Showing 3001 words to 6000 words out of 22316 words

Chapter 2 - Ameenatou Yar Kaka Hausa Novel Complete

Takori   

23 Nov 2024

490

uwarsa na son jin muryarsa."


Dadyne ya mikawa Al-ameen wayar yana "ga shi Ameenatou za ta ma magana."


Rai bace ya karba dan yasan in yaki karba yanzu zai jawa kan shi jidali Yar da bai taba gani ba ta nanike masa.

"Shallo Okul ka mun magana kaji."

Al-ameen ya ce, "kina lafiya?"

Bai jira ta amsa ba ya datse wayar tare da mikawa Dady yana ba network,jin tsanar yarinyar yake ji har ransa mara dalili duk da cewa bai taba ganin ta ba.


Ameenatou kuwa ta dage sai magana take taji shiru

Kuka ta fara, "Kaka ni wallahi ban gama jin muryarsa ba abun ya dauke ni akiranmu shi ni wallahi ban yarda ba."

Birgima ta fara yi akasa tana akira mata Al-ameen

23/10/2021


_LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_

_*Urs Xayyeesherthuo🤍*_
[12/1, 3:23 PM] +2348037420816: https://chat.whatsapp.com/GeuRcMbmDGuHPBZu4928K8

*IN KINA NA FARKON KAR KI SHIGA WANNAN PLS🙏*


°°°°°°°°° _*AMEENATOU*_
_('Yar Kaka)_


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_RUBUTAWA_
_*Xayyeesherthul-humaerath*_

_SADAUKARWA_
_*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_

_*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_

_NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_

_*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_



*FREE PAGE-4*


Kaka ta karbi salular tare da mikawa Halliru, "ka ga karba abun ka."


"Haba Ameenatoun Kaka kiyi shiru kin ji zaki kara waya da shi anjima na tabbata Audu zai ƙara kira, kin ga jarumar jikata ba ta kuka sai dai tasa ayi ko?"



Ameenatou ta girgiza kai, "Amman sai har in Zaki goyani inyi barci ni."


Kaka ta wage baki, "ina ni ina daukan buhun sumunti?"

Nan da nan Ameenatou ta kara bajewa akasa , "To ni wallahi mutuwa zan yi in baki goyani ba."


Kan kace me Kaka ta dauko zani ta saba gardiyar jikarta abaya.


Tamkar wata jinjira tai lum abaya.

Su Lantana kuwa sun zama yan kallo ba abun suyi magana ba cibi ya zama kari.


Daga karshe ma Ameenatou cewa ta yi , "Kuma tafi gida wallahi dan ba cin kifinnan za kuyi ba kwalelanku ehee naga ai Tumbiɗan cewa na yi ina son shi, munafukai ku bar mana gida."


Dukkannunsu sai da sukai wani hamshakin hadiyan yawo domin ransu ya gama biyaws Amman ba yadda suka iya.


"Munafukai ku fice mana wallahi."


Haka Ameenatou ta korasu ba dan sun so ba


Suna tafiya kuwa ta dirka abayan kaka ta fara damkar kifi.




"Oh ni Indo Sale Ameenatou anji kunya da rowa ni da uwarki kam ba haka muke, yanzu dai sammun ladan goyo nima."



"Ysn,ysn,ysn dan dai ina sonki ne amman da bazan sammiki ba ."


Dan ficil kamar kuda ta gutsiro ta mikawa kaka, "ga shi dai amaida mugun yawo."


"Yoo ina zan sa wannan? Aiko hanjin wuyana ba zai shige ba."


Ameenatou ta ma kaka wani kallo kan ta ce, "bani,bani abuna nace tunda kin rena."


Tuni Kaka ta zurma abaki tana mamula dan ta san halin Ameenatou sarai zata iya kwace abunta.



WASHE GARI

kamar kullum da asussuba Ameenatou ke tashi dibo ruwa saboda tafiya makaranta.

Duk yan garin Ana idar sa salla suke fita diban ruwa.

Lantana da Furera ne suka biyo mata yadda aka saba.


Furera ta ce, "Goggo kiyi sauri mu tafi kin ga mu ka tsaya ba zamu samu da wuri ba."


Ameenatou ta ce, "Wallahi tallahi na rantse sai na yi kashina baku isa ku hanani kashi ba,kuma na kama layi ai tun dare dan haka wallahi sai mun diba ba wanda ya isa ya hana."


Ta karasa maganar tana shigewa bandaki


(Wannan kashin gado kenan,dan kullum goggo in ba tai kashin nan da asuba ba to ba kwanciyar hankali)


Tana shiga ji kake bututu bututu ga shegen bala'in wari da ya kaure gidan.

Ban da toshe hanci ba abun da su lantana ke yi.


Can sai gata ta fito tana nishi.

"Dilla can ku bude hanci ai gwanda nawa kashin ma akan na innoninku mai warin jaba."


Bakoti ta dauka suka bita abaya kawai.


Suna zuwa wajem diban ruwa Ameenatou tai kane-kane ta matsar da botikan mutane tasa nasu..


Adamu ya ce, "haba Ameenatoun ba ki ga layi ake bi ba ne?"

Kan ya karasa magana Washa ta ce, "kam bala'i wallahi ba ki isa ba aradun Allah in kinga su suna tsoron ki da masifar kakarki to wallahi ni na keresu."


Ameenatou ta kallesu sama da kasa ta ce, "in kuna son zaman lafiya ku bar ni na diban ruwannan ko kuwa ayi ruwan bala'i da masifa a karkarar." Ta karasa maganar tana daura dammara da dan kwalinta.


Ganin Washa bata ma san tana yi bane yasa Ameenatou kama hanya domin tasan tana kara magana zata iya domkota.



Kofar gida taje tana kwallawa kaka kira, kaka na fitowa Ameenatou ta fara kuka "Kaka kin ga wani Washa za ta ce ma munafuka jikar munafuka?"

Ta kara fashewa da kuka

"Dan kawai na....

Kan ta karasa kaka ta ce, "Jar uba!

Kara cino cinin bakin nan nata tai alamar za ayi masifar karshen zamani

"Muje na ce muje sai ta fadamun yadda akai ta mai da mu munafukan."


Suna zuwa Kaka ta bokatan kowa ta sanya na Ameenatou kan rike kugu tana, "Yawwaa gareki Washa kike ko washo? In ma masai kike to aradu ahir dinki da jikata kije ki tambayi kakar uwar kakarki da Ni Indo Sale da Ubanta mai fitsarin kwance nai munafurci ba da ku ba,yo ke har ma kuna da bakin magana daga kakannin naku har iyayen naku daga mai fitsarim kwance sai kashi awando,uwar uwarki ma yaushe yaushe ta gama cin tasono a karkarar nan?"

Ameenatou da sauran yaran wajen ban da dariya ba abun da suke.


Adam ya katse kaka da fadin, "Haba Kaka ba ki san meke faruwa ba kawai zaki fara magana haka?"


Kaka ta zaro ido can kuma ta fara shekan majina, "Adamu ni ka ke ma tsawa a karkarar nan? Ni ka ke ma tsawa to wallahi kaje ka tambaya ko uwar ubanka ba ta isa ta mun kallon banza ba bare ta fadamun magana, kaf kauyenan an sani kune kamfanin faso,kakanin kakanku ma duk fason kafa ne ya kashe su tsabar tsiro.


Adamu na jin kaka ta fara jero jawabai ya kama hanya domin inya tsaya zata iya ba da Labarin danginsu kaf.


Tana face majina da zaninta tana, "Yoo ai sa ka tsaya dan gwanda ni ban gudu ran daren aurena ba yo uwar kakanka sai da aka kwana ana nemanta dan ragwanci."


Malam Hashimu ne yazo wucewa ya durkusa yana, "lafiya kaka?


Fashewa da kuka tai tana daura hannu aka

"Wai har ni.....

. Comments din ku shine karfin gwiwata🙏


*ALƘAWARI NA NA NAN BEST 3 COMMENTERS ZA SU KARANTA FREE IN SHA ALLAH,DUK WADDA TA SAI AMEENATOU KUMA ZATA KARANTA WANI LITTAFINA NA KUDI GUDA DAYA*

24/10/2021
_LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_

_*Urs Xayyeesherthuo🤍*_
[12/1, 3:24 PM] +2348037420816: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_
_('Yar Kaka)_


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_RUBUTAWA_
_*Xayyeesherthul-humaerath*_

_SADAUKARWA_
_*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_

_*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_

_NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_

_*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_



*FREE PAGE-5*


_*KADA KUCE YA YI KADAN KUCE YA YI YAWA KUNJI🥺MAI YAWA ZAI ZO GOBE IN SHA ALLAH*_

_*Kalaman Soyayya*_
_Zan so ace ko da na rana dayane kaji kwatankwacin irin son da nake yi maka azuciya,ina sonka,ina kaunar,ina fatan kasancewa da kai har karshen Numfashi na_🤍💫



"Adamu zai kalla yacewa mayya? Abun ba ma ga Jikata kadai ya tsaya ba har da ni?"

Wiwiwi Kaka ta hwara zubda hawaye kai kace da gaske ne.



Malam Hashimu ya ce, "kai Adamu dawo nan lallai ka cika mara kunya, kasan wace Kaka kuwa agarinnan? Maza ka bata hakuri."


Adamu ya ce, "Baba Wallahi ban ce mata Mayya ba,cewa na yi fa....

Kan ya karasa Kaka ta katse da

" Na yi karya ko? Na ce na yi karya ko? Dazu ka ce mun Mayya yanzu kuma ka karyatani,to wallahi ko tsohuwar kakar,kakarka ba ta isa ta karyatani ba dangin masu faso,na ga ubanka yana yaro har satan goruba suke zuwa gonar malam mudi, Amman yau ni za ka ci ma mutunci." Ta karasa maganar tana kars fashewa da kuka ana shekan majina.



Malam Hashimu ya ce
"Kaka Dan Allah kiyi hakuri yarone bai san ke wacece ba, Adamu maza bawa kaka hakuri."


Adamu ya ce, "Dan Allah kiyi hakuri Kaka."


Fara share hawayen tai tana "Aradu yau ka ci sa'ar Hashimu ne,shi ma dan dai mun sha tsallaka katangar gonar mai gari da Da Kakarsa Jummala Auduwa satan mangoro ne,amman Aradu yau da kaji ajikin ka dan kuwa tamola zan da kai, maza in kaje gida ka cewa uwarka ya akaji da hakurin Kandala mai tambotse? Ko da yake ma dakyar in ta Santa dan ko mahaifiyarta bana jin tasanta, dake Kakar, kakar ta ce."


Malam Hashimu dai ya dau hanya batare da ya ce komai ba, gudun kar acigaba da tone-tone.


Ba yadda suka iya haka suka bar Ameenatou da kawayenta suka gama diban ruwa kaf har suka gama Kaka na tsaye tana surfa uban bala'i.


Karfe takwas Sun kammala shirin tafiya boko.

Ameenatou, Lantana,tare da Furera.

Ameenatou anci gazal daga gira har kunne,jan baki kuwa saman ido da baki kamar manja ita adole yar gayu, andaga wando zuwa iya gwiwa an dago safa fara saboda Aga safarta ta yan binni,kaf kauyen ita kadaice mai safar angayu da aka kawo mata daga binni.



Tafiya take tana wani juyi da rangwada.

Kai ku dakata ma aradu fures,lantus ku bini abaya ba zai yu inyi shigar yan binni ina jerawa da ku ba,sai kusa arainani ai."

Haka suka bi bayanta tamkar boodyguard dinta.

Can kuma ta kara tsayawa tana
"ni fa wallahi sai na sha mangoro kan muje bokonnan danni bana so muje da wuri yanzu wannan malamin me *wata mie si niem* (what is your name) ne a ajin ya cika iya yi ya ce sai munyi yaren turawa."


Furera ta ce, "Aiko na ga bishiyar gonar Baba Datti ta tsiro harda wa inda suka nuka fa."



"Nima na gani wallahi, kuma manyane."


"Munahikai shine baku fadamun da wuri ba? To aradu yanzu ko can zamu kuma kadan zan sammaku."


Nan suka kama hanyar tafiya gona.

Sunci sa'a kuwa Malam Datti ba ya nan.

Tuni Ameenatou ta dane kamar tsuntsu.

Cinkowa take tana jefamasu.

"Yawwa wannan ne na biyar kenan, Aradu sai mun tsinke goma ko ashirin."


Lantana ta ce, "Ameenatou wallahi ga Malam Datti nan Shikenan mun shiga uku inya kama mu wallahi mugune."

Furera kuwa ido ya yi rudu-ruɗu an rasa abun fadi ma.

Ameenatou ta masu tsawa, "Matsoratan banza da wofi to wallahi ba zan sauko ba sai na dibi rabona yo abun da in ya nuku ba zakka ake mana ba,ai gwanda mu diba rabonmu."


Ameenatou na zuba zance su fures kuwa anga ba yi an tsere.


Ji ta yi ana, "Kambala'i aradu yau Sai kinci Kuntsin Uwarki A karkarar nan."

_LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER 08103080717 SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_

_*Urs Xayyeesherthuo🤍*_
[12/1, 3:25 PM] +2348037420816: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_
_('Yar Kaka)_


*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*

_RUBUTAWA_
_*Xayyeesherthul-humaerath*_

_SADAUKARWA_
_*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_

_*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_

_NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_

_*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_



*FREE PAGE-6*

_*INA MATUKAR BUKATAR ADDU'O'I DA GA BAKU NAN KU MA SU ALBARKA MASOYA🥰🙏KOMIN KANKATA KO GAJARTA KUMIN DAN ALLAH*_

_*KALAMAN SOYAYYA🤍💫*_

_"Ina ji ajikina cewa duk randa na daina sonka to numfashi na ne yazo karshe,ka sani ka kara sani in har zanyi numfashi to sonka na cikin raina ko ince rayuwata ma gabadaya, indai ana so bayan rai, tabbas zan ci gaba da sonka har bayan raina,tare da yi mana fatan kasancewar mu atare,shin ka san mahimmacin murmishinka gareni kuwa? tamkar yiwa makaho addu'ar budewar ido ne, misalta irin Farinciki da yanayin da zai shiga,to wannan kwatane a Farincikin da nake shiga aduk sanda na ga kana murmushi,bance ni kadai za ka so ba,amman ina da tabbacin zanyi kokarin cike duk wani gurbi da ke zuciyarka ta hanyar da ba za ka taba so ko tunanin kulla alaka da wata 'ya mace ba,Ina Sonka tamkar Raina! Ko ba yanzu ba kuma ba yau ba koda kuwa bana duniya ina fatan ka so ni kwatankwacin son da nake ma hakan zai matukar kara faranta mun rai Habeebiy Da'eeman ba iya suna bane ina fatan hakan akullum in sha Allah."_
_*Fisabillah🥰duk wanda yaji dadin kalaman ya kara mun àddua*_


A firgice ta jiyo tsabar firgita saura kad'an ta fad'o, duk da yanayin tsoro da ta shiga hakan bai ta yi laushi ba.

"Kai dai Malam Dattin nan ka fiye jaraba da rashin ha'kuri, daga kawai ka ga mutum saman bishiya sai ka fara zage-zage, kamata ya yi ka samo tsafga ka ce keee uban me kike yimin a saman bishiyata, Ni kuma sai in ce bishiya ba ta uban wani ba ce tashen Allah ce sai dai mutum ya zama sanadi, na zo d'ibar zakka ce da ka gagara fitarwa, in kana iyawa sauko da Ni ka zane, sai ka kamo ni ka sauko ka fara duka, amma ka wani zo kana ta hayayaga ba."

Kamar yadda ta kawo shawara haka Malam Datti ya yi, domin kusa da shi ya samu tsafgar, yana shaud'a mata d'aya a duwawunta ,ban da ihu da tsalle, ba abun da take, sai da ya yi mata shida masu shiga jiki a na bakwan ne yana shaud'a mata ta shige cikin malun-malun dinsa, cakulkulu ta fara yi masa mai kama da yakushi, da ya kai bulalar da niyyar duka sai ta zille, kuka take wujiga-wujiga har da majina, hakan bai ya sa ta nutsu ba ta daina, ganin tana neman haukatar da shi ne yasa ya fara 'ko'karin cirota, sai da 'kyar ya cirota yana haki, ganin ta ku'buta da 'kyar yasa ta bawa wandonta iska, har ta yi nisa ta dawo ta kwashe magwonron da ke 'kasa ta kara gaba fitttttt.

Haka ta kama hanya tana tafe tana kuka harda majina tana kuma shan mangworonta kamar dole.

Lokacin da ta iso bokon an fara tarar 'yan makara, firifect d'in da suke tsarewar tsabar dariya ko tsaida ita ba su yi ba, ita d'in ma bata yi niyyar tsayawa ba, amma ta 'kuduri aniyar duk wad'anda suka yi mata dariya tun daga hanya har makaranta sai ta d'au mataki a kansu.

Tun daga nesa ta hango Malamin da ke cikin ajinsu, Malamin *wata mie is niem* ne a ciki.



Tana zuwa ta shige aguje kamar zaburarriya.

Tsawa ya mata yana, "You ba? You ba? U ar just coming now? Eheen I will deel with you in and out."

Kallon shi tai tana daura hannu aka , "Onkul Aradu I Noyin Going to bishiyar Dirimi, going to Bishiyar Mangoron Baba Datti kadai,kuma shi ma Kaka ta ce dan uwanmune Kakan kakanshi abokin makocin Kakanmune wallahi Onkul."


Uncle Ibrahim bai san lokacin da ya tintsire da dariya ba.

Can kuma ya make, kan ya ci gaba da cewa, "Oya Go Out, i said Go Out." Ya karasa maganar yana nuna mata hanyat fita da hannu.


Gatsinan Mangoron ta tai kan ta ce, "Sholly Onkul I noyin Karawa wallahi Na ce ma mangoro ne ba dirimi ba,kuma in zaka sha ma ga shi sai inje gida in karbo ma gishiri gun Kakata."


Ba yadda ya iya haka ya bar Ameenatou a ajin nan ta zauna dan inya biye mata ba za suyi karatu ba sai dai cikinsa ya kulle dan dariya da takaici.

Zama tai agefe su Furare na kallonta sai ta galla masu harara

"Onkul wallahi i no lyk botin yara,ni ka ce masu stopi kallo mie, ehee in baka haka ba na kama yara wallahi botin (bitin) din su zan kuma sai na haifosu ehee dan ina da cikinsu." Ta nuna su Lanata da hannu.


Kallon su ya yi ya ce, "Ku daina kallon mana sarauniyar turanci in ba so kuke ta kashemu da turancinnan ba."
Wani dadi Ameenatou taji adole ance mata ta iya turanci kara washe bakinnan tai tana damkar mangoro.

"Oyaa Class Wanene zai fadamun me za ace in Mutum bai da lafiya da turanci? Kun ga yanzu dai mu ka gama kuma duk wanda ya fada dai,dai zan mi shi kyauta." Cewar uncle .


Ban da zaro ido ba abun da suke suna kallon juna domin duk basu san me zasu ce ba.

Tuni Ameenatou ta daga hannu.




Uncle ya ce, "Oya Meena."

Ta tashi ta ce, "Onkul wallahi inna fada me kadai zaka ba wa kyautan ko?"


Ya ce, "Eh Go On."


Ta washa baki

"Ita Noyin Lafiya Wal."

Kallonta kawai ya tsaya yi.


"Onkul ba ka ce su tafa mun ba fa kuma na fada ai."

Dariya ya yi kan ya ce za su tafa miki amman Hausa da turanci kika hada ai.....

Kan ya yi magana aka biga bell din fita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login