimakon da ba za ki manta ba, ina son ki nutsu zan bar ki zuwa ranar sadakar uku, yaushe ne?” Ta ce, “Juma’a.” Ya ce, “In nazo sai ki fada min, kiyi shawara da Innarku da Yayanki, ki dubi mene ne burinki sai in taimake ki a kai, kin ji ko?”Ta ce, “To Yaya, Allah Ya saka da alkairi, Ya baka duk abin da ka ke so duniya da lahira.” Ya ce, “Babu komai, ki koma gida.”
Yana shiga mota Munnir ya ce “Gaskiya mutanan nan suna cikin tsananin bukata, dubi irin gidan da ‘yan Adam ke rayuwa, kuma suna da makota masu hali sun sani amma ba za su iya taimakonsu ba.
Shatima ya ce, “Ai ba ka sani ba, su fa masu
hali in za su yi taimakon nan sai dai su taimaki
masu karfi ‘yan uwansu.” Haka suke tattaunawa har suka zo layin su Kaka. Ya ce, “Yauwa, bari mu shiga in fada ma su Kaka a rinka kawo abin sadaka gidan mutuwar nan.
Munnir ya ce, “Haka ne. Allah Ya taimake
mu.” shi kanshi Shatima yana mamakin irin yanda
lamarin yarinyar nan ya hana shi sukuni. Har yaje
yake ba wa Hajiyar shi labarin yarinyar da
iyayenta. Hajiya ta tausaya, ta ce “Akwai masara a store, ko za ka sa a kai musu buhu biyu?” Ya ji dadin haka sosai. Ya ce “Gobe ne zan je, in na dawo aiki. Tunda gobe rabin rana ce zan dawo da wuri.
Wani abu da ya yi ta bai wa Shatima mamaki yanda har sakon Aliya da ya shigo na Juma’ar yau bai sami damar budewa ba, kowane lokaci zuciyarshi tana can gurin tunanin yarinya Salma. Abin da yafi tsaya mishi a rai, ‘yar shekaru sha biyar ke rike da gida.
Salma da ke kwance a tsakar dakin Baito kan yar tabarma, ta rufe kafafunta da hijabinta, nan take kwana kasancewar Baito bata da miji.
Juyi kawai take yi tana tunanin maganganun Shatima, dole tayi nazari sosai a kan kanta kafin ta tunkari su Yaya Hadiza, burinta da yake magana a kai shi ne take tufka da warwara a kai. Ta sani tun da ta taso fatanta Allah Ya bata
ilimi mai albarka, ta zama ‘yar Jarida ma aikaciya
a gidan TV ko Radiyo. Tun lokacin da Mahaifinta ya farka. Duk da cewa makarantar Gwamnati take kullum sai ya bata Naira talatin zuwa Naira talatin dawowa, in da kudi har Naira dari yana bata don ta samu dan na kashi.
Mamansu tana aikin gida, a gidan wasu masu hali, itama dole aikin ya tsaya saboda jinya. Tun daga lokacin Mahaifinta ya soma zancen aurar da ita, kullum sai ya fadawa Innarsu cewa shi ya tabbata ciwon shi ba na tashi ba ne amma yanason don Allah su aurar da Salma don ta daina wannan wahalar ta talla, za su ci abinci daga abin da Yaya Auwal yake samu.
Tunda in an aurar da ita sai Umar da Sani kannenta su ko maza ne. Ko ranar da zai mutu sai da ya yi zancen aurar da ita, abin da ya tsaya mata a rai har da kuka ya yi lokacin da ya ke maganar.
Tana wannan tunanin ne sakamakon zancen da Shatiman ya zo mata da shi. Dole ta aje burinta na karatu, saboda in ya dauki nauyin biya mata kudin Makaranta da takardu da komai, kudin mota na yau da kullum zata dora masa ne?
Ita dai kawai zata ce abu dayan da ya ce ta zaba ta zabi ya aurar da ita ga Basiru saurayin da ya nuna kaunarsa gareta, ya yi mata kayan daki tunda shi ne burin mahaifinta.
Washegari da safe kula guda katuwa aka kawo cike da waina daga gidan su Kaka.
Salma tana jin mutane na ta yabon Hajiya Kakar su Shatima, suka ce duk in da aka yi rasuwa ko basu sanka ba sai sun kai.
Salma ta ce ma Yaya Hadiza “Ai Hajiyar Kakar wannan Alhaji ce da ya ke taimakonmu, kila ma shine ya sa a kawo.” Bayan yan addu’a sun watse ta ce Amira ‘yar gidan Yaya Hadiza ta leka ta kira Yaya Auwal.
Inna ta ce, “Mene ne?” Salma ta ce, “Alhaji ya bani wani zabi ne, shi ne ni ke so muyi shawara da ku.” Bayan sun hadu, Salma ta fada musu yanda suka yi da Shatima. Yaya Auwal ya
cc, “Mc zai hana ki ce ya sai mana gida?” Ta ce. “Burina ya ce wai in zaɓi abu daya, ba wai namu ba. Kowa yasan bani da burin da ya wuce in yi karatu in zama ‘yar jarida. Sannan kuma burin Baba shi ne ayi min aure
To ina son ku duba ku gani a cikin nan wanne zan zaba?” Yaya Hadiza da Yaya Auwal suka ce, “Ki zabi karatun.” Inna ta ce, “A’a in ba ku manta ba, zancen
aurar da ita yana daya daga cikin kalaman
Malam na karshe. A nawa tunanin tunda ga
Basiru yana sonta, kuma yana da dan abin yin sa,sai a ce ya fito.
Shi kuma sai ya taimaka ya yi mata kayan aure. Hadiza tace, “Haka ne, to ayi hakan. Yaya Auwal ne dai shi bai gamsu ba, amma ganin ita Salma ta yarda sai ya mika wuya shima.Salma tasan ita bata son wani Basiru, bata ma san kowa don ba hakan a gabanta.
Tana bacci taji ana cewa ga buhun nan masara ana shigowa da su. Duk da ba ta fito ba tasan shakka babu Shatima ne. Yaya Hadiza ta leko dakin Baito.
“Salma ki zo ga Alhaji ya aiko da buhun Masara guda biyu.” Ta fito ta samu su Inna suna tsaye bakin kofa suna godiya. Hadiza ta ce “Kai wannan bawan Allah Yana taimakonmu, Allah dai ya saka mishi da alkairi.”
Salma ta ce “Ya tafi ne?” Yaya Auwal ya ce, “Yana waje cikin motarsa.” Ta saka takalmi ta fita. Gaban motar ta gani a bude, daga gani ta samu matsala ne, shi kuma yana tsaye yana waya.
Ta tsaya daga inda take, tana iya sauraron abin da yake fadi. Ta fahimci da Bakanike (mai gyara) ya ke magana. Don taji yana cewa “Zafi take yi, kazo ka same ni a nan Tudun Wada…” Ya ci gaba da yi masa kwatance.
Da ya gama ya tsallako suka tsaya a inuwa inda “yan zaman makoki suka watse. Ya ce. “Salma! Tace. “Na’am! Yaya.”_____
*🏚️RANA DAYA 🏚️*
CHAPTER 10
*BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*
*Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account number👇🏻*
```ACT<<0700549935
Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925```
*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can sama👆🏻👆🏻ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin shirya sai kiyi magana*
*Masu son a tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427 zamuyi maku cikin sauki*
```🧕🏻🧕🏻Ina kuke kasaitattun mata, Hajiyata kada ki bari ki zama bora agidan auren ki yi kokari ki tsuma kanki da ingantattun magunguna na gyaran jiki 07032895551🍉🍉🥥🥥```
```Mun zo maku da ingantattun magunguna masu kyau da inganci akwai TABAJE mai kyau gangariya 5litres 5k 07032895551```
```Muna da hadin Abulbulo, akwai Dan saudiya Hajiyata kada ki bari wannan hadi ya wuceki,dagajin sunan ABULBULO kinsan akwai aiki 4k ne kudin shi🙈🙈```
```Akwai sa Buzu Kuwwa,muna da kafi Budurwa uku sai angwada akansan na kwarai```
```🗣️🗣️🗣️Ina matan da mazajen su kebin matan banza to matso kusa Hajiyata Muna hadi na musamman duk macen da tayi amfani dashi mijin ta be karajin dadin wata mace, wannan hadi in kinsan kinada kishiya don Allah kada ki siyeshi 8k ne kudin shi🥥🍉```
```Akwai dahuwar kaza gangariya sai kin gwada Hajiyata zaki bani labari🙈🙈 akwai Dan dakarawa ya matseki tsam ya kuma saukar maki da ni'ima, akwai kafi sugar, kwallin mata dan matsi daya tamkar da dubu kenan🍉🥥```
```Akwai hadin Zama daram,munada miski mekyau original, akwai dahuwar kaza ta amare da uwar gida🐓🐓🐓 Akwai Sabulun infection ya matseki ya yi maki maganin infection,yasa wajen yayi sulbi Hajiyata```
```Muna garin katsina Muna aikawa ko ina a fadin Nigeria har ma da makotanmu Niger 07032895551```
```Sai angwada ake sanin na kwarai, amma don Allah idan baki shirya siya ba kada kiman magana 07032895551 muna bada sari game bukata🙏🏻🙏🏻```
Mun tsaya
Salma ta ce “Ya tafi ne?” Yaya Auwal ya ce, “Yana waje cikin motarsa.” Ta saka takalmi ta fita. Gaban motar ta gani a bude, daga gani ta samu matsala ne, shi kuma yana tsaye yana waya.
Ta tsaya daga inda take, tana iya sauraron abin da yake fadi. Ta fahimci da Bakanike (mai gyara) ya ke magana. Don taji yana cewa “Zafi take yi, kazo ka same ni a nan Tudun Wada…” Ya ci gaba da yi masa kwatance.
Da ya gama ya tsallako suka tsaya a inuwa inda “yan zaman makoki suka watse. Ya ce. “Salma! Tace. “Na’am! Yaya.”
Ta tsugunna ta gaida shi, ya amsa tare da fadin “Mike.” Ta mike tsaye tana wasa da gefen hijabinta. “Ya karin hakuri?” Ta ce “Alhamdulillah.” Ya ce, “Kin daina kuka ko?”
Ta ce, “Ai tun da ka hana ni ban kara ba.”
“Yauwa, ki dangana. Yanzu wace shawara ki ka yanke, ko in ee me ki ke so in yi miki?”
Ta kalle shi tayi dan guntun murmushi, sannan ta sunkuyar da kai. Ya ce, “Ki fada ni na baki zaɓi kuma na dauki alkawarin ko me ki ke so zan miki, ko nawa zan kashe. Gidanku kuma naso ace zan gyara muku amma ina cikin shirin bikina.”
Tayi ‘yar dariya “Aure zaka yi?” Ya ce, “Aure zan yi, za ki zo min ko?” Ta ce “Zan zo.’ Daidai lokacin Bakaniken ya sauka a Mashin. Ya ce “Ina zuwa, bari muyi magana da Bakanike.”
Sun kusa minti takwas sannan ya bar shi yana duba motar ya dawo gurinta. Salma ta rasa yanda zata yi masa maganar. Ya ce, “To karatu ki ke so ne ki ka kasa fada?”
Ta ce, “Karatu naso Yaya, amma dai akwai burin mahaifina a kaina, kuma har a ranar da zai mutu sai da ya maimaita yana kuka…Hawaye suka soma zubo mata, tayi kokarin Isayar da kukan sannan ta ci gaba da magana cikin raunanniyar murya mai cike da tausayi.
“Naso in zama ‘yar Jarida a rayuwata, amma dole in shafe babin haka in yi aure kamar yanda Mahaifina ya bar wasiyya..”
“Aure!?” Shatima ya katse ta cikin mamaki.
Ta kalle shi fuskarta sharkaf da hawayè. “Aure Yaya.”
“To dama kina da saurayi kenan ko?” Ya tambaye ta.
“Akwai wani Basiru da yake sona.”
Kanshi ya sake kullewa, ‘yar yarinyar nan tana soyayya! Ya kalle ta. “Tun yaushe ku ka fara soyayya da shi?” Ta ce. “Zai kai wata biyu dai yana zuwa gurina, tun ina zuwa Makaranta ya taba cewa yana sona na ce mishi karatu zan yi.
Da na daina zuwa kuma sai ya dawo lokacin
Baba ya soma zancen aurar dani sai na hakura na saurare shi.
Ya ce, “To ke kina sonshi ne?” Ta ce, “Ni ban san wani so ba.” Tayi ‘yar dariya tare da rufe fuska. Ya ce, “Ban gane ba?” Ta ce, “Ni dai
kawai in aure shi amma Yaya wallahi ban san so ba.”
Ya ce “Misali ba ki tunanin shi? Ba ki son ganinshi da makamantansu?” Ta ce, “Yaya ni fa in ya zo yazo, in bai zo ba har mantawa ni ke Allah yayi ruwan tsirar shi.”
Shatima bai san lokacin da ya kwashe da dariya ba, domin yanda ta fadi kalmar ta ba shi dariya sosai. Ya ce, “Har akwai wani ruwan tsirar mutum? Lallai Salma kin iya magana. To kin ga ba son wannan Basirun ki ke yi ba.”
Ta ce, “To ko bana son shi Yaya zan aure shi haka don in cika umarnin Mahaifina, kai sai ka yi min kayan daki ka aurar da ni kawai.”.
Yayi shiru yana kallonta. Itama ta kalle shi, sai taji kunya. Ta saka tafin hannunta ta rufe fuskarta. Ya ce, “Mamakin ki ni ke yi Salma, yanzu in aka yi miki aure kin san ya za ki zauna a gidan mijin?”
Ta kama gefen hijabinta ta rufe fuska, “Zan koya Yaya.” Ya ce, “Karatunki ya zama tarihi kenan yanzun?” Ta ce, “Ya zan yi, dole in hakura.”
“Sana’ar me shi saurayin naki yake yi?” “Gyaran famfo, da kuma Achaba.”Ya sake kallonta cikin tausayi. “In kin samu wanda zai ba ki dama kiyi karatu, kuma ya aure ki za ki bar Basiru?”
Ta ce, “Sosai ma. Ban san adadin farin cikin da zan yi ba.” Ta runtse ido “Allah Ka tabbatar min da haka.” Ta manta a gabanshi take, sai taji an ce “Ameen.”
Ta bude ido da sauri, tasa hijabi ta rufe fuska. Ya ce, “Kina amsa addu’a ba ki san Yaya mijin yake ba?” Ta ce, “Ai ko wane iri ne in dai Musulmi ne shi.” Ya ce, “To zan je in yi shawara da shi in zai yiwu zamu zo da shi.”
Bata ma lura da wani bakanike ya gama gyara har ya dana motar ya dawo ba, sai da taga ya tsallako ya ba shi makulli. Ya ce, “To zan tafi Salma, sai dai na zo.” Ta ce, “To me zan ce musu a gidan?”
Ya ce, “Ki ce zan canza miki wani miji wanda zai bar ki kiyi karatu har ki cika burinki.” Ta ce, “Na gode Yaya. Dazu naji ka ce zaka gyara mana, ai haya muke yi.”
“Haya? Wannan gidan ne ake haya?” Ya tambaya cikin mamaki. Ya kalli agogon hannunshi, “Bari in tafi zan zo.” Ta ce. “To sai anjima.” Tana tsaye har motarsh ta bace.Hajiya ta kira shi, yana dagawa ta ce Momiyo tana ta kiran ka ba ka daga ba.” Ya ce, “Ina tuki